《HASEENAH》PAGE 115&116
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story & written
By👇🏻
'''Aysher Abbakar ChuChu (Meerah)'''
® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
Follow me on Aysherabbakar
*115~116*
Mummy ce ta dubesu tace" kun Kai wa mummy nasu IV din?"
Duban juna sukayi Dan Basu gane wace mummyn ce ba.
A tak'aice mummy tace" ina nufin matar Abbanki, mummyn Saratu"
Yatsina fuska haseenah tayi tace" bankai ba"
"Oya ku tashi kukai"
Kaman zasuyi kuka suka had'a baki sukace" Dan Allah mummy kiyi hak'uri tunda gobe ba inda zamuje semu Kai da safe"
"To shikenan ga abincin ku can"
Duka tashi sukayi suka hau dinning suka fara cin abincin.
Washegari misalin k'arfe goma su haseenah suka fito a shirye Dan Kai wa mummy invitation, sallamar su haseen ne ya tsayar da su.
Mummy ce ke faman murmushi tana fad'in" kaga angwayen mummy saukan yaushe?"
" Wlhy jiya muka iso mummy"
Mahmud ya Bata amsa sanann suka gaisa.
Su Umaimah ko murna fal zuciyar su.
Haseen ne ya kalle su yace " ina zuwa enmata?"
Baby tace" can gidan su haseenah zamu Kai ma mummy invitation Wai"
Zaro ido haseen yayi ya dubi mummy yace" to su kad'ai zasu je?"
Harara ta dalla mishi tace" da guards kake so na had'a su?"
Girgiza Kai yayi sannan ya ce" ba haka bane mummy kawai kinsan halinta ne, Dan Allah mummy ki Bari mu raka su plx"
Shuru mummy tayi sanann tace" to shikenan Amma wlhy kana kaisu ka dawo mun da yarana safe and sound, karka wuce dasu wani waje"
Dariya sukayi sannan yace" haba mummy yanzu zamu dawo muma ai magana mukazo yi"
Juyawa mummy tayi ta koma ciki.
Advertisement
Suma fita sukayi suka tsaya a gaban mota cirko cirko.
Sameer ne ya dubi Mahmud yace" ka shiga motar ka ka biyomu mu xamu shiga wanann dukanmu"
Tura baki yayi yace" gaskiya bro baby tazo mu shiga Ni kad'ai zaku Bari lonely?"
Dariya haseen yayi yace" da gaskiyar ka, baby je ki shiga na angon ki, Ni da su Umaimah zamu taho a wanann"
Da sauri kuwa ta nufa wajan motar, da dukkan alamu itama taji dad'in hakan.
A tare suka fice Haseen na gaba Mahmud na binsu a baya.
Idi Mai gadi ne ya bud'e musu gate, Yana hango Haseen ya hau wangale baki Yana kwasan gaisuwa.
Parking sukayi ganin motar dad hakan ya tabbatar musu Yana ciki.
Haseenah ce a gaba suna binta a baya.
Sallama sukayi daga waje.
Shuru ba a amsa ba, suka sake yi, saratu ce ta fito tana fad'in "waye?"
Ganin haseenah ya Sanya ta tsayawa tana kallonta tace" ai ke ba bak'uwar gidan bace da Zaki tsaya daga waje"
Lek'awa tayi haseen kawai ta iya hangowa, tsuka taja tace" ohooo kice keda....
Kasa k'arasawa tayi ganin kallon da haseen ke Mata, sannan ta tuna dukan da ya ta6a Mata da ta kirashi d'an iska.
Komawa tayi ta zauna a kan sofa.
Juyowa haseenah tayi tace" ku shigo"
Shigowa dukan su sukayi harda su Mahmud da Sameer.
Saratu da ke zaune se faman taunan chewing gum take.
Had'a ido sukayi da Sameer, cak taji kaman an d'auke wuta, zuba mishi ido tayi ko k'iftawa batayi, har suka nema waje suka zauna, Sameer ko kau da Kai yayi, har lokacin saratu idonta na kanshi, a zuciyarta ta furta Kai gaskiya gayen Nan ya had'u.
