《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER TWENTY EIGHT
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
_Ignore any errors seen_
🌼BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS🌼
Page 130-135
_GEFEN MUBEEN_
Fadima ta fad'a masa cewar sun soma shirye-shiryen exams,toh sai yaga ya dace ya bata chance tayi concentrating akan karatunta,shine ya d'aga zuwan nasa wai har sai ta kammala jarabawar wanda zasu kwashi kusan sati biyu suna yi.Fadima kuwa ko ajikinta,hasalima hakan da yayi ba k'aramin dadi yai mata ba.Ta rasa sanin dalilin daya sanya ko kad'an bata damu da wannan shawarar daya yanke ba.(lol taya kuwa zata sani bayan Engr. ya gama tafiya da imaninta).
Dama ranar juma'a zata zana exams din k'arshe,don haka sai suka ajje cewar ranar asabar zai shigo garin.
Yau kuwa ta kama ranar asabar din wacce ta kasance ranar ne Mubeen zai kaiwa Fadimar tasa Ziyara.Sai dai kuma tun adaren jiya zazzab'i mai k'arfin gaske ya rufe Hanan.Sosai wannan cikin ke bata wahala,don da'ace baiyi kwari yakai 4months ba toh kuwa da an dad'e da cire shi sabida wahalar da take sha.Bata ma iya haihuwa da kanta don ko haihuwar Jasmine operation aka mata.
Gama shan tea dinta keda wuya wanda shi kadai ta iya dan sakawa acikinta,tana gamawa taji amai na neman taho mata,da sauri tayi yunkurin mik'ewa daga jikinsa.
Ruk'o hannunta yayi yace"Ina kuma zaki? "
"Amai zanyi..... "awahalce ta bashi amsa tana kokarin son k'wace hannunta.
Maida ita yayi jikinsa yana fadin"yi ajikina.... " Bai gama rufe bakinsa ba sai gashi ta k'wararo masa aman akan farar T-shirt dinsa.Sai daya bari ta gama aman sannan ya kwantar da ita ah gefen gadon yana fad'in"Sannu babyna....... "
Ita kuwa kai kawai take ta d'aga masa don jikinta duk ya mace sabida aman da tayi.Ficewa yayi zuwa kitchen,sai gashi ya dawo da bottle water da kuma wani bowl,ya taimaka mata ta mike zaune,ta kuskure bakinta ta zubar da ruwan bakin cikin bowl din daya kawo.Maganin tsaida amai ya bata tasha sannan ya had'a mata ruwan rayuwa don ta sami kwarin jiki.
Cike da tausayawa yace"Hanan d'ita idan har Allah ya saukeki lafiya ina ganin zaki dan huta don kina wahala sosai... Ni gani nake mah kamar wannan cikin yafi baki wahala..... "
"Abu jasmine badai kana nufin planning zamuyi ba? " Ta fadi hakan kamar zata saki kuka.
Mubeen dake rik'e da wata riga yana kokarin sanyata bayan ya cire wacce ta baci,jin abinda ta fad'a ne ya sanyashi saurin zira rigar,sannu ahankali ya tako zuwa inda take zaune,zaunawa yayi akusa da ita tare da riko duka yatsun hannayenta yana d'an murzasu ahankali.
"Hauwanah...... " ya k'irawo sunanta cike da so da k'aunarta
Ak'asan mak'oshi ta amsa da"Na'am mijin Hauwa'u.... "
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Matata please ki bari muyi planning din kinga ko wani ciki kika d'auka wahalar min dake yake.......... "
Sakin wata kuka tayi tare da rungumosa tace"No please mijina karka min hakan wallahi ina masifar son naga na tara 'ya'ya dakai sabida irin son da nake maka....mijin Hauwa'u please........ "
"Ba wai ina nufin bazan bari ki sake haihu min bane,a'ah so nake kawai ki dan huta na dan lokaci kema ki samu ki dawo da jikinki......ur sister shall continue from where u stopped........ "
Da sauri ta tureshi daga jikinta tana fadin"Yauwaa! yanzu naji batu.... Mubarak yau kayi nasarar nuna min cewar da gaske baka qaunata kamar yadda nasha tunanin hakan dats why kake bakin ciki na haihu dakai.... Kila mah Jasmin da wannan babyn da nake dauke dashi duk 'ya'yan kaddara ne awurinka tunda baka qaunata.... Zahranka kawai kake qauna kuma ita kake son ta shigo ta haihu dakai.........wallahi har naji na soma tsanarta yanzu tunda har take k'ok'arin shiga tsakanina da mijina............ "
Advertisement
Tassss!!! kake ji ya kwasheta da wawan mari,idanuwansa sun rufe da b'acin rai da har ya sanya ya manta cewar bata da wani isasshen lafiya.
