《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER FOURTEEN
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA HUDU🌼
Page 65-70
Na dawo daga rakiyarsu Ash na tarar Suhaima da Lubna na gyara wajen da muka yi breakfast.
Ko sake kallon ita Suhaimar banyi bah,nace wa Lubna"Lubna ina Umma?"
Tace"Ta tafi bangaren Abba... "
Jin hakan ya sanya na nufi d'akina ba tare da na sake cewa komai bah.Ina shiga daki, wanka na soma yi don naji dan dad'in jikina.Doguwar riga mara nauyi na sanya sannan na dauko wayata na kunna.
Wayar tana gama booting, sai text messages suka hau shigowa kamar dama can jira suke abude wayar.
Text d'in Ash na soma budewa wanda nake tsammanin tun jiya ah Kano tayi min(idan zaku tuna sanda zata dauki Mubeen hoto tayi ignoring wasu messages.... Remembered?)
The message goes lyk dix, "Fadima idan kina yiwa Allah ki taho ki kwashe shanyar da kika yi.... Kayan sun gaji da bushewa...kina can kina soyewarki da Man d'inki ayayin da mu kuma kika barmu ana cin mutuncinmu anan.... "
Murmushin takaici nayi sanda na tuna da Mummyn Mubeen wanda itace Ash ke nufin taci mutuncinsu.Har yau mamaki nake da suka ce min matan nan tayi musu rashin mutunci akaina, sabida sam koh kusa ba tayi kama da wacce zata iya yin hakan bah.Ko da yake such is life... Diz life is full of wonders... Dan'adam tattare yake da abubuwan mamaki kala-kala.
Sauran text messages d'in kuma wanda ake aiko wa mutum ne idan kayi missing voice call.I missed about 20 voice calls daga Ummana wanda hakan na nufin tayi ta trying numbata kenan koh Allah zai bata sa'a ya shiga, she never gave up.... Uwa -Uwa kenan... Believe me if I say, No one like mother.
Sauran calls d'in dana yi missing kuma, daga Leedar ne da Ash, sai kuma Mubeen.
Mubeen kenan sai ayanzu ya fad'o min arai. Nasan yana ta trying line d'ina bai sameni bah, kuma maybe yana cikin wani hali ayanzu I guessed, idan har da gaske yana sona kenan as he said, sabida ni yanzu na daina yadda da love stories na d'a Namiji..'' ya mugun koya min hankali.
Ji nayi kamar na kirashi, sai kuma na fasa because its not my class ni na fara nemansa,shi din mah ya kamata ya k'ira yaji ya muka kawo gida.Don haka zan k'yaleshi duk sanda yayi trying line d'in yaji ta shiga toh Alhamdulillah, amma idan bai k'ira bah toh Wallahi ni d'in mah bazan sake kiransa bah.
' ne ya fad'o min arai.Murmushi nayi ina tuna sanyin halinsa.Namiji ne kamilalle,maganarsa ahankali cikin sanyin voice.Abinda yafi bani dariya agame dashi bai wuce yadda idan na masa tambaya.. Instead ya maido min da amsar tambayata, No sai dai shima ya jefo min tasa tambayar.
Abin dariya ya bani wanda har nake ta k'yak'yatawa, kofar d'akina naji an bude aka shigo.
It's Umma, ganinta bai hana ni daina dariyata bah,dariya fah hadda hawaye.
Ina kallon Umma wacce sai kallona take cike da sha'awa tace"Masha Allah! 'Yar Kareematu burina bai wuce na ganku cikin farin ciki bah akoda yaushe.... Na san koh baki fito fili kin fad'a bah.. tabbas daga ganin wannan hawayen murnar, its an indication dat surukin nawan ya mugun kwanta miki arai. "
Jin kalaman da suka fito daga bakinta ya sanyani tsai da dariyata at once.
