《HASEENAH》PAGE 33&34
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*33~34*
Ganin Yana k'ok'arin Mata mummunan fahimta yasa Haseenah cewa" shikenan kayi abunda ya Dace"
Dad'i ne ya Kama Haseen lokaci d'aya ya mayar da jikin shi ya kwantar Kan kujerar ya lumshe Ido, hango su kawai yake yanda suke tafiyar da rayuwar auran su.
D'agowa yayi ya dube ta sannan yace" yanzu wajan Abba Zan aika ko wajan yayan Abba?"
Sunkuyar da Kai tayi sannan tace" ka samu Mummy Zuwaira ita zata sanar dakai"
Farin ciki ne ya dad'a rufe shi, Dan ji yake kaman ya rufe Ido ya bud'e ya ganshi gaban Mummy Zuwaira.
Bayan sun gama komai Haseen ya biya bill d'in sannan ya sake musu take away suka mik'e, motar shi ya shiga yace su Umaimah da baby su shiga ya mayar dasu gida Dan Kar su wahalar mishi da Mata.
Dariya suka sa Banda Haseenah da ta tura Baki Dan ba hakan ta so ba, Amma ba yanda zatayi Haka ta shige ita da Aaman suka d'au hanyar gida.
Yana Isa gidan ya shige ciki, Mummy Zuwaira ya hango zaune a palour ita kad'ai tana Shan fruits.
Zama yayi gaban ta shima ya d'au toothpick ya fara Sha, bayan sun gama ne Nan ya sanar da Mummy abunda ke tafe dashi.
Sossai taji dad'in Haka Nan ta Kira Mummy Saudat ta sanar Mata da abunda ke faruwa, itama farin ciki ne fal zuciyar ta, duk da tasan mahaifiyar shi batada hali Amma shi ya fita daban a cikin su.
Dan Haka tace wajan yayan su zai turo Kuma zata sanar mishi, Nan take tanbaya yaushe zasu turo yace Nan da kwana biyu.
Bai wani dad'e ba ya Kama hanyar gida, baiyi wata wata ba ya sanar da daddy shi, shima ya amince saboda ya yaba da hankalin Haseenah.
Mum d'inshi ce kawai da farko ta k'i yarda saboda tsoron Mummy, Amma daddy Haseen yace shi ba ruwan shi da wata Lauratu, abunda d'an shi yake so shi zai mishi tunda shi kad'ai yake da shi a duniyar Nan.
Ba Dan mum ta so ba Haka ta yarda, Amma tasan ba makawa cin mutunci na Nan zuwa.
Da daddare Haseen ya shirya ya nufa wajan masoyiyar shi wato Haseenah, lokacin itama ta shirya cikin Riga da skirt na Atampa, ba k'aramin kyau tayi ba, a palour ta mishi masauki, Nan ta cika mishi snacks da exotic juice da ta had'a wa Ummah.
Seda ya gaida Ummah sannan ya rik'o hanun Aaman suka dawo palour, ba.a jima ba Haseenah ta shigo hanun ta d'auke da warmer Wanda ta dafa jealouf na couscous, Wanda yaji kayan had'i, zuba mishi tayi Nan ya fara ci, seda ya k'oshi sossai sannan ya dube ta yace" swtlov kamar dama kinsan banci komai ba"
Advertisement
Dariya kawai tayi ba tare da tace komai ba, Nan suka Fara hirar su, ita dai kunya ta Hana ta sake wa daga tace " umm ko Kuma tace a'a"
Amsar da take bashi kenan, duban ta yayi sannan yace" nidai Nanda wasu kwanaki duk wannan kunyar zata kau, Dan Nanda kwana d'aya Zan Kai kud'in aure"
Kunya ne ya kamata hakan ya sata sunkuyar da kanta.
Ganin batada niyar magana 'yan miskilan cinta sun motsa ya sashi wucewa wajan Ummah suka cigaba da hirar su.
Wajan k'arfe goma ya fito zai tafi, Nan suka had'u da Mummy ta fito kitchen, ganin kallon da take mishi ya sashi kau da Kai gefe ya nufa hanyar fita, kallon shi Mummy tayi shek'ek'e tace" ayi dai mugani, kwartan ci ya wuce waje har sai an shigo cikin gida, da kwana kayi ai inaga zaka fi samun abunda kake so"
Yau Haseen Yana cikin farin ciki, Dan Haka bashi da lokacin tsayawa mayar Mata da dogon magana, dubanta yayi yace" karki manta kallon uwa nake Miki, karki Bari in rufe ido inyi abunda Bai Dace ba"
Yana gama fad'in Haka ya sa Kai ya fice.
Ran mummy ya 6aci matuk'a, hakan ya sata bin shi da ashar Amma ko juyowa Bai yi ba.
Yau da misalin k'arfe 8 na dare yayun daddy Haseen suka Kai goron gaisuwa da kud'in auran Haseenah naira dubu d'ari.
