《HASEENAH》PAGE 37&38
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
Ina me miƙa sakon ta a ziya ta ga duk masoyin wannan littafi, mutane da yawa da bina pc suna faɗin bai kamata na musu haka ba, wasu na faɗin Allah ya sa mafarki ne, wasu kuma cewa suke aina za.a samu wata haseenar, wasu na cewa shkan littafi ya gama dad'i,to abinda nakeso ku fahimta shine kusa aranku yanzu littafi ya fara dadi, Ni dai bazance komai ba, amma ku cigaba da biyoni don jin yanda abun ze kaya, sannan masu yin kuka da meerah tace ku share hawayen ku, banson ganin kukan ku, wanda jininsu ya hau kuma kusha ruwan gishiri zai sauka. Lol na ruwana Amma.
*Heart u guyx*
*37~38*
Duban daddy Haseen yayi yace" daddy? Me nakeji kana cewa? In hak'ura da Haseenah zan samu wata? Soyayya ɗaya ce kuma tun randa na fara son Haseenah na damk'a mata zuciyata da kuma ruhina, bazan ta6a auran wata ba, ko da kuwa kun matsa mun sedai ta aura gangan jikina"
Ganin Haseen ba cikin hankalin shi yake ba yasa daddy Fara janshi Dan an Fara watsewa, tirjewa Haseen ya fara yi, da k'yar aka jashi suka shiga cikin mota.
Kuka Haseen ya saka ya dubi daddy yace" daddy Ashe baku Sona bak'u k'auna ta? Ashe Zaku iya juran ganina cikin wannan halin?, Ba zaku iya bani farin ciki ba? Daddy...
Girgiza kai Daddy ya fara yi yace" Haseen hak'uri zamu yi duka, lokaci ne yayi kuma dukan mu ita muke jira, in lokaci yayi ba makawa semun tafi"
Cikin wata irin murya Haseen yace" to meyasa Ni ban fara tafiya ba sai ita? Me yasa za.amun haka? Meyasa....
Ganin baya cikin hankalin shi yasa daddy dad'a Kama shi tare da toshe mishi baki.
Advertisement
Driver ne ya fara jan motar dan barin wajan.
Juyawa Haseen yayi yana waiwaye yana faɗin" daddy Kar kumin haka, kace mata tazo mutafi dan Allah Kar mu tafi mu barta anan, Daddy kayi alk'awari duk abinda nake so shi zakamin, dan Allah ka tsaya in taso ta"
Ganin yanda Haseen lokaci ɗaya ya birkice kaman ƙaramin yaro yasa daddy Fara hawaye, bai taɓa tunanin akwai ranan da zatazo ta zartar mishi da d'a haka ba.
Kasa cewa komai Daddy yayi har suka fice wajan.
Ganin da gaske tafiya zasuyi yasa Haseen fara k'walla mata kira" Haseenah! Haseenah!!"
Janyo shi daddy yayi ya mayar ya zaunar.
Lokaci ɗaya kuma yayi shuru bai sake cewa komai ba, sai saukar ajiyar zuciyar shi da bugun k'irjin shi kawai kake ji.
Haka suka koma gida duk zuciyar su babu dad'i.
Can gida kuwa shuru kake ji kaman babu jama'a, Mummy Zuwaira ta Zama tamkar marainiya, Umaimah da baby kuwa kwance suke yanda zazzaɓi ya rufe su.
Mummy Saudat da tazo kuka ta saka tana faɗin" ban ta6a ganin gobarar da yaci sashi ɗaya sauran lafiya k'alau ba, wallahi sai an nemo sanadiyar tashin wutan nan, in ba haka ba hankalin kowa saiya tashi"
Da k'yar suka rarrashe ta tayi shiru.
Mummy kuwa tasa Saratu tayi gaba a d'aki tana faɗin" ba zaki rufamun baki ki dena kukan ba? Koba akan ki nayi komai ba? In kuma bakison Haseen d'inne saiki faɗa mun"
Share hawayen ta tayi,amma cikin zuciyar ta ta razana da jin furucin Mummy, wato ita ce ta saka wutar? Ba makawa in asiri ya tonu tasu ta k'are.
