《ƘADDARAR RAYUWA》ƘPage 1
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
Zaynab bawa
Haske writers association💡
Alhamdulillahi Allah nagode maka daka bani damar fara rubuta wannan littafi kura kurenda zan rubuta aciki Allah yayafemin wanda nayi dai-dai kuma Allah yabani ladansa, Godiya ta tabbata ga ubangiji mai kowa mai komai daya bani damar dawowa mukuda wannan labari bayan hutun shekara d'aya."
Makaranta littafina inaso kusani shi d'an adam akullum tara yake bai cikawa goma, idan nayi kuskure cikin rubutuna ina maraba da gyara amma banda cin fuska,
Yawwa sannan kuma abuna gaba book dinnan yanada yawa kada nafara rubutu qananun magana su taso akan cewa inajan book kamar yanda yafaru abook dina na baya, Allah yasa mudace Amin."
Page 1
Iska sosai ake kad'awa yayinda ko'ina yadauki sanyi, qura ta lullu6e ko'ina yayinda aka samu karancin wucewar jama'a saboda qarfinda iskar take dashi, yanayinda ake ciki agarin yanayine mai cikeda ban sha'awa da d'aukar hankali
Domin iska busawa takeyi tako'ina ka dukkan alamu hadarine mai qarfin gaske yakeson had'uwa,
Ganyayyaki na bishiyoyi sai kadawa sukeyi suna bada iska mai dad'in gaske.*
Cikin qanqanin lokaci hadari yahad'u sosai garin yayi baqin qirin, daga nan gari yad'aure hadari yafara bugawa alamun kowani irin lokaci ruwa yana iya sauka."
Yanda hadari ya hadu alamu yanuna ruwa zai zuba sosai, duk wani mahaluki kamata yayi ace yanemi hanyar gida, saboda Allah kadai yasan lokacin tsayawar wannna ruwan idanya barke,
Wanda yake waje kuwa to tabbas hankalinsa bazai kwanta saboda gabaki daya hankalinsa zaiyi gidane.
D'an muskud'awa yayi akan y'ar yololuwar katifarsa, wanda yakejin bugawar hadari dakuma tsawa kamar wanda zai rusa gidan yafad'o akansa, saboda rashin qarfin ginin da dukkan alamu ginin yadade sosai gashi na qasane hattada rufun kwanon yatsufa yayi tsatsa,
Daga yanda yake kwance yana hango yanda hasken walqiya yake ratsowa ta bulellen bugun kwanan, ya tabbata yau idan akayi ruwannan d'akin sai yayi yoyo'
Nisawa yayi sannan yaSanya hannu ya lalu6o wayarsa itel mai torch wacce taji jiki sosai idan ka ganta a'ido bazakayi tunanin tana amfaniba,
Kunna torchin yayi sannan yajuya gefe ya dubi wacce take gefensa tana kwance, d'an bubbugata yayi yana fad'in daga kwanciya har kinyi bacci'
Cikkn muryar da take nunida tafara bacci amma baccin baiyi nisaba tace" tukunna dai,
Ajiye wayar yayi agefe yana fad'in kinga hadarine yahad'u sosai agarinnan yarinyarnan kuwa tadawo?
Nishi tad'anyi sannan tamiqe tazauna tana mutsutsuka idanuwa sanda tad'an watssake sannan tace" yanzun qarfe nawane?
Tara da kwtaa yabata amsa ayayinda yake kallon lokacin ajikin wayarsa,
Cikin halin rashin damuwa tace aii tanafin hakama domin tana kaiwa har da rabi ko wuce hakama,
Eh nasani amma yanzun hadarine agarin sosai, kuma wannan ruwa idanya barke Allah kadai yasan lokacin tsayawarsa, hankalinku bai kamata ya kwantaba sanin cewa diyarmu tana waje koda nine nake waje wannan lokaci na tabbata hankalina gida zaiyi, jira tayi sanda yagama maganar sannan ta muskutawa tace yanzu hakama tadawo tana d'akinta ai taga hadari bazata bari takai hakaba, idan tadawo nasan dakinsu zata shige dan idan nayi bacci kasan bata tashina, gyada kaii kawai yayi yakoma ya kwanta amma badan hankalinsa ya kwantaba."
