《ƘADDARAR RAYUWA》Q Page 11
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 11
Kuma dik wannan zuwa da sadam yakeyi har yanzu bai san sunan sawwama ba bai ta6a tambaya ba ita kuma bata gaya masa ba,
Shima sunansa daya fada mata bata ta6a kiransa da sunanba saboda ba wata magana mai tsayi ke shiga tsakaninsuba,
Maganarsu bata wuce sallama, sannu, da yawwa,
Idan kacire rana ta uku dayaje wajanta,
Yauma kamar kullum sadam yana saurin ya gama duk wani abunda yake dashi a school yawuce wajan sawwama akwai tambayarda kullum take cikin ransa yau kuma zaiyi mata wannan tambayar in sha Allahu,
Najeeb ne ya dubeshi yana fad'in sadam wai saurin zuwa ina kakeyine haka?
Gida! sadam ya bashi amsa atakaice,
Jijijiga kai najeeb yayi irin bai yarda da maganarsan nan ba, yace" Uhm, uhm dai malam fad'i gaskiya badai gidaba,
Saboda nasan bazata ta6a skipping lactures dan zaka tafi gidaba,
Kodai akwai wani abunne aqasa?
Tabbas akwai wajanda zakaje, najeeb ya fadi hadida buga bench,
Uhmm kawai sadam yafad'i sannan ya miqe zai tafi,
Tsare hanya najeeb yayi sannan yace koka fad'amin yanda zakaje kona hanaka zuwa,
Tunda yanda zakaje ai baifi lactures ba kuma saina fadawa mummy kafara skipping lactures,
Kasan halinta ai kasan yanda zata kaya muku karshe madai tadawo dakai zaman hostel kaga shikenan ni aii abu yayimun dad'i,
6ata rai sadam yayi sannan yace kagani najeeb banson irin haka,
Idan zaka bani hanya kabani kuma nafada maka gida zanje,
Tun yaushe muke jira malamin idan zaizo yanzu yaci ace ya iso aikoh??
Kusan 40minute da kamawar lokacin lactures dinsa,
Qara tsare hanya najeeb yayi shikuma sadam ya qara tamke rai yana fad'in kaga malam dallah matsamin a hanya shi lactures din dolene?
D'age kafada najeeb yayi sannan yace ba dole bane amma zaka sanine wajan mummy idan taji labari dan zan sanar da ita,
Advertisement
Idan ka fasa sanarda ita, kuma yanzu daga nanma gida zan wuce idan yaso saita ganewa idonta basai an gaya mataba,
Yana fadim haka cikin jin haushin najeeb danshi yanzu gabaki d'aya hankalinsa yayi wajan sawwama dan gani yakeyi kamar wanda yashiga tsakaninsa da ita,
Kokad'an sadam baison aikin karfi daba hakaba daya ture najeeb yawuce,
Baqin ciki yasanya yaja gefe ya tsaya yana jira yaga najeeb zai matsa ko bazai matsaba,
Ganin irin kallonda sadam yake jifansa dashi yasanyashi barin hanyar yana fadin malam karma katsaya karatun ai ma kanka zaka yiwa,
Gara da kasan hakan sadam yafad'i sannan yafice yanda ya ajiye machine dinsa yabi yadauka kai tsaye ya fice daga cikin school d'in,
Bai zarce ko'inaba sai wajan sawwama,
Kamar kullum dan aiken qasone ya sanar mata da isowarsa wato kamshin turarensa,
Da sallama ya qarasa ta amsa sannan tayi masa sannu shima ya amsa da yawwa,
Wani d'an dutsi yajaa yazauna kusada ita ya fuskanceta,
Ganin haka yasa sawwama duk tabi tawani duburburce bai saba zama haka kusada itaba kuma gashi ya fuskanceta ya tttara hankalinsa duka akanta,
Akullum ya tsareta da idanuwa kasa aiwatarda komai takeyi bare yanzu yanda yazo kusada uta haka,
A duburburce ta gaidashi, ina wuni?
