《HASEENAH》PAGE 121&122
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story & written
By👇🏻
'''Aysher Abbakar ChuChu (Meerah)'''
® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
Follow me on Aysherabbakar
*121~122*
Gidan mummy zuwaira ya dad'a cika da mutane, yau saura kwana biyu a d'aura aure dan haka bak'i na nesa sun fara isowa.
Da safe masu aikin da mummy ta yo haya suka fara gyara gida masu abinci na yi.
Da wuri suka tashi suka shiga wanka nan suka zauna tare da su saratu da friends dinta dan yin breakfast.
Aaman ne ya shigo yana sanye Cikin English wears, Cikin Riga yellow colour anyi rubutu a gaban rigan da blue, wandon shi ma blue jeans ne se k'aramar sneakers a k'afarshi, hanun shi d'auke da k'aramar flask me feeder a jiki ko ba a tanbaya ba kasan custard ne a Ciki.
Ya dad'a wayo da kyau ga haske Kama suke sossai da haseenah.
Kai tsaye wajenta ya nufa itama ta mik'a hannu ta hugging d'inshi, rabon da ta rik'e shi a jikinta tun da aka fara hidimar binkin nan, sedai taga wucewar shi.
Zama yayi kan cinyarta yace" aunty ina kinje? "
Dariya tayi tace" babu ina nan Aaman Kaine de ka gudu"
Be san me ze cemata ba kasancewar ba wani magana sossai ya iya ba, mik'a mata feeder yayi dai dai bakinta yace" sha"
Kar6a tayi ta ajiye ta fara bashi kwai a baki.
Tunda ya shigo saratu take kallon shi, to wannan d'in waye? Tanbayar da ta kasa samun amsa kenan.
Kuma gashi yana Kama da haseenah ko dai d'an yayar umman haseenah ce?
Kasa hak'uri tayi Cikin murmushi tace" aunty haseenah wannan fine boy d'in fa babyn waye?"
Cikin mamaki haseenah tace"baki gane Aaman ba? "
Gyad'a kai saratu tayi alamar eh.
Haseenah tace" yaron Ummah nane fa Wanda aka haifeshi"
Xaro ido saratu tayi tace" shine ya girma haka? Ji kyau dan Allah, wlhy he's super handsome"
Advertisement
Dukansu dariya sukayi suka cigaba da breakfast, Aaman kuma na musu tad'i suna ta dariya.
Kasancewar yau juma'a ne ta Kama yau za'ayi walima washegari kuma a d'aura aure.
A gidan za'ayi shiyasa kafin wani lokaci an gama gyara ko ina.
An buga temples a ta bayan gidan an jera carpets da kujeru da tables.
Ko wani table kujera hud'u ne kewaye da shi.
Ta can gefe kuma chefs ne wato masu girke girke su hud'u kowacce da apron jikinta, gaban table d'in da suke kuma abinci ne jigbe Kala Kala da snacks.
An k'awata wajan se ya zamana kaman liyapa za'ayi.
Wajan k'arfe hud'u mutane sun fara cika.
Dan haka amare ma na ciki ana shiryasu.
Cikin lipaya aka shiryasu Maroon colour da yasha white stones a jiki.
Ba k'aramin kyau sukayi ba.
Ba tare da 6ata lokaci ba aka fara gudanar da walima.
Sossai aka fad'akar da su Wanda ya Sanya jikin su yin sanyi, haseenah ko tafi kowa kuka a Wajan, abun mamaki Harda Saratu a kuka dan ta tsorata sossai kuma ta k'udiri niyar canja rayuwarta.
Anci an sha anyi pictures da videos sannan aka watse.
Misalin k'arfe goma kuwa su saratu suna tare da su Haseenah a d'akin su.
Zama sukayi duka sunyi shuru an rasa me magana.
Can Umaimah ta kalli haseenah tace" sis gobe by this time bamu tare fa an raba mu"
Haseenah da idonta ya cika da hawaye ta rasa me zata ce ma.
Baby da yake itace k'aramar Cikin su seta fara kuka.
Matsowa kusa da su tayi ta shiga tsakiyansu ta rungumesu, kukan ta ya tsananta sossai, ba k'aramin shak'uwa sukayi ba, gashi zasu rabu lokaci d'aya.
