《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》PART 2:CHAPTER SIX
Advertisement
*💘
*
Can de na cije na sanya 'yar yatsa na sharce hawayen da har xuwa wannan lokacin sunki daina zuba,sae mah dad'a gangarowa suke kamar ana korosu ko kuma nace tamk'ar ruwan famfo.
"Brother inlaw har kayi round up na labarinka banji ka ambaci kalmar *'ba wanda abinda nafi k'osawar naji inda ka sami wannan sunan kenan.... " Na kafeshi da jikakkun idanuwana ina meh jiran naji bayanin da ze biyo baya.
Saukar da wata wahalalliyar ajiyar xuciya naji yayi,kana yace"Fadima da fari dai don Allah ina son kiyi cancelling wannan *'din da kike k'irana da ita,pls stop it banaso,am now ur husband so pls kindly upgrade my name to a romantic one,I want to feel being love again..... "
Wata uwar harara na watsa matsa,amsa nayi niyyar bashi amma kuma se na tuna cewar ban gama jin duk abinda nakeson naji daga gareshi ba,don haka se nayi ladab tare da maida wuk'ar.
"Naji dear nah daga yau na sauya maka suna .... " na fad'a in a very romantic way.Har cikin xuciyarsa yaji dadin wannan sunar,ji yayi kamar Zeeynsa ce ta fada masa hakan don haka take k'iransa da *'
Ni kuwa da gangan nace *' don na sosa masa xuciya yaji kamar Zaynab din ce agabansa.
Axuciyata nace"Kaji dan malohon har ya wani susuce don na k'irashi kawai da 'Dear nah',lallai na yadda mace de shed'aniyace,ko shaid'an din mah yana Sara mata,tasan ta yadda zatayi ta zautar da d'a namiji,kissa da kisissina da duk wani salon yaudara duk atafin hannun mace suke...... "
Ji nayi ya katse min tunanina,yace"Nakowa de da kike taji ana fada family name dinmu ne,tun asali mahaifinmu ne ya sami wannan sunan daga bakin jama'a,sabida shi din mutumin mutane ne,kowa nasa ne,haka kuma yana da tausayi da kuma taimakon na k'asa dashi,dalilin daya saka mutane ke k'iransa da *'kenan,ba dukanmu muke amfani da sunan ba,ina daya daga cikin wa'enda basa amfani da sunan acikinmu,shima Mubarak din baya amfani da ita,we're juz bearing *'ta siyasa na tambayi Mubarak ko ya tab'a fad'a miki family name dinmu? Sae yace wallahi be tab'a ba,so yake idan yazo gabatar da Kansa awajen mutanenki,sae asannan ne ze bada cikakken sunansa,sosae nayi murna da hakan da kuma ganin wautarsa,shiyasa na bada wannan sunan awajen mutanenki don nasan tabbas bazakiyi saurin d'agowa ba....... "
Tafa hannaye na soma yi kamar wata 'yar coci,shi kuwa kallo ya bini dashi,k'wayar idanuwan nan nasa dauke suke da tsananin tsoron actions din da xanyi taking.