Lafiya ya amsa sannan yace inaso muyi magana dake,
D'agowa tayi ta dubeshi sannan ta tattaro duk wata nutsuwarta ta miqa masa, sannan ta sunkuida kanta qasa,
Sanda yadanyi gyarar murya sannan yace" inason nayi miki tambaya tunda dadewa bansan yanda zaki dauki zancenba shiyasa ban tofa ba,
Amma yanzu naga yadace nayi miki magana,
Menene dalilin dayasa baki zuwa makaranta?
Shiru tayi takasa bashi amsa,
Ehem ke nake sauraro yafad'i jin tayi shiru,
Kanta yana qasa tana wasada yatsunta cikin ranta tana fadin toh wannan wace irin amsa yakaso tabashi.
Shin ce masa zatayi iyayenta basuda kudi sun kasa biya mata kudin makaranta kokuma yaya?
Ita dai aiya saninta wannan ba huruminsa bane hurumin cikin gidansune,
Advertisement
Daya tsaya aiya mutumci dake tsakaninsu na siyan abun sana'arta daya keyi kawai yafi,
Bayan hanata sukuni dayake da tunaninsa da mafarkai akansa yanzu har yakai yanason shiga rayuwarta?
A kullum inaso idan nayi miki tambaya ki zage ki bani amsa muryarsa ta katse mata tunaninta, d'agowa tayi ta kalleshi sannan ta qara maida kanta qasa, ganinka yasa yadaura da fadin banason kame-kame da kikeyi aduk lokacinda nazo wajenki,
Banida niyyar cutar nake,
Babu abunda nakeda nufinki dashi sai alkhairi yakamata ace kin fahimci hakan,
Baki ganin kina yiwa rayuwarki illah? Ya jefo mata tambaya,
Baki zuwa makarantar boko baki zuwa ta islamiya wannan babbar illace,
Nayi obverving dinki, wannan hanyar tadawo hanyar wucewana duk dan saboda ke saboda nadamu da rayuwarki,
Amma da safiya ne kawai idan zan tafi bani kallonki anan,
Shin zamanki anan shine mafita?
Jijjiga kai tayi sannan tace eh zamana anan shine mafita ga rayuwata,
Sannan kuma zancen zuwa makaranta wannan itace QADDARAR RAYUWA TA a kullum nakan tsaya a iya matsayinda ubangiji ya ajiyeni toh nan shine matsayina,
Shiru yayi jikinsa yayi sanyi cikin ransa yana gidiya ga ubangiji dole duk wani hali da kake ciki idan ka kalli wasu ya wajaba kayiwa ubangijinka godiya da ni'imarda yayi maka,
Dakyar ya iya bude bakinsa ya furta shekarunki nawa?
Sha biyar tabashi amsa atakaice,
Sha biyar ya maimaita sannan yaqara fadin 15yrs amma hankalinki laffuzanki da kalamanki sunfi karfin shekarunki,
Inane gidanku?
Ya sake jefa mata tambaya,
Da kamar bazata amsaba saboda tambayarsa tafara yi mata yawa,
Baya ta juya da hannu ta nuna masa gidan kai kallonsa wajan yayi sanda ya qarewa gidan kallo tsaff sannan ya sauqe ajiyar zuciya, cikin zuciyarsa ya furta subhanallahi runtse idanuwansa yayi hoton gidan yana masa yawo a idonsa,
Wannan ne gidansu? Ya tambayi kansa,
Dama mutane suna rayuwa cikin wannan gidan?
Jijjiga kai yayi wani irin tausayinta yana ratsashi,
Dakyar ya iya bude bakinsa yace in nemi wata alfarma d'aya awajanki?
