《HASEENAH》PAGE 43&44
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*43~44*
" Ammi Dan Allah ki Dena turani wajan yarinyar nan in har ba so kike Nima a kwantar da Ni ba, wallahi bazan iya ba"
Ya 'karasa maganar haɗe da riƙe k'afar Ammi.
Cike da mamaki ta dubeshi tace" Baby meye haka? Ba kyau abinda kake yi fa, itama fa da mutum ce 'yar uwarka tsautsayi ne ya faɗa mata,kuma kaima bakafi k'arfin haka ba"
Share hawayen ya fara yi sannan yace" Ammi kiyi hak'uri zan je amma ba yanzu ba"
Duk abinda suke Sameer na kallon su saman stairs, shi mamakin Mahmud yake ganin yanda lokaci ɗaya yake fita hayyacin shi.
Dole Ammi ta yi shiru ta k'yale shi, dan tasan in ta matsa mishi zai iya daina fitowa palour ta ma.
Mummy kuwa rad'ad'in da bakin ta yake mata shi yafi d'aga mata hankali, kallon fuskanta tayi a mirror, kau da kai tayi da sauri ganin yanda kamannin ta suka koma, musamman bakin ta sai kace ja6a.
Fashewa da kuka tayi tana faɗin" Allah ya isa mun wallahi, wanda bazata gama da duniya lafiya ba"
Ana haka kuwa k'awayen ta wanda suka saba zuwa mata yawo ɗaya daga cikin su ta kira ta a waya, nan Mummy ta shaida musu itakam batanan tayi tafiya, dan bazata iya bari suga wannan abun kunyar ba.
2 weeks later
Jikin Haseenah ya gama bushewa ya d'aye tas ba komai, sai dai tabo da sauran wajan da bai warke ba, dan yanzu tana iya zama taci abinci da kanta.
Amma ba umm ba uhm, saidai tayi ta binsu da kallo, wani lokacin kuma sai kuka, gashi anyi mata tanbayar duniyar nan Bata amsawa, abunda basu sani ba ma batajin abunda suke faɗa, ita dai kawai tana ganin bakin su na motsi.
Tana son yin magana amma babu hali, ganin ta a wajan da bata sani ba duk shi yafi d'aga mata hankali, gashi duk cikin wanda suke zuwa babu wanda ta sani.
Saidai tafi ganin Sameer da Mummy sai nurses d'inda ke kula da ita sai Dr Abeed.
Advertisement
Tana son tanbayar ina Umman ta? Dasu Aaman da Haseen amma ba hali.
Iya abinda take iya tunawa tasan wajan su ya kama da wuta.
Sannan ko yaushe inta kwanta bacci salatin Umman ta ke yawo cikin kanta.
To ina Umman take? Meyasa suka barta anan? Kodai sun gujeta ne ganin jarabawar data fad'a mata?
Wata zuciyar ta bata amsa da ko da duniya zasu gujeki Umman ki bazata ta6a barin ki ba.
To ina suke?
Ba ta da wannan amsar, shiyasa takanyi kuka sossai inta tuna da haka.
Sai dai Sameer yayi ta bata hak'uri da Mummy, Amma Bata fahimtar abinda suke cewa.
Ganin ta samu sauk'i ne aka fara shirye shiryen Mata theatre, sun tsayar da rana satin da za.a shiga ran Monday kenan.
Addu'a kawai suke Allah ya basu Sa'a dan basu da wani ishesshen kayan aiki.
Dr Abeed ke ba Sameer k'arfin gwiwa, amma shi duk ya karaya.
Yau da sassafe ya shigo asibitin Mahmud na binshi a baya d'auke da basket d'in abinci.
Kana kallon Mahmud zaka ga yanda yayi kicin kicin da fuska, dan ba son ranshi ya zo ba, dan rabon da ya ganta tun ranar da suka d'auko ta, yanzu ma dan yana shakkar Sameer ne Amma wallahi da bazai zo ba.
Kai tsaye d'akin da Haseenah take suka nufa.
Suna isowa bakin k'ofar Mahmud ya ja ya tsaya, duban Sameer yayi yace" bro should I wait for u here?"
Harara kawai ya watsa mishi ya shige ciki, nan Mahmud ya bishi da sand'a.
Lokacin ko bacci ma take bata tashi ba, dan haka Sameer ya hau kujerar da ke gefen gadon ya zauna.
Mahmud kuwa jikin bangon d'akin ya mak'ale ko k'wak'k'waran motsi ya kasa.