Lokacin da Mummy ta fito taji abinda Mummy Saudat ke faɗa hankalin ta ya tashi, da gudu ta wuce bayan gida dalilin murd'awan da taji cikin ta yayi lokaci guda, tana yi tana sharce gumi.
Haka aka cigaba da kar6an gaisuwa.
Haseen kam dama gida aka wuce dashi dan Sam bai sake cewa komai ba.
Advertisement
Sedai yayi ta bin kowa da ido kamar zautacce haka ya zama.
Lokacin da labarin mutuwar su Haseenah ya tarar da mum Haseen , hankalin ta ya tashi Dan tasan ba makawa 'yar uwar ce ta aikata haka.
Dan haka a gigice ta d'au makulli ta fice a guje.
Tafe suke cikin tank'ashe shiyar motar su bak'a land cruiser, wani matashi ke jan motar yayin da wani wanda bazai wuce shekara 20 ba yake gefen shi.
Dukan su suna sanye cikin manyan kaya k'amshi kawai ke tashi cikin motar, sautin karatun Alqur'ani ne yake tashi wanda ya sanya su duka yin shuru.
Har sun wuce me jan motar me suna Sameer ya dawo da baya, duban shi Mahmud yayi sannan yace " bro me ya faru kuma?"
Ba tare da ya kalle shi ba yace" nan zamu shiga dan kai ziyara kabarin bappa, kaga tun rasuwar shi rabon da mu shigo Kano, kuma kaga yanzu in muka tafi babu ranar dawowa, shine nakeso mu shiga"
Tsilli-tsilli Mahmud ya fara yi da ido kamar zai yi kuka yace" bro Dan Allah mu tafi wallahi banson shiga wajan nan tsoro nake ji"
Ɓalle murfin motar Sameer yayi ba tare da ya kalle shi ba yace" zaka iya zama cikin motar ka jira fitowa ta"
Da sauri Mahmud ya fito dan yasan abinda zai biyo baya.
Hakan ya sashi rufa mishi baya badan ya so ba.
Seda sukayi addu'an shiga sannan suka cire takalmi suka shiga.
Sun dad'e sossai a wajan kabarin bappan nasu daga bisani sukayi addu'a duka sannan suka kama hanyar fita.
Wucewar da Sameer zaiyi sai ya kula kaman wani kabari na motsi, hakan ya sashi tsaya wa ya tsura wa kabarin ido Dan gasgata abinda yake gani.
Aiko ba gizo idon yake mishi ba da gaske motsi kabarin yake yi.
Mahmud kuwa ya gama razana, kama hanun yayan nashi yayi yana jan shi na faɗin " bro plx let's leave, I think is a ghost or something terrible"
Fisge hanun shi Sameer yayi cike da masifa yace" don't let me set my anger on u, u can leave"
Ya nuna mishi hanyar fita.
Shuru Mahmud yayi amma zuciyar shi kamar zata fito waje saboda yanda k'irjin shi ke bugawa.
Da sauri Sameer ya nufa wajan masu gadin mak'abar tar Nan ya sanar mishi da abinda ya gani.
Ba tare da 6ata lokaci ba suka fara tonawa.
Sunyi sa.an fito wa da ita amma lokacin ta dena motsi.
Kama hanun ta yayi nan yaji vein d'in hanunta na blinking.
Duban su yayi yace " akwai rai jikin ta bata mutu ba"
Zare ido masu gadin suka fara yi dan basu san ya zasuyi ba.
Ganin haka yasa Sameer suran ta ya sanya ta cikin motor.
Binshi masu gadin suka fara yi suna faɗin" ranka ya dad'e ina zaka kai ta?"
Kuɗi ya ciro ya jefa musu sannan ya dubi Mahmud yace" zaka shigo ne ko in tafi?"
Cikin tsoro ya buɗe gidan gaba ya shiga yana waiyayen baya yana kallon mutun cikin likkafani.
Juyawa da kan motar Sameer yayi ya koma gidan su dake G.R.A duban shi Mahmud yayi yace" bro Ina Kuma zamu"
6alla mishi harara yayi sannan yace" if I hear a single word from u again, wallahi ranka zai 6aci"
Mai gadi na ganin su ya wangale gate, da sauri suka wuce ciki ko parking Mai kyau bai yi ba ya fito ya sureta suka wuce ciki.
