《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 13
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 13
Gabaki d'aya sadam yadauke qafarasa daga wajan sawwama yadaina zuwa wajanta yadaina nemanta, ya yanke duk alqarsa da ita, duk wani hanya da zata iya sadashi da ganinta yakan gujewa faruwar hakan dama tun can sai yaje yake ganinta kokuma yabi hanyarda take sana'arta, qarfi da yaji ya cirewa kansa tunaninta ya rage tunaninta sosai koda tunanin yazo masa yakanyi qoqarin yakicewa,
Harkokin gabansa kawai yakeyi amma wani lokacin yakan tunata sa'i-sa'i,
Qoqaarinsa kawai ya fisge ya cireta acikin ransa,
Dukda yayi nasara ta wani fannin amma ta wani fannin yakasa,
Yarage tunaninta sosai amma kuma bawai yabari gabaki d'aya bane wani lokacin haka yakanyi tunaninta,
Afad'insa yace tunda batason alaqarsu shida ita batason ya ra6eta batason duk wani abunda zai hadasu shikennan yarabu da ita yabarta tayi farin ciki saboda yaga zuwansa wajanta yana sanyata cikin damuwa,
Bazai qara takura mataba kamar yanda take nunawa adik lokacinda yaje wajanta,
Hakan yasa kawai ya saka harkokin karatunsa agaba dama gashi test sukeyi hakan yaqara dauke hankalinsa daga gareta nasa wajan kenan."
————-
Sawwama kuwa anata wajan ta zuba idanuwa amma shiru yake babu shi babu alamunsa,
Akullum idan halima tafita wajan sana'ar sawwama taringa leqawa kenan koda zata ganshi, amma shiru,
Lokuta dayawa takan tambayi halima, halima ta shaida mata baizoba,
Ranarda ta qara tambayarta halima tadubeta tana fadin wai nikam sawwama wayeshi kullum kike tambayar wajansa?
Akwai wata alaqa tsakaninku ne,
Girgiza kai sawwama tayi tafara kame-kame tarasa amsarda zata bawa halima,
Sai can wani abu ya fado mata cikin ranta tayi saurin fadin A'a kawai yana bina bashine,
Inaso idan yazo nabashi kudin sane shiyasa nake tambaya,
Jijjiga kai halima tayi tace auu akan wannan nema, ai idan kudin sane zanbashi duk ranarda yazo idan kuma bai zoba Allah yabaki lafiya kici gabada sana'arki saiki bashi da kanki,
nunfashi mai dumi kawai sawwama ta furzar batareda tace komaiba, bata qara tadawa halima zancensaba bata qara tambayarta akansaba amman koda yaushe tana cikin tunaninsa ahaka harta warke tafara fita wajan sana'arta,
Ga dukkan alamu sawwama abun yafi zafi ta wajanta dan kuwa ita bata ko qoqarin mantawa dashi, akullum qara tunaninsa takeyi, bata bar tunaninsaba saboda data zauna zata hau aikin tunani, dan anata ganin it ace ta 6ata mata rai,
Sau dayawa mama takanyi mata magana akan yawan zaman tunanin,
Amma abun ya faskara hakan yasa mama take tunanun ko abunda yafaru da ita abayane yake damunta shine yake sanyata yawan tunani,
Advertisement
Idan tana tunanin mama takan fara kwantar matada hankali, kuma itama mama takan shiga damuwa hakan yasa yanzu take 6oye damuwarta gaban mahaifiyarta, lokuta da dama sai tashiga d'akine abun yafi damunta saboda acikin gida koyaya tazauna bazata rasa mai d'ebe mata kewaba,
Lokuta da dama sawwama takan zauna tayita neman dalilin wannan tunanin nasa datakeyi amma takasa,
Sawwama qaramar yarinyace mai rauni da sanyin hali rayuwarta tafi yawa ita kad'ai bawasu qawaye garetaba balle ace tafad'a musu damuwarta su bata ainihin amsar abunda yake damuntaba,
Ba kuma zata iya fadawa maman taba,
Haka tayita riqe abun acikin ranta
Amma mikin rashin ganin sadam yananan cikin ranta,
A kullum zuba ido takeyi da ganinsa , sanya rai takeyi da sake ganinsa amma kuma ko mai kamanninsa bata qara ganiba."
