《HASEENAH》PAGE 75&76
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*75~76*
Cikin Baccin tayi mafarkin Haseen, wai bashida lafiya mutane tsaye akan shi, banda sunan ta ba abinda yake kira, ita kuma ta na can gefe tana lek'en shi cikin kuka, ba wanda yake ganin ta sai shi kaɗai, miƙa mata hanu yakeyi tazo kusa da shi, amma bata son mutane su ganta, hawaye ne sharkaf a fuskanta tana kuka.
Mum Haseen ta gani durk'ushe a kan k'afarta tana furta " son karka tafi ka barni dan Allah , karka manta kai kadai muke da shi"
Tana maganan ne ta damk'e hanunta cikin nashi, k'ank'ame hanun nata shima yayi cikin ƙarfin hali yana son nuna mata Haseenah amma ya kasa d'aga hanun.
Ana haka kawai hanun Haseen ya silale ya fad'i alamar rai yayi halinsa.
Mum Haseen ne ta kurma ihu tana faɗin" wayyo my son karka mutu ka barni"
Haseenah da gumi gaba ɗaya ya jik'a ta ganin abinda ya faru ya sata farka wa a razane haɗe da kurma wata irin ihuuu *Haaaaseeen*
A firgice ta tashi tana waige waige gashin kanta duk ya wargaje, toshe bakinta tayi da duka tafin hanunta lokaci ɗaya kuka ya su6uce mata.
Ba tare da ta sani ba ta fara sambatu" wayyo Allah Haseen karka tafi ka bar....
Cak ta tsayar da maganar ta mik'e da sauri cike da mamaki, inba hauka tayi ba kaman ji tayi tana magana ko?
Abinda ta tanbaya kanta kenan, dan tabbatar da abinda take zargi ta sake cewa" Ummah na"
Ya subhanallah, she can't believed that, is she dreaming?
Duk da haka bata yarda ba, a hankali ta shiga toilet ta bud'e pampon jacuzzi, Nan ta Fara jin ƙarar ruwan, juyawa tayi ta kalli mirror bathroom din, wanke fuskanta tayi sanan ta sake kallon madubin, still she can't believe that, Dan Haka ta fara muna kayan ban d'akin one after d other tana fad'an sunan su.
Nan ma gani take duk k'arya ne, dan haka ta fito ta dauka gwangwanin coke ta buga a ƙasan tiles d'in, jin ya bada sauti ya sata daka wata uwar tsallen murna.
Advertisement
Zubewa tayi a ƙasa haɗe da yin sujuddus shukur, nan ta fashe da wata irin kuka.
She never think or thought a day like this will come, buh what a sudden coincidence, oh Allah Alhamdulillah.
Toilet ta shige ta yi alwala, ganin lokacin 3:30 na dare ya sata shimfid'a sallaya ta fara jero nafilfili tana godiya wa Allah.
Addu'oi kam ranan ta yi su kaman bazata dena ba, tana yi tana kuka, addu'a take wa Umman ta, tana rok'ar mata rahamar Ubangiji.
Nan taji kewar gida ya kama ta.
Seda aka kira sallar asuba sannan ta mik'e ta kawo raka'a biyu.
Nan ta koma ta kwanta, kasa bacci tayi dan yau ji take kamar duka damuwarta sun tafi.
Gani take ba wanda yau zai gwada mata murna.
Amma tayaya zata sanar wa Ammi?
Wata dabara ce ta fad'o mata dan haka ta saki wata murmushi.
Nan baccin dad'i yayi awon gaba da ita.
Wajen ƙarfe 7 na safe ta farka, miƙa tayi haɗe da salati sannan ta tashi.
Jikin mirror ta nufa ta dubi kanta a madubi, murmushi ta saki haɗe da faɗa wa kanta
"hi Haseenah"
Abun sai ya bata dariya ganin tana k'ok'arin zaucewa.
Toilet ta wuce tayo wanka cike da nishad'i, ta fito nan ta zauna ta shafa mai ya feshe jikinta da turare, dogon riga ta zura sannan ta daura mayafin shi, yan kunne manne ta sanya da zobe da wrist watch.
Ba k'aramin kyau tayi ba, dan haka ta kama hanyar fita ta nufa palour dan tasan yau Monday da wuri y'an gidan zasu fita.
Bata samu kowa a palour ba dan haka juyawa tayi ta nufa d'akin Ammi, a hankali ta kutsa kai ta shiga kaman yanda ta saba.