Murna wajan Haseen ba'a magana Dan shi ji yake kaman ya mallaki Haseenah an gama.
Da daddare Abba ya shigo hanun shi d'auke da goro da carton na sweet da sauran tarkacen gaisuwa.
A palour ya tarar da Mummy da Saratu na zaune, mummy na ganin shi ta hau wangale Baki, waje ya nema ya zauna sannan ya tura Mata kayan gaban ta.
Janyo wa tayi ta dube shi fuska a sake tace" Abban su Dan kaga kwana biyu inacin goro shine zaka siyomin da yawa Haka?"
Kau da Kai yayi gaban shi na fad'uwa yace
" a.a na tanbayar auran 'yar ki ce aka had'o da sadaki"
Washe Baki Mummy ta Fara ta dubi Saratu tace" ke wanene kuka sasan ta Kuma Baki fad'amun in Fara shiri ba gashi har an kawo gaisuwa da sadaki"
Cikin rashin fahimta Saratu ta yamutsa fuska tace" Mummy Ni kuma?"
Ganin suna son cika mishi kunne yasa Abba cewa" ba fa ita nake nufi ba, Haseenah nake nufi, itace Haseen d'an wajan k'anwar ki ya tura da kud'in aure"
Tun kafin ya Kai aya Mummy ta zabura ta mik'e, k'afa ta saka tayi patali da goro da mintin, Nan ya watse a palour, girgiza Mummy ta hau yi tana fad'in
" Ni za.a mayar k'aramar yarinya aci Amana ta? Ni za'a tozarta a garin Nan, har za.a had'a Baki da 'yar uwata aci Amana ta? Wallahi indai Ina raye kasa a ranka ba'a ta6a maganan auran Nan ba"
Advertisement
Mik'ewa Abba yayi ya wuce ciki.
Saratu kuwa kuka ta saka Dan Nan duniya ta mace Kan Haseen, sonshi take kamar ranta, itama Mummy ganin akwai 'yan chanji a hanun Haseen ya sa take da kudirin tana gama kau da su Ummah zata tursasa wa k'anwar ta lallai ta sa Haseen Auran Saratu, sai gashi ba zato ba tsammani ana k'ok'arin haramta Haka.
Birgima Saratu keyi tana fad'in" Mummy Dan Allah karki Bari ya aure ta, wallahi sonshi nake Kuma Dani yafi dacewa, Mummy in ban aure shi ba mutuwa zanyi"
Bige Mata Baki Mummy tayi tace" Dan ubanki Dena cewa Zaki mutu wallahi su zasu mutu ba ke ba, in dai Ina raye daga yau wannan magana ya Zama tarihi"
Ummah dai dake cikin d'aki tana jiyo hayaniya, amma Sam batasan abunda ke faruwa ba, saboda itama Haka kawai taji gaban ta na fad'uwa ga wani irin bugawan da zuciyan ta keyi.
Hakan ya sata Kiran Haseenah daka d'akin ta ita da Aaman tana mishi wasa.
Fitowa tayi da sauri ta zauna gaban Ummah tace gani" k'ura Mata Ido Ummah tayi na wasu mintina sannan ta umarce ta ta d'auko Mata Aaman.
Ba musu ta d'auko shi, mik'a hannu tayi ta kar6e shi ta rungume shi jikinta, sai hawaye, hakan yasa Haseenah fashewa da kuka itama ta rungume Ummah, cikin kuka Haseenah ta Fara cewa" Ummah na ki fad'amun me yake faruwa, Mai yasa ki kuka?"
Shuru ba amsa sai kuka, gashi ta rungume su kaman zata mayar dasu cikin ta, sai saukar ajiyar zuciyar ta kawai kake ji, hakan ya dad'a d'aga hankalin Haseenah.
Sun kai kusan minti talatin a Haka sannan Ummah ta sassauta rik'on da ta musu, Kama hanun Haseenah tayi ta saka cikin na Aaman ta matse, sannan ta dubeta cikin hawaye tace
" Haseenah ko bana Raye ga amanar ki da na Aaman na damk'a a hanunki da Kuma Wanda ya halicceku, ki kare mutuncinki ki rik'e kanki da k'anin ki, karki yarda ki maimaita irin rayuwar da kikayi a baya, ki kasance Mai 'yan ci da girmama na gaba da ke, ki kasance me biyayya da Kuma hak'uri Kan duk wata rayuwar da Kika samu kanki a ciki, daga k'arshe inason Koda bayan Raina a kullum kikasance kina tunawa Dani, ki kasance Mai yimun addu'a da neman gafarar ubangiji, ki Kuma ji tsoron Allah, ki bawa k'aninki irin tarbiyar Dana Baki, inda hali mafi da wannan"
Tana kaiwa Nan kuka ya k'wace Mata, Haseenah ma kukan take, ganin Haka yasa Aaman fashewa da kuka shima.