Umaimah ma kukan ta fara yi, haseenah da yake itace babba ta daure ta share hawayenta sanann ta ce" haba mana kuyi hak'uri, dukanmu fa gari d'aya zamu zauna, when ever we felt like seeing each other we will"
Su saratu ko zuba musu ido sukayi suna ganin irin tsantsan kulawa da shak'uwa wajan su haseenah.
Dee ce tayi murmushi tace" kuyi hak'uri ku gode ma Allah, gwanda ku zakuyi auren ma mukam ai gamunan duk mutanen banza ke zuwa mana"
Advertisement
duban su haseenah tayi Cikin tausayawa tace" hakuri zakuyi ku gyara rayuwar ku, ku nutsu se kuga Allah ya tausaya muku Cikin k'ank'anin lokaci se kuga komai ya zama tarihi"
A tare suka had'a baki suka ce " in shaa Allah "
Haka suka cigaba da hirar su har Wajan 12 na dare, Aaman kam yayi bacci yana jikin haseenah, dan yau so take su kwanta tare dan tasan Daga gobe ganinshi ze mata wahala.
Dukan su a d'akin suka kwana dan su saratu ma basu tafi d'akin ba.
Washe gari yau kenan ya Kama asabar dan misalin k'arfe goma za'a d'aura aure.
Tun daren juma'a Haseen ya fara had'a kayan da ze tafi dashi abuja kai kace shine amaryar.
Mum ce ta shigo d'akin, ganin akwatina tayi a kan gado har uku, duban shi tayi tace " wannan kayan fa"
Sameer ya kwashe da dariya yace" mummy wai kayan da ze tafi dasu gidan aure ne"
Salati mum ta fara yi tana tafa hannu, girgiza kai tayi sanan tace" da alama wannan aure yana neman zautar da kai, Anya kuwa k'alau kake? "
Dariya ma yayi sanann yace" mum dan Allah bayan na tafi, incase in nayi mantuwa a biyoni dashi plx"
Kasa magana tayi kawai ta juya ta fice.
Duban agogo sukayi lokacin 8:30 ne.
Wanka suka shiga suna fitowa mum ta had'o musu breakfast, da k'yar Haseen ya nutsu yaci dan shi cewa yayi suyi sauri kar suyi latti.
Harara Sameer ya 6alla mishi yace" dalla malam in zaka nutsu ka nutsu yanxu fa ko 9 beyiba zaka bi ka d'aga ma mutane hankali".
Ganin masifan zeyi yawa ya sanya shi zama suka fara cin abincin.
Can su haseenah hankali ya fara tashi, kasa cin abincin ma tayi, idonta yayi tsuru-tsuru, tunanin ummanta kawai takeyi, Ji tayi komai ya koma mata sabo.
Zuciyanta zafi yake mata ta kasa yin komai.
Sun mata rarrashin duniya Amma tak'i.
Umaimah ce ta kira mummy ta sanar mata.
Nan mummy ta Sanya ta gaba seda ta shanye tea sannan ta barta.
Kowa na cire kayan da ze tafi dashi Amma Banda Haseenah.
Bayan Umaimah ta gama nata ne ta d'auko akwatinan Haseenah tace"wanne zaki tafi dashi"
Girgiza mata kai tayi, bata sake kulata ba ta bud'e, duk kayan da tasan sabi ne kuma haseenah tanaso ta had'a mata a akwati d'aya, inner wears da sauran tarkacen da zata buk'ata ta had'a suma a akwati guda.
Sauran kayan ta dubeta tace " sis kinada Wanda zaki basu ne? "
A hankali tace" ba ma su suratu su cire Wanda suke so sauran suyi kyauta dasu"
Aiko murna Wajan su saratu ba a magana ita da friends d'inta.
Wardrobe haseenah ta bud'e ta d'auko wata k'aramar jaka, jakanda ta baro gidan su Sameer da shi tunda ta ajiye bata sake bud'ewa ba.
Bud'e jakar tayi ta ciro set d'in English gold Wanda Sameer ya siya mata ta saka a jaka.
Ganin yanda yake walwali kasan ba k'aramin sark'a bane.