Ta cigaba"Dama zuwa nayi muyi 'yar hira ni dake... Wanted to know ya kika gan Mubarak d'in? Shin ya kwanta miki arai or not? "... But now I hav already gotten my answers, kuma ni kaina nayi matuk'ar farin ciki... Kareematu always wants the best for her children... Allah ya sanya alheri"
Advertisement
Cikin rashin kuzari na amsa da"Ameen Ummu Fad'ima u the best.. "
Tace"Yanzu Mal. Iroro ya dawo, ya dauko motar...Wai dama wata injin ce ta sami matsala but an gyarata... Shine kuka bar min kuloli cikin motar kuka yi ta kanku right? "
Dariya na sanya don har ga Allah ni nama manta da batun wasu kuloli,ashagwabance nace"Haba ummata yanzu kulolinki sun fi 'ya'yanki kenan? "
Murmushi tayi tace"Juz kidding... Haba ai 'ya'yan Kareema always cumx first.... Bata had'a 'ya'yanta da komai... "
"Tankx best mum... " Na fad'i hakan cike da k'aunar mahaifiyata.
Tace"Abbanku wai kizo ku gaisa.... "
Atsorace nace"Umma am scared to face him..... "
Tace"Come on daugh... Wallahi he knows nothing abouh ur late journey back... Trust ur mother, na dai fad'a masa cewar around 1pm motarku ta lalace, shine kuka kirani sai na aika Mal. Abu mai gadi da tawa motar ya d'aukoku, don kin san baya cika son kuna shiga lift dat's why banyi gangancin fad'a masa cewar taimakonku akai bah... Yadai d'anyi fadar wai meyasa ba'a sanar dashi bah aka barshi acikin duhu... "
Tasowa nayi na rungumota, nace"Ummata thank you so much for everything...I love you so much mother"
Ahankali tace"Stop thanking me my baby...ai ciwon 'ya mace ta 'ya macece... "
"Exactly mommana.. " Na fad'i hakan sanda muka fice daga dakin zuwa bangaren Abba.
Azuciyata nace"Allah sarki ummata da'ace kin san Mubarak nada Mata harda 'ya nasan da kin fini bakin ciki kuma ba zaki taba bari na aureshi bah... am scared of ur reactions duk randa kika yi find out.... Ya Allah! gani gareka... Kai kadai kasan abinda zaiyi daidai ga rayuwata... Allah ka zabar min miji mafi alheri.... "
Atake naji wasu hawaye masu d'an d'umi sun gangaro saman kumatuna, da sauri na goge kada Umma ta gani. Har muka iso falon Abba hira take min.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Mubeen ne kwance saman d'aya daga cikin kujerun falonsu, yayi matashi da hannun kujerar da yake kwance akai. Hanan ce ah kicin tana wanke kwanonin da suka yi breakfast dasu.
Mubeen ya d'auko wayarsa ya sake sanya k'iran Fadima akaro na barkatai tunda gari ya waye. Wannan k'aron yaci sa'a K'iran ya shiga wanda hakan ya sanyashi mik'ewa da gudu yana kwalawa Hanan k'ira.
"Wifey am lucky... Yanzu line d'in sister d'inki ya shiga... "
Jin hakan ya sanyata saurin dauraye hannayenta ta nufo falon da murnarta tana fad'in"Hubby are u serious? "
Bai samu damar bata amsa bah don tuni Fadima tayi picking call d'in har sun mah soma magana, ganin hakan ya sanya Hanan komawa kicin don kada ta saurari abinda zasu ce. Hawaye masu d'umi taji sun zubo mata saman kumatu ayayin data ji wani mugun kishin Zahra ya tokare mata kirji. Zafi sosai kirjin ke mata bana wasa bah.
Kuka ke neman kufce mata amma sai tayi kokarin dannewa kada Mubeen yaji. Ah sanyaye ta cigaba da wanke-wankenta.