Nace"Wow!wow!bravo!!... so smart & intelligent being.... Hmm! Nakowa's family..... "
Sake maimaita sunan nayi cike da alhini"Nakowa's family........ "
"Nakowa's family wallahi babu wani mahaluk'in daya kama kafarku wajen iya tsara takun basaja,believe me wallahi kune sahun gaba ah iya tafiyar da takun basaja very smoothly ba tare da an sami wata tagargad'a ba,Ni Fadima sa'ad wai *'da *' suka ta yawo da hankalina da kaifin tunanina.Da fari de,*'ya b'oye min cewar yana da mata hadda 'ya,sae matarsa tayi takun basaja axuwan ita k'anwarsa ce don de kawai kada na d'ago cewar ita din matarsa ce,sannan kuma wai don kada nayi zargin cewar al'akar soyayyata dashi is secret,family dinsa basu da masaniya,don haka idan har ita ta tarb'eni axuwan fiancee dinsa,toh tabbas xanyi tunanin cewar ai sauran mah sun sani,kawai kawaici suke nuna min,sae kuma aka sami matsala,takun nasu ya sami d'an targad'e,mahaifiyarsa da 'yarsa suka b'ata musu shirinsu wanda hakan ya saka na d'ago cewar tabbas akwai wata ak'asa,wai hakan da matar tasa tayi aganinta son miji ne ya saka ta biye mishi ko menene? Idan kuwa hakane xan iya cewa ita din k'atuwar dak'ik'iyace,raina mata hankali kawai akai awannan shirin,shirin *'itace '*
Advertisement
Dan murmushin takaici nayi,kana na cigaba"Bayan komai ya d'an lafa,sae kuma *' ya kunno mana da tasa k'alar takun basajar wanda ya shallak'e tunanin duk wani meh tunani,friends dina sunsha fad'a min cewar kamar brother inlaw dina is having a crush on me!,amma kasan meh? Saurin k'wab'arsu nayi akan karsu sake min wannan zancen banzar,and do you know why I said so? Sabida aganina brother inlaw dina baze tab'a tunanin cin amanar dan'uwansa ba,kawai de k'yautatawace da kuma kulawa kake nuna min amatsayina na budurwan k'aninka,sae gashi tashi daya ka shayar dani madaran mamaki,sae da kasan ta yadda kayi ka aureni,ayau gani ga *' wan *' amatsayin mijin auran '*gaya min,isn't dat a shameful thing to us? Sannan kuma mutane sun sami abin fada cewar ai 'wa' ya auri budurwar 'k'aninsa,kaga wannan shirin taka itace *' don daga kai,wallahi insha Allahu babu wani d'a namiji da xan yarda ya sake tsara wata takun basajar akaina......never wallahi........ "
"Fadima please listen....... " ya fada awahalce.
Da sauri na daga masa hannu"Malam saurara min nan!.... lokacin zancen soki burutsunka ya riga da yayi expire,yanxu kuwa lokacin maganata ne,it's my turn to speak out and take actions,lokacin zartar da hukunci yayi......... "
"Bayan igiyoyin auren na rataye ah wuyana shine kike tunanin zartar da hukunci da kanki?taya zaki zartar da wannan hukuncin baby doll? ko kuwa atunaninki ni Mahmood xan tab'a furta kalmar '* ne agareki?toh kuwa idan hakan kike tunani,toh ina son ki sani,Ni Mahmood baxan tab'a sakin matata Fadima sa'ad ba,Mahmood ba ragon namiji bane ko kuma wani sok'on ba da har zeyi tunanin rushe ginin daya dad'e yana ginata ba,baxan tab'a gangancin sakinki ba don na dad'e ina jiran zuwan wannan ranar ta mallakarki amatsayin matar aurena,Fadima ina son kisa aranki cewar ni dake aurenmu mutu ka raba ne takalmin kaza,don haka baxan tab'a sakinki ba,ruwan daya tafasa ya dad'e be k'one ba...... "
Gabana ne naji ya yanke ya fadi da jin maganganunsa,amma kuma se na d'aure nace"Mahmood wallahi se ka sakeni adaran nan ba sae an kai gobe ba,don banzo da shirin fuskantar tashin hankalin dake shirin kunno kai acikin family dinka asanadin aurena ba,baxan tab'a yadda Mubarak ya min kallon 'maciya amana' ba balle har na lamunci tsaya jin yana jifana da wannan kalmar ba,never! wallahi I'll never permit dat..... "
Cikin d'aga murya nace"Mahmood ina meh umartarka daka gaggauta sauke igiyoyin aurena duka ukun dake rataye ah wuyanka don bazan tab'a so ayi mah tunanin gyara wannan auran nan gaba ba....... "
Cike da takaicinta Mahmood yace"Ban tab'a tunanin cewar ke din dak'ik'iya bace sae yau,atunanina ilimin arabi ya gama ratsa k'wak'walwarki,ashe abinda ban sani ba da sauranki,kin kuwa san girman laifin duk wata matar data buk'aci saki da bakinta daga wurin mijinta? Nasan kin fini sanin abinda Allah (SWT) ya tanadar mata,amma shine ke don toshewar basira da kuma tsananin b'acin ran da kike ciki yasa har ke kike nemar mah ayi miki sakin da manzon Allah (SAW) yayi mana hani da yinta,wato saki uku!!,,wa'iyazubillah!! wallahi Fadima ki gaggauta yin istigfari ga ubangiji,sannan kuma ki nemi tsari daga shed'an don duk shine ke neman sakaki ki k'auce hanya,Fadima ina son ki rungumi kaddararki da hannu bibbiyu,ina son ki sanya aranki dama can Allah ya rubuta cewar ni din mijinki ne,ke kuma matata,saki de kamar yadda na fada,kinji nace wallahi bazan tab'a sakinki ba,aurena dake mutu ka raba ne,zaman auranmu daram!,,ni dake kamar magnet da k'arfe haka zamu kasance,am fully ready to face any problem coming soon............ "
Advertisement
Wasu hawayen bakin ciki ne suka soma shatato min saman kunci,xuciyata ta sauya zuwa xuciyar kafirai marasa imani,idanuwana sun rikid'e sun koma na tsantsar bala'i.ko daya daga cikin karatun daya karanto min babu wanda yayi nasarar shiga cikin k'wak'walwata.