Umaimah da ke faman harararta kishi ya taso Mata Bata San lokacin da ta furta "Sweetheart ka fara karanta li ilafi saboda miyagu da mugun Ido da baki"
Advertisement
Mamaki ne duka ya kamasu duk da sunsan da Wanda take Dan Suma sun kula da kallon da take Masa, Amma abunda yafi Basu mamaki jin ta furta Sweetheart, kallonta sukayi ita ko ko a jikinta Dan ranta ya 6aci Ana kalle Mata miji.
Kau da ido saratu tayi jiki a sanyaye tace.
Jin hayaniya ya Sanya mummy fitowa.
Ganin su haseenah ya Sanya ta yin turus tace" lafiya meye ne kuma? Naga kun cika mun palour bataliya guda, yak'i ne? Ko an turoku ku sake dukanane? "
Da k'yar haseenah ta furta Ina wuni.
'Daga Mata hanu mummy tayi tace" ba abunda na tanbayeki ba kenan"
Fitowan Abba ya Sanya sukayi banza da ita suka juya suna gaida shi, amsawa yayi da farin ciki ya kalli haseen yace" a.a harda bak'i ne kuke?"
Haseen ya amsa da " eh"
Sannan ya cigaba da cewa" wannan shine ze aura Umaimah, ya nuna Sameer" sannan ya nuna Mahmud yace" wannan kuma baby ze aura"
Oh " kace duka sune Wanda za'ayi tare da naka"
Sunkuyar da Kai Haseen yayi Yana murmushi yace" in shaa Allah"
Haseenah ce ta dubi mummy tace" dama mummy ce tace in kawo muku invitation d'inku"
Ta ciro envelop cikin jaka ta mik'o, da sauri Saratu ta sa hanu ta amsa, mummy se zabga Mata harara take Amma ko kula ta Bata yiba, ita dai damuwarta ta duba taga in akwai hidimar shagala.
Aiko tana ganin events guda biyar ta daka tsalle tayi ihu tace" akwai na zuwa a wajen Nan"
Zaro ido su haseenah sukayi suna kallon juna.
Abba da duk bak'in ciki ya rufe shi yace" Saratu Allah shirya ki"
Matsowa tayi kusa da haseenah tace" akwai anko ne?"
Da sauri haseenah ta girgiza Mata Kai alamar babu.
Dan in wanann ta fito a masu anko ba makawa se dangi an zagesu, danma abun er gida ne da anji kunya.
Mik'ewa su haseenah sukayi sanann sukace" Abba mu zamu wuce"
Tare suka fita ya musu rakiya.
Mummy da ke mak'ale jikin labule tana kallon tsala tsalan motocin da suka Zo dasu.
Aranta fad'i take Allah ya kashe ya Basu..
Saratu ne ta dubi mummy tace" mummy ki duba kiga Wanda zasu aura? Duk cikinsu da gani sun shak'i dollar"
Tsuka mummy ta ja sanann tace" ke rufamun baki munafuka, kema in Kika dage Zaki samu Wanda ya fisu"
Mik'ewa tayi tace" Amma mummy auran Nan fa za a chashe, ba k'aramin kutuma za ayi ba"
Tsuka mummy ta ja ta bar wajan tana fad'in" aikinki kenan ai daga sati har monday"
Itama saratun d'aki ta shiga ta fara Kiran watsattsun friends d'inta maza da Mata Tana fad'a musu akwai yayarta Wanda zatayi aure gobe akwai henna deco..
Aiko suka sa ihu suna tsara irin shigan da zasuyi.
Yau ta Kama za a fara shagalin biki, Dan haka duka gidaje ukun cike suke da 'yan uwa da abokan arziki.