Sauri-sauri takeyi tagama had'a kayanta takama hanyar gida saboda yanda hadari ke bugawa,
Ido tatsura ma wasu samari wanda ga dukkan alamu su take jira su gama su bata kwanonta takama hanyar gida,
Advertisement
Had'e jikinta tayi tatakure awaje d'aya saboda iska da akeyi ga wani irin sanyi da yake shigarta, sun d'an dauki lokaci kafinnan suka gama suka miqa mata, sauri-sauri ta kar6a tahad'e cikin kayanta takama hanyar gida, wani irin tsorone yashigeta tafiya takeyi cikin sauri saboda bbu kowa ahanya kafa tad'auke, ga kuma wani irin duhu da hanya tayi, wani lokacin sai hadarin yad'an harba kafinnan take hangen hanya,
Batayi auneba tajita ta buge mutum dasauri taja baya cikin tsoro saboda kokad'an bata lurada waniba itadai kawai taji ta bugi mutunme,
Wani irin nishi taji mutumin yanyi kamar wanda ake shirin zare ransa ga dukkan alamu baida cikkekken lafiya,
Gudu tayi niyyar arcewa dashi saboda atunaninta aljanine,
Amma ina kafin tayi wani yunkuri wannan mutumi yakamata wanda baya iya kallon fuskarsa saboda baqin da garin yayi,
Ihu ta kwala tana neman taimako amma babu wanda yajiyota saboda yanayinda garin yake ciki,
Sun batu tafarayi tana fad'in" dan Allah kuyi hakuri bansan ku bane awajan yasanyani nabi hanyar harna bugeku bansaniba, tana fad'in haka ita atunaninta cewa aljanine,
Ita bata saniba wannan mutumi wani nufi daban yake dashi akanta,
Cikin qanqanin lokaci yafara qoqarin aiwatarda mummunan nufinsa akanta, hakan yayi dai-dai da sauqowar ruwan sama, duk ihunta takeyi babu wanda yajiyota sakamakon ruwan sama dayake sauka da qarfi, har saida yagama aiwatarda nufinsa akanta."
Jin sauqowar ruwan sama gabaki d'aya sai hankalinsa yatashi, miqewa yayi yafita qauren d'akin yara yabude amma wayama bata ciki, qannenta ne kawai aciki,
Juyawa yayi dad'an sauria yana kwala kira, ummi! Ummi!
Ad'an tsorace tamiqe tana lalu6en torchinta wanda take gefenta, daukowa tayi ta kunna tafara bubbugawa saboda bettery din cikinta yayi sanyi domin harya fara ruwa, dakyar torchin takawo tatashi tafito, ganinsa ahaka cikin ruwa yana dukansa yasanya ta tsorata taba fad'in me yafaru??
Yarinyarnanfa bata dawowa,
Bata dawoba? ta maimaita zancensa qarfe goma har kusan da rabi ake nema, ad'an tsorace tace lallai ba lafiyaba duk dai bata wuce tara da rabi idanma ta gota kadanne,
Kinga dawo nan kizauna da yaran barina fita na dubata ya umarceta,
to tace sannan tabude qauren d'akin tashiga shikuma yafice domin nemanta, haka yabi hanya yana dubawa,
Wajanda take zamada tallanta tafara zuwa yasamu babu kowa awajan,
D'aya hanyar yabi wacce bata ita yazoba,
Ahankali yake tafiya yanayi yana duba tako'ina,
Gabansane yayi mummunan faduwa saboda hango mutum dayayi akwance can nesa dashi dasauri yaqarasa wajan aikuwa ya kalli d'iyarsaa kwance cikin wani irin yanayi,
Lakar jikinsane yadauke gabaki daya yakasa aikata komai a mutum mutumi yake jinsa,
Yafi 5minute ahaka zuciyarsa tanayi masa zogi da quna,
Tsugunannawa yayi ya cicci6eta yanufi gida bai tsaya bin takan kudin tallar ba balle kayan tallan, babu sallama yashiga gida' saboda qofar da buhu aka Rufe yasanya bataji mostsin shigowarsaba, ajiyeta yayi akan barandarsu wanda akayita da duddu6in laka,
Haka yazauna yazuba uban tagumi ya lula wata duniyar,
Jin shiru ga lokaci yaja yasanyata fitowa domin leqawa,
Arazane taqarasa wajansa tana kallon yarinyarta datake kwance, tana kallonta hankalinta yabata abunda yafaru, hannu tasanya akayi takwala qara tana fadin mun shiga uku mun lalace,
Sai alokacin hankalinsa yadawo kanta bai iya kulataba har tagama koke kokenta kusan awa daya sannan numfashin yarinyar yafara sauka da qarfi-qarfi,
Awannan dare mahaifan wannan yarinya sunga tashin hankali duk da kasancewar bacci 6arawone amma bai samu damar d'aukansuba,
Advertisement
Cikin dare mamanta tayi qoqari tadaure zuciyarta ta gyara d'iyarta."
