《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》PART 2:CHAPTER TWO
Advertisement
*💘SHIN SO DAYA NE? 💝*
*MALLAKAR:HAFSAT AL-MUSTAPHA*
*WATPADD:HAFNANCY💞*
*KASHI NA BIYU:RIKICIN KARSHE*
🌼BABI NA BIYU🌼
*💧💧💧KAI AMARE💧💧💧*
💧💧 💧💧
💧 💧
*page 3-6*
Har muka isa kanon ban mah san mun iso ba sabida tun shigata motar,cigaba nayi da sana'ar kukana,Ash kuwa sae aikin rarrashina take don ni da ita kawai muke xaune agidan baya,ita kuwa Zuwairah gidan gaba ta xauna wacce jefi-jefi suke d'an taba hira da meh tuki wanda na lura kamar yana cikin abokan ango.Shi din mah yayi rarrashin duniyar nan amma naki nayi shiru,can yace arabu dani kila so nake shi angon nawa yazo ya rarrashi abarsa da kansa,abin ya baiwa su Ash dariya,ni kuwa haushi maganar tasa taban kamar na tashi na kifa masa lafiyayyun mari.
Mubarak ne ya fad'o min arai,yanzu shikenan mun rabu kenan? Yanzu baza'a taba k'irana da matar mubeen ba kamar yadda nake ta burin hakan sae matar Mahmood Nakowa?abin mamaki mah wai dangin mijin nawa ah kanon suke,kada watarana fa mu had'e dashi.... Wani b'angaren xuciyata kuma yace"xancen banza keda mah ah Zaria zaki zauna? Sannan meye naki na wani damuwa akan mutumin da baya qaunarki,mutumin da kuma sam be damu da rayuwarki ba?
"Toh! amaryar Nakowa mun iso,sae ki had'iye kukan naki ya isa hakanan kinga gidan surukai xamu shiga kada suga kina koke-koke su aza ko surukar tasu ba jaruma bace...... "
Ash ce ta katse min gajeriyar tunanina alokacin data bud'e min kofa da k'yau wai na fito,sae asannan na ankara da cewar har mun iso ban sani ba.
Sannu ahankali na sako kafafuwana waje tare da dire su akasa,wani daddad'ar ni'imtaccen iskar yammacin nan ne ya soma min barka da xuwa.fitowar tawa tayi daidai da wayar da wannan meh tukin keyi wanda ayanzu nasan sunansa don naji Zuwairah ta ambaci sunan wai *'KHALEED'*.
Cewa yayi"Kai dan iskan ango kana ina? gashi fah mun iso amma anki bamu amaryar..... "
Saurarawa naji yayi,can yace"Na taba maka irin wannan wasar ne? Ka yadda dani anki bamu ita wai sae kaje da kanka.... "
Ya sake saurarawa,can ya d'an d'ara yace"Kai wasa nake maka mallam karka min hauka,ga amaryarka nan mun kawo maka ita,tasha kuka kuma har yanxu tana kan yi ne sae kazo ka lallashi abarka........ "
"Ayyyirihiiiiiiii,lale marhaba da zuwan amarya.... " rangad'e rangad'en gudar dangin mijina ne ya hana min jin k'arshen maganar Khaleed da mijina.Ni kuwa jin sun nufoni ya saka na k'ara jan mayafina gaba don kada suga fuskata.
Wata 'yar matashiyar budurwace naga ta rungumeni tana fadin"Oyoyo!amaryarmu sannu da xuwa...... "
Mama Jamila ce ta rad'a min magana akunne,cewa tayi"Ki shiga da kafar damarki tare da bismillah,haka kuma xakiyi idan aka maidaki can gidanki.... "
Daga mata kai nayi alamar naji jawabin nata,daga haka naji wasu mata su wurin uku suma sun rungumeni kamar zasu kada ni akasa suna min sannu da xuwa har muka shige gidan.
Wani daki aka saukemu aciki wanda muka ji wani daddad'ar kamshin turaren wuta ya mana maraba da xuwa,gaskia ba laifi suma kanawa akwai son kamshi.Maganar gaskia ba k'aramin karramamu akai ba,nima sae naji na d'an saki jikina amma har xuwa wannan lokacin ban yaye mayafin kaina ba,ina nan lullub'e aciki kamar wata munafuka,lokaci xuwa lokaci nake dago kai na d'an saci kallon mutane.