Yace"Akul! dinki.... Karki kuskura ki sake cewa kin tsani Zahrata agabana....don yadda kike gani na din nan bana qaunar duk wanda baya qaunar Zahrata..... Its beta for u to continue loving her idan har kina son Mubarak ya cigaba da yi miki kallon matarsa........ "
Tsaida kukanta tayi,cike da mamaki take kallonsa da jajayen idanuwanta tace"Abu Jasmin tunda mukayi aure baka tab'a d'aga hannu da sunan marina ba,amma ayau wata side chick ta sanya ka d'aga hannu ka mari matarka ta sunnah... Amma ina son ka sani yakai mijina,tunda har ka d'aga hannu ka mari Hauwanka toh ina mai tabbatar maka da cewar watarana zakayi dana sani mara amfani.......... "
"Koda yake sam banga laifinka ba... I will blame myself for everything dat is happening to me... Nice silar faruwar wannan salon cin fuskar da kake min,don da'ace tun farko ban cusa kaina gareka kuma na nunawa mummy cewar ina sonka ba toh kila da bata kaimu ga yin aure har na fuskanci matsalolin da nake fuskanta daga gareka ba,burin kowacce 'ya mace ta auri namiji nagartacce mai kuma sonta tsakani da Allah,wanda take burin ta sami dukkan farin ciki agidansa,take kuma burin su shinfida rayuwar soyayya abar kwatance da kuma birgewa ga kowa.....amma ga dukkan alamu ni banyi dace ba sabida kamar ni nakeso amma ni kuma ba'a son nawa,afilli ana nuna min kamar ana son nawa,alhalin acikin zuci ko kusa bani da wani gurbi acikin zuciyarka....Allah ne kawai ya kaddara auren U...........Mijina duk da cewar ban tabbatar kana qaunata ko akasinta ba,ni shaidace akan yadda kake nuna min kulawa sosai,tanan zan iya cewa kusan nafi kowacce 'ya mace sa'a don Mijina akwai iya kulawa da iyalinsa.... Amma zuwan wannan Zahran cikin rayuwarka ya ruguza komai...shigowarta cikin rayuwarka ta sanya nayi ban kwana da duk wani farin ciki,ko kana tunanin wai ko kadan ban damu bane akanta shiyasa kake yin duk abinda kaga dama agabana? Wani lokutan mah haka kake yin waya da ita agabana sai idan kaga kamar raina ya d'an baci shine kake barin wajen,toh ka sani bawai bana kishinta bane kawai dannewa nake,kuma kai kanka ka kwana da sanin cewar kukan zuci yafi na filli ciwo da kuma illa.......Ni ban hanaka k'aro aure ba amma don Allah ka daina nuna min agabana cewar kafi qaunarta because u are silently killing me hubbyna............. "
"Hauwa'u enough please! U are hurting me the more......... ". Ya fada da karfi.
Itama cike da tsiya ta cigaba da magana abinda bata tab'a masa ba,tace"Mubarak ka kyaleni nayi magana don abin naka ya gama cika mini ciki,kai kanka kasan gaskiya amma sabida mahaukaciyar soyayyar dake dibarka ta sanya kake take gaskiyar kuma kake kuntata min.Kai aganinka za'a iya samin wata 'ya mace da zata iya yi maka abinda ni nayi ne? Na danne kishina na baka gwarin gwiwa da kuma goyon baya tare da tayaka kafa gwamnati agun wata budurwa..... Na kuma yi takun basaja azuwan ni k'anwarkace sabi kawai kada ta d'ago cewar ni matarkace,kuma don kar taga acikin dangi babu wanda ya tarbeta azuwan fiancee dinka..... Ka gaya min wacce macece kake ganin zata iya yin hakan.......? "
(lol Halima zaki iya kuwa?)