Washe gari haka dukansu suka tashi da baqin ciki gashi babu wanda zasuyi blaming dan faruwar wannan abun domin kuwa kowa yanada nasa laifin akan tallan datakeyi,
Koda qannenta suka tashi dasafe suga ga yayarsu ahaka sun shiga tashin hankali,
Qaramar cikinsuce wacce bazata wuce 3yrs ba tadubi mamansu tana fad'in mama menene yasamu adda??
Koda mahaifiyarsu taji tambayar da d'iyarta tayi mata sai tadubi yarinyar kokadan batasan yanda zata yiwa yaran bayaniba,
Hasalima ita tafiso ta6oye abun cikin ranta saboda daga ita sai babansu da ita kanta yarinyar domin bataso koda makwafta su fahimci abunda yake faruwa,
Kamo yarinyar tayi zuwa jikinta sanna tace addanki batada lafiyane!
Meya sameta?
taji babbar cikinsu wacce aqalla zata iya kaiwa 11yrs tatambaya
Zazza6i tabasu amsa atakaice,
Sannan tadaura da fadin kuyi mata addu'a,
Hada baki sukayi wajan fadin Allah yasauwake, amin ta amsa sannan ta miqe,
d'akinta tanufa azaune tasamu baban yaran zama tayi gefensa cikin daurewar zuciya tace baban Hafsa yakamata katashi kafita haka nan, wannan zaman bazai kaimu ko'inab kaga dara tayi,
D'agowa yayi yadubeta cikin karyewar zuciya sannan yace" bazan iya fitaba ummi duk yanda kike tunanin wannan abun yawuce nan azuciyata,
Mun tarwatsa rayuwar d'iayarmu,
Duk wannan laifin nawane daban kasance mai biyawa iyalaina buqatava wanda har hakan takaiga daurawa d'iyata talla,
Cikin lallashi tace" baban hafsa kadaina daurawa kanka laifi kana iya qoqarinka wajan ganin ka biya mana buqatunmu,
Kumafa kasani idan Allah yarigada yarubuta faruwar abu bbu makawafa saiya faru, koda kuwa bata wannan hanyar ba, shidai abu kawai yakan kasance yanada sanadine amma faruwarsa rubutaccen al'amarine, jarabawace ta ubangiji addu'a kawai zamuyi mata Allah yabata lpy Allah kuma yabamu damar cinye jarabawarmu, Wannan QADDARAR RAYUWARTA kenan bamu isa canja mataba,
Yanxu katashi kafita kasamo mana abunda zamu d'aura domin kwayar hatsi babu acikin gidannan, sannan kuma ajikinta yayi zafi sosai dole zamu saya mata koda pracetamol ne,
Idan baka fitaba mutannen anguwa zasuyi zaton wani abun nikuma bana buqatar kowa yasan wannan lamari murufa kanmu asiri mu sirrinta wannan lamari, idan wasu sunyiwa abun fahimta maikyau wasu bazasuyiba kowa da irin nasa tunanin kowa kuma akwai fuskarda yake kallon lamari,
Sanyayyun magana tayita masa har Allah yasa hankalinsa yad'an kwanta yatashi yamiqe,
Wani d'aki yashiga yafito wheelbarrow da buhu, bude buhun yayi ya juye yalo acikin baho, wasu daga cikin yalo dinma harsun fara yanqonewa,
Wannan yarinya da bazata wuce 11yrs ba, matsowa tayi tafara wanke masa yalon tana zubawa akan wheell barrow din shikuma yamiqe yafara jerasu,
Yanayi yana fad'in Allah yayi miki albarka sadiya, amin ta amsa taci gabada wanke masa harta gama,
Sannan ya shirya kayansa yafita ita kuma sadiya takoma wajan y'ar uwarta saboda zazza6inta duk yabi yadameta,
Hannu ta sanya tata6a jikin y'ar uwar tata jikin yadauki zafi sosai,
Sannu tafad'a tana mai qara tausaya mata,
Sai can mahaifiyarsu tashigo tadubi sadiya tana fadin halima ungo nan tamiqa mata kofi, jeki gidan yawale ki kar6omin koko na ishirin kice idan babanku yadawo zan aiko mata, hindatu harta fara yimun kukan yunwa gashi yarku itama bataci komaiba idan tasha ko zazza6in zai fita,
