《HASEENAH》PAGE 25&26
Advertisement
[7/17, 7:48 PM] 💄Meerah💋: 🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*25-26*
Banda zare Ido ba abunda Abba keyi, Ummah kuwa hawaye kawai ke kwaranya, bak'in cikin ta d'aya yanda taga Mummy ta sasu gaba saikace Wanda tayi cikin shege?
Jijjiga shi Mummy takeyi tana magana da d'aga murya tana fad'in" kamun magana ko baka ganin abunda yake jikin ta ne?"
Girgiza Kai kawai yakeyi, ganin bashida niyar magana hakan ya dad'a fusata ta, ta koma Kan Umma ta d'auke ta da Mari had'e da cakume ta tace
" Ki fad'amun gidan uban da Kika samo wannan abun kunyar, in Kuma ba Haka ba wallahi sai na Tara Miki jama'a"
Ji tayi an hankad'e ta can gefe, sannan aka janyo ta aka Mata Mari biyu masu kyau, d'ip duhu ya ziyarci idanunta, wani haske taga ya wulga kamar walk'iya, Bata Ankara ba ta sake jin wasu tagwayen Marin, jiri taji ya kwashe ta ji kake dim Mummy ta fad'i k'asa,tayi zaman 'yan bori, Bata gama dawowa dai-dai ba ta tsinkayi Muryar Mummy Saudat, wato babbar yayar su Abba tana fad'in" kaji mun 'yar iska kasheta zakiyi? Zaki shak'e Mata ki sata gaba kina zazzaga Mata ruwan bala'i, kina tanbayarta aina ta samu ciki? Bata da miji ne? Ko kuma iskanci da neman sheganta mutum?"
A razane Mummy ta d'ago ta dubi Abba Dan gasgata abunda Mummy Saudat tace, sunkuyar da Kai yayi k'asa alamar rashin gaskiya.
Nan ko Mummy ta tuma tace " wallahi Nima seka mun cikin Nan munafiki kawai, inba munafunci ba yaushe kake zagawa ban saniba, sai anyi magana kayi ta k'ifta idanu sai kace an maka k'arya"
Advertisement
Dariya Mummy Saudat ta saka tace" Aiko ya kamata ya Miki cikin, zoki kwanta ya Miki"
Nan Mummy ta birkice lokaci d'aya ta fita hayyacin ta tace sai anje an zubar.
Ana cikin Haka saiga Mummy Zuwaira, tun daga gate take jin ihun Mummy, da sauri ta shiga Dan ganin abunda ke faruwa, jin ba.asi yasa Rai 6ace ta dubi Mummy tace " Lauratu na rantse da girman Allah daga Rana Mai kamar ta yau, ko ciwon ciki 'yar uwata tayi wallahi saina sa an d'aure ki, in Kuma yatsunki ya ta6a jikinta wallahi sai kinyi Dana sanin Zama a raye"
Sannan ta dubi Umma tace" kekuma tunda kin Zama Saratu uwar asara, karki fasa ruwan ciki"
Tana gama fad'in Haka tasa Kai ta tafi zuciyar ta duk Babu dad'i.
Hajiya Zuwaira ma Haka ta gama masifeta Amma ji take lokacin ma take da niyar aiwatar da abunda take shiri.
Komawa d'aki tayi ta figi gyalenta da mukullin motarta ta fice, Bata tsaya ko Ina ba sai gidansu Haseen, daga waje ta sa aka Kira mata ita, tana fitowa suka figi motor suka d'au hanyar gidan boka.
Gudu take kawai kamar zata tashi sama, Banda ajiyar zuciya ba abunda take, can saita bugi sitiyarin motor da hanunta ta Kai duka wa iska.
Tsoro da firgici kawai zaka dubi Mum Haseen kasan tana ciki ganin kamar mutuwa zasuyi irin gudun da sukeyi, gashi tayi tanbayar duniya Amma ko kallonta batayi ba.
Haka suka k'araso bakin kogin, Nan suka tsunduma ciki, suna fita suka hau tsauni, saboda bushewa da zuciyar Mummy tayi ko tsoro Babu a idonta balle zuciyar ta.
Suna gama Hawa suka tsaya yanda sukayi ranan.
