《HASEENAH》PAGE 111&112
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story & written
By👇🏻
'''Aysher Abbakar ChuChu (Meerah)'''
® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
Follow me on Aysherabbakar
*111~112*
idi me gadi ne yayi saurin wangale gate Jin yanda ake horn Ana nanatawa, duk tunanin shi ya d'auka Mai gidan ne ya dawo kuma Yana sauri.
Ganin su Hajiya Zuwaira ya Sanya shi washe bake Yana gaida su Dan ya San yau ze samu 'yan canji.
Nan ko ta ciro dubu uku ta bashi ya rusuna Yana godiya.
Shiga ciki suka yi Nan sukayi parking a parking lot.
Fitowa duka sukayi suka nufa ciki, tsayawa sukayi suna sallama.
Mum da ke zaune kan kujera hanunta rik'e da remote tayi kaman ba ta ji ba, Dan ta gane muryan.
A Karo na biyu suka sake sallama Bata amsa ba.
Abba dake Shirin fita ne ya amsa sannan ya dubi mum yace" Wai ko bakiji ne?"
Kallon shi tayi sannan tace" tunda ka amsa Allah ba da Lada"
Shigowa su mummy sukayi ciki, Abba ya taresu da murna Nan suka nema waje suka xauna ba tare da sun kula mummy ba.
Ta cika tayi fam a tunanin ta zasu gaisheta.
Bayan sun gaisa da Abba ne mummy tace" dama mun kawo Maka Kaya ne ka gani"
Abba se faman washe baki yake yace" to an kawo ne?"
"Eh"
Fita mummy tayi sannan tayi magana wa me gadi da me wankin gidan.
Boot ta bud'e Nan suka cicciro akwatinan suka jera.
Kwasa suka fara yi suna kaiwa ciki mummy na tsaye wajan motar.
Tunda suka fara shiga da kayan gaban mummy ya fara fad'uwa, tanbayan kanta take wannan akwatinan fa?
Seda suka Gama shiga dashi duka sannan mummy Zuwaira tabi bayan su.
Advertisement
Nan aka bubbud'e wa Abba, ba abunda yake fad'i se "tubarkallah Allah Sanya albarka"
Duban mummy yayi da ita ma Satan kallon kayan take ganin yanda aka zuba manyan Kaya da lace's a ciki.
Saurin kau da ido tayi ta cigaba da kallon TV ta.
Fitowan saratu ne ya Sanya Abba kallon ta yace" saratu ga kayan er uwarki an kawo fa"
Cikin rashin fahimta tace" wa kenan Abba?"
" *Haseenah* ya Bata amsa.
Da sauri ta k'arasa taje ta zauna Tana d'aga kayan.
Se Santi take.
Mummy kuwa se aikin harara take watsa mata.
Duban Abba tayi tace" wa zata aura Abba?"
"Dan uwanki mana Haseen"
Tsam ta mik'e ta cire hanunta, had'a ido sukayi da mummy idonta ya ciko da hawaye.
'Daki ta wuce da gudu ta toshe baki saboda kukan da ke Shirin zuwa mata.
Mik'ewa mummy tayi da nufin barin wajan, mummy Zuwaira tace" ladidi ki dawo ki kalli kayan 'yarki ki Sanya albarka ai ma ke muka kawo ki gani"
Kallon banza mummy ta mata sanann tace" me zanyi da kayan tsiyarku, kuje tunda an shiga an fita an shanye mun yaro ta Allah ba taku ba, munafukai matsiyata 'ya'yan Allah bani ko ta halin Yaya...
Tsawa Abba ya daka mata sannan ya ce" ladidi banason rashin mutunci ki Kama kanki"
Harara ta watsa mishi sanann tace" tunda kaima sun shanye ka da ruwan rubutu sun jik'a sun baka ai seka Zo ka rufeni da duka"
Rufe akwati mummy ta fara yi sannan tace" ku tattara mun kayan d'iya Kar a banka musu wuta kaman yanda aka kashemun er uwa"
Aiko Nan mummy ta fara tsalle Tana zage zage ba ji ba gani.
Da Abba ya mata magana ma ta had'a da shi ta fara zagin shi.
