《HASEENAH》PAGE 61&62
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*61~62*
Haseen suka gane zaune k'asa, ya jik'e sharkaf da gumi, dafe kanshi yayi yana jujjuya wa, ji yayi kanshi ya mishi nauyi, duniyar ta mishi zafi, kallo d'aya zaka mishi kasan yana cikin tashin hankali.
Da sauri mum ta zauna k'asa kusa da shi ta rik'e hanun shi, matse hanun shi tayi da k'arfi sannan tace" me yake damunka Haseen? Faɗa mun menene?"
Cikin kuka ya fara faɗin" mum Haseenah ce, wallahi tana raye, jikina yana bani wallahi tana nan"
D'ago ido mum tayi ta dubi dad dake tsaye duk tausayin Haseen ya rufe shi, kasa magana shi kan ma yayi.
Kallon Haseen tayi cikin san sayyiyar murya sannan tace" son kaga dare yayi sossai ynxu, kayi hak'uri safiya tayi se muyi magana, yanzu ka kwanta kayi bacci"
" Bazan iya ba wlhy, Ni tafiya zanyi neman ta, kuma bazan dawo ba seda Haseenah"
Lokacin tsoro ya kama mum, gani take shikenan ita kam d'anta ya zauce, Aljanu sun shafe shi.
Da k'yar ta saita natsuwar ta sannan tace" kayi hak'uri zamu sa a fara addu'a, in Bata dawo ba sai ka tafi nemanta kaji?"
D'agowa yayi dan tabbatar da abinda take faɗa, gyad'a mishi kai tayi alamar she mean her words.
Wata ajiyar zuciya ya sauke sannan ya jingina kan shi jikin gadon.
Da k'yar ya tashi ya kwanta, sai da ta tabbatar bacci ya d'auke shi sannan suka fice kowa da abinda ke sak'awa a ran shi.
Can kuwa Sameer in Yana gaban Ammi kicin kicin yake da fuska.
Advertisement
Abun dariya yake ba ma Ammi amma tayi banza dashi.
Kwanan su uku bayan an gama aikin Haseenah suka fara shirin dawowa Nigeria.
Dan Mahmud ya d'aga wa Ammi hankaki shidai ta dawo ya gaji.
A dole ta sa suka shiga gari suka yi shopping, kaya sossai ta siya wa Haseenah dan dama ba wani kaya sossai.
Duk inda ya ga ana kallon Haseenah kuwa sai ya hau harare harare.
Ita kan ma bata ma san yana yi ba.
Ana gobe zasu tafi ne Dukansu zaune a palour, sun baje Kaya Ammi nata jerawa cikin akwatina Haseenah kuma na ninke wa.
Sai wajan 12 na dare sanann suka gama komai, da yake jirgin k'arfe 7 zasu bi, dan haka suna gama wa kowa ya wuce ya kwanta.
Da asuba bayan sunyi sallah ba wanda ya koma bacci, wanka sukayi duk suka fito da kaya, driver ya loda kayan sannan suka d'au hanyar airpot.
6:30 suka isa, nan da nan suka fara hawa jirgi.
7am sharp jirgin su ya d'aga zuwa Niger, lumshe ido Haseenah tayi yayin da komai ya fara dawo mata sabo.
K'walla ne ya cika mata idon ta, Umman ta kawai take tunawa da Aaman, ga Haseen d'inta dasu Mummy, Umaimah nd Baby.
A hankali hawayen ke zuba tana sharewa.
A haka bacci yayi awon gaba da ita.
Mahmud kuwa murna ba'a magana, amma in ya tuna da wannan yarinyar wato Haseenah zasu dawo duk sai yaji bayaso.
Da isha suka iso dan haka Mahmud ne ya turo driver d'aukan su, Dan generator Yana ta bashi wahala yaƙi tashi, shiyasa ya fita neman me gyara.
Lokacin da suka dawo Mahmud bai dawo ba, Junaid ne kawai ya musu sannu da zuwa, ya dai ga Ammi da wata bak'uwa amma baiga fuskanta ba dan kanta sunkuye yake.