Bangaren Mubeen kuwa bayan Fadima ta d'aga call din,wani sassanyar ajiyar zuciya ya sake kafin yace"Haba Zahrata kin san halin da kika sanyani ciki tun jiya kuwa? Ur line wasn't getting through sai yanzu naci sa'a ya shiga.... Ina ta tunanin halin da kuke ciki......... "
"Hey! Man relax....toh ka bani damar nayi maka bayani mana... Huh? "
Ahankali yace"Alright baby Zahra ina sauraronki.... How was ur journey? "
Murmushi nayi nace"Alhamdulillah!! Allah made the journey to be safe for us through out.... " Na rasa dalilin daya sanya na kasa labarta masa gaskiyar lamarin yadda motarmu ta lalace da kuma yadda Engr. Mahmood ya taimaka mana.
Yace"Okay baby toh meya hanaki kunna wayarki diz morning after charging it? "
Advertisement
"Wallahi was so much tired... Inata bacci, tashiwata kenan mah na kunna wayar, sai ga kiranka ya shigo" Na sami kaina da yi masa wannan k'aryar.
Cike da kulawa naji yace"Babyna ai dole ki gaji... Tankx for coming and am really sorry for everything including duk wulakancin da mahaifiyata tai wa 'yan'uwanki.... Kuma insha Allah ni Mubarak ina mai yi miki alkawari da cewar.... Muna gama waya yanzu zanje na sameta na fad'a mata cewar ke nakeso kuma ina son na aureki....... "
Da sauri nace"Anya Mubarak kana ganin zatayi na'am da Zancen nan naka kuwa? "
Wani bangaren zuciyata kuma yace"Idan har mah ya samu ta amincen, ke mahaifiyarki zata amincen ki auri mai mata ne? "
Murmushi naji yayi yace"Zahrata kisa aranki kamar ta riga ta gama amincewa ne..... Ke dai kawai ki soma shirin zama amaryar Mubeen..... "
K'arar fashewar abu yaji akicin wanda jin k'arar ba karamin firgitasa yayi bah,da sauri yace"Babyna will call you back later please.... "
Ya yanke call d'in ayayin daya nufi kicin da saurinsa. Abinda ya gani ne ya matukar tsoratashi, nan da nan idanuwansa sukai jawur kamar garwashi, jijiyoyin kansa suka mimmike tamkar zasu tsinke.
Salati kawai yake yi yana dada nanatawa"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Hanan mai zan gani haka? "
Glasses ne atarwatse akasa duk sun sha jini ayayin da tafin hannun hagunta duk jini ya gama wanke mata shi har yana zuba akasa.Kukan da take rerawa ahankali, ayanzu ta samu sararin fitar dashi fili ah sa'ilin da tayi ido hudu da Mubeen.
Da sauri ya rugo hannun nata yana fadin"Sweetheart garin yaya hakan ta faru? "
Ahankali tace"Hubby tsautsayi ce kawai which I can't explain how it happens.... "
Yace"Yanzu dai muje nayi miki dressing d'insa kada jinin ya gama tsiyayewa kinga kina da juna biyu.. "
Ya fad'i hakan tare da ciccib'arta yayi dakinsu da ita, don shi sam bai yadda da wannan batun nata na wai tsautsayi bace, shi dai jinta kawai yayi amma ba wai yayi believing bane.
Bathroom ya kaita ya wanke mata hannun sannan ya dawo da ita ya ijjeta saman gado. Zuwa yayi ya d'auko first aid box don Likita kamarsa baya wasa, yakan ijje wasu kayan aikinsa agida incase of irin situation na Hanan yanzu.
Dressing din hannun yayi da bandeji bayan ya gama treating d'insa da maganin injury wato 'iodine'. Sai kuka take don zafi.
Shi kuwa sai aikin cewa yake"Sorry babyna it shall be well with you... Sannu kinji... "
Yana gamawa ya bata magunguna tasha, ciki kuwa hadda na bacci don she need to rest.Ai kuwa tana gama sha koh Mintuna goma ba'a dauka bah, wani nannauyar bacci yayi awon gaba da ita.