Ammi ta hango ita ma tana k'ok'arin fito wa.
Dan haka kawai ta sakar mata murmushi yanda suka saba gaisawa kenan.
Wannan karon Ammi yak'e kawai ta mata dan ita sam tafison ta mayar da Haseenah gida, in ba haka ba kuwa lokaci ɗaya gidanta zai wargaje.
A sanyaye Haseenah ta juya Ammi tabi bayan ta, dining suka nufa dukan su.
Suna zama su Mahmud ma suka iso, dan haka duka idon su a kanta yake.
Bayan sun zauna ne Sameer ya dubi Ammi yace" mrng mum"
"Mrng"
Ta amsa mishi a tak'aice, yasan dalilin hakan dan haka bai ce komai ba , nan Mahmud ma ya gaida ta, shima ba yabo ba fallasa ta amsa.
Advertisement
Nan kowa ya fara cin abincin shi, lokaci lokaci sai su kalli Haseenah dukan su.
Tana gamawa ta koma kan sofá ta zauna tana kallon TV.
A gurguje Sameer ya koma sama ya d'auko brief case d'inshi, d'ayan hanun sak'ale da ward coat dinshi.
Ganin ya kusa latti gashi yau Monday ba ƙaramin hold up zai samu a hanya ba, duban Ammi yayi yace" Ammi na tafi sena dawo"
"Allah kiyaye hanya" exclaims Ammi.
Mahmud dake faman cika yana batsewa Ammi ta dubeshi sannan ta dubi Haseenah, ganin hankalin Haseenah baya wajan su ya sanya ta fara cewa.
" Dukan ku na kula da take taken ku, to wallahi tun wuri kusan yanda dare ya muku, dan babu wanda zaiyi gigin kawomin wata maganar banza kan yarinyar da ba kusan inda ta fito ba, kanaji ko?"
Gaban Haseenah ne ya bada daaammm.
Tsoro ya cika ta jin abinda Ammi take faɗa, bata gwada alamar taji abinda suke faɗa ba tunda dama ba wanda yasan tana ji yanzu.
Nan Ammi ta cigaba da ja wa Mahmud kunne ta ƙare da cewa" bari Sameer ya dawo shima zan ja mai kunne, in Kuma Baku ji ba to duk zan d'au mataki a kanku"
Tunda ta fara maganar bai ce komai ba, dan shi baya jin akwai wanda ya isa ya hana shi son Haseenah ko auran ta, sedai duk abinda za'ayi ayi.
Duban shi tayi sannan tace" ba dakai nake magana ba?"
Cike da jin haushi ya dube ta sannan yace
" to dan Allah Ammi what did u want me to say? atleast am matured enough to choose d ryt nd perfect partner for my self, am not a child anymore, so nidai kiyi hak'uri I can't live without her, Dan Ina sonta".
Yana gama faɗin haka ya mik'e ya nufa hanyar d'akin shi.
Cike da mamaki da tashin hankali ne ya bayyana ƙarara a fuskar Ammi, kiran sunan shi ta fara yi akan ya saurareta ya dawo amma ko juyowa baiyi ba ya shige d'aki, ƙarar bugo k'ofar taji ya danna key.
Dafe kai Ammi tayi tana furta innalillahi wa inna ilaihir raji'un, na shiga uku Ni Fatima.
Wannan wace irin masifa ne?
Haseenah da lokaci ɗaya taji tsoro ya shige ta ganin abinda ya faru, mik'ewa tayi ta bar wajan da sauri dan kar Ammi ta gano halin da take ciki.
D'aki ta shige ta kulle k'ofa ta saki kuka.
Ta rasa kukan me take, na farko ba son Mahmud take ba ballan tana tace kukan zafin rabuwa dashi take, sannan na biyu kuma ba haushin Ammi ta ji ba tunda gaskiya ta faɗa, basusan ita wacece ba haka suka rungume ta suka tallafa ma rayuwarta.
Ita lokaci ɗaya taji tsabar tsanar Mahmud, inta tuna irin wulak'anci da cin fuskar da yayi mata a baya.
Sannan batajin son Sameer ko kaɗan cikin zuciyar ta, tana mishi kallon yayanta ne, dan haka duk bata da case da su.
Haseenah bata fito cin abincin rana ba, Ammi ma bata damu ta nemo ta ba, dan itama damuwar da ke faman tunkaro ta ya ishe ta.
Mahmud ma bai sauko ya ci ba, Sameer dama sai yamma zai dawo.