Shima bai damu ya ganta ba dan jin yanda Mahmud ke kushe ta ya sa baya ma son ganin ta.
Advertisement
D'aki duka suka wuce dan rage kayan jikin su.
Suna rama sallolin su Haseenah ta koma ta kwanta kan gado.
Take away Sameer ya musu dan haka a d'aki taci nata.
Lokacin da Mahmud ya dawo kuma basu haɗu ba, bai ma tanbaya Ammi ina take ba.
Zama yayi ya cika ta da surutu, sai da ta Kore shi tace zata yi bacci sannan ya barta.
Washegari bayan Haseenah ta idar da sallan asuba ta koma ta kwanta saboda har yanzu akwai gajiya, dan haka har Ammi ta tashi ta gama aikin gida.
Ƙarfe 10 Ammi ta shigo Dakin Haseenah ta tashe ta, wanka ta shiga da sauri ta fito.
Dogon riga kawai ta saka ko mai bata shafa ba ta yane kanta da gyalen ta zura takalmin ta, da sauri ta fice dan tasan suna can suna jiran ta.
Mahmud kuwa se ƙananan magana yake wai shi akan wata halitta za.a ajiye su, bayan shi yunwa yake ji.
Babu wanda ya kula shi balle su san yana yi ma.
Kanta sunkuye ta fito, Sameer zuba mata ido yayi yana kallon ta, yayin da Mahmud ya kasa ƙarasa maganar da yake yi, ji yayi numfashin sa ya kusa d'auke wa, duk tunanin shi hala gamo yayi da kyakkyawar aljana.
Dan haka zabura yayi ya mik'e da sauri yayi bayan Sameer, rik'e shi yayi jikin shi na 6ari bakin shi na rawa, fad'i yake " wayyo Ammi kuna ganin abinda nake gani kuwa?"
"Me kenan?"
Be kai ga bata amsa ba yaji ya kusa suma sakamakon kusa dashi da Haseenah tazo Tana neman wajan zama.
Hakan ya sashi sandara wata uwar ihu yana cewa"......
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial9 Chapters
The War Of The Three Regions
In the year 2025 a rift tore between earth and the Nandoria society they invaded with advanced technology and our Heroes have to survive in their world to gain their freedom.
8 96 - In Serial24 Chapters
Pokemon Castaway
A failed league challenger retires to live his days out in relative quiet until a lie and a storm lead him back to Unova to embark on a new journey.
8 165 - In Serial52 Chapters
Not a Genius's Survival Rules
Hello! Do you have any trouble recently? This is a magic novel, as long as you read it, your troubles have 90% chance to solve! No matter you are in any age, you have any trouble, I sincerely invite you to read this novel.I have a biggest wish that girls can get the happiness they want! When life is in trouble, how do we get out of it. I just hope that my experience can bring you some reference and enlightenment. Thank you for watching! This is a story about the campus, the hero through the cultivation of martial arts, save the heroine in the cycle of time and space.
8 332 - In Serial6 Chapters
Sound and Fury - Book 1 of The Rhapsodic Troubadour
Barely average, meek chunk of a human, Dominic, wakes up one day to find that he's been transported to another realm of life, and is being hunted by minions of a Dark God who wants him for... nefarious purposes. This is a LitRPG work in progress. I welcome feedback.
8 106 - In Serial143 Chapters
Jam Fest Book Club
Looking for more helpful comments, steady reads, and good friends? Look no further! Here at Jam Fest, we're a community of close-knit members dedicated to helping one another in this chaotic journey we call writing. With a unique reading group process, we aim to get your entire book reviewed by hard-working adults like yourself. If you put in the time and effort, you'll gain more than feedback, you'll gain a meaningful place in our festival of friends, no matter which genre you jam out to. Currently accepting applications. (18+)
8 140 - In Serial64 Chapters
One-Eighty || Taekook
"Can't you be nice?""Are you trying to make me laugh Kim?"~In which Taehyung, a new and hardworking lawyer, gets the case of his lifetime but pretty quickly finds out why nobody else wanted to take the case of the countries most dangerous gangleader who has no desire to help Taehyung at all.~Complete~
8 199