Bakinta har kumfa yake d'an kwalinta Yana tintsirewa tsaban bala'i.
Advertisement
Saukan mari taji a kumatun ta Bata Ankara ba har sau biyu.
Duban Abba tayi sanann ta fara magana Tana dafe da kumatu" akan way'an Nan 'yan iskan xaka mareni?"
'Daga hanu yayi ze k'ara mata mummy ta tare shi tace" Abba kayi hak'uri, mukam ai ba bak'in kunya bane, mun Riga da mun San halinta, ta dad'e da Zama mahaukaciyar karya, se hak'uri"
Suna Gama fad'in haka suka sa Kai suka fice.
Abba ma juyawa yayi ya shige d'akin shi ya barta Nan.
Nan ta cigaba da zage zage, me gadi sun shigo zasu d'iba Kaya ma sukai mota ta bisu da wuk'a Wai duk Wanda ya shigo seta kasheshi.
Aguje suka fito daga palour, mummy Zuwaira ce ta dubesu tace "lafiya?"
Nan suka mayar mata da abunda mummy tace.
Aiko mummy suka had'a ido ita da k'annenta biyu.
A tare suka sa Kai cikin gidan mummy tace me gadi su biyota.
Mummy suka gani har yanzu wuk'an na hanunta kanta babu ko d'an kwali sekace mahaukaciya.
Se zare ido takeyi Tana huci.
Aunty Hajara ce tace ma me gadi" ku shigo ku kwashe Kaya ku Kai mun mota inga Wanda ze ta6a ku shege ka fasa"
Nan suka shigo cike da tsoro me gadi ya tsuguna ze d'au akwati, da gudu mummy Tayo kanshi Aiko malam idi ya saka ihu yayi hanyan waje.
Ganin abun bana k'are bane ya sanya su Aunty Hajara da autan su cire gyale suka aje gefe.
Mummy Zuwaira kuwa waje ta nema ta zauna a kujera tana son ganin ikon Allah.
Mummy Hajara ce ta dubi mummy sanann tace" ina kina tunanin ke mahaukaciya ce ko? To mu munfi mayaukaci hauka, in nasa a fita da Kaya ki sake wani yunk'uri kiga yanda xanyi dake"
K'walla wa me gadi Kira ta sake yi.
Lek'owa da Kai malam idi yayi a tsorace yace" Hajiya KU kaita d'aki karta kasheni"
Cikin masifa tace" Dan Allah kazo ka fita mun da Kaya in ga me zatayi"
Ba musu ya sunkuya mummy ta sake zaburowa, mummy Zuwaira dake zaune ta Sanya mata k'afa ji kake dim.
Mummy ta fad'i, d'agowa tayi bakinta har ya fashe.
Duban mummy Zuwaira tayi tace" Kika fasamun baki?"
Girgiza Kai mummy Zuwaira tayi tace" ba haka naso ba, karyaki naso nayi ki gode ma Allah ma, Dan in Kika sake wani rashin hankali wa'yannan zansa su Miki shegen duka"
Ta nuna su mummy Hajara.
Idi Kam Allah ya bashi sa'a ya fara fita da Kaya me wankin na tayashi.
Kafin kace meye fuskan mummy ya aune ya kumbura saka makon fad'uwan da tayi, bakinta har Wani karkacewa yayi.
Har aka fita da kayan Bata sake cewa komai ba.
Abba Yana jinsu a zuciyar shi ya so su mata kafirin duka su kakkaryata kaman yanda mummy Zuwaira ta so.
Saratu ma na d'aki Amma bak'in ciki ya Hana ta fitowa.
Haka mummy tana ji tana gani suka tafi ba ta iya ta6uka abun arziki ba.
Suna barin gidan Abba ya fito, ganin yanda fuskanta ya canja ya Sanya shi fad'in" kad'an ma Kika gani"
Kasa magana tayi Dan gaba d'aya fuskan zogi yake mata kuma ta kasa tashi.
Saratu ce ta fito a d'aki da niyar fita Dan ta Sha k'ananan Kaya,
Had'a ido sukayi da mummy Bata San lokacin da ta fashe da dariya ba har da tsugunawa.
Mummy ke Mata kallon mamaki.