Cikin k'ank'anin lokaci muka ga an cika mana gaba da kayan ciye-ciye da shaye-shaye.Mama Sadiya ne suka dan taba amma babu yadda basuyi dani ba amma naki ci.Ce musu nayi ak'oshe nake.Ak'arshe dai ruwa kawai na d'an sha.
Advertisement
Mama Jamila ce tace"Yarinya idan zaki mah saki jiki toh tun wuri ki saki don anan zamu barki,gobe idan Allah ya kaimu komawa gida abinmu xamuyi..."
Juyawa tayi ga Mama Sadiya tace"Sadiya hanzarta ki gama cin abincin ki min rakiya xuwa gidan wata k'awata dake nan jambulo,bazamu jima ba..... "
"Toh Addah... "acewar Mama Sadiya don Mama Jamila na gaba da ita.
Ni kuwa wani sabbin hawaye naji sun ziraro min saman k'unci,tayaya xan soma rayuwa agidan wasu bayan na sab'a da namu?taya mah xan soma had'a shimfid'a daya da wani k'aton gardi amatsayin mijina?
Yaye min mayafi naji anyi ana fad'in"Ai kya bari muga fuskartaki muga ko kin fini kyau koh? "
Ji nayi an fashe da dariya,ni kuwa gabana ne naji ya yanke ya fad'i,dakyar na iya d'ago kai ina duban wacce ta yaye min mayafina,ido hudu nayi da wata tsohuwa wacce kana ganinta kasan ta dad'e ana cin sallar idi da ita.Sae dai ba'a wani gane tsufanta don jikinta meh k'yau ne.
Tace"Masha Allah!.. Ashe dai megidan nawa balarabiya ya zab'o mana shiyasa yake ta rawar kafa da dokin auranta..... "
Aka sake fashewa da dariya akaro na biyu,ni kuwa d'an murmushin leb'en baki ne kawai ya sub'uce min,atake anan na gane cewar wannan tsohuwar kakarsu ce.
Tace"Amarya share hawayenki,don ni dake xamuyi zaman lafiya idan da hakan kika zo,idan kuwa da akasinta kika zo,toh nima nan uwargida ashirye nake...... "
wasu 'yan mata ne naji sunce"sae kakus! Kakaaa rigima.... " aka fashe da dariya.
Haka dai tayi ta mana barkwanci da wasannin wanda atake anan naji kawai tsohuwar ta shiga raina.Su Mama Jamila kuwa suna gama ciye-ciyensu suka sa kai suka fice xuwa unguwar da suka ce xasu,muka rage daga ni,Ash,Zuwairah sae kuma Anty Hajaar wacce ga dukkan alamu jininta ya hadu dana Kaka rigima,don sae hira suke ta xubawa.
Ba'a wani jima ba muka ji an soma k'iraye-kirayen sallar magrib,daya bayan daya muke shiga bandaki muna dauro alwala.
***
Itama Suhaima anata b'angaren an musu tarban mutunci,sosae aka karramasu.Reedah itace wacce ta soma rungumota,ta rad'a mata magana akunne"Oyoyo sahibata,barka da xuwa,yau Allah ya cika muku burinku ta mallakar junanku,Suhaima dear welcome home as matar yayanah...... "
Ita kuwa Suhaimar murmushi kawai tayi abinta tana meh jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na ratsa xuciyarta.
Leedar da Engr. bazan iya kamanta muku irin tsananin farin cikin da suka tsinci kansu aciki ba na ganin ayau sun mallaki 'the women of their dreams'.Bama kamar Mahmood wanda jinsa yake kamar Zaynab d'insa ce ta dawo.
***
"Anty Fadima inji Yaya Mahmood wai na kawo miki wa'ennan kayan ki saka wai xuwa qarfe takwas za'a taho ah daukeku xuwa reception...... "
Hafeezah 'yar baba Mu'azzam ne ke yiwa Fadima wannan maganar wacce take kusan sa'ar su Suhaima.
Kokarin magana nake sae naji Ash ta rigani,cewa tayi"K'anwata zubasu saman gado yanzu xata shirya kinji? "
"Toh.. " kawai tace sannan ta zubasu saman gadon dakin ta fice.