Kar6an kofin tayi tafice mamansu tazauna gefen hafsa wacce take rawar sanyi dukda kasancewar yanxu ba sanyin akeyiba,
Amma dake ita zazza6ine yake damunta yasanya takejin sanyi sosai,
Hawaye taji yana zurara akan kumatunta yayinda take qarewa yarinyar kallo,
Abubuwa dasuka faruwane suketa tariyo mata aranta, duk cikin zantuttukanda suka dawo mata babu wacce ta tsaya mata arai kamar maganar surukarta wato mahaifiyar mijinta kakar yaran kenan,
Akullum koda zuwa gidan tayi nadan wani lokaci idanta kalli yaran sai tafara fad'in shikam hamisu yana shan wahala ko d'aya baida mataimaki yara mata Akullum damuwa suke zamowa bbu wata hanyarda zasu taimaki mahaifinsu, shiyasa har yanzu yakasa tara abun kansa,
Yara mata! Yara mata! Takan fadi hakan yakai sau uku sannan sai tace yara mata aii rayuwarsu hatsarine garadai namiji zai shiga ko'ina,
Nisawa tayi ta matse kwallarta akullum mahaifiyar mijinta tafadi wannan magana takan tsaya mata arai,
Ayau kam ta tabbatarda maganarta datake fadin yara mata rayuwarsu hartsarine akullum suna buqatar akillacesu,
Wata irin tsoro da faragabanebya d'areu cikin ranta ahankali ta furta wato idan kanada d'iya mace hankalinka bazai kwantaba har sai ranta akace yai gashi sunyi aure,
Nisawa tayi data tuna nata gida biyar da suke nan mata riras, d'aga hannu sama tayi had'eda fadin Allah kakaremin yarannan da kariyarka,
Sadiya tadan dauki lokaci bata dawoba tsakanin fitarta da yanzu Allah kadai yasan halinda mahaifiyarsu tashiga tunani kala-kala aranta jitakeyi kamar tatashi tabi bayanta' tana saka da warwara cikin ranta saiga sallamar yarinyar nan tashigo, sauqe ajiyar zuciya tayi domin tasamu sanyi aranta,
Miqawa mahaifiyarsu kunun tayi tana fadin mama wai akwai naira goma ranarda yaya hafsa ta kar6owa hindatu ba'a kaiba,
In sha Allahu za'akai mama tafadi sannan tace tashi ki daukomin kofi,
Miqewa tayi tadauko nata kofi ta zuzzzuba musu dukda bawani yawane dashiba amma hakan dai yaraba musu amma ita ko tunanin kantanma bataiba, dakyar tasamu hafsa tadan sha mata tanasha tana rarrashinta da fadin yawwa sawwmana in sha Allah sai Allah ya saka miki sha abunki,
Dahaka harta samu tadan sha,
Sai yamma sosai babansu yadawo,
Alhmdllh yadanyi ciniki bbu laify kamar ansan halinda yake ciki,
Tundaga hanya ya auno musu shinkafa yasiyo barkono da maggi da mangyda,
Sai alokacin kafin tasamu tadaura musu abinci yaran yunwa harta galabaitar dasu,
Saboda sun saba ko yaya idan mamarsu tayi abun sayarwa kafin yayarsu tafita dashi, sai sunci sannan idan babansu yadawo abunda yasamu sai adaura,
Magani suka bata tasha zuwa jimawa zazza6in yadan saketa."
Cikin d'an kwanaki Alhmdllh tawarware amma sai dai halinda suke ciki awannan gida abun baya misaltuwa domin kuwa tallanda takeyi yake dan taimaka musu, jarin babansun kadanne gashi sun
Cinyeshi acikinsu,
Ita kam hafsa sauda yawa takan zauna tayi tagumi tana tunani,
Idan mahaifiyarta tadan rarrasheta sai kiga ta ware tashiga cikin qannenta sun cigaba da al'amuransu,
Mahaifiyarta idan tazuba mata idanuwa takanji tausayinta saboda tasan yanzu bata wani san illar abunda yafaru da'itaba sai nan gaba idan tafi haka girma abun zaifi damunta,
Domin kwata-kwata aynzu shekarunta sha uku kacal."