Nan saratu da k'yar ta tsayar da dariyar da take ta dubi mummy tace" mummy kin ganki kuwa? Sun sauya miki Kama sekace gwoggon jeji"
Kuka mummy ta Sanya ta dubi saratu sannan tace"....
Half bread it's better than none... Kuyi hak'uri da wannan.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial126 Chapters
Tales of Astora: Legacy (FINISHED)
This is a series of multiples books compiled together. It starts out with the basic setting of a fantasy adventure world but I assure that as things continue, you will be in for quite a surprise :) : Book 1 (Finished): Over the course of time, countless heroes have risen to defeat the demon lord. Their names, recorded in history. Tales of their achievements are known across the land. But what about the demon lords who have fallen? What of their side of the stories? One such tale is about a young boy born of Dark. What would he do now that all the powers of the old demon lords of the past belong to him? Would he pursue the path of Dark he was destined to? Or would he reach out to the Light at the cost of his own life? There is no other path. And yet he seeks it, insatiably. Book 2(ongoing): Tales of Astora: Insurrection
8 138 - In Serial9 Chapters
THE NUMBERS: RON THE 63
RON: is one of the best assassins in his world his codename is *the red Abomination* ranks 63his family are assassins and killers his father codename *the God of death* ranks 0 and his mom *the mad one* ranks 1 his family is in the thousandhe Only knows two of his spellings, his older brother's codename *the dark crow* rank 20, and his older sister's codename * the singer fox* his life is fine tell his father was trying to eat him He has survived three times. The first time was when his father put him in the fridge after he seasoned him But his brother saved him, and the second time, when his father put him in an oven, his brother saved him againThe last time he was in prison and dropped the soap, his brother saved himAfter the last accident, he lived a full life of escaping and killing tell one day one of his father's followers find him codename *the doctor* rank 21* the doctor*: wow you are really an abomination look at you a cat ear on the left and a wolf one on the right and foxtail and your green eye is like a Beast eye good Thing you have one eye and your rank 63 for a 10-year-old hell kid now I believe you are the boss son the boss want you alive but you are dangerous for this goodbye *bang* *bang* *bang* Ron He was shot three times, once in the heart, once in the liver, and once in the head Ron looked at his killer and He closed his eyes for the last time, or as he thought
8 193 - In Serial8 Chapters
Electric (Phillip Carlyle x OC) ~DISCONTINUED~
Just a little fanfic I made up with the help of wildmustang4002 who inspired me to write this story!
8 73 - In Serial11 Chapters
The Sole Cultivator
Bai Long or Asran? Either way, it's the same person who manages to return back to his own home. Home that he had been longing for since the past millennia. Yet the home he expected had changed to the unexpected. Monsters and superhumans ran around the whole world changing the home he knew into something else. Everything happens all because of these interdimensional gates known as portal. It brought along a whole new ball game for Asran who had returned to being the weakest. For the sake of protecting his mother from dangers of the world that spans from small-time gangsters to monstrous creatures, Asran has no choice but to cultivate himself from the beginning. Since... He's the Sole Cultivator of Earth.
8 202 - In Serial90 Chapters
Reborn as The Riser Phoenix
WHAT HAPPENS WHEN YOU DIE AND REBORN AS A STEPPING STONE OF THE PROTAGONIST AND HOW WILL YOU CHANGE YOUR DESTINY1st dxd 1 st devil1 st rias1 st hsdxd1 Phoenix (7 April 2022) 1 riser1 Ravel 1 GremoryAll the rights and photos belongs to there original owner I only own the story
8 167 - In Serial18 Chapters
Fortnite: Golden Skyes
Skye and her friends, as well as some new faces, return in the C2S4 installment of Fortnite: Quest Buddies!When a girl claiming to be Skye's little sister turns up at Catty Corner, Skye begins to wonder if her past is what she thinks it is. And when superheroes begin to pop up around the Island, it is clear that something is up. Will Skye be able to juggle her life and her job, or will she fall under the pressure?The Fortnite: Quest Buddies Series:Book 1 - Fortnite: Quest BuddiesBook 2 - Fortnite: ALTER EGOBook 3 - Fortnite: The Great FloodBook 4 - Fortnite: Golden SkyesBook XX - Fortnite: The Agent Files
8 71