Baby ce ta furta" Wow sis wanann golds d'in fa"
Murmushi kawai tayi tace" nawa ne"
A jakar ta saka sannan aka saka key aka rufe.
Mum ce ta lek'o tace su shiga wanka dan ana d'aura aure zasu wuce dan tsakanin kano da Abuja akwai d'an tafiya.
Jiki a sanyaye suka shiga wanka.
Tun a toilet haseenah ta fara aikin kuka, su umaimah da baby duk sun fito har an fara shiryasu Amma bata fito ba.
D'aya Daga Cikin sisters d'in mummy ne ta shigo tana gud'a tana fad'in aure ya tabbata.
Cak haseenah taji numfashinta ya d'auke na wasu lokuta.
Sulalewa tayi a Cikin toilet d'in ta fad'i.
Jin k'arar fad'uwan abu ya Sanya su nufan hanyar toilet d'in da gudu.
Allah ya temaka bata saka key ba.
Ganinta sukayi zube a k'asa d'aure da towel da alamu tana shirin fitowa haka ta faru.
Da gudu suka shiga suka fara jijjigata.
Ganin bata motsi ya sanya baby k'walla ihu ta fita tana kiran sunan mummy.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial53 Chapters
The Core: The Hive Daughter (Book 2 of 3)
Hi! Welcome back! This story continues from book 1. Here is the link to that if you haven't read it yet: https://www.royalroad.com/fiction/43381/the-core-the-first-guest-book-1-of-3 After witnessing the destruction of Magus the 2nd's Core, Kevin and his AI are on the way to pick up Meditati. Magus the 1st dreams of battle and enemies rising up against him. He will stop at nothing to relive the glory of war. The object his clone dug up from the star before it was devoured might hold the key to his dreams.The AI of the Tela plan in secret, trying to trap their first Guest into letting them go. An egg is found, a drunk driver puts a child in a coma, and the Arbiter observes Earth.
8 179 - In Serial13 Chapters
We reincarnated as a two-headed dragon!
Kyle Lewis 25 years old, business man and Amelia Evans 18 years old, high school student otaku don’t know each other. They both died at the same time and reincarnated as a two-headed dragon. They now share the same body and must cooperate to survive in an unknown world. LITRPG story with levels, skills... Note: This is my first novel. Sorry for any mistakes. English is not my native language.
8 372 - In Serial11 Chapters
Cursed World (LitRPG Fantasy Adventure)
A new virual reality game. Where the playing is virtual... and the dying is real.POSTING SCHEDULENew 2000+ word chapters will be posted every Monday, Wednesday and Friday.
8 238 - In Serial29 Chapters
My husband, My bully (Complete✔️)
Salam u alaikum readers! I wanted to inform you guys that I've started making edits to this story. Some chapters are the same while some are completely different. Anyway, I hope you enjoy! ________________________Anisa Malik. The famous confident hijabi in class 11-A. She's headstrong and beautiful but could be a short tempered kid when provoked. She's got her hands full and the handsome bully in her class just makes it worse for her. Little did she know, the annoying boy who never ceases to piss her off might be a bit more important part of her life than she takes him for. He might just be the one chosen to be her other half. Ali Hassan. That name sent girls shrieking and blushing all over. That was no wonder. His charms and looks were enough to send any girl's heart racing. And he knows it until he meets the only girl who plays hard to get. Her clear cut comebacks, her sassy attitude just sparks something inside him. Despite this feeling, he takes every chance to humiliate her. The only guy bold enough to step up to the confident Anisa Malik, he just seems to be the perfect bully for a girl like her. What happens when Anisa and Ali are forced to get married? The two can't even get along for two minutes in a classroom let alone spend the rest of their lives together. She's got her problems and this marriage is another one added to her list until the bully starts showing a side she has never seen. One thing is for sure. It's one shell of a bumpy ride.
8 114 - In Serial50 Chapters
Muslim & Pakistani Love stories
Love has no reasonsLove have no seasonWhen you love someone,all you wish to spend time with them, wishes to a day to become long.'' Kya hoga agar mere lab tere lab se lag gaye Naraz kyu ho rhi ho tum badla he le lo
8 206 - In Serial11 Chapters
Boardwalk 《David the Lost Boy》
David ff
8 71