Dan haka palour babu kowa sai ƙarar AC dake tashi.
Bayan anyi sallar magrib ne suka fito.
Ammi ko kallon inda Mahmud yake bata yi ba, shima baice komai ba.
Dan haka zaman kurame akayi kowa na gamawa ya tafi abin shi.
Washegari Sameer bazai fita aiki ba dan haka basu tashi da wuri ba sai 10am.
Wanka yayi ya sanya Black jeans da riga red colour an rubuta handsome a gaban.
10:30 suka fito dan cin abinci.
Mahmud ne ya gaida Ammi ta yi banza da shi.
Hakan ya ba ma Sameer mamaki, shima ya gaida ta a dak'ile ta amsa.
To me hakan yake nufi?
Bayan sun gama cin abinci ne kowa ya koma ya zauna.
Sameer ne ya dubi Ammi kanshi a ƙasa ya fara cewa" Ammi Please i want us to talk"
Ba tare da ta kalle shi ba tace
" am all ears"
" Ammi Ni da ke kawai nake son muyi maganar kuma ga Mahmud zaune"
"Atleast shima he's part of d family so just say it"
Exclaims Ammi.
Jikin shi ya fara sanyi da irin amsar da Ammi ke bashi dan haka kaman zai fasa sai kuma ya tuna, to tunda Mahmud na wajan ai this is d ryt time da Yakamata ya faɗa, so that in ma akwai wani abu a ranshi ya cire.
Dan haka ya fara da cewa"......
First comments 08144932303
Advertisement
- In Serial1363 Chapters
VRMMO: The Unrivaled
Lu Chen used to be a ranker of the most popular VRMMO game, Spirit of Grief. After a car accident turned his dreams into dust, his disability left him incapable of escaping the pit of mediocrity he was thrown into. Helpless and defeated, his story ended.Two years later, the Eternal Moon Corporation launched a new VRMMO called "Heavenblessed", and Lu Chen stumbled into another terrible accident that left him in a complicated situation far beyond his ability to handle. That won't stop him from rising to the top, however. Not again.Come witness the rise of the sword-wielding zombie and the relationships he makes during his journey to the apex! For riches and bi- ahem, for career and love!He wields a demonic sword from Hell, he dons armor shining with Heaven's light. His boots stride across the sky as his helmet devours the souls of his enemies. On his left side sits the Goddess of Death. On the other, the Angel of Beauty.From the land of ice and death, a generation of Asura Kings rises, their roars reverberating throughout the world.Tremble in fear, noobs!
8 8156 - In Serial1353 Chapters
Refining the Mountains and Rivers
A young man's life changes when he stumbles upon a mysterious item. Qin Yu had never been a lucky person. Weak of body, bullied by his peers, and with only his friend as his family, he struggles day-by-day to live. But everything changes when he stumbles upon a little blue lamp. An immortal and demonic cultivating adventure.
8 3345 - In Serial2455 Chapters
Mortal Cultivation Biography
A poor and ordinary boy from a village joins a minor sect in Jiang Hu and becomes an Unofficial Disciple by chance. How will Han Li, a commoner by birth, establish a foothold for himself in in his sect? With his mediocre aptitude, he must successfully traverse the treacherous path of cultivation and avoid the notice of those who may do him harm. This is a story of an ordinary mortal who, against all odds, clashes with devilish demons and ancient celestials in order to find his own path towards immortality.
8 1051 - In Serial1503 Chapters
Dragon Prince Yuan
Destiny stolen at birth, the prince of the once mighty Great Zhou Empire, Zhou Yuan, has been plagued all his life by a fatal poison, forced to suffer powerlessly until one day when fate draws him into a mysterious domain where he meets a beautiful girl in green, a bizarre dog-like creature and an unfathomable old man in black.Join Zhou Yuan as he is thrust into the whirlpool of destiny while he seeks the pinnacle of cultivation.
8 1058 - In Serial677 Chapters
Ranker's Return
In the early days of the virtual reality game, Arena, meleegod was the strongest ranked player! He deleted his character and suddenly left. In order to restore his bankrupt family, he returned to Arena!"Do you want to create a character?"
8 1715 - In Serial1525 Chapters
Monarch of Evernight
Qianye rose from hardship but was felled by betrayal. From then, one man, one gun; he tread the path between Evernight and Daybreak and became a legend. Even if Evernight was destined to be his fate, he still intends to become the ruler who dictates.
8 22865

