《HASEENAH》PAGE 93&94
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar chuchu (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*93~94*
Wuni ranan Mummy tayi tana zage zage, saratu kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta shiga ta fita duk tana jiran zuwan Haseen.
K'arfe 5 na yamma kuwa Haseen ya iso, fita Haseenah tayi ta ajiye musu plastic chair dake ajiye a harabar gidan ta gefe wanda aka ajiye domin zama.
Umaimah ce ta kawo mai ruwa da drink da snack d'in da sukayi yau ta ajiye mishi.
Kallon ta yayi yace" ku dai ba a rabaku da wanan abu sannun ku da aiki"
Dariya tayi sanann tace" wanann aikin Aunty Haseenah ce"
Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba.
Zuba ma Haseenah ido yayi yana kallon ta, sunkuyar da kai tayi tana Wasa da yatsun ta, kusan wasu mintuna suka d'iba a haka sanann ya daure yace" meyasa bakiso nayi ma daddy maganan auran mu? Ko dai yanzu kin dena sona ne?"
Da sauri ta d'ago ta kalleshi jin abinda ya furta.
Gyad'a mata kai yayi alamar eh.
Ganin batada niyar magana ya sanya shi cewa" tunda baki son magana dani shikenan barina tafi"
Mik'ewa yayi da niyar tafiya da sauri batasan lokacin da ta rik'o hanunshi ba.
Tsayawa yayi cak ya kasa motsa wa, da sauri ta saki hanun a hankali ta furta" am so sorry plx ba abunda kake tunani bane, amma ba komai gani nake kaman yayi wuri, amma ka samu Mummy Zuwaira ka sanar da ita duk yanda kukayi dai dai ne"
Sai alokacin yaji wani sanyi a ranshi, bai san lokacin da ya koma ya zauna ba, duban ta yayi sanann ya ce" Are U serious?"
Advertisement
Gyad'a mishi kai kawai tayi itama tana murmushi k'asa k'asa.
Nan ya fara cin snacks sunayi suna hira, jifa jifa take amsa mishi.
Can ta nisa tace " yaya Haseen dama inaso na maka magana kan komawa ta makaranta ne"
Duban ta yayi sanann yace" nima naso miki magana to amma se nayi shuru saboda nayi tunanin karkice daga dawowarki baki huta ba shiyasa"
Girgiza kai tayi alamar a'a.
" To ai ba a ciro result d'in naki ba"
" Eh zanje in Ciro"
" No ba saikin je ba in Zan tafi ki d'aukomun slip d'inki in tafi dashi"
Cikin jin dad'i ta amsa da to Nagode.
Nan suka cigaba da tattaunawa.
Can cikin gida kuwa saratu ce ta tsala wanka ta fito ta sanya kaya, zama tayi gaban mirror ta shek'a kwalliya, turaren ta d'auko ta bulbule shi duka a jikinta, ita kanta warin turaren be mata dad'i ba amma ya zatayi.
Kwallin ta bud'e ta shafa har yana gangaro wa, abun ba kyan gani.
Mummy ce ta shigo ta fara mata masifa me take jira da bata fita ba.
Nan saratu ta kalli kanta a madubi yanda tayi sai kace balamar rago, duban Mummy tayi tace" dan Allah Mummy ki ganni fa?"
" Dalla ki fita damuwar mu a samu biyan bukata, ko kin daina sonshi ne?"
Girgiza kai tayi.
Nan ta fice ko gyale babu, Baby da Umaimah dake zaune a palour suka ga fitowar ta, kasa gimtse dariyar sukayi suka tuntsire da dariya, Baby har da hawaye..
Ko kulasu batayi ba ta fice, Haseen da Haseenah ta hango zaune gefe, nan ta canja taku har ta k'arasa basu sani ba.
Warin turaren ta ne ya bugi hancin su , da sauri Haseenah ta dubi waye me wanann warin? Ido biyu sukayi da Haseenah, sunkuyar da kai Haseenah tayi tana dariya k'asa k'asa.
Advertisement
Haseen kuwa zuba mata ido yayi yana kallon ikon Allah...
Ita duk tunanin ta tarkon tane ya kama, dan haka ta hau rausaya tana fari da ido.
Dariya ma shi abun ya so ya bashi.
Kujera d'aya taja wanda ke gefen Haseen ta zauna.
Lokacin ranshi ya fara 6aci ga warin ya fara damun shi.
Dubanta yayi yace" ke lafiyar ki kuwa?"
Cikin wata murya tace" me ka gani yaya Haseen?"
Tooo fa, yau ga ikon Allah .
Ji yayi kaman zeyi amai hakan ya sanya shi toshe hanci ya dubeta yace" ke kinada lafiya kuwa? Rabon ki da wanka sati nawa? Kinji warin da kike yi amma kika iya shiga mutane?"
Sororo tayi ta na jin kalaman Haseen kaman yana zuba mata wuta..
Ganin yanda ta zuba mishi ido hakan ya sanya shi daka mata tsawa yace" ki dena kallona da wannan idanun naki marasa kyan gani"
Kasa daurewa tayi ta fashe da kuka ta mik'e ta shige ciki tana matsanancin kuka.
