《HASEENAH》PAGE 23&24
Advertisement
: 🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*23-24*
Haka Haseenah suka cigaba da managing rayuwar su, time to time Hajiya Zuwaira tana Kiran Haseenah Don jin abunda ke faruwa, wani lokacin ko in Bata samu zuwa ba aike take tura musu.
Ta wajan Mummy kuwa ta gama kanainaye Abba, bashida wani sak'at, duk abunda wannan boka ya Bata tayi amfani dashi Kuma ance tsafi gaskiyar maishi, Dan Haka gani take duk duniya yanzu Bata da wata damuwar data wuce guda d'aya, wannan damuwar kuwa shine Haseenah da Ummah, ko kallon side d'insu batason yi ballan tana taji wata motsi.
Haseenah kuwa ta Zama tamkar baiwa, Bata da wata hutu sai in a islmaiya take ko school, tana dawowa kuwa maganar Zama ba Tata bane.
Gashi yanzu ta shiga SS3 ko waec lesson d'in da akeyi ma ita ba hali, tunda ta tsaya sau d'aya Basu tashi da wuri ba sai dab magrib ta shigo gida, Nan Mummy ta hau zagi har Abban ta yaji ya fito ya dank'ara Mata duka shikenan Bata sake tsayawa ba.
Umma kuwa ynxu tayi nauyi, cikin ta na wata takwas ne harda d'ori.
Dan Haka yasa duk abunda Haseenah keyi seta zaga ta dubata sannan ta dawo ta cigaba da aiki.
Yau dai su Haseenah an fara Waec, cikin dare da asuba kawai take samu tayi karatu sauran lokacin duk aiki take.
Saratu ma Waec d'in take Amma baccin ta kawai take Sha.
Ana sauran biyu su gama gashi yau essay da practical takeda shi, tasan bazata dawo ba sai dab magriba.
Dan Haka tunani take wa zaima Mummy aiki, Dan tasan ba abunda zai hanata cin azaba.
Advertisement
Da wannan tunanin ta nufa makaranta duk damuwa cikin zuciyar ta.
Aiko Mummy tasani Sarai Haseenah Bata Nan Amma ta nufa wajansu ta hau doka Mata Kira, Ummah na jin muryarta tayi saurin zura hijabi, Nan Umma ta Bata amsa da cewa Bata dawo ba ai yau sai yamma.
Zagi Mummy ta zabga tace" to yau uban wa zai mun aikin eye?"
Shuru Ummah tayi ba tare da tace komai ba, hakan ya dad'a fusata Mummy Nan ta juya tana fad'in" barina Kira Wanda nake zaman shi inaga zaifi sauki shi yamun aikin"
K'walla wa Abba Kira takeyi tun daga corridor har bakin k'ofar shi, Yana bacci ya tashi a firgice, murza idanuwa ya hau yi Yana mazurai, da sauri ya diro jin Muryar hajiyar shi ce, har Yana tuntu6e, Nan sukayi kici6is a bakin k'ofar ta dube shi shek'ek'e tace " ai dole kayi bacci tunda k'undun ka ya d'auka, Ni in yunwa zai kasheni wato in mutu bakada asara ko?"
Rusunawa yayi yace" ranki ya dad'e meya faru kayan abincin ya k'are ne?"
"In da k'arewar yayi ma ai da sauk'i 'yar iskar 'yarka dai da kakasa nuna iko akanta itace tun safe har yanzu Bata dawo ba wai tana makaran ta, Ni Kuma kasan bazan shiga kitchen ba"
Ranshi ne ya fara 6aci yace" to meye amfanin uwarta da bazata dafa Miki ba, ita ta nane a d'aki sai kace amaren da"
Wata tsuka yaja ya nufe ta ita Kuma tana binshi a baya har suka Isa bakin k'ofar, k'afa ya sa ya tokari k'ofar saida ta bud'e sannan ya kutsa Kai ciki Nan Mummy murna fal ranta tabi bayan shi.
Tunda Ummah taji su hankalinta in yayi dubu to ya tashi, ta rasa me yake Mata dad'i.
Tarar da ita sukayi zaune da ka kalle ta kasan tana cikin mummunan tashin hankali, shek'ek'e ya dube ta yace " munafuka kullum kina sunne cikin hijabi ke ba tafsiri ba ba Kuma yad'a da'awa ba, sai uwar k'iba da kike labtawa sai kace saniyan gona, kin ajiye kumatu tashi mu tafi mutuniyar banza"
Advertisement
Ummah batasan ta Ina zata Fara tashi ba Dan tasan yau ba abunda zai hana Mummy ganin cikin Nan.
Tsawan da ya daka Mata ne ya sata sake razana, hawaye ne ya fara gangaro mata, zuciyarta tayi zafi, sawa kawai tayi a ranta gwanda da tashin duk abunda zai faru ya faru, inma kashe ta Mummy zatayi ta kashe ta ko Haseenah zata samu kwanciyar hankali.