Jim kad'an sai gasu tsugune gaban boka.
Dariyar da ya rink'a yi ne ya dad'a 6atawa Mummy Rai har Yana wani shid'ewa.
Ji take kamar ta tashi ta shak'e shi Amma ba hali.
Advertisement
Seda yayi me isarshi sannan ya tsagaita ya dubesu, kafin ya furta wani Abu Mummy ta cilla mishi bandir d'in dubu d'add'aya harna dubu d'ari biyar, sannan tace" boka asan yanda za.ayi a salwantar da matar Nan da abunda yake cikin ta, bana buk'atar ganinta a raye, damuwata in koma in samu tayi hauka ita Kuma 'yarta ta shiga duniya ta Fara yawon karuwanci"
Boka yasan ko giyan wake yake sha hakan bazai yuwuba, Amma ganin wannan k'udin da ke zube a gaban shi ya sa shi fad'in "an gama"
Ya nuna musu hanyar k'ofa yace "Zaku iya tafiya"
Nan suka kamo hanya murna fal zuciyar Mummy, yau tasan burin ta ya cika komai yazo k'arshe.
Can ko bayan dawowar Haseenah daga school ta tarar Umman ta tsugune a palour tana rik'e da cikin ta.
Da gudu ta k'arasa yanda take ta Kama ta tana Kiran sunan ta, ganin ba zata iya d'agata bane ya sata d'auko waya ta Kira Hajiya Zuwaira, ba jimawa sai gata ta iso.
Kama ta sukayi suka fito da ita waje, dai-dai lokacin sai ga Haseen ya danno da motar shi sai kace an jefo shi.
Ganin an rik'o Umma ya sashi parking da sauri ya fito, harara Haseenah ta watsa mishi ta kau da kanta gefe.
Sakata sukayi a motar Hajiya Zuwaira sannan ta fice a guje ba tare da tako tsaya Haseenah ta shiga ba.
Ganin haka yasa Haseen shiga mota ya dubi Haseenah yace" ki taho mubi bayan su karsu 6ace Mana"
Ba don ta so ba ta shiga gaba ya rufa musu baya.
Kai tsaye labour room aka wuce da Umma, Hajiya Zuwaira sai Kai komo take.
Suna isowa ta dubi Haseenah tace" Ina kayan haihuwan"
Sunkuyar da Kai Haseenah tayi hawaye na k'ok'arin zubo Mata, sai a lokacin itama ta tuna da laifinta ne Ashe ita ya kamata ta siya.
Duban Haseen tayi tace" ku tsaya anan Kai da Haseenah, duk abunda ake buk'ata kayi Ni zanje in dawo"
Gyad'a Mata Kai kawai yayi sannan ita Kuma ta fice.
Addu'a kawai Haseenah keyi Allah fito Mata da Umman ta lafiya, Haseen ma hakan ne, ba.a dad'e ba Mummy Zuwaira ta dawo d'auke da basket, ba tare da tace musu komai ba ta wuce su.
Ciki kuwa Abu ya gagara, ganin Haka yasa Mummy Zuwaira Kiran mahaifin su ta sanar mishi halin da ake ciki, Dan a cewar likitotin Nanda minti talatin in Bata haihu ba C'S za.a mata.
Nan yace zai turo da addu'a a kawo musu.
Ko minti talatin ba.ayi ba saiga aika an kawo, Nan itama ta k'ara tofa nata sannan aka shiga wa Umma da shi.
Ko minti biyar kuwa ba.ayi ba Umma ta haifo yaronta kyakkywa, Kama da Umma suke sossai.
Seda aka gyara yaro sannan aka fito da shi, murna gun Haseenah da Mummy Zuwaira ba.a magana, Haseen kuwa sai kallon Haseenah yake Dan Bai ta6a ganin dariyarta ba, ko yaushe se dai murmushi.
Nan Mummy Zuwaira ta Kira gida ta sanar musu, bayan Nan ta Kira Mummy Saudat wato yayar Abba.
Kafin kace meye asibiti ya cika, Umma kuwa Bata ma San Mai yake faruwa ba saboda baccin wahalar da take.