Baby da Umaimah suka sake kallon ta ganin duk hawaye ya jik'a kwallin da ta lapta ya gangaro sai kace wata boka.
Dariya suka sake yi sanann Umaimah tace" ga dukkan alamu maganin baiyi aiki ba kenan"
Dariya suka sake yi suka tafa.
Nan saratu ta sake cika tayi fam.
Mummy na jin kukan ta ta fito da sauri ta iske ta kan gado tana kuka.
Zama tayi tace" meye ne kuma?"
Cikin kuka saratu ta fara kora mata bayani...
Ran Mummy ya sake 6aci ta d'auka waya ta kira Aminiyar ta, ko gaisuwan arziki basuyi ba Mummy ta fara surfa masifa" amma wanann bokan d'an iska ne, abinda ya bamu ba wani aiki sai cin mutunci"
Da k'yar da shawo kan Mummy sanann tace" to ko dai batayi amfani dashi yanda ya dace bane?"
" To ina zan sani yanzu kam Ni talatu"
Duban saratu tayi tace " kinyi amfani dashi yanda nace?"
"Eh"
Kashe wayar Mummy tayi tace" karki damu k'ila an samu kuskure ne gobe zamu sake jarabawa, in Allah ya yarda kin aure shi an gama"
Dad'i ya cika saratu nan ta manta cin mutuncin da Haseen ya mata.
Sai wajan magrib Haseen ya kar6a slip d'in Haseenah sanann ya fito musu da kayan k'walamar da ya kawo mata ya tafi..
Kai tsaye gidan Mummy Zuwaira ya wuce, bayan sun gaisa ne ya sanar mata da abinda ke tafe da shi. .
Sossai taji dad'i nan tace ya sanar da daddyn shi duk yanda suka tsara shkann zata sanar ma Abba.
Cike da murna ya koma gida.
Bai 6ata lokaci ba nan ya sanar da daddyn shi, daddy ya ce ba damuwa ya faɗa ma Haseenar jibi zasuzo neman auranta.
Tsalle Haseen yayi ya rungume daddyn nashi yana godiya.
Mamaki abun ya ba daddy da Mummy duka, dan rabon da su ga farin cikin Haseen haka its been a while, tun kafin Haseenah ta 6ata.
Murna yayi tayi ranan da k'yar ya iya bacci, tunanin Haseenah ne ya sa shi gaba, sai yanzu yake dana sanin meyasa bai siya mata waya ba?
Nan ya ba kanshi amsa nan da kwana uku zai siya mata in Allah ya yarda.
Haka ya kwana cikin shauk'i da farin ciki, hango irin rayuwar da zaiyi da abar k'aunar shi kawai yake.
Nikuma nace Allah ya nuna mana Ameen....
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial21 Chapters
Zeke Herald, Goblin Slayer
Zeke wakes up inside a small cavemouth, no memories or direction, just the will to live. Also, he's smack dab in the middle of a forest that's teeming with ugly little goblins. The only good goblin is one with a sword sticking out of it, as my father used to say. I tried to incorperate LitRPG elements. I'm only recently introduced to the genre, but I find it really fasinating! So intrigued I even started writing a little story expressing my joy of all things numerical! This story has a focus on hardwork and deliberate progression, no magical deus ex machinas here sorry.
8 136 - In Serial73 Chapters
Sun Collector
Upon entering the age of 16 every person is allowed to request from the gods one ability. In exchange, he has to offer up something of equal value. A class is then assigned to them.
8 171 - In Serial18 Chapters
Dragon's Roar
Follow the story of Logan miles as he plays his first virtual reality game while also dealing with real life problems.Cover art credits to my good friend Ashay
8 110 - In Serial31 Chapters
1974 - A David Bowie Fanfic.
The year is 1974 and Rosalind Chester is an 18 year old girl who is in love with one of the biggest rockstar's of that time, along with a million other David Bowie fans... When Ros decides it's time to leave home to live in Brixton, her whole world changes. "I was just another fan of Bowie's, one of those fans that dreamed of meeting him. But in reality, and the sad truth is, he'd never know I existed. " - Rosalind Chester.But how wrong she was... So what happens when on a normal night out, Ros ends up having a chat with the man she's been in love with for the past 5 years? And how they both change each other's lives within 12 months... Is this the love story of the Brixton Boy and the little Rebel? In loving memory of David Jones (Bowie) - see you soon Starman xIf you enjoyed this story then please go and check out the sequel...! It's called 1984 - link is below! xhttp://my.w.tt/UiNb/kBmGR0vCku
8 253 - In Serial11 Chapters
mario x meggy
Mario and cappy landed in inkopilos and cappy located power moons but Mario saw a familiar inkling. could Mario have feelings for her or not. find out
8 143 - In Serial4 Chapters
Wolfwalkers (Mebh X Robyn Oneshots)
I have no idea what to do with this so it will be a collection of Mebh X Robyn oneshots some based in the modern world and some in the time line of the film
8 139