Sulalewa Haseenah tayi ta Kira Mummy Zuwaira a waya ta sanar Mata ga Umma nata kuka.
Nan tasa aka bawa Umma waya, tamata tanbayar duniya Umma tace ba komai, hakan yasa tayi Mata nasiha har sunyi sallama sai Ummah tace" Yaya ga amanar Haseenah da Aaman na bar miki, Koda bana Raye ki kula mun da tarbiyar su.
Tana kaiwa Nan ta katse wayar gaba d'aya.
Hankalin Mummy Zuwaira ba k'aramin tashi yayi ba, gashi k'arfe kusan Sha d'aya na dare ne ba zata iya driving ba, Kuma daddy su Umaimah baya gari.
Haka ta kwanta tunani fal zuciyar ta, Allah Allah take asuba tayi ta nufa gidan Ummah.
Nan ko Umma na rungume da Aaman har yayi bacci a hanun ta, ita Kuma ta k'ura mishi Ido tana sharar hawaye, Haseenah ma zaune take a gefen Ummah ita ma kukan take, ganin k'arfe d'aya ya yi yasa Ummah duban Haseenah tace" ki tashi ki je ki kwantar da Aaman, kema ki kwanta Nima baccin nake ji"
Ba musu Haseenah ta d'auke shi ta kaishi d'akin shi ta tofa mishi addu'a sannan ta koma d'akin ta jikinta a sanyaye ta ja bargo ta kwanta.
Ummah ma mik'ewa tayi harta shiga d'akin ta sai Kuma ta fito, wajan Aaman ta sake komawa ta zuba mishi Ido sannan ta fito ta lek'a Haseenah ma, takai kusan minti biyar Nan tsaye ganin Haseenah na k'ok'arin juyowa ta bar wajan da sauri.
Alwala Ummah ta Fara yi ta hau sallah , tana yi tana kuka, tun tana yi a tsaye har ta zauna.
Nan bacci ya d'auke ta Kan sallayar.
Ana Kiran sallan asuba ta mik'e taje ta d'auro alwala ta dawo ta tada sallah Dan Bata tashi Haseenah ba Dan wani lokacin ma Haseenah na rigata tashi.
Abunda bata sani ba shine yau Haseenah ta makara.
Tana zaune Kan sallaya tana addu'o I, bud'e k'ofar su taji anyi an gangaro da Abu Mai Kama da k'arfe, kafin tayi yunk'urin juya wa an cillo ashana.
Warin gas Ummah ta Fara ji mik'ewar da zatayi kuwa Nan gas d'in yayi bindiga, kafin kace meye wuta ya Kama ko Ina.
Salatin Ummah shiya tada Haseenah daga barci, da sauri ta duro Dan ganin abunda ke faruwa.
Bud'e k'ofar da zatayi kuwa kaman jira ake wuta ya Kama d'akin Haseenah....
*Innalillahi wa inna ilaihir rajiun*
Hope u enjoyed d page, plx vote nd drop ur comments. 😍😘❤
Advertisement
- In Serial296 Chapters
The Urban Dao Child.
Yang Dao is an orphan. He does not speak much. He is so introverted that if not for his grades no one would have even known about him.
8 1727 - In Serial11 Chapters
World of Mana
My name is Alexander Grey and yes I'm what people call a class-less. I am part of the 1% of the world that are unable to aquire there class when aweaken and am treated like a third class citizen. My family relation is bad, no friends at school, and a future that seems black at best. Yea my life is not easy but even so I will not give up and rise up and become someone no one can look down upon, I shall walk the path of the Eternal! Note: This is my first fantasy novel and is subject to change ever ten chapters or so with revision. Martial art/Fantasy novel about a man born into the world crippled by society standards finding his own way.
8 170 - In Serial6 Chapters
Changing Monster
A skeleton wakes up inside a dungeon. Armed with only a sword and a single memory, it must make decisions on what it should do. Each choice it makes will have a profound impact on itself.
8 140 - In Serial35 Chapters
Our Everlasting Melody
As her senior year begins, Leah has changed, but no one is sure if it is for the better. According to their loved ones, her relationship with her boyfriend is apparently unhealthy. The only thing that their friends and family can do is force them to stay apart.But you can't keep these two away from each other that easily. Instead of breaking up and moving on, they decide to keep their relationship a secret from everyone. But it isn't as easy as it might seem. Old flames arise, and so do other problems that Leah and Blake had never had to face before.Life isn't fair, but Leah and Blake are still learning that love isn't either.(Sequel to Our Song)
8 225 - In Serial16 Chapters
Hiccup (HTTYD) x reader
You are (y/n) a mysterious Dragon rider who spends your time traveling with your Night Fury, Midnight. What will happen when you meet other dragon riders that will change your life forever?...(Written sometime between 2017-2018 when I was a Freshman in High school)
8 164 - In Serial4 Chapters
Secret Jordan Phillips
Heyyy guys this story is just for fun!! I hope you enjoy
8 107