Gaskiyar lamari kuwa shine,alokacin da Mubeen ke waya da Zahra, sanda yacewa Zahra 'ta soma shirin zama amaryar Mubeen' da karfi yayi wannan maganar, wanda kuma Karaf! akunnen Hanan d'in.
Alokacin tana wanke wani glass cup ne taji wannan maganar, wanda hakan ya sanya bata san sanda ta yamutsa glass cup din da hannun hagunta bah don zafin kishi,shi kuma cup d'in azabar daya ji ne ya sanyashi tarwatsewa har ya jijji mata ciwo, daga bisani ta watsar da tarwatsassun glasses d'in akasa alokacin data jiyo takun Mubeen ya nufo kicin d'in.
Mubeen kuma ganin bacci ya d'auketa ya sanyashi sakin wata wahalalliyar ajiyar zuciya.Ya tafi kicin d'in, yayi clearing wajen da glasses d'in suka tarwatse tare da mopping d'in wajen.Yayi spraying wani liquid perfume mai kamshi awurin. Nan da nan wajen ya d'au kyalli da wani fitinannan kamshi.
Ahankali yake magana da kansa"Haba Hanan d'ita meyasa kika cika sona da yawa ne har ya janyo kika yiwa kanki illa haka? Hanan nima zanfi so ace na zauna dake ke d'aya amma kuma ina ganin hakan ba zai yiwu bah sabida yadda Allah ya jarabceni da son '
Ji yayi kamar ana bugun gate d'in gidansu. Don haka da sauri ya fice don dubo koh wanene.
Bugu ake bana wasa bah. Azuciye yace "Don Allah ana Zuwa mana... "
Yana gama bud'ewa yayi arba da Mummy, Engr. Mahmood da kuma Usman kaninsu.
Gabansa ne ya shiga faduwa sanda yaga Mummy ta jefesa da wani mugun Kallo.
Cewa tayi"Tunda jiya wucewarku kukai babu koh sallama don kasan laifin daka aikata dat's why kaki shigowa toh gashi nan ni na biyoka da kaina muyi magana.... Don haka ni bani hanya na shige.... "
Da sauri ya basu hanya suka shigo cikin gidan,lek'awa yayi yaga motar Engr. Awaje.
Ahankali ya maida dubansa ga Mahmood wanda duk jikinsa asanyaye yake, yace"Brother ba zaka shigo da motar bane? "
Engr. Ya juyo yace"No, tace ba dadewa zamuyi bah don nima ina da wurin Zuwa ta sanya na kawosu... "
Jin hakan ya sanya ya maida kofar ya rufe, sannan ya juya ya nufesu wanda tuni sun riga sun shige cikin falon har mah sun zazzauna.
Cike da rashin kuzari ya nufi inda Mummy ke Zaune sai faman aika masa da sakonnin harara take.