A palour ya shimfid'a ta sannan ya fara k'ok'arin buɗe fuskar ta.
Da sauri ya sake haɗe da yin salati ganin yanda fuskar ta koma kaman na wata halitta.
Mahmud kuwa ihu ya saki ya haye sama da gudu.
Hawaye ke zuba a idon sameer saboda tsananin tausayi.
Ganin zai 6ata lokaci ya sashi hayewa sama ya nufa d'akin shi ya d'auko kayan aiki....
Please vote nd drop ur com
Advertisement
- In Serial135 Chapters
Sprig
An endless racial war, a magical island, and a lone girl stuck in the midst of it all. Kaia, one of the last living members of the Treek race, has spent her life in hiding. Each race wields its own form of magic to claim what is theirs and repay the hurt caused by others. When an island appears in the ocean overnight, many see it as a resource. For Kaia, it brings hope that she might one day be with her people again. Join the journey as Kaia fights to find the family that was taken from her. Will the endless hatred push her to seek revenge? Or will she find another way forward? A new chapter of Sprig is released every Monday, Friday, and sometimes on Wednesday. For the most recent chapters, please visit my writing website: Sprig.HoustonHare.com. Sprig is now available in Paperback, Hardcover, and eBook. Sprig is currently on hiatus.
8 449 - In Serial11 Chapters
Neither Snow Nor Rain
Humanity is impotent, no magic can be found in their blood. The hordes of Beasts lack no such problem and wields magic as one would breath. Fortunately for Humanity, though they lack in the spirit, they are adaptable and resilient, because of course... magic isnt the only way to kill a man. This will be a story of betrayal and love. A tale of the most pious kings and of rightous revolution. The world isnt as it seems and the old order is collapsing. What was once buried, will come to the top for the whole world to see.
8 208 - In Serial7 Chapters
Protector, Protector (BL)
They came for him when he was nine. The Shadows. They tore his mother's heart from her chest and left her there to die. Now Azame Jackson is 17, and his time seems to be running out. They exist in the darkness, the very thing Azame's life keeps at bay. He was born a Siren, a creature of light, and the Shadows were his mortal enemy. He could only run. With his Protector, Ajax Gabris, he'll attempt to survive what most of his species can't. All while Azame changes slowly into something just in between both worlds. Can he fight off the darkness that threatens to consume him? Or will he succumb? Perhaps his anchor will be Isaac Harrison, the boy who seems locked within his orbit. Time will only tell. Ajax Gabris is forever bonded to Azame Jackson, one of the last Sirens to enter their world. On his shoulders rests an unbearable weight. Born half-human, Ajax will be pushed to the brink of his strength. Will the Ancient Greek blood that flows through him hold as the pressure builds? Or will Ajax snap and sink? Ajax stands at the crossroads of going straight or betraying everything he'd ever believed in just to keep Grant Snyder by his side. For Grant, he finds. He will set the world on fire. Cover Art Done By Jude Beasley!!!!
8 55 - In Serial7 Chapters
Inner-Self
a group of teens find a way to unlock their hidden potential until it's soon grows out of control.
8 196 - In Serial15 Chapters
♕Shapes♕
Хит был добрым, нежным, любящим мужем, пожалуй даже слишком мягким... Но что случилось в тот момент, когда его рука сжала тонкое горло его жены? Кто такой Гарри и куда делся Хит?
8 171 - In Serial21 Chapters
Poems About Life
Inspirational poems, sad poems, happy poems, advice in poems, just poems in generalIf you like these poems, then please read my other poetry book called "Within the Confines of my Heart." Tell me what poems you want me to write in the comments or on my conversations.I'd also really appreciate it if you would vote on my poems; it really means a lot!!!#6 in whattoread - 12/1/2019# 5 in underrated - 8/9/2020#53 in poetry - 1/14/2021#1 in poesia - 3/29/2021#9 in read me - 1/14/2021#3 in poet - 2/14/2021
8 125