Watannin sunja yayinda abubuwa dayawa sun canja amma yanayin samun gidan yau akwai gobe babu haka dai suketa ci gabada malejin rayuwarsu,
Amma kam rayuwa tayi musu zafi sosai."
____________________________________
Yanayin comment dinku yanayin yanda typing dina zaina zuwa muku
✔️ote
Comment
Share
To be continued
Zaynab Bawa
💕💞
Advertisement
- In Serial17 Chapters
Velteria: The Thief
(Indefinite Hiatus) Life was fine, if a little harsh, for Liliei, a young thief living in one of the biggest city on the continent. That is, until she stole an old ring, and everything went wrong. One of my goal in writing this is to improve my writing skills, so do tell if you have constructive criticism.
8 173 - In Serial25 Chapters
David The Gray Mage
The story of a reincarnated man named David who found himself in a world of magic in the middle of a industrial revolution and a opportunity to learn from the most presitigious academy in his kingdom. The world is very different from what David is used to which makes him question his common sense at almost every turn.
8 63 - In Serial12 Chapters
Tink's Shorts
Amalgamation of shorts, random ideas, notes, and otherwise crap I dont plan on doing anything with for the forseeable future. if you like an idea, setting, character, feel free to use it in your own works; however please be respectful and at least state where you got the idea. this is mostly just a place for me to personally put stuff, if you like/follow/comment, please be aware, things in this group are not connected to each other, although some might appear to be.
8 371 - In Serial75 Chapters
The Diamonds
When two human's named Abigail and Ron find out that they are actually alien creatures called: Diamonds their life gets turned upside down. Everything they thought they knew about themselves was a lie! Now they have to figure out who they really are all over again. The journey to them becomes nothing but one big nightmare after another. But unfortunately it's not a dream. It's for real and there's no waking up from reality no matter how bad it seems.
8 108 - In Serial9 Chapters
Field Trip to the Avenger's Compound
Wow. Soooooo original Marina. Peter taking a field trip to the Avenger's Compound? That's never been done before. If you're reading this, you've probably read other Peter fics. So, you get the gist. What's different about this fic is it's a reader insert! Now I've messed up the timeline A LOT (Barry Allen who?) with this. Aunt May let Peter live in the compound so she could travel the world like she's always wanted to. But (Y/n) and Peter both go to Midtown High. It'll make sense.... eventually. Ships:Implied PepperonyStuckyWanda and VisionI do not own the rights to any Marvel characters. I'm just using these characters to tell a story :)
8 124 - In Serial58 Chapters
Rise of the Night Witch
Demons, vampires, witchcraft, abandonment; Marissa Carter has problems others don't see. As the daughter of a banished witch and a normal human, she lives between two worlds.Once the Veil breaks and demons attack, she must decide. Will she learn magic at the Cunning Folk Academy or continue her normal high school life?She has time until Halloween to find the leader behind the monsters' invasion of the human realm. Life's a witch.[-]Updates on Tuesdays and Saturdays. Also on Geeke. (If this book is on a site other than Wattpad or Geeke or a Wattpad account other than "Auraptor" or "PASharp", it's likely stolen. Also, there are now thousands of accounts claiming my book is stolen. If you check them, you'll see they have no followers and no conversations. They're fake accounts, don't listen to them.)#123 Creepy out of 40.3K stories (30/08/2022)#98 Paranormal out of 86.6k stories (21/11/2022)#406 Anxiety out of 60.7k stories (29/08/2022)#53 Darkfantasy out of 7.9k stories (09/08/2022)#306 Monsters out of 37.5k stories (19/08/2022)#75 Demon out of 55.2k stories (19/08/2022)#70 Fae out of 7k stories (19/08/2022)#22 Secret Identity out of 4.9k stories (05/09/2022)#14 Superpowers out of 26.2k stories (09/10/2022)#255 Magic out of 254k stories (27/09/2022)#73 Supernatural out of 177k stories (21/11/2022)#100 Witch out of 80.7k stories (27/09/2022)#38 Urbanfantasy out of 7.4k stories (21/11/2022)#16 Horror out of 302k stories (21/11/2022)
8 177