Sameer zuba mata ido kawai yayi yana kallon yanda take sauke numfashi a hankali, wani lokacin kuma ta saki ajiyar zuciya kamar wanda taci kuka ta gaji.
Zuba mata idon da yayi zuciyar shi ke raya mishi cewa, duk yanda akayi yarinyar nan kyakkyawar gaske ce.
Dan yanayin siririn hancin ta da k'aramin bakin ta ne kawai ya sashi ganin haka, amma ji yanda wuta ya mayar da ita.
Girgiza kai kawai yayi cikin ranshi yace" poor you"
Ganin Bata motsi ya sa Mahmud lek'a ta, gani yayi tana bacci nan wata ajiyar zuciya ta k'wace mishi, dan yasan da idon ta biyu Allah kad'ai yasan dramar da za.ayi cikin asibitin nan.
Advertisement
Dan ko kashe shi Sameer zeyi wallahi bazai tsaya ba.
Tunda ya fara lek'en ta sameer ya ke kallon shi.
Dariyar mugun ta Sameer yayi sannan ya mik'e ya dubi Mahmud yace" Ni zanje duba patient d'ina, ka zauna anan ka jirani kafin in dawo,in ta tashi kuma ka bata abinci sannan ka kira Ni"
Zaro ido Mahmud yayi dan wannan maganan ta firgita shi, kallon yayan nashi yayi yace" yaya zan raka ka kaga sai nima in samu ladar ziyara"
"No need, Nan ma aikin ladan zakayi ai"
Jikin Mahmud ne ya hau rawa dan yasan ko mutuwa zaiyi bazai yarda ya bishi ba.
Ganin Mahmud ya tafi duniyar tunani yasa Sameer ficewa ya barshi nan tsaye.
Yana fita shima Mahmud ya fice ya zauna kujerar bakin k'ofar d'akin inda security ke zama.
Nan security ya fara cewa" ranka ya dad'e ka zauna ciki mana, in oga ya ganka bakin k'ofa bazaiji dad'i na bar k'anin shi a waje ba"
Cike da haushi Mahmud yace" to jani ka shiga dani mana, ina ruwanka dani ko kai ka bani ajiyar eye?"
"Tuba nake ranka ya dad'e"
Girgiza kai Mahmud yayi yace" to kayi damuwar ka, in kuma kujerar ka zan baka gashi"
Ya k'arasa maganar haɗe da mik'e wa.
Da sauri yace" yi hak'uri zauna"
K'wafa yayi ya zauna Yana mazurai.
Can Kuma sai ya mik'e ya lek'a ta ta window har lokacin bacci take.
Murna ne ya kama shi ganin har yanzu bata tashi ba.
Lek'awar da zaiyi na uku ya hango ta zaune kan gadon tana ta kalle kalle.
Gaban shine ya fara dukan uku uku, da sauri ya ciro wayar ya kira Sameer Amma abun haushi bai d'aga ba.
Tsoro ne ya dad'a kama shi gashi yace mishi ya bata abinci.
A hankali cikin sand'a ya shiga kan shi a sunkuye, da baya baya ya k'arasa ya d'au plate ya zuba mata chips nd egg with sauce, ko kallon ya baiyi ba ya mik'a mata.
Garin kar6a hanunta ya ta6a nashi, wani tsalle ya daka yayi gefe haɗe da ihu yana faɗin" wai mena miki kikeson ganin baya nane eye?"
Ya fad'a kaman zai fashe da kuka.
Ganin Sameer yayi tsaye gaban shi ya zuba mishi ido, da gudu yayi bayan Sameer yace" yaya dan Allah ka tambaye ta mena mata?"
Ko kula shi baiyi ba ya ja kujera ya zauna gefen gadon ta.
Zuba mishi ido kawai tayi tana kallon shi" to wannan d''in waye?"
Ba tada bakin tanbaya sannan bata da wanda zai bata amsa hakan ya sata yin shuru ta ci abincin kad'an sannan ta ajiye.
Nurses ne suka shigo dan gyara ta, hakan ya sa Sameer mik'e wa ya fita.
Mahmud ma yabi bayan shi yana ta faman k'ananan surutu.
*MONDAY*
misalin k'arfe bakwai na safe nurses suka shirya Haseenah cikin kayan da ake saka wa patients in za.a shiga dasu theatre, abinci suka bata sanann suka fice.
Sameer ne ya shigo ya dube ta duk hankalin ta a tashe, zama yayi ya dube ta sanann yace" ban sani ba ko kina jina ko baki ji, amma inaso kisa a ranki kuma kiyi addu'a Allah yasa ayi nasara"
Taga bakin shi na motsi amma bata jin abinda yake faɗa, amma ganin yanayin fuskan shi tasan he's saying something serious, hakan ya sata sakar mishi murmushi kawai.