Cike da isa da gadara nace"Mahmood ga shawara idan har zaka k'arbeta.... Ka sakeni ta ruwan sanyi tun muna shaida juna,idan kuwa kaki,toh ina meh tabbatar maka da cewar lallai kuwa za'a ji kanmu don ta tashin hankali da kuma k'eta za'a rabu,now its left to you to choose one of conditions listed........."
Murmushin leb'en baki kawai Mahmood yayi,kana yace"All of the conditions listed sunyi tsauri da yawa matar Mahmood,don haka none of the conditions listed will be picked up...... "
Da sauri nace"Haka kace ko? "
"Ba wai haka nace ba,hakan de take.... " ya fada tare da kashe min one eyes.
Gani nayi yana nema ya kawo min taurin kai,ni kuwa xuciyata sae ingizani take,tana meh raya min wasu al'amura araina,ai kuwa da hanxari nayi kitchen ina waigensa,shi kuwa sae murmushi yaketa wulla min.
Ahankali nace"Dan iska yanzun nan kuwa zaka yi abinda nakeso.... "
Shi kuwa Mahmood he wonder wat Fadima is upto,atunaninsa wani abin take da buqata shiyasa taje kitchen din.Babu zato babu tsammani sae ganinta yayi ta fito daga kitchen rik'e da wata sharb'ebiyar wuk'a ahannunta.wata irin zabura yayi tare da mik'ewa da sauri.
Cike da tashin hankali yace"Fadima meye haka? Meh kenan kika rik'e ahannunki?"
Ni kuwa ganin tashin hankali da kuma zallar tsoron dake shimfid'e akan fuskarsa ya sakani bushewa da wata dariyar shekiyanci.
Axuciyata nace"Wow! Plan dina yayi aiki,nasan tabbas baxan sha wata bak'ar wahala ba kafin na sami takaddar saki nah... "
"Fadima nace meye wannan ahannunki?" Ya sake tambaya.
Mur! nasha,nace"Ai! wai tambayata mah kake?okay cokalin cin abinci ne....."
Na fadi hakan tare da tunkaran inda yake,jaa da baya ya soma yi yana fadin"A'ah Fadima wuk'ace fa nake gani ahannunki,meh zakiyi da ita? "
"Au! na aza koh idanuwan mijin nawa sun dena aiki ne,ashe tunanina was wrong,the two eyes are still working tunda har ya gano wuk'a ce ahannuna...."
Dad'a tamke fuska nayi kamar ba Fadima meh sanyin xuciya da imani ba,nace"zancen kuma abinda xanyi da ita,so nake nayi gunduwa gunduwa da namomin jikinka idan har kaki bani takaddar saki nah......"
Da tsawa yace"Ke Fadima! kinyi hauka ne? Kisan kai fa kike shirin aikatawa? Wai ni Fadima meya shiga cikin k'wak'walwarki ne?Dama ashe haka kike ban sani ba? Musa ah fuska sannan fir'auna azuci?"
Ni kaina nasan baxan iya aikata abinda nace ba,barazana ce kawai nake son na masa.
Ban tankashi ba,kawai na nufi inda yake tsaye,da sauri naji yace"Tsaya Fadima karki k'araso don naga abin naki da gaske ne,kina iya aikata abinda kika fada,xan baki takaddar sakinki donni lafiyar jikina ya fiye min komai..... "
Ajiyar xuciya na sake,kana nace"Da kuwa ka shafawa kanka lafiya.... "
Yace"Muje daki na rubuta miki don takadda da biro na ciki..... "
"Oya! shige gaba muje..... " na fad'a da k'arfi.Da hanxari yayi gaba yana meh daga hannayensa duka biyun asama kamar wani barawon da dan sanda yayi arresting.(hohoho! Fadima the seargent).
