《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》PART 2:CHAPTER FIVE
Advertisement
*💘
"Fadima I have to take us back,sabida yana da matuk'ar muhimmanci kiji labarin Zeey Maleek d'ita,jin labarin ne ze saka kisan yadda akai naji sha'awar son na aureki,amma kafin na cigaba da baki labarin pls let's eat first don yunwa nakeji sosae...." Ya fadi hakan tare da rik'e cikinsa kamar da gaske,so yake kawai ta d'an tab'a wani abin.
"Ni bana jin yunwa,kaci abinka kawai,kuma ka min sauri........ " na fada atakaice ina meh hura hanci.Da mamaki naga ya bini da kallo,kana yace"Saurin meh kike ne baby doll? Remember from now on,we hav the whole moment to spend together for the rest of our lives,Fadima ina son ki sani cewar aurena dake Insha Allah mutu ka raba ne...... "
Naso tanka masa amma kuma se naga idan na biye mishi zamu ta jan magana ne gwara kawai nayi shiru na bishi ahankali donna samu ya warware min zaren daya sak'a.
"Ki sakko muci idan ba haka ba nima baxan ci ba kuma bazan baki labarin komai ba,kinji nace wallahi... " yanayinsa ya nuna sam babu alamun wasa atattare dashi,hakan ya sa ba tare da na tsaya wani dogon tunani ba na sakko sabida na k'osa naji takun basajar daya k'ulla.Shi da kansa ya firfito mana da abubuwan dake shak'e cikin k'atuwar ledar daya shigo da ita.
"Baby doll wanne zakici aciki? Pizza ko garnished chicken🐓? Or u will like to take all?? "
"Lallai guy din nan ya mugun raina min wayau ba kadan ba,wai ni yakeso ya yaudara da salon soyayyarsa ko meh?hadda wani *'ba damuwa duk kayi ka gama xan bika asannu don mu wanye lafiya."
Hura min idanuwa naji yayi wanda hakan ya maidoni daga duniyar tunanin dana lula xuwa duniyar da muke ciki.
"Matar Mahmood ya naga kinyi shiru? Ko so kike na baki abaki? Iyyeh fada min karki ji kunyata am ur husband.... " ya fadi hakan tare da kashe min one eyes.
Dan guntun tsaki naja,nace"Bannaso ai nima ina da hannun da xan iya ciyar da kaina,garnished chicken🐓 din kawai xan iya ci.... "
Murmushi naga yayi yace"An gama my all,bari na dauko plate" ya mik'e tsaye,naga ya nufi b'angaren dinning,ata gefen dining din naga ya bud'e wata kofa ya shige ciki,atake na gano nan ne kicin din gidan.Ji nayi kamar na arta aguje nabar gidan kafin ya fito,amma se kuma naga rashin dacewar hakan,sam yin hakan ba class dina bane,kuma ai ina son nasan ta yadda akai ya sami aurena,don haka be kamata na gudu ba,xan bari mu wanye ta salun-alum idan yaso hakan,idan kuma ta tashin hankali da kuma k'eta yakeso arabu,then Fadima Sa'ad is ever ready for that.
Murmushin yaudara na sak'ar masa sanda naga ya nufo inda nake da plate ahannunsa.Cike da kissa da kisissina na mik'e na k'arbi plate din hadda wani duk'awa wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bashi ba.
"Dear ya naga plate daya kawai ka dauko? " na fadi hakan ahankali tare da lank'wasa murya.
"Ah plate daya xamuci.... " ya fada yana kallonta cike da mamakin wannan sudden sauyawar tata,daga shiga kicin ya dawo har ta canza ta koma Fadimarta daya sani? Ko dai tunani tayi taga rashin dacewar abinda take masa da kuma maganganun da take ta kwakkwab'a masa? Ko ta haqura ta rungumi kaddararta ne?
