《HASEENAH》PAGE 91&92
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*91~92*
Washe gari da sassafe Mummy ta fara buga ma Haseenah k'ofa, cikin bacci Haseenah taji kaman k'arar abu, a hankali ta bud'e ido dan jin menene, ji tayi bugun k'ofar ya tsananta, da sauri ta mik'e ta nufa palour a tunanin ta abban ta ne, bud'ewa tayi dan ganin waye, turus ta ja ta tsaya ganin Mummy tsaye ga kuma saratu a bayanta tana faman yatsina fuska.
Juyawa tayi ta kalli agogon palour k'arfe 8:05 na safe, sake juyowa tayi ta dubesu tace "lafiya?"
"Lafiyar ce ta kawo haka"
Inji Mummy.
Nan mummy ta cigaba da cewa" ki shiga kitchen ki had'a min breakfast yanzu dan yunwa mukeji"
Wani irin murmushi Haseenah tayi sanann tace" to ba damuwa"
Komawa tayi ta kulle d'akin ta hau gado ta cigaba da baccin ta.
Ita ma Mummy d'aki ta shige ita da saratu suka koma bacci dan a tunanin su in Haseenah ta gama zata tashe su.
Se k'arfe 9 su Haseenah suka tashi, nan suka soya chips da doya sukayi kunun gyad'a sanann suka dafa Lipton, Dama wa Aaman custard sukayi sanann kowa ta shiga wanka.
Baby ce ta tashi da niyar jera musu abinci a dinning, da sauri Haseenah ta dakatar da ita sanann tace" yau a main palour zamuci ku tashi mu fita"
Da mamaki suka dubeta, gyad'a musu kai tayi alamar eh.
Ba musu suka kwashi flask suka nufa palour Aaman na bin su a baya.
Zubewa sukayi kan carpet dukansu.
Haseenah ce ta mik'e ta shiga kitchen ta kwaso warmers guda uku da Flask da mugs ta jera kan dinning d'in palour sanann ta dawo da zauna suka fara ci.
Jin hayaniya ya sanya Mummy da saratu fitowa dan yin breakfast.
Tsayawa tayi ganin yanda suka baje a palour suna faman cin abinci suna hira.
Bata kulasu ba suma ba wanda ya kulata, Mummy da saratu ne suka nufa dinning ganin an jera komai a kai da niyar cin abinci.
Ko kallon su Haseenah bata yi ba sai b'ata rai ma da tayi.
Bud'e cooler saratu tayi da niyar cin abinci amma me zasu gani?
D'anyen dankali ne a ciki a ka yanka da doya aka zuba a ciki, dayan cooler Kuma fulawa aka zuba an kwa6a da ruwa.
Advertisement
Sai k'aramin Kuma Lipton da citta aka zuba.
Duka kasa magana sukayi, Mummy ranta ya Kai mak'ura wajan 6aci, mik'ewa tayi ta dubi Haseenah tace" ke dan ubanki wani irin iskanci kenan? Ina abincin yake?"
Haseenah kaman ba da ita sukeyi ba.
Hakan ya sanya saratu matsowa wajan su ta dubi Haseenah tace" ke dan uwarki ana miki magana shine kikayi banza da mutane ko dan ba uwarki bace?"
Mik'ewa Haseenah tayi ta d'auketa da wani wawan mari, ta sake kwad'a mata mari à jere guda biyu sanann tace" karki sake kiran uwata a cikin rashin kunyar ki, in ba haka ba wlhy zan miki illa"
Gigicewa saratu tayi ganin jini na fita a hancin ta.
Mummy kuwa da tayi mutuwar tsaye se yanzu ta zaburo da niyar dukan Haseenah, Baby ne da Umaimah suka shiga gaban ta sanann Umaimah tace" karki kuskura ki ta6a ta wlhy in Kuma kika bigeta wlhy semun maimaita miki abinda ya faru a baya zuwanki gidan mu"
Cak Mummy ta tsaya kuma ta kasa sauke hanunta.
Murmushi Haseenah tayi sannan tace" da baku dakatar da ita ba, Mummy a baya kin mun abinda kika ga dama, to ina so ki sani lokacinki ya k'are, yanxu nawa ya fara, ki ja girmanki da mutuncin ki sai a zauna lafiya, in Kuma ba haka ba, wlhy in kin mun sau d'aya sai na miki biyar"
Mamaki da tsoro ne ya cika Mummy da saratu, kasa magana duka sukayi banda saratu da ta toshe hancin ta da gyale dalilin jinin da ke zuba.
Komawa sukayi suka zauna suka cigaba da cin abincin su kaman babu abinda ya faru.
K'wafa Mummy tayi ta kama hanyar d'akin ta zuciyar ta fal 6acin rai.
Kai kawo ta rink'a yi ta kasa zama, gani take kaman abun Film ne ko mafarki ne oho.
Anya wanann Haseenah ce kuwa? Kai ina to in ma itace gaskiya akwai aljanu a tattare da ita.
Saratu da hancinta gefe d'aya ya aune ya kumbura ta kalli Mummy sannan tace" mummy meyasa Kika barta kina ganin abnda tamun dan.....