Ina gama ganin ficewarta na dubi inda Ash ke xaune nace"Sannu sarkin felek'e da iyayi,ina fatar da kika amshi wannan kayan ke zaki sakasu kuma ki bisu donni yadda kika ganni nan babu inda zani.... "
Zuwairah ce tayi saurin taran numfashina"Haba babe ya kike neman kwafsa mana ne?"
"Ke dai Zuzu banni da ita da meyi take yi,yanzun nan kuwa xamu hau sama mu fad'o don bazan tab'a bata goyon baya wajen wulaqanta sirikai ba..... "
Advertisement
"Toya isheki hakanan tunda de ba surukan naki bane,don haka babu ruwanki idan mah zaginsu nayi.... " acewata.
Ita kuwa Ash cewa tayi"Wallahi hadaki xanyi da Anty Hajaar ai kin san halinta sarai.... " tasa kai ta fice daga d'akin da nufin xuwa gun Anty Hajaar din wacce take dakin Kaka rigima suna shan fira.
Dama ashe taku ce tai wa Fadimar,babu kai kararta da xatayi gun Anty Hajaar,taku ce kawai tayi,nemo Hafeezah tayi tace mata"Don Allah k'anwata lambar yayan naki xaki ban,wayar amarya ta mutu balle akirashi da ita,ni kuma xancen gaskia bani da lambarsa.... "
Ta fad'a tare da mik'a mata wayar,murmushi kawai Hafeezah tayi tare da k'arban wayar ta latsa mata harufofin layinsa don tasanshi aka,lambarsa babu wuyar rik'ewa.
"Nagode my chuchu... " ta fad'a ah sa'ilin da Hafeezah ta mik'o mata wayar.
Babu b'ata lokaci ta sanya k'iransa,sae daya d'an jaah aji kafin ya d'aga.
"Hello!! pls who's on the line? " ya fad'a cike da k'asaitarsa.
Saukar da ajiyar xuciya Ash tayi,kana tace"It's the bride's best lady Aysha...... "
Tabbas ya ganeta! Sahibar matarsa ce,adakile yace"How may I help you? "
Tace"Gaskia fa kun mana laifi babba,meyasa ba'a fad'a mana cewar akwai reception agidan ango ba sae akurarren lokaci? "
Shi kansa yasan tabbas ko kadan basu k'yauta ba,kuma shi yama so afasa batun wata reception,amma kuma abokansa ne suka nace wai sae anyi don baza suyi asarar kudadensu ah iska ba sabida tun asali sune suka shirya masa wannan reception din.Sam be shirya fuskantar tashin hankali daga Fadima ba,amma kuma yaya ya iya? yasan kila Ash ta tsegunta mata zancensa don haka y xama dole yaje suyi ta ta k'are kowa ya huta,kuma yasan komin haukarta babu abinda xata iya yi don an riga an daurasu kuma igiyoyin auren ahannunsa take.Da wannan tunanin ya sami salama acikin xuciyarsa.
Ahankali yace"Pls we are very sorry tabbas munyi laifi babba amma agafarcemu..... "
Da sauri ta tari numfashinsa"Ni abar wannan xancen mah,yanxu gashi nayi nayi da ita ta tashi ta shirya amma fir tace bazata ko'ina ba,don haka sae kazo ka lallashi abarka ko kuma afasa..... "
Da sauri yace"Am on my way.... "
Ya fadi hakan da rawar murya tare da yanke call din.Dama acikin mota suke,suna kan hanyar xuwa daukarsu ne,abayansu wasu extra five cars ne ke biye dasu wanda za'a kwashi mutanen da keda ra'ayin xuwa agidan.
"Khaleed drive the car fast..... " acewarsa,ai kuwa kamar jira Khaleed yake abashi umarni,nan da nan kuwa sae gashi sun iso. Sai dirin motoci kakeji ah layin.
Ita kuwa Ash tana jin dirin motocin,da sauri tayi ciki,inda tabar Fadima hakanan kuma ta dawo ta sameta,wato lazimi take saman sallaya.
"Oya maza ki gyara ga ango nan shigowa,ke kuma Zuzu fito mu basu wuri.... "
Ta fadi hakan tare da janyo hannun Zuwairah suka bar dakin,Zuzu sae dariya take tana cewa"Kai Ash gaskia baki da dama,wato yanxu sae da kika kirashi shi yazo ya saka mata kayan kenan ko? "
Ash tace"Ai rabu da ita,dani take zancen,idan tasan wata ai bata san wata ba,dole gyad'a tayi mai,idan taki kuwa tasha matsa......... "
Ni kuwa binsu nayi da ido da baki bud'e kamar wata shashasha har suka fice,kafin na tsaya wani dogon tunani naji an doko sallama wanda nake tunanin babu tantama ango nawa ne.