Axuciyarsa yace"No Fadima am not getting you at all... I guess you are upto something freakish & very mean... "
Ni kuwa axuciyata nace"Dan iska mamakin canzawata yake,besan cewa so nake na lallab'ashi ya gayan komai sannan nasan nayi ba,hadda wani wai ah plate daya xamuci abinci,shege daga yau sae de kaci abinci ah kwano daya da uwarka ba dai da Fadima Sa'ad kuma ba.... "
Advertisement
Sosae na sake jiki mukaci mukayi Kat! damu,mafi yawanci shi da Kansa yaketa feeding dina,ni kuwa sau uku kawai na bashi abaki ina meh cike da takaicin kaina.
Bayan mun k'are cin abincin,naga ya kasa haqura yace"Baby doll wat happened? Wannan sudden change din nan taki am suprised fa?kodai u're upto something ne? "
Murmushi meh ciwo na sakar masa,kana nace"No ba komai wallahi,ni de kawai kaban labari.... "
Saukar da ajiyar xuciya yayi,kana ya soma bani labarin rayuwar soyayyarsu shida tsohuwar matarsa **,mace meh tsananin sonsa da tattalinsa,mace meh gudun b'acin ransa da son kowa nashi,wani abin nasu da idan ya fadi sae muyi dariya,wani kuma na abin atausaya musu ne yanda wai matar babanta ta sanyata agaba,ashe wai tun tana 'yar karamarta mahaifiyarta ta rasu.Ta taso ne ahannun matar babanta wanda sam ko kadan bata qaunarta,har tayi aure wani lokutan mah takan zo har gida idan baya nan ta lakadawa ita Zaynab din dukan tsiya ita da 'ya'yanta mata,yayun Zeey din.Dakyar da sudin goshi ya taka musu birki ya kuma sanya aka masu iyaka da gidansu.Gashi ita Zeey din tana da haqurin gaske,komai aka mata sae kaji tace"wallahi dear nah na yafe musu har cikin xuciyata. "
Hakan ya saka Zaynab ta sake samun gurbi acikin xuciyarsa,sae ji yake kamar duk duniya babu ta biyun Zeeynsa,baya jin ze iya rayuwa da wata 'ya mace face Zaynab dinsa ko bayan ranta.
"Sae gashi rana daya na k'aryawa Zeey dita alkawarin dana daukar mata,yau gani ga wata 'ya macen amatsayin *' *'Fadima ranar dana soma ganinki alokacin da kuka kawo ta'aziyya kano,aranar se dana danyi jinyar xuciyata,don ganinki ya tuno min da Zaynab dita,everything about you was juz lyk hers,infact! hatta kamanninki da nata yanaso yayi iri daya.Ah yinin ranar na lura sosae na kamu da matsananciyar sonki,why? Because gani nake kamar Zeey dita ce ta dawo.
"Titsitseyar Hanan nayi,na sakata dole ta bayyana min alak'ar dake tsakaninki da Mubarak wanda ko kusa banso hakan ba,naso ace babu alak'ar soyayya atsakaninku,kuma wallahi banso kika bishi wani gun ba,Fadima sam be kamata ace amatsayinki ta 'ya mace musulma, kuma kamilalla kiyi trusting namijin da baki taba sanin halayyarsa,ki yadda dashi kai tsaye har ki bishi for only Allah knows inda zai kaiki ba,wannan abin ba k'aramin sosa xuciyata yayi ba,amma se na batsar nace toh wai ni miye nawa da damuwa akanki? Ai ke kika kai kanki,duk da cewar na yadda da kanina sam ba mazinaci bane,amma ban san meyasa na kasa sakewa da fitarku tare ku biyu kadai ba,ashe de sonki nake ban sani ba,koda naje gida kasa xama nayi,naji kamar na sanya k'iransa na rufeshi da fada akan ya maido dake gida,amma se naga zagewar zatayi yawa and he might get to suspect something."