Na take masa baya ina meh nuna wuk'ar adaidai saitin bayansa,shi kuwa lokaci xuwa lokaci yake dan waigowa yana dan dubana.
Babu zato babu tsammani naji kawai ya juyo yana k'ok'arin warce wuk'ar ahannuna,kokuwa muka soma yi,dayake k'arfin d'a namiji da 'ya mace ba daya bane,sae kawai yayi nasarar k'arbeta ahannuna.Ni kuwa ganin hakan yasa na sake kwasa aguje nayi kitchen din.
Wata kwalbace da ban san kota mecece ba na gani saman wata cabinet,wawurarta nayi,na nufi waje,adaidai Kofar kitchen din muka jame.
Ba tare da wani b'ata lokaci ba na daga hannu na rotsa masa wannan kwalbar aka,ai kuwa ta sameshi agoshi.
Ji kake "Ahhhhhhhhh! Wayyo Allah,innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Fadima kin kasheni......."
Agigice na cillar da sauran fasasshen kwalbar daya saura ahannuna.
Fashewa da kuka nayi,nace"Wayyo! Allah na shiga uku na kashe mijina... " na fadi hakan ina meh k'ok'arin kai hannu na tab'a inda jini keta bulbulowa.
Ture hannunta gefe yayi,da hanxari ya shige kitchen din ya kunna famfo,ya wanke fuskarsa gabaki daya har inda jinin ke bulbulowa,kana ya koma falo duk ina biye dashi ina kuka sae cewa nake ya yafe min,amma k'ala bece min ba.Keys din motarsa ya kwasa da wayoyinsa,yayi waje,nabi bayansa.
Kafin na k'arasa ga k'ofar naga kawai ya rufota tare da kulleta da padlock.
Mahmood na fita waje,ya duba agogonsa,its to eleven.
Daga murya yayi yace"Mal.Bello yi sauri ka bud'e min gate...... "
Da hanxari ya nufi motarsa,sae daya k'ira wani abokinsa dake aiki ah Aminu kano teaching hospital,yaci sa'a kuwa yana kan aiki ne,babu b'ata lokaci ya tada motarsa,yayi reverse,yana jin sanda Fadima keta girgiza kofa kamar xata ballata.
Ah 360 yabar gidan,Mal.Bello ya rakashi da "Yallabai ashe bakace bazaka sake fita ba? "
Ina!! Mahmood ya riga ya masa nisa,maida Kallonsa yayi ga b'angaren su Fadimar,ahankali yace"Anya lafiya kuwa? Kai ban tsammani komai sumul yake ba don yadda Yallabai ya fice acikin mota atsiyace dole akwai ayar tambaya anan,Allah de ya kyauta.............. 📝
*
Advertisement
- In Serial199 Chapters
Protagonist: The Whims of Gods
Book one now also on Amazon! After quitting her job as a therapist and grabbing some work at a dog shelter, Tess's life became pretty slow. A tad boring, even. It thus came as no small surprise when she was chosen by a god. Thrust into a new world where magic, monsters, and character levels are suddenly a reality, Tess will quickly find that just surviving can be a challenge. It doesn't help that dark forces are stirring, she's woefully underpowered, and that spiders keep trying to claw her face off. One thing's for certain, though: The possibilities are endless. Will she end up wrestling a dragon? Becoming an arch-mage? Opening a quaint, bookstore, coffee shop, and wine bar for elves? The choice is hers... As long as she can live long enough to make it. Protagonist is a fairly classic LitRPG novel with character levels, classes, stats, settlements, and other LitRPG elements. Unlike a lot of LitRPG stories, while the protagonist has some perks, she doesn't start off overpowered. You can expect to see her struggle as she advances. This novel also takes the opportunity to explore some less frequently seen builds, shying away from any min-maxing. Chapters are about ~2000-3000 words and are released at 8:00am ET every other day.