Tuni gabana ya hau dukan uku-uku,rud'ewa nayi nama rasa abinda xanyi da kuma inda xan saka kaina. Mik'ewa tsaye nayi tare da gyara saman hijab dina wacce ta Anty Hajaar ce na ara.
Sae dana baiwa kofa baya sannan na k'arba masa sallamarsa,kai tsaye naji ya shigo yana furta"Amincin Allah da albarkarsa su tabbata agareki amaryar Mahmood..... "
Kunnuwana ne suka dauki kuwwar maganarsa,ji nake kamar na tab'a jin wannan muryar awani wuri,dakyar na danne wannan tunanin nawa tare da furta"Gareka kaima wanda ya yakice farin cikina har yaci nasara aka aura masa ni..... "
Ina gama fad'ar hakan naji wasu hawaye masu dumi sun ziraro min saman kunci har ina ji suna diga ak'asa.Shi kuwa sautin murmushinsa kawai naji,kana yace"Subhanallah! ah ina kika tab'a jin wani masoyi meh matuk'ar qaunar masoyiyarsa ya rabata da farin cikinta? A'ah sae de mah dada tsundumata cikinsa da zeyi..... "
K'ok'arin magana nake,sae kawai naji yayi saurin taran numfashina"Gimbiya pls safe the discussion for later,yanxu zuwa nayi na rokeki da pls ki rufamin asiri nasan sam bamu k'yauta muku da bamu sanar daku xancen reception da wuri ba sae akurarren lokaci,don Allah amaryata amana afuwa,ki taimaka ki rufa wa angon naki asiri ki halarci reception din nan,pls kada kisa naji k'unya agun abokaina don su suka shirya abin......... "
Afusace nace"Nasan tabbas an fad'a maka cewar bana jindadi,kuma yanxu ka nuna min cewar baka damu da rashin lafiyar matarka ba,ta k'unyar abokanka kake right? toh bari kaji,agaskia babu inda zani naje na kwaso sanyi abanza na janyowa kaina farawa daga square one ta rashin lafiyar ba......... "
"Fadima Zahra banfa sanki da Kafiya da taurin kai ba,haka kuma ban sanki da tsiwa da rashin kunya ba,infact ko bah kece da laifi ba,kina da saurin bada haquri,then why all diz all of a sudden changes? "
Gabana ne ya tsananta faduwar gaba,ah iya tsawon rayuwata nasan mutum d'aya ne ke gaya min wannan kalaman da bawan Allahn nan ya fad'a kuma shine *ENGR.MAHMOOD*.
Yana yawan cewa"Kai sister inlaw ni dai halayyarki sun mugun min,sam baki da hayaniya,baki da girman kai,komanki da sanyi kike yinsa,abinda yafi birgeni dake shine saurin bada haquri koda kuwa ba kece keda laifi ba.... "
For the very first time na samu kaina da son yin ido hudu da *Mijin Kaddarata* (another name for the novel).
Sannu ahankali na juyo da kaina xuwa gareshi.Fes! na sauke rinannun idanuwana akan fuskarsa.Hasken lanta din dakin ne ya bani damar k'arewa handsome face dinsa kallo.
Shock!startled!astonished!Amazed!.... and any other type of surprise mood u could think of,duk na shigesu alokaci daya ah sa'ilin da idanuwana da nashi suka gauraye cikin na juna.....
Kun san wah nake gani agabana??.......... 📝
A/N
Hahaha! amaryar Nakowa maida wuk'ar,duk mun riga da mun sani kece kurum aka bari cikin duhu,yanxu tambayar itace "Taya zamar auranku ze kasance? " mun fa k'osa mu gani.
*Hey! Hafnan's freaking fans! wai atunaninku family house za'a sauketa?? Haba its too early to start separating fight mana,atleast biko let dem enjoy their first night tukun Koya kukace? Lol
Pls ur comments & votes are getting down,I need like 100votes before I move on,lol juz kidding amma nasan inda zan kamaku ai.....!!