"Babu kam............. " Ya fadi cike da tausayinta.
"Then isn't dat enough for u ka tausaya min ka daina fifita wata 'ya macen akaina? Kai idan ba namiji mah butulu ba ai yaci ace na fita matsayi acikin zuciyarka,amma da yake dama can ni ba'a son nawa shiyasa ake nuna min kiri-kiri wata can ta fini daraja da kuma matsayi............ "
Advertisement
Matsawa kusa da ita yayi tare da rugumota yana fadin"Haba Hanan d'ita wallahi wallahi idan kika cire iyayena mata,toh wallahi babu wata wacce ta fiki matsayi da kuma daraja aguna,bar ganin ina son Fadima da kuma yadda kike ganin ina nuna sonta ah filli kice ta fiki matsayi aguna,wallahi sam, my dear wife '' always cumx first kuma wallahi believe me ba dadin baki nake miki ba................ "
Kokarin magana take sai yayi saurin had'a bakinsa da nata ya soma tsotsa cike da kwarewa da wani salo.Wasanni sosai ya shiga yi da jikin nata,sai da ya tabbatar ya kashe mata jiki har take nemar ayi mai gaba dayan sannan ya janye jikinsa don shi kansa hakuri kawai yayi sabida rashin lafiyarta idan ba haka ba da sun kashe arna da safiyar nan.
"Babyna kinga ayyuka basa bari kwanan nan ina zama na kula dake,shine nake tunanin kona kira Goggo Ladidi ne tazo ta zauna anan gidan har ki haihu? meh kika gani?
Da k'yar ta iya daidaita numfashinta tace"Nayi zaton koh wurin mummy zaka kaini na zauna har sai nayi arba'in? "
Gwalalo idanuwa yayi waje yace"Ke! har kusan watanni shidda acan? No I cant,ke kanki kin san bana iya kwana ni kadai ba tare da na jiki akusa dani ba.... Kawai ki zauna anan,yanzu zan kira Goggo Ladidi kuma nasan zata zo don ba miji gareta ba kuma tana da tausayi..... "
(Hahaha! dan jaka kasan da hakan kuma kake son ka mata kishiya?).
Tana kallo ya sanya kiran Goggo Ladidin,babu bata lokaci yayi mata bayani tare da fada mata bukatarsa na son ta dawo nan da zama ta kula masa da matarsa har ta haihu.
"Kai d'an nan har sai ta haihu fa kace? acewar Goggo Ladidi.
Yace"Goggo don Allah taimako zakiyi wa 'ya'yan naki,kinga ni sabida bana zama ne shiyasa nace bari na kiraki mu nemi wannan alfarman......
Sauke numfashi tayi kafin tace"Toh! naji shikenan amma sai naji daga bakin sauran yaran nawa don baku kadai ne ya'yana ba,kaga suma suna da hakki akaina......... "
"Haba Goggo har sai kin nemi izini daga gun su Tijjani kafin kizo? Ki tuna fa muma 'ya'yanki ne ba bare bafa..... "
Tace"Ayya d'an nan baka fahimce ni ba amma ba damuwa ina nan tafe bayan sallar azahar...... "
Cike da farin ciki yace"Masha Allah! Goggo an gode Allah ya saka da alheri.... Insha Allahu zan turo direban gidansu Mummy anjima ya taho ya daukeki bayan sallar azahar din...... "
"Madallah nagode...... "
Goggo Ladidi wata k'anwar mahaifinsu Mubarak ce da take zaune take zawarcinta ah 'rijiyar Zaki'. Shekarar mijinta kusan biyu kenan da rasuwa kuma tun bayan rasuwar tasa batayi wani auran ba.'Ya'yanta biyar,maza biyu,mata uku.Duk mazan sun girmi su Mubarak,dayake ita tayi saurin aure,tana zaune ne agidan 'ya'yan nata tare da surukanta wato matayensu ayayin da duka matan uku suna dakunan mazajensu.Mazajen dai ba wani karfi garesu ba amma agaskia suna kokari,Tijjani shine babban danta,yana siyar da kayan miya ne akasuwa ayayin da Buhari yake aikin walda.