A gidan mummy Zuwaira za'a yi henna, Dan tun sassafe akazo aka fara decoration d'in wajen, zuwa 9 suka Gama aka fara jera tum tum kowani gefe, anyi deco d'in da white and black colour.
DJ kuwa 9:30 ya iso..
Kafin kace meye gida ya cika waje ya d'auka da sauti, ga shimfid'an da akayi na alfarma a wajen carpets ne masu girma da laushi.
Masu yin zanen lalle aka d'auko kusan su goma, Amma na Amare daban ne.
Dan k'awar mummy ce ta kawo wata daga Sudan suna kiranta kaltum.
Amare su uku jere kan tum tum sunsha fararen Kaya dogon Riga Ana musu Zane.
Wata motace ya yanko da mugun gudu cikin harabar gidan.
Kowa bin wajan da kallon yayi Ana jiran waye ze fito cikin motar.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial26 Chapters
A dungeon core story: Magic with a hint of Science
Sometimes, you only feel alive after you have died and got granted a second chance.After a gamer and aspiring chemist dies and is granted a second chance in the form of a dungeon core, he decides to make the most out of it.Along with a knack for gaming and creatively using 'game mechanics', he also brings forth the power of chemistry, biology and physics to a medieval-like world where magic is real and where people level up to get stronger. This fiction has LitRPG elements and will contain stat based fantasy, some gore, some humour and most importantly of all, an MC who likes to unleash his inner mad scientist. Special thanks to Kaiverta for making my cover and on such a short notice; It looks amazing
8 237 - In Serial22 Chapters
Inglorious Bastard
My life is in no way unbearable or hard, I fully recognize that it could always get much worse in a multitude of ways. Be happy with what you have and all that. But the future looks bleak and boring no matter how I look at it. Spend 40~50 years trying to educate the bossy rich kids of Pinecove private school and retire having wasted my life or throw everything away in hopes of a more fulfilling job, risking to go under? This world has no place left for excitement and adventure - everything there is to explore and discover was found a long time ago; everything that can be created is here already in one way or another; because of laws, borders, inflation and back-breaking taxes an average Joe just can't do anything too crazy or too ambitious, lest they decide living in prison or being penniless is a great way to lead your life. If only it was possible to be released from all constraints and start anew in some other place, in a different time. Drop the masks and live a life with no regrets. Impossible and childish wish, I know. But a man can dream...
8 120 - In Serial10 Chapters
Goblin Combe
This story follows Jack Chaque-Travail, an Illusionist determined to usher in the next generation of Druids to make sure he doesn't have to watch the earth die around him. Druids used to be awakened high on mountain tops, or in deep caves, but now there are so few left they must be shipped into a summer camp to at least eke out what little potential they have. 'Come with WildWise™ and get away from the buzz of the city and towards the buzz of the sacred bee!' as quoted from their website. As years have gone by, and ozone has deteriorated, Druid training is less summoning treants and more kumbaya-ing. If there is no connection to nature, there are no more Druids, and that means horrible things for everyone left behind. Join Jack as he grifts his way through being a childrens educator, cheating and tricking them into being valuable members of society.
8 98 - In Serial14 Chapters
The park master.
8 83 - In Serial45 Chapters
Gentle Turbulence - Uchiha Madara Love Story
Uchiha Madara.He was one person that every single person in the world feared, right? WRONG!! There was one person, a very ordinary person who absolutely loved to annoy him to no end! Hard headed, prideful, never backing down with a fight; our Jung Mi Ho was the one person you could count on to send him into shock with sassy and comedic back answers!Of course, being Uchiha Madara, Mi Ho will obviously have difficulties handling him. Read on to see Madara as he deals with this loud mouthed and adamant girl that he surprisingly has a strange interest for!~~~~~~~~~~Naruto and all its franchise (C) Masashi KishimotoOC and creative plot (C) Midnight_Lilac
8 186 - In Serial26 Chapters
Bloody Heart 3
Третья часть моей серии книг "Bloody Heart")))По вашим просьбам :3
8 146