Gyada kai tayi sannan tace Allah yasa zan iya,
Zama ki iya yafad'i,
Inaso duk wani abunda kike da buqata ki sanar dani, sannan ki daukeni matsayin yayanki,
Girgiza kai tayi sannan tace" A'a dan Allah kabarni ayanda ka ganni,
Bana buqatar taimakonka,
Muna rayuwarmu batareda neman taimako wajan kowaba plss katsaya iya matsayinka dan Allah👏 tafad'a hadeda hade hannuwanta biyu,
Nisawa yayi yabita da kallo yaga tsantsar gaskiyar abunda tafada akan fuskarta,
Zaiyi magana ta d'aga masa hannu hadeda kauda kanta gefe, miqe yayi batareda yaqara qoqarin furta mata koda kalma dayaba, amma daga kallon yanayin yanda ya tashi zakasan ransa ya6aci,
Yarasa mai yake ingizashi akan yarinyar nan wani lokaci koda baida niyyar yin abu amma sai kiga ya aikata,
Yarasa mai yasa yarinyar batada yarda shi har cikin zuciyarsa baida niyyar cutarda ita,
Haka kawai Allah yadauki matsayi mai girma yabata cikin zuciyarsa,
Haka yayita sake-sake harya isa wajan machine dinsa
Yaja machine dinsa yayi gaba,
Gabaki daya jikin sawwma yayi sanyi ganin yanda yatafi da jiki duk yayi sanyi, gabaki daya takejin babu dadi kamar bata kyauta masaba,
Amma ina bazata iya barin wani namiji yashigo rayuwarsuba saboda batasan nufinsaba duk kuwa da cikar kamalarsa,
Ta sare da cin amana da kuma halim zalinci irinna maza,
Mutuminda bata sanshiba yayi mata muguwar zalinta ba baqanta rayuwarta ya sanya mata baqin cikinda har zata koma zuwaga ubangijinta bazai goge cikin zuciyartaba, hakan yasanya yanzu tana tunanin duk wani namiji ba abun yarda bane atunaninta duk halinsu dayane,
Idan ta yarda da wannan yazo ya zalinceta zalincinsa zaifi mata zafi akanna kowa,
Shiyasa tun farko bazata bari yashiga jikintaba bazatayi wannan sakenba,
Zatafi jin dadi ace yatsaya iya matsayinsa."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial79 Chapters
Avatar Online
Skilled, disciplined and merciless.
8 129 - In Serial61 Chapters
Bored Gamer in Other Worlds
Bored Gamer in Other Worlds. A spoiled brat journeys in mystical worlds and beyond.
8 181 - In Serial11 Chapters
Legacy of Kail
The white-haired Kail is a member of the mercenary guild Anima. Having seemingly appeared out of nowhere one day, his life before Anima is surrounded is unknown to his peers. Now he takes on various jobs that have him travelling across the land of Terra Deorum, meeting a variety of friends and foes in his travels. In a world of warring nations, magic, and monsters, Kail has many obstacles to overcome. Although he has his own unusual ability to help him on his way; the ability to see and speak to the dead.
8 178 - In Serial23 Chapters
The Legend of the Hunched Swordsman
Set in a fictional version of pre-modern Japan called Chūshin, this is a story about Torakichi, an old samurai and how he helps Hanabira undo the curse that aflicts her child, the curse of petrification, the curse of the Ashen Beetle. Torakichi and Hanabira will have to traverse through a war torn kingdom, ascend the Shinsei Mountains and find the cure in a tale of perseverance, determination and hope.
8 150 - In Serial22 Chapters
Watching Grass Grow
So my story is pretty cliche killed by the gods, reincarnated into a different world I even get a status screen. Yeah this story is probably not gonna stand out very well so whats different well I'm a plant, still not enough my status screen looks more like a base builder in strategy games, need more how about my growth rate is so fast I can grow 100 meters faster than an Olympic Athlete can run it. Now your interested click to read about how I Joseph Phisher a sentient plant shows the world who's really top of the food chain.Author: This will be my first fiction so I hope you cut me some slack that said I'm open to constructive criticism. Because of circumstance the release times might be far apart but i plan on finishing this thing even if support is nonexistent. My inspiration came from Re: Monster, Verdant Lord, Plants vs Zombies and Little Shop of Horrors. Warning: Mature rating is mainly for violence and foul language but others things might also come later.
8 167 - In Serial46 Chapters
Ley World-The Game
it is the year 2027 and the world's first VR-MMORPG is coming out. Jayson is lucky to be one of the 10,000 people selected to "Beta-Test" the game 2 months before it officially came out. He wants to explore the world, and if possible, become one of the best. He has two months to go strong before the rest of the world attempts to take a piee of the world for themselves. Follow him as he begins his new life. SPOILERS BELOW ARC 1-The Station After appearing in the "tutorial" part for his race, Jayson has to quickly become stronger and learn how to fend for himself. For now, life seems quite nice and cozy, but he has a lingering suspicion that something is wrong in all this.
8 183