K'iran Mummy yayi bayan sun gaisa yake cewa"Don Allah mummy zuwa bayan azahar ki tura Malam Audu yaje ya taho mana da Goggo Ladidi walhi jikin Hanan dince har yanzu sai ahankali jiya mah ba muyi wani baccin kirki ba,shine na kira Goggon na roki alfarman ta dawo nan da zama ta dunga kula da ita har ta haihu tunda ni ba zama nake ba balle na dunga kula da ita........ "
"Allah sarki Hanan da gani wannan cikin yafi bata wahala akan ta Jasmin.... "acewar Mummy
Yace"Walhi nima shi na gani mummy.... "
"Amma ita goggon ta amince zata zo din? "
Yace"Ta amince.... "
"Shikenan bayan azahar din zan tura shi,ka gaida min da ita Hanan din zanyi kokari na shigo gobe idan yaso sai na taho da Jasmin din gaba daya sabida makaranta.... " dayake tun jiya Jasmin din ta tafi weekend.
"Ba matsala! mummy an gode..... "
Ajiyar zuciya ya sauke yace"Baby ya kamata naje na amsa kiran oganmu kinga tun jiya yake nemana kuma ni bana son na barki ke daya agida,kuma dakwai sauran lokaci mai tsawo balle nace na jira ita Goggon tazo kafin na tafi..... Meh kika ce? "
Kwantar da kanta tayi saman k'irjinsa tace"Deserved one ka tafi kawai kada yace ka rainasa,kada ka damu dani I will be fine.... "
"A'ah bari dai na k'ira Labeebah idan tana gida tazo kafin Goggon ta iso hankalina zaifi kwanciya..... "
Kan tayi magana ya sanya k'iran Labeebah,bugu daya,ana biyun ta daga,bayan sun gaisa yace"Kina ina? "
"Ina gida." acewarta
Yace"kina wani abin ne?
"A'ah.... Yaya lafiya? "
"Qalau.... Ina Mus'ab? " tace"Gashi nan tare dani.... "
"Toh bashi wayar..... "
Mikawa Mus'ab wayar tayi,bayan sun gaisa Mubarak yace"Inlaw don Allah wata alfarma nake nema.... "
"Yaya fadi ina jinka.... "
"So nake don Allah ka mana aron Labeebah tazo ta kula min da Hanan wallahi jikin ne har yanzu kuma oganmu na nemana urgently,don Allah zuwa bayan azahar zata komo.... "
Yace"Haba yaya don wannan shine saika rokeni? Ka tuna kaima fa kana da iko akan Labeebah?... Shikenan yanzun nan zan kawota Allah ya bata lafiya.... "
Sosai yaji dadin kalaman sirikin nasa,yace "Ameen Mus'ab nagode sosai....Allah ya bar kauna da zumunci.... "
Cikin mintunan da basu wuce talatin ba,sai ga Labeebah ta fado dakin tare da sallama.
"Har kun iso? " acewar Mubarak yana kokarin mik'ewa.
"Eh! Yaya ina wuni ya mai jikin? "
"Qalau.... Mijin naki fa? "
"Yana falo.... "
Zuwa yayi suka gaisa sannan ya komo dakin yana fadin"Oya! tafi ki sallamesa wai zai wuce.... "
Ta fice.Komawa inda Hanan take yayi,yace"Baby mai zan taho miki dashi idan zan dawo....? "
Tunani ta tsaya yi,can tace"Gasasshiyar kaza,sannan idan kaga goba itama ka siyo min.... "
Lak'atar karamin hancinta yayi yana fadin"Da alamun wannan babyn tamu akwai kwadayi..... "
Murmushi kawai tayi abinta.Yakai mata simple peck sannan ya fice yana fadin"Take good care of urself for me,make sure dat kafin na dawo kin ware....... Love you matar Mubeen..... "
Sosai taji dadin maganganunsa,ita kanta tasan Mubeen na qaunarta amma ah ganinta yafi qaunar Zahra.