————
Sadam yadawo wani irin mutum mai zafin rai ko qannensa lokuta dayawa abu ba abuba sai yhausu da masifa,
Balle najeeb da suke wuni zubur tare akan abu qarami yake sauke zafin ransa,
Najeeb kuwa yanzu tun yana fushi da sabon halin sadam harya hakura yadaina,
Idan yayi masa wani abun kawai sai dai ya maida wasa kokuma ya share wani lokacin ya maida masa idanna maidawane,
Saudayawa sai bayan sadam yayi abun daga baya sai yazo yaga rashin dacewar abunda yayi,
Mummy kuwa anata wajan koda yana yiwa qannensa masifa bata cewa komai karshema saita hau kansu da fad'a tana fadin aii laifinsune saboda ita har indai sadam zaiyi karatu toh bata ta6a barin wani abun ya takurashi,
Kaffa-kaffa takeyi dashi tana lalla6ashi har indai yana karatu,
Hakan yasa suma qannesaa dasuka lura suka daina shiga sabgoginsa sai dai idan mummy ne ta aikesu sukai masa wani abun shima hakan suna kai masa zasu juya abunsu."
——————
Najeeb keta kiran wayan sadam yaqi dagawa saura 5minute su shiga test amma sadam bai qarasowa hakan yad'agawa najeeb hankali yakira wayarsa kuma sai tayi ringing harta katse amma bai dauka,
Iska mai zafi najeeb ba furzar baison mai yake damun sadam ba gabaki d'aya yanzu yadawo wani iri abunda yaga dama shi yakeyi
Bai gama ida tunaninsaba saiga sadam ya iso, cikin zafin rai najeeb ya nufeshi yana fadin sadam amma kaga time kuwa?
Yanzu saura 3minute ashiga amma sai yanzu kake isowa?
Ko kulashi sadam baiyiba yawuce ciki abunsa dasuari najeeb yabishi yana fad'in sadam na dadefa anan ina jiranka amma shine daka iso ko kallo ban ishekaba zaka wuce sannan kuma nasan kaga kirana kaki d'agawa,
Advertisement
Tsaki sadam yaja yana fadin wai kai ina ruwankane?
Wai kai nake yiwa karatun kowa kaina?
Idan naga kiranka saime? banyi niyyar dagawa bane yafad'i sannan yashige ybar najeeb awajan da mamaki,
Gabaki daya yanzu sadam ya canja,
Baison mai yake damunsaba,
Yanzu duk jiransa da yayi wulakancin da zai saka masa dashi kenan?
Can ciki sadam yawuce ya zauna alamun bayaso kowa yazo wajanda yake,
Ganin haka yasa najeeb shima ya naimi waje nesa dashi yazauna,
Ahaka har aka shirya test din aka yi aka fiffito,
Bayan angama najeeb yatashi yafice bai ko kalli wajanda sadam yakeba,
Kusan 2hours sadam yana zaune babu najeeb gabaki daya sai yaji wani iri duk jikinsa yabi yayi sanyi yasan abunda yayiwa najeeb bai kyautaba,
Shikansa yasani idan aka cire mahaifiyarsa babu mai nuna kulawa akan lamarinsa fiyeda najeeb,
Kifa kansa yayi jikin table wani iri yakeji cikin ransa shi kansa baison mai yake damunsaba yarasa mai yasa yake nuna zafin rai akan kowa,
Wanda canda bahaka yakeba baisan dalilin dayasa yanzu abu kadan yake 6ata masa raiba,
D'ago kansa yayi yana duba cikin class din koda zaiga najeeb amma bai ciki,
Fushi najeeb yayi ransa ya raya masa, tafin hannunsa biyu ya sanya ya rufe fuskarsa yana fadin ya Allah🥺 shi kansa yasan halin najeeb yasan wanene najeeb, kwata-kwata bai iya fushiba duk zamanda zakayi dashi idan kace kaga fushinsa to kayi masa karya,
Tunda yau njeeb yayi fushi yasan ba qaramin 6aci ransa yayiba, gabaki daya saiya dawo yanajin haushin kansa, yana cikin wannan tunanin yaji anzauna kusa dashi,
Bud'e idanuwansa yayi ya saukesu akan najeeb,
Murmushi najeeb ya aika masa hadeda miqa masa wata y'ar bag yana fadin nasan bakayi breakfast ba natafi nema maka abinda zaka karya dashi kuma sai yanzu nasamu layi yayi yawa,
Najeeb yana maganane kamar babu wani abunda yafaru,
Da kallo kawai sadam yake binsa cikin ransa yana ayyanawa inama dashine da zuciya irinta najeeb,
Yadade baiga mutum mai sauqin kai irin najeeba ba,
Daga masa kai najeeb yayi yana fadin malam wannan kallon fa?