Tsawa Mummy ta daka mata sanann tace" dan ci ubanki in Kika sake mun magana shegiya jakar mata, meyasa ke kina gani ta bigeki ta ci mun mutunci baki rama mana ba saini ne kike tunanin xan kar6a miki faɗa?"
" To Mummy Dan...
Katseta tayi da cewa" wallahi saratu kika kuskura kika sake mun wata magana sena canja miki halittar baki yar iska kawai, tashi ki fita tun kafin in kakkarya ki"
Advertisement
Sum sum saratu ta fice tana k'ananan surutu.
Waya Mummy ta d'auko ta kira k'awarta.
Nan ta kwashe mata abinda ya faru, nan ta ce mata tana zuwa ta shirya zasu fita zuwa wajen boka.
Ba musu ta tashi ta shirya jiran zuwanta kawai take.
Within 30mns ta iso nan suka fantama gari.
Mummy ce da Aminiyar ta zaune gaban boka yana ta faman zane zane, duban Mummy yayi sanann ya cigaba da hidimar sa, ya riga da ya sani abinda suke buk'ata ba samuwa zaiyi ba, amma ganin yanda Mummy ta d'aga hankali kuma jin tace zata iya bashi ko nawa ne a haukatar da Haseenah sanann a kashe Aaman Haseen Kuma ya koma son saratu ganin yanda saratu ko yaushe take damunta tana son Haseen d'in,
ya San hakan ba mai yiwuwa bane amma ya gyara zama yace wa Mummy" aikinki ya gama saura biya"
Nan Mummy ta Ciro bunch na d'ari biyar guda biyu ta zube mishi.
Da sauri ya kwashe sannan ya d'auko wani d'aurin magani guda uku ya mik'a wa Mummy yace d'aya ta barbad'a a k'ofar d'akin Haseenah da sassafe, d'ayan kuma ta zuba a harabar gidan wajan da tasan Haseenah na takawa d'ayan kuma kwalli ne yace ta ba saratu duk lokacin da ta tabbatar Haseen ya zo ta saka a idon ta in dai sukayi ido huɗu to magana ya k'are.
Nan ya sake d'auko wani turare a k'aramin kwalba yace shima ta shafa in ya zo.
Murna ya cika Mummy Nan ta fara godiya gani take damuwarta ya yaye.
Nan suka fice, kana kallon Mummy kasan tana cikin nishad'i.
Basu suka dawo ba sai yamma.
Saratu kuwa abokan yawon ta sun kirata amma tace bazata samu fitowa ba wai tana aiki, hakan kuwa bataso suga illar da Haseenah tayi mata ne.
Da magrib Mummy ta shigo gidan, su Haseenah ta gani yanzu ma baje a palour suna kallo suna shan fruits salad.
Sai Haseen dake zaune kan sofa yana ba Aaman chocolate.
Ba Wanda ya kulata itama wucewar ta tayi, a ranta kuwa fad'i take wataran fa Haseen da saratu zasu zauna haka, zuciyar ta ta bata amsa da kamar yanzu ma kuwa.
Murna da dad'i ya cika Mummy ita nan dole saratu zata aura Haseen, ga kyau ga kuɗi ga kuma aji.
Young millionaire kenan.
Ita kad'ai tayi murmushi sanann ta wuce ciki.
D'akin saratu ta nufa ta ganta kwance kan gado.
Duka da sakar mata a cinya tace" ke tashi dan ubanki kwanciya bai ganki ba"
Da sauri ta tashi had'e da tura baki tace" inaji"
Nan Mummy ta Kora mata bayani sannan ta ciro kwalli da turaren ta bata.
Da murna saratu ta kar6a, nan taji duk wata damuwar ta ta kau, Haseen ya zama nata, mafarkin ta ze zama gaskiya.
Rungume Mummy tayi tana murna.
Nan Mummy ta dad'a ja mata kunne kan ta nutsu.
Mik'ewa saratu tayi tana k'ok'arin shafa kwallin, rik'e hanun ta Mummy tayi tace " meye haka kuma?"
" Shafawa zanyi wallahi ai yanzu yana nan in ya ganni kinga shikenan komai ya tsaru"
Tsuka Mummy ta ja sanann tace" ke wallahi na rasa wata irin k'wak'walwa ce da ke, za a miki bayani kaman kin gane amma ina, da rana zaki shafa ko da safe yanda zai ganki da kyau doluwa kawai"
Tura baki tayi sannan tace" to Mummy Dan Allah ke sai kin zageni ne ba zaki iya yin shiru ba"
Tsuka Mummy ta ja ta fice daga d'akin dan yunwa take ji...
Washegari da asuban fari Mummy ta fito ta barbad'a magananin a k'ofar d'akin Haseenah, sanann ta nufa wajan motar ma ta zuba d'ayan ta dawo d'aki.
Kasa komawa bacci tayi dan ita yanzu result kawai take jira in gari ya waye.
Su Haseenah ko se kwasar bacci suke abunsu hankali kwance.
Sai wajan 10 suka tashi sanan suka fara gyara gidan.