Tafe yake acikin mota amma duk maganganun Hanan sai dawo masa suke aka,ya sani tabbas baya k'yauta mata ko kadan,ya kuma san yana masifar qaunarta amma besan ko wani irin so ne yake yiwa Fadima ba da har yake jin bazai iya cigaba da rayuwa idan har bai sameta ba.Maganar Hanan dinsa gaskiya ce da take cewa bai dace yana nuna mata yafi son Zahra akanta ba,sam bata cancanci hakan ba.Atake anan yayi alqawarin zage damtse wajen nuna mata cewar tafi kowacce mace matsayi da daraja acikin zuciyarsa.
"Ko dai na rabu da Fadima ne because agaskia ina son matata,bana jindadin yadda nake kuntata mata...... " ya fadi hakan ahankali.
"Nooooo!! agaskia bazan iya hakura da Zahrata,sai dai zan dunga kokarin danne zuciyata na daina nuna son Zahra agabanta kamar yadda Yaya Mahmood ya fada.....toh ko Yaya zancen brother da batun mummy? Anya yayi mata maganar kuwa?idan har yayi toh ina aka kwana da zancen?... Bari zan kirashi naji................. "
*********
"Yauwa Dr. Mubarak dama so muke mu turaku wata course na tsawon watanni shidda akasar india kaida abokanan aikinka Dr. James da kuma Dr. Vero,don haka idan kun shirya nan da sati biyu saiku tafi..... "
Da sauri yace"Haba sir! ya zaka min hakan? Koka manta da lalurar matata ne?Sir tana bukatar kulawata,she really need me by her side....so please sir ka taimakeni kasa ah canzani da wani,don Allah ka daure ka min gatan nan..... "
Cike da tausayinsa Dr.Abdullahi yace"Haba Dr. Ina son ka sani wannan umarnin daga gun Chief medical director ne (CMD),ba wai ni na sanya sunanka ba,ka tuna fa wancan karon mah haka ka kawo excuses,da k'yar ya yadda aka canzaka da wani,kuma yanzu idan aka sake kai masa wani uzurin naka baka tunanin zaiga kamar raina masa hankali muke? Ina ganin kawai hakuri zakayi wannan karon kaje idan ba so kake ni da kai mu rasa aikinmu ba.... "
Shiru Mubarak yayi cike da jin haushin CMD din nasu don ya lura sosai ya saka masa ido,komai sai kaga yace shine zai yi wai sabida yana da kokari,hazaka da kuma fahimta.
"Zan dai iya maka taimako daya? " acewar Abdullahi.
"Wacce taimako kenan.... "
Yace"Tukunna dai.... Cikin nata wata nawa ne yanzu?
"4months 2weeks.... " ya bashi amsa atakaice.
"Good.... Zan sanya wani Doctor ya dunga zuwa gida yana kula da ita har ta haihu..... "
"Shikenan nagode.... " Mubarak ya fada azuciye ayayin da ya juya zai bar office din don sosai yake jin haushin Dr.Abdullahi din don ya tabbatar hadda hadin bakinsa acikin wannan batun course din da ake son aturasu.
Kome ya tuna kuma,sai gani nayi ya sake dawowa gun Dr.Abdullahi din.
"Akwai abinda kake bukata ne kuma?acewar Dr.Abdullahi.
"Bana bukatar likita namiji ya dunga kular min da mata...abaiwa female wannan aikin...... " Ya fada cike da kishi.
Dariya sosai Dr.Abdullahi yayi,yace"Dr.Mubarak sarakan kishi kenan.... Karka damu ni Dr.Basira mah nake tunanin baiwa wannan aikin..... "
"Good... Sir am sorry to say it won't look funny idan har aka kuskura aka baiwa namiji aikin nan,kada akuskura because ko kadan bana wasa da iyalina........ "
Ya juya ya fice zuwa office dins.shi kuma Dr.Abdullahi wata malalaciyar tsaki ya sake yana fadin"Kaji banza! Sai shegen nuna isa da iko.... Toh Waye baya kishin matar tasa? Don't worry na kusan ladabtar dakai da wannan jijji da kan naka don baka san yadda nake jin haushinka ba sabida yadda CMD ke ji dakai... Komai kai ake sanyawa kayi why? Mu ba mutane bane?.... Mtswwwwww wawa kawai......... " ah iska yake fadin wannan maganganun don tuni Mubarak ya dade da zama acikin office dinsa.