Russunawa yayi yana gaidata"Mummy an kwana lafiya... ? "
Saurin taran numfashinsa tayi"Da ban kwana bah Zaka ganni da safiyar nan agidanka? "
Shiru yayi mata,ganin shirun nasa yai yawa ya sanya ta cigaba"Ina ita Hanan d'in take mai shegen son miji da har zata iya tunanin had'a kai da kai ta hanyar boye min abu kamar haka... Toh albishirinku duk naji komai da kuka yi discussing awaya jiya.... "
Da karfi tace"Nace ina take? "
Da sauri yace"Tana kwance bata ji dan dadi bane, ta samu bacci ya d'auketa. "
Cikin halin koh ajikina ta cigaba"Wannan kuma ita ta sani...kadan mah ta gani kenan na rashin jindad'i idan har ta cigaba da baka goyon baya ka karo aure.. Idan banda abin shashashar mah wacce macece take kaunar ayi mata kishiya? "
"Toh wallahi Mubarak ka bud'e kunnuwanka ka saurareni da k'yau... Kama cire batun yarinyar nan acikin zuciyarka don muddin ina raye kuma ina numfashi adoron kasar nan toh wallahi bazan taba bari ka auri wata mace bah... Matarka d'aya anan aduniyar, kuma itace 'Sai dai idan so kake ka nuna min cewar bani 'ce na haifeka bah...... "
Da sauri ya d'ago jajayen idanuwansa yana kallonta,yace"Mummy kin isa dani kuma ni kallon uwar data haifeni nake miki.... Amma mummy ina son Zahra kuma ina son na aureta ba wai kuma don na daina son Hanan bane.......... "
Da sauri tace"Mubarak ayau ni kake fad'awa ra'ayinka?.... Ina baka umarni amma kai kana neman ni nabi ra'ayinka......? "
Kokarin magana yake, ba zato bah tsammani yaji Engr. ya sako baki"Kai ana nemar zab'a maka abu mai k'yau ga rayuwarka amma nema kake ka kawo taurin kai.... har nawa kake da har mummy take zartar da hukunci akanka kake nemar ta bi naka ra'ayin?..... wai ni mai mah ka nema ka rasa ne agun wannan yarinyar kirkin Hanan da har kake neman jajibo wa kanka fitinar k'aro aure? Koh baka san wani sa'in keeping more than one wife fitina ce ba?.... Bar ganin Mummy da Umma(mahaifiyar Mubeen) sunyi zamar lafiya kayi zaton koh kaima hakan za'a samu anaka gidan.... Sam, it might turn out to be a negative view in ur own case..... "
"Brother pls stay out of diz... Bah damuwarka bace idan mah na tara mata d'ari acikin gidana tunda dai ba'a cikin naka gidan zan ijje su bah, its non of ur business..... Wannan maganace tsakanina da mahaifiyata don haka ka cire bakinka aciki.... Ka kuma kama girmanka...... " Mubeen ya fad'awa Engr. Wannan maganganun cikin zafin rai.
Mummy ce ta wanke masa fuska da Mari tana huci"Iyyeh Mubarak rashin kunya zaka yiwa dan'uwanka na gaba da kai akan 'ya mace? "
Kafin ta gama rufe baki taga Engr. Ya mike shima yana huci, ya tunkaro inda Mubeen yake yana fad'in"Mubarak ni kake fad'awa na kama girmana kuma na cire bakina acikin maganarsa? "
Mubeen shima mik'ewa yayi ba tare da ya damu da Marin da Mummy tayi masa bah, yace"Mahmood an fada maka hakan.... Do ur worst.... "
Da gaske fah so suke suyi dambe, don sanda Mahmood ya tunkaro inda Mubeen yake, mubeen d'in hadda cire T-shirt d'in jikinsa yayi.
Mummy ce tace"Wallahi kar ku kuskura kuyi min dambe anan.... " Ta fad'i hakan cikin tashin hankali don ta san dukkansu akwai shegen zuciya.
Hanan ce ta fito falon don hayaniyarsu ce ta tasheta. Ah daddafe ta fito falon don jirin da take ji.
Ganin Mijinta da Mahmood na shirin dambe ya sanyata fashewa da kuka, da sauri ta nufesu tana fad'in "Abu jasmine pls kar kayi fad'a da dan'uwanka akan mace..... Yaya Mahmood pls ku bari" Arude take fadin hakan...
Tuni Mubeen yakai wa Engr. Naushi ahancinsa................... 📝
HAFNAN'S POV
Hahaaha!!! Anayi muna shan Lipton agefe..... Anfa zo gun dearie's
Don Allah muna barar addu'a agareku... Matar wana is seriously sick... Ur prayers are all needed pls... Thank you all!!!
Pls ignore any errors seen ayayin typing d'ina... Kun san nobody is perfect!!!