8 4856 - In Serial51 Chapters
Transmigration Retiree
"What's that you say? I can never leave this reality ever? Good!" Ed, was a normal man in a world full of superheroes, so he didn't really have too many complaints when that first truck fell on him. After all he'd read enough comics to know that sometimes things just happen. Besides he'd been getting on in years when it happened, and his life till then, though lonely, had more or less been fully lived. The second time around when that one guy pushed him off a cliff for a chalice of immortal ambrosia, wasn't so cool though, and then there was that third time when he was just getting used to life as a lady, and that crazy goddess showed up out of nowhere and started ranting about purging the demon menace....then some other stuff happened and he briefly got to go back to earth before falling into a coma where he adventured in the world of dreams. Then the aliens came, and the dream ended and he was suddenly stuck being the AI Overmind for the whole damn star systm. The aliens died, and because he was all mechanical and what-not he just kind of had to keep on going. Forced to continue collecting the materials and data from countless worlds that were destoryed in the process. Then there was that whole war with the gods business that followed...mostly because of all that world destroying he did because of some fairly faulty programming. Anyway, thankfully someone pulled a "rocks fall" on that whole curfuffle, because by the time he was in control of himself again, things had long gotten out of hand. Now the powers-that-be tell him that he must spend the rest of his existence in single lonely section of the cosmos. Trapped in a single portion of a single universe. And now he weeps...No worries though, these are tears of joy. Hopefully this final unending existence he's been given will be the quiet life he's been looking for. A Man who's seen everything gets abducted by aliens and is converted into an AI that sits at the helm of a fleet of alien ships and behind the computer systems for most their planets. This Alien AI goes to war with the gods and ends up nearly destroying an entire reality. The Angels condemn the troublemaking AI to life as normal child on a far off world....All truth said, the "AI" couldn't be happier. His life's been far too interesting(read: Scary, Inconvenient and Painful) in his opinion and he could do with a bit of normalcy.
8 170 - In Serial74 Chapters
The Birth of Fantasy
Fresh out of the academy, Zeal is on his first solo outing as an Abator. The anomaly he's sent to study prevents his death and transfers him to a new universe. Universe Six, as The System tells him, has vastly different fundamental laws. They include the governing of magic and the strange tattoos that ink themselves onto the body called Stigmata. Journey with Zeal as he makes friends, enemies, and bonds with an adorable Kobold named Luin. The Birth of Fantasy is a Gamelit, Litrpg with Cultivation progression instead of stats. The release schedule will be Monday through Friday.
8 120 - In Serial24 Chapters
Forged
Legendary swordsmen, whose feats are hailed and names known far and wide. Many wish to be one, but few have the dedication to follow the path of the blade all the way through, with all of the trials and tribulations that entails. But those who reach the end can become something far greater than they once were. Great warriors aren’t born, they’re forged. A coming-of-age story mixed with a Martial journey story. Think Youxia, Musha Shogyou, or Knight Errant. A martial arts and action heavy story with a focus of slow progression, and detailed character development over time. One protagonist, but a significant amount from other character's POVs, and a notable amount of focus on other character's development. Disclaimer:Title/cover is metaphorical, no literal forging as of this time.
8 322 - In Serial12 Chapters
Starsign Lord
In a world that is governed by starsigns, Rare individuals who are born have the chance of awakening super-powers and becoming mages or warriors. The abilities they will gain will be predetermined by their Starsign.Fraus is a young man with no knowledge of the world. He finds himself in this world and will do everything to survive and reach the top of the world. When all of this is going on, Fraus will become aware of his own hidden characteristic specialties. He hid in the depths of his soul, waiting for the power to come to him.
8 153 - In Serial19 Chapters
Ducosym - My Dungeon Core System
In the world of magic, ‘Cores’ emerge. They are powerful entities with power over the very fabric of reality. They can alter the world through their mind, enslaving other creatures to build powerful structures only known as “Dungeons”. But what happens when a core isn’t born into the heart of lava or cold of ice, but the dirty mud? What happens when a core doesn’t start out as a tyrant over trolls or the leader of a nation, but the prey of spiders and bugs? “Huh?” Sunny wakes up in the prison of a gemstone, missing all his memories. And what appears to be just another fever dream soon becomes a challenge for survival. – – – Hi! This is a novel I’m very excited about. If you have any suggestions on what creatures and monsters to include in the next chapter, feel free to leave a comment on the latest issue! I love listening to your creative ideas! I have the best readers ever! ^w^ Don’t forget to join our Discord server if you like fantasy and memes!!! Discord: https://discord.gg/keXHAYP5
8 243