Shima mayar mata yayi.
Dai dai lokacin Dr Abeed ya shigo da wasu nurses biyu, ɗaya daga cikin nurses d'inne ta Mata allurar Anesthesia sanann suka kwantar da ita.
Ganin dishi dishi ta fara yi wa mutane, can kuma taji duk jikinta yayi nauyi, within 5 mins bacci mai nauyi ya d'auke ta.
D'aurata sukayi kan gadon suka tura ta zuwa theatre suka fita da ita.
Likitoci biyar ke kanta, Sameer kuwa sai kai kawo yake a k'ofar theatre d'in, tun 7:30 aka fara mata har 10am basu fito ba.
11am sharp aka fito da ida fuskanta gaba d'aya an nad'e da bandage, ko motsi batayi kamar gawa haka aka turota.
Cikin A&E aka wuce da ita sai dai an ware mata wata d'aki ita kadai ke ciki.
Robar abinci aka zura mata a hanci aka nad'e da bandage.
Babu abunda kake hangowa a fuskanta dan gaba ɗaya aka nad'e ta.
Kana kallon fuskan Sameer kasan Yana cike da damuwa.
Wayarshi ne ta fara ruri yana dubawa yaga Ammi ke kira, picking yayi ya kara a kunne shi, ji nayi yace....
Please share, vote nd drop ur comments
Advertisement
- In Serial43 Chapters
Re:Hammer - The Hammering
Sequel to the sort of liked Re:Hammer. Set in 40k universe, and generally on course. Personal changes are detailed in the Prologue because it's quite a bit. It's not really ended nor is it an attrocity like End Times, but I've got a few things to change. To note: Druchii arc (If this means nothing to you, go read Re:Hammer first) has been learned from and will be avoided. This is not to say there won't be any sex, but we will certainly try to keep it less crazy. Feedback is, as always, appreciated and worked with.
8 91 - In Serial12 Chapters
New Admission: An Original BPS Fanfiction
Caramel Charlatte, a novice animator, is a shy Humancorn living in the mountains with the Ninja Twins. Though often bullied and afraid to come out, she dreams of being accepted into the most popular animation studio in the city: Black Plasma Studios. There's just one problem: she is the ONLY out-of-place player. While the rest of the city residents are humans in skins that range from normal-to-intriguing, she is the ONLY Humancorn. Acceptance is hard, and the competition is harder. She finds new friends in the Obsidian Patron Guild, but also new enemies, such as the H.E.N.D Corporation. Can Caramel overcome her challenges and fears and become a part of BPS? Or will reality come crashing down on her like a wrecking ball?
8 128 - In Serial54 Chapters
The Wandering Scholar
Zhou Mingzie, A young Chinese American is suddenly brought into a mythical land, similar to China in many ways, but is most definitely not. This new world appears to contain cultivation elements like the Wuxia and Xanxia stories he read throughout highschool, but he can also gain Levels and Skills, I mean Paths and Techniques. Sure he is Chinese, but he grew up in America, so he doesn't want to ascend to the heavens and fight spirit beasts, does he? But Mom wants him to embrace his heritage more...jk...unless? [participant in the Royal Road Writathon challenge] Inspired heavily by The Wandering Inn and Beware of the Chicken, as well as cultivation novels in general, this story hopes to take a Westernish approach to the standard Cultivation approach, being more subtle and changing how it approaches the standard tropes of the genre, without abandoning them entirely.
8 197 - In Serial17 Chapters
the title say it and guys if u want some lemonade just tell me😉anyway ,the boys who r in this book:kageyamaoikawaiwaizumikurookenmaatsumuosamuand that's it ! i'm sorry if ur fav haikyuu characters are not here maby i'll add some after just request!!love ya and stay healthy(btw these r only for fem reader)
8 101 - In Serial17 Chapters
Perpetuo Servaturum
Это мир, в котором каждому человеку суждено быть со своим "истинным". Неважно, сколько лет пройдет, они все равно будут вместе. Если до совершеннолетия "истинные" не наши друг друга, они перестают стареть, так как старость они должны встретить вместе. История об учителе, который сотню лет ждал, как оказалось, своего ученика.
8 169 - In Serial61 Chapters
Theirs | VxBTS ✔
In which the student Kim Taehyung accidentally caught the hearts of six immensely dangerous menTopBTSBottomTae
8 118

