《HASEENAH》PAGE 21&22
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*21-22*
Hanyar side d'in Abban ta ta nufa Nan taji muryarshi na fad'in " Kika kuskura Kika taka k'afarki cikin wajan Nan wallahi sai jikinki ya Gaya Miki"
Juyawa tayi ta fasa ta shiga wajan su, palour ta zube ta rusa kuka, Umma tana jinta Amma ta kasa tashi Dan Bata ma San me zata ce Mata ba.
Sai kawai ita ma ta fashe da kukan.
Zuciyar Mummy kuwa fal farin ciki sai wani rawan Kai takeyi.
Haka rayuwa ta kasance wa su Haseenah dukan su sun rame ga Umma cikinta ya shiga wata biyar, ba wadataccen abinci, makaranta ma a k'afa Haseenah ke tafiya, ga Haseen tunda ya jibgi Saratu Mum d'inshi tace yazo ya bada hak'uri yace ba zaije ba shikenan ya d'auke k'afar shi.
Ga Umma Zuwaira tayi tafiya Bata zo ba, hakan yasa duk suka koma abun tausayi, ko fitowa Basu Isa suyi ba indai Abba Yana palour daga ita har Umma Babu Mai sukuni.
Yau ko abincin da zasu ci Babu, ganin hankalin Umma ya tashi yasa Haseenah saka hijabi ta fice ba tare da tasan inda zata nufa ba.
Tana fita zuwa k'ofar gate d'insu ta nema waje ta zauna gefen flower gidan nasu, had'a Kai da gwiwa tayi kawai saita hau kuka, horn d'in mota taji Nan tak'i d'ago wa, Dan tsoro take Kar Abban ta ne ya dawo Dan Yana ganin ta tasan ba makawa duka da zagi ne zai biyo baya.
Kashe motar tayi taji an d'ago ta, wa zata gani? Umma Zuwaira ta gani k'anwar Umman ta, dubanta Hajiya Zuwaira tayi tace" me kikeyi anan meya faru?"
Advertisement
Girgiza Kai Haseenah tayi ba tare da tace komai ba, janta tayi sukayi cikin gidan, Kai tsaye d'akin su ta nufa, Nan ma ta tarar Umma na kukan, salati ta Kama yi tana fad'in "me Zan gani yau? Me yake faruwa sai kace marasa lafiya duk kun fita a hayyacin ku?"
Dukkan su Babu Mai magana, mik'ewa Hajiya Zuwaira tayi ta wuce kitchen da nufin d'auko ruwa, Nan taga wayam ba komai a kitchen d'in, hasali ma Babu alamar yau anyi amfani da kitchen d'in.
Bata ce komai ba ta fito ta dubi Haseenah tace " zo muje ki rakani"
Nan Haseenah ta mik'e tabi bayan ta, Basu tsaya ko Ina ba sai kasuwa, buhun shinkafa ta siya biyu, indomie carton biyar, spaghetti carton biyar,macroni carton biyar,cous cous carton biyar, Maggi da sauran kayan spices kowanne carton, mangyad'a da manja ko wanne jarka, Naman da kifi ta sissiya Suma, ta siya musu kayan Miya da yawa ko wanne aka markad'a suka siya Sabin bokiti aka juye ciki, Nan aka cika boot tam, Nan suka shiga ciki Nan ta siya wa Haseenah uniform na school da na islamiya da yadin hijab guda biyar da dogayen riguna, Umma ma ta siya Mata atampopi, ta bada d'inki sannan ta siya musu omo dasu sabulu da Mai, seda aka cika har bayan seat sannan ta tsaya shagon waya ta siya k'arama ta had'a da sim suka tafi.
Kai tsaye gida suka wuce, Nan ta saka driver ya rink'a shiga da Kaya, ya d'auko na k'arshe kenan Nan Haseenah da Hajiya Zuwaira suka bi bayan shi, zai wuce kenan Mummy ta daka mishi tsawa tace" gidan ubanwa zaka Kai ko ba wajena aka ce ka kawo ba?"
Daga waje taji ance " gidan uban matambayi, ko kinyi aika ne Kika ga ba.a kawo Miki ba?"