SAHIBARKU CE
©QUEEN HAFNAN©
Advertisement
- In Serial21 Chapters
Aytelia
A magical world embracing chaos as powerful entities and worlds fight for survival or power, observed by the "universals", a sentient species no one can fathom or reason with. Their knowledge, comparable to the vast amounts of years they have existed for and their power feared by even some Gods, capable of destroying and creating entire universes, Aytelia being their proudest creation. Amongst all these the name of one of them is profound even amongst them, both feared and respected - Righteousness. As a lone girl wakes up in a large strange fountain, filled with other individuals in the same position such as herself, she lifts her drowsy head to find her surreal surroundings. The civilians walking around said fountain are all weird creatures that could only come out of a fantasy - orcs, elves, dwarfs, dragonewts, all wearing all different kinds of medieval armor, weaponry and artifacts. What will happen to her in this world? Will she be able to find a place in it and will the mysteries behind her current circumstances be revealed? Why is she so different than those around her? Warning: Character is extremelly OP and the lore behind it doesn't get covered till chapter 14. Updates once a week. First time posting my writing on the internet so feedback would be appreciated.
8 197 - In Serial29 Chapters
Troubled // Irondad
Peter's been through a lot in his life, so when something so horrible happens to his aunt, it messes with him and causes a chain of events.
8 186 - In Serial31 Chapters
Silence ✔️
Zelda Harkinian is a girl with impaired hearing and has been bullied mercilessly for it her entire life. Years later, one of her former tormentors, Link Forrester, sets out to make amends, in hopes of earning her forgiveness and help with the new problems he now faces. ••The Legend of Zelda and its characters belong to Nintendo. Cover art was created by Finni Chang. If you would like your art removed, please pm me!Inspired by the Japanese animated movie "Koe No Katachi" (A Silent Voice). All writing is mine. Please do not repost my work anywhere else.Highest Rank: #1 in Zelink3rd place in the Popularity Contest under the Modern AU category for the Zelda Watty Awards 2018!Word Count: 52KPublished: January 22, 2017 11:07 PMCompleted: May 2, 2017 10:51 AM-KatyWritesStuff- ©
8 142 - In Serial89 Chapters
Justice in the One Piece World
After a tragic death, the sisters Kara and Diana got a deal from God. "You can mess up the One Piece Storyline for my entertainment!" "Can we have some cheats? We don't want to die right away" "Sure, here you go" "Holy crap, seriously?" Follow the 2 OP sisters as they join the Marines and mess up the Storyline. Warning: This story is mostly light hearted with 2 OP MCs on the loose in the One Piece World. if you do not like this sort of novel, I recommend you do not read it. Note: This story was heavily influenced by Kestix's "Lia and Lara will Seek the One Piece" Please go support his work as well. Of course, I do not own One Piece. I only own the OC (Original Characters) that I put into the story. Enjoy! I recommend reading this story at 20px. You can choose the font size above :) Also, I do not own the Cover Art. It is from One Piece Wiki Fandom
8 295 - In Serial25 Chapters
Revenant
Everyone dies. Not everyone gets back up again afterward. The Deep Paths are a cursed place, meant for those similarly cursed souls whom the gods themselves denied the sweet release of death. Revenants haunt the underworld, wielding forbidden powers and often consuming those who lack the strength to join them. At least, that's the story that parents teach their kids up on the surface. Reshid can't remember what he might have done to deserve such a fate, but he learns quickly that there is more to undeath than the gods and their faithful preach to the living. Revenants have a unique connection to essential magics that allows them to develop their powers in extremely diverse ways. Wherever there is power, though, there are those seeking to wield it, whether they be governments and gods from above, or mythical elder races from below.
8 143 - In Serial10 Chapters
My halfbie - GwinamXreader
An unlikely friendship and a zombie apocalypse. What could go wrong-I do not own any of the all of us are dead characters or plot-
8 158