Jan gwauron numfashi yayi kana yace "Na takaice miki labari,dawowa nayi na xauna jiran dawowarku awaje,ita Hanan duk ta tsure duk aganinta tashin hankali xan haifar sanin da tayi na cewar mahaifiyarmu bata qaunar wani acikinmu yayi tunanin qara matar aure,aganin ita Hanan din xan taya Mummy hukunta Mubarak ne,na nuna mata cewar karta damu ba wani tashin hankali xan haifar ba kawai Fadimar ta min kama da wata wacce na sani ne.Kamawa daga wulaqancin da mummy tayi wa 'yan'uwanki,da korosu waje da tayi duk akan idanuwana ne,koda naje ina bata haquri zageni tayi tass! ta ajje agefe wai har ni ina da bakin magana? Ai gwara Mubarak din tunda shi yayi tunanin qaro aure amma ni fa? dayar mah na gagara ajjewa ina nan kamar wanda aljana ta aure,sae kace kaina farau aka soma yiwa mutuwa. Maganarta daya fi sosa min rai har ya saka na dan zubda kwalla shine wai,da alamu haka xan k'arashe rayuwata babu magaji,wanda ze dunga daga hannu sama yana min addu'ar samun rahamar ubangiji,sae de nata daukar 'ya'yan abokaina ina sha'awarsu,hakan data fada shi ya k'ara min kaimi da kuma k'warin gwiwar gwada sa'ata awurinki,ban damu da cewar ke din budurwar kanina bace,burina kawai nasan ta yadda xan bullo miki har na samu shiga awajenki,because nima ina buqatar asake sona,I want to share dat love again with someone,Fadima I really want to see my own children,kuma ke kadai ce naga kamar Kinfi dacewa da rayuwata shiyasa nayi tunanin xuwa gareki,nabi bayanku don nasan gidanku,koda naga motarku ta lalace,sae na samu wuri nayi parking adan nesa daku don Kar nayi saurin tunkaranku ku d'ago wani abin.Sae dana dan ja lokaci kuma na tabbatarwa Kaina lallai bazaku dago ba sannan na tunkareku."
Advertisement
Anan Mahmood ya baiwa Fadima labarin komai na yadda akai yata fama da xuciyarsa da kuma kokarin son ya yakice soyayyarta acikin xuciyarsa,amma hakan ya faskara,akan dole yabi son xuciyarsa,ya kudura aransa cewar dolene ya baiwa xuciyar abinta takeso.
Yace"A.B.U Zaria ta dade tana aiko min da request akan suna matuk'ar buqatar nazo na dunga aiki dasu,don suna da labarina yadda nake da basira da kuma fasahar sarrafa na'ura meh k'wak'walwa,I hav turned down their requests on several occasion,ganinki ya saka ni da kaina na aika musu da sak'on amincewata da offer dinsu,wanda tsananin murnar hakan ya saka suka bani k'yautar wata madaidaiciyar gida don nuna godiyarsu agareni.Ni kuwa gani nayi rayuwata xata dawo sabuwa dal kamar an ciro daga kwali,xuciyata fes! raina yayi haske ganin nayi close dake,wani abin dadin dadawar kuma,wai kema A.B.U kike schooling, hakan yasa naci alwashin bazan tab'a wahala wajen shigar da kaina gareki ba,xanyi kokari naga na koya miki yadda zaki soni,sannan daga baya na aureki kota halin k'ak'a. "
Ya bata labarin yadda sukai tayi da Mubeen,yadda Mubeen din keta nemarta awaya baya samunta da kuma yadda yayi masa karyar wai sabuwar wayace take jira,da kuma hana masa xuwa Zaria da yayi don dubata,da kuma wucewarsa India da dramar da kullum suke sha awaya.
Yace"Wallahi ko jiya mah se daya k'ira amma naki dagawa.... "
Afusace na mik'e nace"Agaskia Mahmood kaci amanar Mubarak ba kadan ba,Allah sarki bawan Allah inata tunanin kila dama can yaudarata yake baya qaunata shiyasa be damu yasan halin da nake ciki ba,ashe abinda ban sani ba,kai kana can kana shuka masa bishiyar k'arya har tayi nasarar tasiri da kuma girma acikin xuciyarsa,why? Because ya yadda dakai,yasan bazaka tab'a masa k'arya ba,Mahmood meyasa zaka ci amanar Mubarak? Why? Meh yayi maka arayuwa da har zakayi tunanin ramuwar gayya irin wannan? Kamar yadda kake ikrarin kana sona,toh wallahi Mubarak ya fika sona sau dubun dubanni,ka kuwa san irin tashin hankalin da kake kokarin haifarwa acikin zuri'arku? Ka tab'a tunanin cewar anya xuciyarka ta maka adalci wajen sona kuwa? Tukunna mah de gaya min wanene *'agareka,sannan kuma ina family dinka suke da akayi wannan auran?"