Dai dai lokacin Mummy ta Danno hancin motar ta gida, da farin ciki ta shigo, ko parking me kyau ba tayi ba ta 6alle murfin motor ta shige ciki, ganin Haka yasa Mum Haseen rufa Mata baya.
Suna shiga side d'insu Haseenah ta Fara kalla, Nan taji shuru.
K'walla wa Saratu Kira ta Fara yi tana fad'in.....
For comments only 08144932303
Advertisement
- In Serial19 Chapters
System Tournament
The land started to expand before my eyes. What was supposed to be a big pond became a grand lake. What was once the nearby and sheltered political science campus became a bastion, hours away from the city. All this, brought down by a whim. The Start of the Ezro-Hoktan System Tournament. And we need to prevail in this new, hostile, environment.
8 87 - In Serial17 Chapters
Lust, like Vengeance, Demands Red
Yu Yuan was robbed from her mother's arms and sold for an orphanage owned by the righteous sect of light, At the age of eight. She was intelligent but naive in due to her youth. She was used and manipulated for years. Those years twisted her. Time and time again. she bottled her madness into a facade. Soon she wasn't needed anymore. But before the day of her death, she found a demonic spell. 'Give your soul away, and live again in the flesh.' Yu Yan got ahold of her dagger, plunged into her heart and screamed in madness "TODAY I DIE AS A LAMB, TO LIVE AGAIN AS A DEMON!"
8 120 - In Serial27 Chapters
Radiant Earth: Emergence
In a world where monsters and man must coexist, a teenage boy comes to terms with his half-human self. He writes of his struggles and choices in a red leather journal, one which he intends for his future child. It is a story of emergence, a coming of age, or a transformation of the self through which all people go through. But not all transformations are for the better. And not all things can be forgiven.
8 406 - In Serial14 Chapters
Battlestar Invictus
What would happen if the most powerful battlestar the Twelve Colonies of Man could create escaped the cylon extermination and instead ended up in a new universe?To escape the extermination of his own ship and crew, Commander Price ordered a blind FTL jump just before dozens of nuclear warheads detonated against his ship.Though because of strange workings within the navigation computer the Battlestar finds itself way beyond the Red Line, Uncharted space.They find themselves within the Imperium of Man. In the middle of the Gothic sector during the 12th Black crusade lead by Abbadon the Despoiler. How will our group of brave souls get themselves through this one?+++++++This is a project from over a year now and still going. I thought it was time I shared it with you guys. I hope you enjoy reading it as much as I enjoy writing it. Be sure to give me some constructive feedback!
8 171 - In Serial278 Chapters
System Only Gives Me Useless Gifts
Li Yun grew up with a system that gave him useless gifts. He wanted a reward that could prove the existence of the system, but ended up with abstract gifts like culture. Without physical proof, he was stuck wondering whether his mind was truly sane, all the while dealing with the reality of life. How will the "useless" system help Li Yun navigate medical school, hospital politics, criminal cases, treasure hunting, farming and cooking? Author's Note: This is a slice-of-life novel about a doctor with a mission-type system. It's written as a faux modern Chinese novel, so there are many 1-off characters and episodic mini arcs. Just a bit of warning, the tone of the story is very different after the childhood arc and jumpy as it chronicles Li Yun's life. I'm trying to make it less apparent in the rewrite, but there are still a lot of time skips. RR is the rewrite version, no set schedule. See webnovel for OG. scribblehub is a combo of both . I recommend scribblehub since it has pictures. Copyrights of the novel and cover are owned by Chocomug. Novel is free to read and download for personal use, such as offline reading, only.
8 832 - In Serial65 Chapters
Vibin' • Yoonkook [✔️]
[COMPLETED]in which a laid-back college student accidentally texts a serious, college medical student×cursingfluffmemesvibingHIGHEST RANKS[#1 kookgi•1/25/20][#1 yoonkook•2/19/20][#1 vmin•9/2/20][#4 jeongguk•4/7/21][#15 btsjin•12/18/20][#39 btssuga•9/12/20][#49 btsjungkook•9/12/20][#34 rm•12/24/20][#25 namjin•9/22/20][#80 jhope•9/15/20][#92 suga•12/30/20]
8 176