Ya tarar da aiki sosai ah office dinsa kuma ya tabbatar duk muguntar Dr.Abdullahi ne,ga kuma wasu patients da aka turosu don ya duddubasu,yama rasa ta inda zai fara,kuma yana son ayau din nan yaje ganin Zahransa.
Sanya kiranta yayi ya fada mata cewar ta saka ido ahanya insha Allahu yana nan tafe bayan sallar la'asar.Sai daya gama duba duka patients din sannan ya sanya kiran Mahmood don ya fada masa yana nan shigowa Zaria kuma ya shirya yi masa rakiya zuwa gidansu Fadimar.
Bayan sun gaisa ya kuma tambayesa ya aiki? Ya bashi amsa da Alhamdulillah!
Yace"Brother! dama so nake na gaya maka cewar zuwa anjima kadan zan shigo Zaria ganin Fadima shine nake son if u are less busy don Allah sai ka min rakiya kaga bai dace naje gidan surukai ni daya ba....."
Gaban Engr.Mahmood ne ya yanke ya fadi,ya rasa mai zaice wa Mubarak,dakyar ya daure yace"Kash! brother meyasa baka fada min da wuri ba idan yaso sai mu tsara ranar da zamuje? don wallahi yanzu haka ina kaduna munje wani seminar kuma sai gobe zan komo Zaria.... Why not ka hakura sai zuwa wani lokaci idan nayi free sai muje? "
"No,brother gwara naje din yau don na mata alqawari,kuma idan banje yau din ba toh ban san ranar zuwa ba sabida ayyuka sun min yawa acikin kwanakin nan,and the worst part is dat nan da sati biyu wai za'a turamu wata 6months course ah India......... "
"Alhamdulillah!! Kafin ka dawo I will make sure dat na kammala komai... " Mahmood ne ke fadin hakan acikin zuciyarsa.
Afilli kuma yace"Allah sarki!... Agaskia kam ya kamata kazo ka ganta ku daidaita da ita kafin ka tafi..... "
"Yauwa! Brother ya zancenmu? Kayi wa mummy maganar? "
"Haba! dan'uwa mai kake ci na baka na zuba ne,kai dai juz focus on Zahra,kabar zancen mummy ahannuna,idan komai ya daidaita zan sanar dakai.... "
Cike da farin ciki yace"Okay nagode brother Allah yabar kauna da zumunci...... " sukayi sallama.
**
Engr. Mahmood na gama waya da Mubarak,yaji hankalinsa yayi mugun dagawa,don da gaske din yaje Seminar din ah kaduna.Sam baya son Mubarak yaje gun Fadimarsa (lol kuji sata da tsakar rana). Ji yayi kawai yana son jin muryarta.
Advertisement
- In Serial63 Chapters
Yora Chronicles
[Arc 0 - The Prologue] Airen and Yuelei Casteya - Two twins separated in act of revenge not of their own doing. One is sent to the frozen north, where she is adopted by a frost phoenix and taught to survive in the harshest of conditions, eventually meeting with the forces that govern nature itself. The other is sent to the southern deserts and is saved by a band of slaves-turned-raiders who take him in as one of their own, where he eventually came into contact with a being that calls herself the History Eater. The two sought power and the forces of the world would soon listen, but not without their own aspirations. And perhaps if the two were to meet again, they would be so warped by their own hands and would not even recognize the other. [Arc 1 - Disciple of the History Eater & Knighthood] Under the guidance of Fieluri, the whimsical being from the Archive, Airen moves south to the Red Slate Republic to attend Stonewall Military Academy. There, he finds himself wrapped up in the History Eater's ploys, and at the same time, learns of the somber side of society in the slave-driven republic. Eventually, under Fieluri's instruction, he descends into the depths of dungeons where he eventually reunites with an old acquaintance. Yuelei, who has grown used to living in the snowy mountains, moves north to the Holy Land of Ecclisa to attend the Royal Knight Academy. After Lin leaves, she slowly adapts to living with humans again, but not without ceaseless caution. The thinly-veiled peace is eventually broken, for the monsters that haunted the nights in the Whitefrost Mountains are returning once more. In response, the Holy Land of Ecclisa slowly prepare for war, but Yuelei is not just a mere bystander. All paths eventually leads to conflict. When it arrives, one can choose to deter it away, or to revel in it. [Arc 2 - WIP] NOTE- Based on an internal discussion, please be advised the earlier chapters of this novel [Arc 0 and Arc I] is going through a major revision and rewrite to gap the 6 years experience since the first draft of this novel. For questions,concerns,comments or contributions, feel free to join us on our discord: https://discord.gg/Vdp2k6v © 2018 by Phyantasm. All Rights Reserved.