Hakan ya sa Ummah share hawayen ta ta yunk'ura ta mik'e, Nan Mummy ta juya ta fice ta tsaya a bakin k'ofar tana jiran fitowar Ummah.
Abbah ko sata yayi a gaba Yana biye da ita, har waje inda Mummy ke tsaye.
Fitowa Ummah tayi ta dubi Mummy tace" me Zan dafa muku?"
Salati Mummy ta Kama tana tafa hannu tana k'arawa, duban ta Ummah tayi Dan ganin me yake faruwa, ganin inda Mummy ke kallo yasa Umma Kai dubanta zuwa wajan, ba wani waje bane illa cikin Ummah.
Jikin Mummy ne ya hau tsuma ta yunk'ura ta shak'o Ummah ta manne ta jikin bango tana fad'in" me nake gani kamar ciki? A gidan uban wa kika samo cikin?"
Umma batayi yunk'urin hana ta ba balle tan 6an6are hanun Mummy daga jikin ta sema kallon Abba da Umman take yi.
Hakan ya dad'a d'aga wa Mummy hankali Nan ta saki Umma ta tuma ta shak'o Abba tana fad'in " zo Nan muna fiki yimun bayani"
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial16 Chapters
Void Hopper
The Progenitors are long gone, but their technology and culture live on. Trillions of beings from hundreds of species speak the Progenitor language, eat Progenitor foods, and use Progenitor technology. The backbone of this society are Hoppers - smugglers who transport goods through the dangerous dimension of the Void. The crew of the Discordant Note is on another routine job when they come across a member of a species nobody has ever seen before - a human. He has no memory of his past, his culture, or of the world he came from. What does he remember? He knows how to operate a multitool, fire a blaster, and how to kill a Sarcorian with his bare hands. Now, the crew and their newest member must steal a powerful ancient artifact, evade the clutches of the powerful Encephalon corporation, and discover the truth about the Progenitors.
8 181 - In Serial12 Chapters
Arpeligo
A brother and sister struggle to operate their independent interstellar transportation company within the confines of discriminatory laws and arrogant aristocratic enterprises. But fortune blows their way when they stumble upon a relatively ignorant human who also happens to be a fully authorized Citizen of the Empire, with all the legal rights and responsibilities associated with that status. Taking advantage of the situation, the sister proposes a deal to the citizen to try to secure their tiny company's future. But things are not what they seem and war between the noble families is reaching a breaking point within the sectors, causing mayhem, instability, and disastrous consequences for our interstellar crew on their trial run with the citizen. ** The setting is largely influenced by my experience in the transportation industry. I hope you enjoy it!
8 137 - In Serial32 Chapters
Everyone Dies Alone but not necessarily in space
Djaer is a lonely outsider from a species of interstellar tyrants, who finally has his dream job: a waste transport mission expected to take thousands of years, with nobody to bother him, and a small group of delicious humans to subjugate and ultimately consume. He was just settling in to relax for what felt like the first time in his life, when he finds out W.A.S.T.E. Unincorporated has saddled him with an assistant. It mostly seems like she only exists to annoy him, but it turns out there's more to her than meets the eye. Join an ensemble cast of characters in exploring a universe in which life is nasty, brutish and all-too-long, as they uncover the truth of who really makes the galaxy tick, and try to do something about it.
8 122 - In Serial62 Chapters
The Age of Heroes AU
The Multiverse is in constant danger Lucky a new Dawn is upon it as The Age of Heroes Begins. Takes place on Earth 4
8 170 - In Serial185 Chapters
The Cursewright's Vow
[THIS STORY WILL BECOME FREE ON MAY 27, 2021]Ammas Mourthia is a cursewright: an outlawed magician sworn to break curses. Contracted by the Emperor's daughter, he's pursuing a curse he may never break. *****Ammas Mourthia is a cursewright -- an outlaw magician who casts and breaks curses. Practicing his trade in the bustling city of Munazyr, he is hired by the last person he ever expected: Princess Carala, the daughter of the Emperor who murdered his family. Bound by his oaths, Ammas delivers the cure to Carala ... only for it to fail. Confronted with a sickness he cannot treat, pursued by werewolves who want Carala for their own purposes, and forced to return to a nation where he is a wanted criminal, Ammas must find a real cure. But there are forces at play he cannot control, and dark secrets waiting to be revealed. Fulfilling his vows might be the last thing Ammas Mourthia ever does.[[Wattys 2018 Winner: "The Heroes"]][[1st Place, Rebel Wars @Rebel_Town]]Trigger warning: Graphic violence, sexual situations, strong language.[[word count: 300,000-350,000 words]]
8 198 - In Serial13 Chapters
walking disaster
a burnt child loves the fire tfatws bucky barnes x oc
8 156