Ajiyar zuciya sadam yasauke sannan yace" dama ba fushi kayiba?
Zaro ido najeeb yayi yace fushi kuma😳 sannan yanuna kansa yace ni? A'a nikam ba fushi nayiba,
Nayi fushi kuma awani dalili?
A dalilin cewa na 6ata maka rai sadam yabashi amsa,
Murmushi najeeb yayi sannan yace eh tabbas datsu ka 6atamin rai kuma naji babu dadi amma yanzu yawuce,
Ni bazanyi fushi dakaiba sadam a kullum nakan baka uzuri komai dan adam yayi arayuwa kafin kayi fushi ko daukan wani mataki kayi tunanin dalilinsa na aikata wannan abun,
A kullum nakan bawa mutuminda nake tare dashi uzuri saboda wani lokacin bazaka ta6a fahimtar halinda wani yake cikiba idan ba yafada makaba, bazaka ta6a fahimtar mai yasanya ya aikata abunda ya aikataba, wasu abubuwan idan ba kaine amtsayin mutumba bazaka ta6a fahimtar halinda yake cikiba, bakowani abu bane ake aikatashi babu daliliba, dole inbaka uzuri sannan in sake baka uzuri har indai bazan baka uzuriba akan kayimun abu ba dai-dai ba menene amfanin zaman taren sadam?
Nasan cewa ba haka halinka yakeba dole wani abu yake damunka yasanya ka canja wanda bakason fadansa idan bazan takuraka ka fadamin damuwarkaba kaga ai bazan gaza wajan hakuri da abunda zakayiminba,
Kaga ko kadanne nima nadamu da damuwarda take damunka,
Da ido kawai sadam ya tsareshi, gabansa yana wani mummunan faduwa kalaman najeeb keyi masa yawo a dodon kunnensa, ji yakeyi kamar najeeb da biyu yake maganarnan,
Uzuri! Ya maimaita a fili,
D'an dukan kafadansa najeeb yayi yace ehem uzuri nama mutumina,
Sau dayawa idan zaka yiwa wanda kake tare dashi uzuri zaka samu koda damuwace ba lallai ka shigeta sosaiba, bana yanke hukunci batareda nasan dalilin dayasa aka aitakata wani abuba,
Wani irin sanyi jikin sadam yayi sosai bai iya cewa komaiba sai rungume najeeb dayayi,
Nisawa najeeb yyi ya tabbata sadam yana cikin damuwa amma bazai takura masa akan saiya fada masa damuwarsaba zaiyi addu'ar Allah ya yaye masa sannan kuma zai jira har lokacinda zaizo ya fada masa da kansa,
Sakeshi sadam yayi yadauki bag dinda najeeb yakawo masa yace sutafi
wucewa sukayi hostel acan sadam yayi breakfast amma hankalinsa gabaki d'aya yana kan maganganun sadam,
Sai yanzu yake ganin rashin dacewar abunda ya aikata shi kansa yasan baiyi dai-dai ba, awancan lokacin daya bata uzuri akan halayyarta yabata uzuri akan maganaganunsa duk haka bata faruba,
Wani Gauron numfashi ya sauke, juyowa najeeb yayi yana dubansa yana kwance idanuwansa suna lumshe amma ba bacci yakeyiba saboda yanata jijiiga qafafunsa,
Lafiya? Najeeb ya tambaya, sanda sadam yadauki dan lokaci sannan yace lafiya qlau,
Kai kawai najeeb ya gyada ya maida kansa yaci gabada damuwarsa shikuwa sadam yaci gaba shima da aikin tunaninsa,
Yana kwance kamar wanda aka tsikarashi ya miqe tsaye zumbur."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial18 Chapters
Dragonic Evolution [Old]
Killed by pure luck and sent to be reborn. That is how the story starts, but watch as this little dragon grows to become the strongest dungeon beast!!! With a system to help him, this is going to be an interesting ride so hop on and start reading. (Updates are on Tuesday and occasional bonus updates on Friday)
8 185 - In Serial27 Chapters
The Dead Lands