8 435 - In Serial204 Chapters
Summoned and Unwanted
Continue reading here: https://www.webnovel.com/book/summoned-and-unwanted_17037711905226605 _________________________________ At a young age, Vincent lost his parents to an unknown widespread mutation infection. He survived but got mutated as well. In the end, he blamed himself for their deaths as he was the one who insisted to go. Years later, Vincent met with an infection survivor named Kevin who helped him heal his heart. However, not all stories have a happy ending. Kevin would pass away ten years later, leaving a mysterious book with six heroic tales. As Vincent finished reading the book, it teleported him to another world. A world of magic and sword.A world where heroes are referred to invaders by the people of the land, where summoned heroes are unwanted, hated, and hunted. Vincent would gain a unique hero class, yet his mutation develops a class as well. He would become the first being with two classes in the world. This is the journey were Vincent starts from a zero to a hero. From a single young teen to a harem lord, from a nobody to an important person to many. A god, a king, a miracle worker, a husband, a lover, a hero... Well, these are the few titles he will gain as he will live his new life, his new beginning. This is the story of how the seventh unwanted hero tries to do his best while learning from every experience he encounters. To go back to his world?To protect his new loved ones?To find the mystery of the book?Or to create a haven where he and his loved ones can live in peace? Those questions are for the readers of the book of heroes to find out._________________________________ Chapter words 1,800+ (1-182)Chapter words 1,600+ (183+)_________________________________ Support Author https://paypal.me/SummonedAndUnwanted ________________________________ Discord https://discord.gg/CSg5Baf ________________________________
8 176 - In Serial31 Chapters
Planet At War
A planet in a perpetual state of war. And the story of its soldiers fighting on it. I'm using this book to challange myself to write everyday, so if you find any bad grammer or weirdly structured sentences, please tell me! That's how a writer get's better at writing. Thanks for giving this book a chance
8 180 - In Serial32 Chapters
HER BLACK SOUL
Her black eyes was looking at a far distant image that soon dissapered . Her once happy life has turned into a total mess.Moreover this hot ,extremeley handsome,cold man is making her life more miserable.Her so ordinary life has taken a new turn. She was once a bright ,cheerful girl. But now all it remains is far distant from what she use to be..unfolding truth about herself ,even the man who is beside her is not simple as it seems to be. Reality isnt what she sees but is a truth hidden in mystery.
8 90 - In Serial8 Chapters
Ghastly Adventures
A deity, some terrorists, an oil baron's son, a time traveller, a psychopathic detective, and the strongest man alive all meet in one ghastly tale. This tale, among many others, will be told along our ghastly adventure. This is vaguely inspired by the "Villains Unite" genre.
8 202 - In Serial233 Chapters
Reborn As The Villain
I was walking to the convenience store and the next moment I knew, I was inside the villain's body!? What is going on!? This world is known as the world of Star Fantasy, a popular RPG that dominated the gaming charts. Tournaments were held all over the world to celebrate the success of this game. The top ten guilds were invited for every tournament to recruit new talent for their teams. Liam was part of the third strongest guild in Star Fantasy. He suddenly woke up as the son of one of the strongest knights in the empire. He was known as one of the main villains of the story. Arnold von Berkley. He must find out if there are more of him out there. Was he the only one summoned? If so, how can he avoid his inevitable death? By eliminating his death flags!
8 1182