*IT'S YOUR LADY HAFNAN*💞
Advertisement
- In Serial96 Chapters
Royal Scales
A part-time enforcer, all Jay cared about was those closest to him and a job that let him hit people. That was before a betrayal sent him packing. Four years later he’s back, but his former boss thinks he lost his edge. Reduced to proving himself, he's thrown a straightforward task: collect on an overdue debt from some elf. As if life was ever that simple. With a vampire ex-girlfriend out for blood and a friend caught up in something dangerous, he has his work cut out for him. Jay always thought he was human, but his search for the elf raises questions that threaten his identity. Book 1, Once Lost Lords (Complete, Cover) Book 2, Lady's First Knight (Complete) Book 3, Trials of the Chief (Complete) Book 4, Prince in the Tower (Complete) Book 5, Rex of Never Was (Not started) Book 6, Gentleman Dirt (Not started) Book 7, The Emperor’s Flame (Not started)
8 238 - In Serial154 Chapters
Outlands
The Outlands stand as twisting spires of stone and cracked earth under an emerald sky, warped by feral magic and scorched by searing sun. Emaciated creatures scurry through its gullies and across its plains, feeding off what meager tufts of grass they can find. At night the darkness comes to life, shadows churning from an ages old curse. Sin's Curse. A lone hunter stalks these plains. In his bones are memories of ages past. In his blood burns searing vengeance. His people cry out for revenge, for he is the last of their number. These are his lands, and he will claim his birthright.
8 222 - In Serial78 Chapters
Demon King 101
Airumel. A world scarred by constant wars. With peace being nothing but a mere dream for weaklings with no standing in this harsh world. For thousands of years, conflicts arise between the forces of the Heaven Realm, which is an alliance of humans and their allied races, against the numerous demons of the Demon Realm. All in the name of superiority to decide who is the true owner of this world.In the midst of the conflicts come our main character, a Japanese high school student who was summoned as a familiar for a powerful mage from the Demon Realm. An unextraordinary teenager, armed with his will and guts as the strongest weapon he has in disposal. Can he survive this unexpected ordeal and prove himself among the ranks of the demons ?
8 58 - In Serial80 Chapters
Gravity and Divinity: Apocalypse System LitRPG
B-boy and parkour performer Jay Luckrun and others from his high school get an offer they can't refuse. A leveling system with stats and skills, access to other dimensions where dungeons hoard incredible loot, and magical powers that'll alter reality as they know it. There's a price, of course. Upholding the responsibilities of a near-extinct pantheon of multiverse protectors and facing oncoming cosmic doom, which sounds way over Jay's head on a drunk Friday night. But hey, how can he say no? Yeah, he'll fight monsters, divine apocalyptic forces, assassins, and many others, but that's par for the course in this Power Fantasy. The offer is coming from the most beautiful girl ever. And it nets him an OP Affinity to a fundamental force. Freaking Gravity.
8 199 - In Serial7 Chapters
Hardwork(a naruto fiction)(DROPPED)
So this dude is just a normal guy i guess.its a isekai? Not to sure but the mc died by another dude and pretty much he meet god and got tranported into a naruto world not all naruto i gonna add some of my ideas so enjoy. I don't own Naruto or any related stuff except My ideas.oh and the cover is not mine I don't know where i got it i just type sharingan on goolgle and images.
8 164 - In Serial51 Chapters
I am the king of all villainous villian : Volume 1 : against hell devouring beast
"fell in hell , suffered in pain , felt despair and terror for countless time , walked the path of life and death …… he will rise and become the one to rule over dead , spread terror against livings and rule over worlds. ….. mercy isn't thing he knows ,trust ? he doesn't even have one in himself. He , the one who rised from the ashes, crawled out from the depth of hell will now show the world who the true master of the world is ? celestials and demons shall be his vanguard, true dragons and divine phoenix shall be his war mounts , gods and devils shall be his war puppets. heaven shall be his war tetra and everyone remaining shall be his soldiers that follows him with whole heart loyalty. kill anyone that oppose me that's my principle. sometimes when death comes looking for me , I mistake it for my life long friend…..While I mistake life for long lost friend… I shall order and you all shall follow it….. let them show their powers , because a real villain only makes his moves when his pawn and chess pieces has finished their job for the chess master. which is me , a master…….. ……………….be gone thots !!
8 104