Jaden Harris is a professional card player, playing the trading card game Magigio. That is until he wakes up drunk in a field with no idea where he is. The addition of a shy french maiden who barely speaks english, and a fiery red-head with a black belt compound his problems. Not to mention that the world has ended, and the afterlife is run by a cartoon paperclip. Will Jaden be able to survive the end of the world, learn magic, and deal with the cruel whims of a sarcastically cheerful god-like being? Note: Anything posted here is essentially the rough draft for a book that will eventually be posted to amazon/kindle unlimited. I apologize for any spelling/grammar issues, they'll be sorted out when my editor/wife does the editing. Extra note: the stat pages are intended to be red, but there is no color option on the text editor for this website. As a result, they default to black. Sorry, I'm doing the best I can with what I have. If you like what you've read, please join my facebook group at: https://www.facebook.com/groups/201449257405559/ For other books that I've written, you can find them at: https://www.royalroad.com/amazon/B07L476H4G (as a function of royalroad for whatever reason, I have to link to a book, and not my author page. Just click on my name on the amazon page beneath the title to see the rest of what I've written)
8 200 - In Serial13 Chapters
Reversing Supernova
In a blink of an eye, she found herself waking up as May Ling, a denizen of Planet Er-na, with no idea how she got there.To make things worse, she had absolutely zero clue of who this May Ling supposed to be.Saddled with a defective body and memory as holey as Swiss cheese, the Earth-native resolved to find a way home. If that meant borrowing this May Ling's body like a wraith wearing a corpse's skin, then so be it.However, she would soon realize that May Ling's life was not as mundane as she had initially predicted and her miscalculation might cost her everything.
8 247 - In Serial39 Chapters
Elite Crushers
Elite Crushers is the most popular fighting video game in the world with a tournament scene filled with polarizing personalities. Gordie Ross is only fourteen when he enters his first major tournament, and he goes with his brother Michael -a rising legend- but Michael isn't his usual self. Their ultimate dream is going to the Miami Team Invitational tournament, but it will be a challenging road with many obstacles before either get an invite. ***New chapter every 3 days!***
8 155 - In Serial36 Chapters
Something To Believe In [Dean Portman] ✓
♪𝖽𝗈 𝗒𝗈𝗎 𝗄𝗇𝗈𝗐 𝗐𝗁𝖺𝗍 𝗂 𝖻𝖾𝗅𝗂𝖾𝗏𝖾 𝗂𝗇? 𝗅𝗈𝗈𝗄 𝗂𝗇𝗍𝗈 𝗆𝗒 𝖾𝗒𝖾𝗌 𝖺𝗇𝖽 𝗌𝖾𝖾♪𝗂𝗇 𝗐𝗁𝗂𝖼𝗁 𝗌𝗈𝗉𝗁𝗂𝖾 𝗋𝖾𝖾𝖽 𝗃𝗈𝗂𝗇𝗌 𝗍𝖾𝖺𝗆 𝗎𝗌𝖺 𝗍𝗈 𝗉𝗅𝖺𝗒 𝗂𝗇 𝗍𝗁𝖾 𝗃𝗎𝗇𝗂𝗈𝗋 𝗀𝗈𝗈𝖽𝗐𝗂𝗅𝗅 𝗀𝖺𝗆𝖾𝗌 𝖺𝗇𝖽 𝗆𝖾𝖾𝗍𝗌 𝖽𝖾𝖺𝗇 𝗉𝗈𝗋𝗍𝗆𝖺𝗇𝗈𝗋𝗂𝗇 𝗐𝗁𝗂𝖼𝗁 𝗍𝗐𝗈 𝗍𝖾𝖾𝗇𝗌 𝗇𝖾𝖾𝖽𝖾𝖽 𝗌𝗈𝗆𝖾𝗍𝗁𝗂𝗇𝗀 𝗈𝗍𝗁𝖾𝗋 𝗍𝗁𝖺𝗇 𝗍𝗁𝖾𝗆𝗌𝖾𝗅𝗏𝖾𝗌 𝗍𝗈 𝖻𝖾𝗅𝗂𝖾𝗏𝖾 𝗂𝗇
8 107 - In Serial16 Chapters
Iridescent ↳ Peter Maximoff
❝You are all my children, and you're lost because you follow blind leaders. These false gods, systems of the weak, they've ruined my world. No more.❞ - Apocalypse| iridescent | : adj. Showing luminous colors that seem to change when seen from different angles.[set during X-Men: Apocalypse]DISCLAIMER: I DO NOT OWN ANY OF THE XMEN CHARACTERS, I ONLY OWN MY ORIGINAL CHARACTER, BRIANNA XAVIER, AND THE STORY SURROUNDING HER.
8 214