Advertisement
Ido hud'u sukayi da Hajiya Zuwaira Nan Mummy ta had'e rai, Hajiya ta cigaba da cewa " ke Lauratu kiji tsoron Allah wallahi, nasan duk abunda kike, karki kuskura ki k'ureni wallahi ranan Mai k'wacen ki duk anguwan Nan Babu shi"
Tura d'an kwali Mummy tayi gaba ta cigaba da kad'a k'afa, Mummy tace" oho dai in kinji haushi ki d'auke ta ku tafi in Kuna son ta"
Dariyar takaici Hajiya Zuwaira tayi tace" Aiko kinsan cikin gatan ta aka d'auko ta, ba mabaraciya bace balle tayi rok'o, Kuma ke kanki kinsan da ubanta yanada masaniyar abunda yake faruwa wallahi da ba.a Kai wannan matsayin ba, shegiya da fuska kamar kashin makaho"
Haushi da bak'in ciki ne ya Kama mummy jin an ambaci kashin makaho, wato kashin uwarta kenan ko.
K'wafa tayi ta shige ciki ba tare da tace komai ba.
Duban Haseenah Hajiya Zuwaira tayi tace " wuce mu tafi uwar zurfin ciki"
Sum sum Haseenah ta d'au hanya Hajiya Zuwaira ta d'aka Mata duka tace " sai naci ubanki Kan wannan iskancin in ana Miki Abu Baki ramawa"
Ita dai batace komai ba suka shige ciki.
A store aka jibge musu komai, sannan Hajiya ta d'auko waya ta bawa Haseenah tace" ga wannan zanna kiranki saura kimun k'arya inzo har gida inci mutunci ki"
Kar6a tayi tare da godiya.
Kud'i ta d'auka naira dubu goma ta Basu tace su siya abunda Bata siya ba sannan tana Hawa mashin tana tafiya school Banda zuwan k'afa.
Nan har Hajiya Zuwaira ta tashi ta tafi Mummy ko lek'owa Bata sake yi ba.
Nan Haseenah ta dafa musu pepper soup na Kifi Nan sukaci, Dan rabon da suci sun manta ranan.
Mummy kuwa Haushi da bak'in ciki ne ya Kama ta, Dan Bata so hakan ba.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial107 Chapters
Sokaiseva
Erika Hanover received her magic on her twelfth birthday—far earlier than anyone was supposed to—and suddenly, everything in her life made sense. Magic could solve everything. Magic was all she'd ever wanted. When she was offered a spot on the roster of a mercenary group policing magic-tinged crime in her home of upstate New York, she jumped at the chance. Anything to get away from her hometown. It didn't matter what the work was. She didn't care. Now, though, with almost a decade between herself and her time as a child soldier with the Radiant, things aren't as clear as they used to be. Part slice-of-life, part coming-of-age, part surreal absurdist nightmare, Sokaiseva is the tale of a shell-shocked shadow-war's veteran recounting her time growing up as the last line of defense in a world secretly teetering on the brink of disaster. Book Two (Teardrop Two-Step) is going live now! New chapters go up Wednesday and Sunday.
8 167 - In Serial18 Chapters
The Rise of an Armament Emperor
A survival of a human boy who has escaped alive from a calamity and the adventure of him reaching the pinnacle!"Why? Why? WHY!?""More! More! More! I need more strength to protect everyone!""I'll never leave you behind even if my limbs been cut off!""This is all you got? Then OUT OF MY WAY! You don't even have the qualification to fight me.""Die"Hira, a boy from a small village that has been blessed with a peaceful environment and top-grade talent . But without any warning his daily life has been destroyed by the sudden attack of the demons and has been thrown into the abyss. With zero knowledge about the world, he stand up and want to find the way to survive!Schedule Release: Every week will have a guaranteed five chapter released.
8 152 - In Serial30 Chapters
Again
Most villains, no matter how terrifying, are defeated by a hero on the first try. The hero may be forced to flee or otherwise delay the real confrontation, but it’s still certain that he will win when it occurs. But some villains simply defeat all comers. Against an opponent like that, the only options are to give up or to try again. --- This story is a participant of the WriTEr's pledge. In short, I promise to finish it, and may I be Hall of Shamed if I don't.
8 92 - In Serial13 Chapters
I'm clueless in another world.
I, Tsukasa Tsutsukakushi is your average, everyday seventeen-year-old high schooler. However, my simple life is suddenly turned upside down when I'm summoned to a fantasy world! But by whom? And why? There's no truck, I'm still alive and kicking, there's no shining magic circle either. It just happened. Anyway, my favourite manga hasn't finished yet and there's a remake for my favourite game, so I guess I should search a way back. I mean, just how hard that will be, I'll possess some unique ability, right...?
8 111 - In Serial17 Chapters
Wii deleted you Austin x Eteled
nothing better than off brand transformers and bald miis
8 131 - In Serial19 Chapters
UQUBAR UWAR MIJINA
Based on true life storylabarine akan wata baiwar Allah wanda uwar miji tajefata cikin matsanancin baƙin ciki ɗa gararin rayuwa,sanadin hakan ta..just read and find out
8 104