Jikin Mahmood ne yayi sanyi qalau kamar kankara,ahankali ya bud'i baki ya cigaba da mata bayani"Baba Mu'azzam shima family dina ne ba hayarsa nayi ba kamar yadda kike tunani,k'anin mahaifina ne,shak'ikinsa kuwa,ma'ana ciki daya suka fito da mahaifina,matarsa daya itace Haj.Fa'iza wacce akafi sani da 'Mami',ya'yansu biyar kuma duk mata,Zaliha itace ta farko wacce take kusan sa'ar Maryam (Meema) qanwata,nasan kin ganeta don da aka kawoki mah tana gidan,tana auran wani dan sanda ne anan kanon,sae Zaineema meh bi mata,ita kuwa sa'ar Usman kaninmu ne,ita kuwa tana aurene ah katsina,ita bata zo bikin ba amma nasan yan'uwanta sun gaya mata,sae meh sunan Kaka rigima wacce ake k'ira da 'Afreen',ita kuwa sa'arki ce,sae Hafeezah sa'ar Suhaima,sannan auta Rafi'ah.Sanda kika fada min cewar ai mahaifinki shine chief justice ta yankin federal high court Zaria,sosae nayi murna don na sanshi da dadewa,Baba Mu'azzam ya tab'a zuwa dani wurinsa sau daya ah office dinsa,mahaifinki abokin baba ne sosae don ta sanadiyyarsa ya samu aikin alk'alanci,lokaci daya sukaje nemar aikin,se akace mutum daya kawai za'a dauka,anso daukar Baba ne amma se kuma yaga kamar abokinsa Sa'ad ya fishi buqatar aikin,se ya haqura ya bar masa,shi kuma ya tafi ya soma kasuwancinsa kadan da kadan har Allah ya sanya albarqa,ya tallafa masa ya habbak'a kasuwancin nasa ta man fetur.Sosae justice ke ganin mutunci da kuma darajar Baba don aganinsa ya taimaki rayuwarsa ba kadan ba,sati daya da soma aikina ah A.B.U naje office din mahaifinki,sosae yayi murnar ganina don ya shaidani,bayan yan gaishe-gaishe,na gabatar masa da kaina amatsayin meh sonki da aure,dan Jim yayi yana tunani."
(Alokacin tunani yake akan Haidar kada ya watsa musu k'asa ah ido don bazai iya hana dan Baba Mu'azzam auran 'yarsa ba,kawai zeyi tunani akan hakan)
"Ni kuwa gani nayi kamar bazan samu abinda nakeso ba,atake anan naji gwiwowina sunyi kasa,can ya karbi lambar wayata tare da ce min zeyi tunani akai. "
(Bayan kwana uku da ganawarsa da Mahmood,shine al'amarin su Fadima ya bullo,ya danyi murna da hakan,kenan ai Haidar bazai ce an watsa mishi kasa ah ido ba,yanxu yana da damar baiwa dan Alh. Mu'azzam auren Fadimar don kwarai ya yaba da hankalin Mahmood).