Jin an bud'e k'ofa ne ya sanya Mummy bud'e labule Dan ganin meye.
Baby ta gani rik'e da tsintsiya a hanunta alamar zatayi shara.
Da sauri Mummy ta duro a kan gado ta fito dan dakatar da Baby amma me, Baby har ta fara shara.
Wata uwar tsawa Mummy ta daka mata tace" ke wata irin jaka ce da zakizo kina shara ma mutane da sassafe iye?"
Mamaki ne ya cika baby to Ina ruwanta ta sharanta kuma?
Duban ta baby tayi sanann tace" wata irin jaka ce Ni? Irin ta waccan d'akin ce Ni"
Ta nuna d'akin Saratu.
Ran Mummy yayi matuk'ar 6aci, tsuka ta ja ta juya shknan yarinyar nan ta wargaza mata shirin ta na yau.
Yanzu ba don tana da sauran maganin ba da shkann ta rasa, dama boka yace babu k'ari in ta zubar.
D'aki ta koma ranta a 6ace tana surutu......
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial11 Chapters
Feral: The Story of a Half Orc
Char has lived in Jarvin his entire life, subjected to hatred and suspicion for his Half-Orc heritage. He avoids the crowd, only wanting to focus on his blacksmithing and runes. Right up until the girl who is prophesized to save the world decides to become his friend, pulling him into assassination plots, conspiracies, and caves full of giant spiders. Yay?
8 164 - In Serial52 Chapters
Hero Soul: Jetriser
Erin was only weeks away from finishing college and starting her life in earnest, so dying was inconvenient, to say the least. Thrust into a new life in the magical world of Jetriser, she must scramble to survive a botched reincarnation in a less than newb-friendly region. Hiatus: I'm in the process of moving and changing jobs, all of which is happening rather unexpectedly, so I'm sorry to say the story will be on hiatus until I get settled.
8 145 - In Serial58 Chapters
Hero Scout
Powerful criminals are to become villains and bring catastrophe. All 18 are sent into a Fantasy world using a Quantum machine called the Medusa. Yet one dies prematurely, his corpse turned to stone. Kenji, the cunning gamer, is brought in to replace him. A master of strategy, quick thinking, and quicker with his silver tongue, Kenji the gamer is set into the death-game a tad confused. With nothing but his ability at gaming up his sleeve, Kenji is expected to out-think his enemy and prove them fools through his fantastical schemes. All 17 crime lords are given powerful starting abilities, hellish and heavenly, designed to unleash destruction upon the people of this new world. Yet Kenji alone is singled out, and after some quick thinking, attains a new title. Instead of being a new villain of this fantastical world, he'll scout out and protect budding heroes from the crime lords wrath. Kenji will become... The Hero Scout!
8 407 - In Serial12 Chapters
PriCore Academy - Status : Zeros
In this fantasy world, if you want to get your status, build your skills, level up? Then you have to go to school. Pricore academy where graduates can reach mythic levels of power and ready their lives as that of heroes, adventurers, and possibly so much more. But they all have to start from somewhere. Zeros until they get their first level. Authors Note: This is my first attempt at a serial and my plans are to release one chapter a week in the beginning. I have a few books, but you probably haven't heard of them. I mostly want to get my stuff out there to be read and this will be my attempt with this community.
8 168 - In Serial579 Chapters
The Journey to find the New Golden Emperor
As someone is transmigrated, you learn most of the world through their eyes and who maybe close to her.Sahara has lived and died once before, making her adapting nature look strange and unfitting. In this new world she is a father’s daughter and adopted grandchild to the same man…Go ahead and laugh, she did…Sahara doesn’t want to put up with nonsense, like getting picked on just because she is smarter than the average person her ‘age’…I mean, she did transmigrate, so of course she’s smarter than what her body’s age should be!Nonetheless, this world is a dog-eat-dog world, a world where only the strong survives, and so, there are times when a darkness inside of her is used to keep herself and her loved ones safe… Over a century ago, there was a Golden Emperor, and a golden bridge that connected all the Haven’s together…Now there is no Golden Emperor and there is no Golden Haven…To become the one and only Golden Emperor though, one must get the trust of all the Haven’s to accomplish that feat once again…And so, we continue this journey as the strange occurrence of transmigration has happened…Which only leads to a fate that had started long ago…
8 493 - In Serial53 Chapters
One More Time
Ranked 1 in #asian on 09.05.2020 1 in #forced marriage on 29.06.2020 1 in #hope on 20.2.2020 1 in #Kolkata on 24.10.2019 1 in #second marriage on 16.10.2019 1 in #bengali on 25.10.2019 1 in #marriageproblems on 15.10.2019 1 in #positive on 14.1.2020 1in #patience on 15.1.2020 1 in #onesidedlove on 20.2.20Koustav Mallik,27, lost his wife and unborn child in a road accident 3 years ago.Ria Basu,21, a student....she had a crush on Koustav...but her dreams were shuttered after koustav's wedding...After 3 years, Ria and Koustav are married .....Checkout this book to see Ria and Koustav's journey together.
8 129