"Bayan kwana biyu sae ga k'iran Baba Mu'azzam wai yana son ganina,koda naje sosae ya nuna min murnarsa na samo 'yar gidan mutunci da tarbiyya amatsayin wacce nakeson na aura,wai justice na musamman ya kirashi ya labarta masa komai tare da bada go ahead din aturo,toh anan ne na rokeshi kan don Allah kada asanar da mahaifiyata don bata qaunar yarinyar,sannan kuma kada ayi wata gayyata don kada maganar ta bazu har ya isa kunnanta,sosae yayi mamaki da zancena har yace shi baze goya min baya nayin auran nan ba har se naje na nemo izinin mahaifiyata da kaina,rok'ansa nake tayi harda kuka akan ya taimaka ya shige min gaba na samu na aureki Insha Allah bayan auran sae asanar da mahaifiyar tawa,dakyar da sudin goshi ya amince ya shige min gaba don shi kansa yana bala'in son wannan hadin har ransa,toh kinji-kinji yadda akai na sami auranki,sannan ko daya acikin yan'uwana babu wanda yasan da wannan auran hatta shi Mubarak din........ "
Kallonsa nake cike da tsanarsa da kuma k'yamar hanyar daya bi ya aureni ba tare da samun albarqan mahaifiya akan wannan auran ba,hawaye sae bulbulowa suke saman kuncina babu gaggautawa,kuma ko kadan ban damu nasa hannu na sharce su ba...............📝
A/N
Ga alqawarinku nan na cika,Insha Allah zaku dunga ganin update kullum as frm now on!!!
*
Advertisement
- In Serial1363 Chapters
VRMMO: The Unrivaled
Lu Chen used to be a ranker of the most popular VRMMO game, Spirit of Grief. After a car accident turned his dreams into dust, his disability left him incapable of escaping the pit of mediocrity he was thrown into. Helpless and defeated, his story ended.Two years later, the Eternal Moon Corporation launched a new VRMMO called "Heavenblessed", and Lu Chen stumbled into another terrible accident that left him in a complicated situation far beyond his ability to handle. That won't stop him from rising to the top, however. Not again.Come witness the rise of the sword-wielding zombie and the relationships he makes during his journey to the apex! For riches and bi- ahem, for career and love!He wields a demonic sword from Hell, he dons armor shining with Heaven's light. His boots stride across the sky as his helmet devours the souls of his enemies. On his left side sits the Goddess of Death. On the other, the Angel of Beauty.From the land of ice and death, a generation of Asura Kings rises, their roars reverberating throughout the world.Tremble in fear, noobs!
8 8156 - In Serial1353 Chapters
Refining the Mountains and Rivers
A young man's life changes when he stumbles upon a mysterious item. Qin Yu had never been a lucky person. Weak of body, bullied by his peers, and with only his friend as his family, he struggles day-by-day to live. But everything changes when he stumbles upon a little blue lamp. An immortal and demonic cultivating adventure.
8 3345 - In Serial2455 Chapters
Mortal Cultivation Biography
A poor and ordinary boy from a village joins a minor sect in Jiang Hu and becomes an Unofficial Disciple by chance. How will Han Li, a commoner by birth, establish a foothold for himself in in his sect? With his mediocre aptitude, he must successfully traverse the treacherous path of cultivation and avoid the notice of those who may do him harm. This is a story of an ordinary mortal who, against all odds, clashes with devilish demons and ancient celestials in order to find his own path towards immortality.
8 1051 - In Serial1503 Chapters
Dragon Prince Yuan
Destiny stolen at birth, the prince of the once mighty Great Zhou Empire, Zhou Yuan, has been plagued all his life by a fatal poison, forced to suffer powerlessly until one day when fate draws him into a mysterious domain where he meets a beautiful girl in green, a bizarre dog-like creature and an unfathomable old man in black.Join Zhou Yuan as he is thrust into the whirlpool of destiny while he seeks the pinnacle of cultivation.
8 1058 - In Serial677 Chapters
Ranker's Return
In the early days of the virtual reality game, Arena, meleegod was the strongest ranked player! He deleted his character and suddenly left. In order to restore his bankrupt family, he returned to Arena!"Do you want to create a character?"
8 1715 - In Serial1525 Chapters
Monarch of Evernight
Qianye rose from hardship but was felled by betrayal. From then, one man, one gun; he tread the path between Evernight and Daybreak and became a legend. Even if Evernight was destined to be his fate, he still intends to become the ruler who dictates.
8 22865

