《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 14
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 14
Kallonsa najeeb yayi yana fadin ina zuwa haka naga ka miqe ko har zamu tafi venue?
Iska sadam ya furzar tunawa dayayi yanada lactures kuma sai yamma kafinnan su gama,
Tsaki yaja yakoma ya kwanta duk yanajin wani iri hankalinsa gabaki d'aya yayi gida yanzu hakama dan yasan idan yace zai tafi ran najeeb zai 6acine amma da gida zai wuce,
Komawa yayi yazauna yaqara jan wani tsakin sannan yakoma ya kwanta,
Duk abunda yakeyi idon najeeb yana kansa ganin ya kwanta yasashi ta6e baki yana fadin koma dai menene idan tayi tsami ai zamuji,
Sadam bai kula shiba ya runtse idonsa da kar6i."
Juya kan mashin dinsa yayi zuwa wajanta saboda yau kam baya tunanin zai iya bacci idan bai sanyata a idanuwansaba,
Tun farko yaci ace yabata uzuri amma yakasa bata uzuri,
Kamar wanda tasan ya iso wajan tayi saurin waigawa idanuwansu suka sarke cikinna juna,
Da sauri-sauri ya qarasa wajan ya zube guiwowinsa aqasa,
Tsura masa idanuwa tayi ahankali yafara magana yana fadin kiyi hakuri nasan ban kyauta mikiba,
Ban baki uzuri alokacinda ya daceba ban baki uzuri natsaya naji dalilinkiba,
Ki yafeni nayi alqawari bazan sake nesa dakeba,
Bazan qara nesantarda kaina daga garekiba,
Ke wata sashine cikin rayuwata, kasancewarki cikin rayuwta shine babban burina, zan kasance mai baki uzuri akowani irin hali,
Kuka takeyi kamar wanda ranta zai fita takasa furta komai,
Langa6arda kansa yayi zuciyarsa tayi rauni da kukanda takeyi,
Azabtuwa yakeyi da kukanta kowani zubar hawayenta ji yakeyi kamar wanda ake qonashi da garwashin wuta,
Cikin karyayyar murya yafara fad'in kice wani abu, kibar kukannan ki furta koda kalma d'ayane ko zanji zuciyata tayi sanyi,
Hannu tasanya ta share hawayenda yake kwaranya akan fuskarta,
Dakyar ta bude baki zatayi magana,,,,,,,,.,,
Advertisement
Bubbugashi najeeb yakeyi yana fad'in sadam badai baccin har yayi nauyiba??
Katashi muna shirin makarafa,
Miqewa zaune sadam yayi hadeda dan murtsuka fuskarsa alamun baccin nasa yafara nauyi,
Huuuuuu ya fidda wani numfashi saannan yadubi najeeb,
Wani qululun baqin cikine ya tokare masa ransa tunawa da mafarkinda yakeyi najeeb ya d'agashi tana shirin fada masa magana yatasheshi dama yabari tafadi abunda zata fada masa kafinannan ya tasheshi,
Kome take shirin fada ohow,
Tsaki yaja azuciya yamike fuuuu yafice
Girgiza kai najeeb yayi ya furzarda iska yabi bayansa,
Basu suka gama lactures ba sai 6:00pm dake ranar friday ne najeeb yacewa sadam zai bishi agida zaiyi weekend dan haka saida yakoma ya shirya kayansa sannan suka dauki hanya,
Najeeb kuwa yanata damun sadam da surutu yana fad'in kasam sadam tunda nakoma school rana d'ai-d'ai da bana tunanin awararar yarinyarnan,
Kasan a school muna fita musiya da daddare amma ba cikin gariba sau dayawa bana iyaci yanzu haka badan dare yayiba damun wuce wallhy amma gobe in sha Allah zanu taho,
Sadam yana jinsa yagama sunbatun surutunsa bai tanka masaba har yayi shiru,
sadam yaci burin ganinta yau amma haka badan yasoba yawuce yafara kai najeeb sannan yajuyo zuwa gida amma hankalinsa gabaki d'aya yana wajanta,
Haka yakoma gida badan ransa yasoba sai dan dare yayi babu yanda ya'iya."
Yagama duk wani abunda sukabi masa jiki wanda yakeyinsu kafin ya kwanta bacci,
Yakwanta domin samin hutu amma sai me? Bacci ya gagara,
Kalaman najeeb ne wanda yayisu datsu suka runga dawo masa cikin ransa,
A kullum nakan bawa mutuminda nake tare dashi uzuri saboda wani lokacin bazaka ta6a fahimtar halinda wani yake cikiba idan ba yafada makaba, bazaka ta6a fahimtar mai yasanya ya aikata abunda ya aikataba, wasu abubuwan idan ba kaine amtsayin mutumba bazaka ta6a fahimtar halinda yake cikiba, bakowani abu bane ake aikatashi babu daliliba, dole inbaka uzuri sannan in sake baka uzuri, har indai bazan baka uzuriba akan kayimun abu ba dai-dai ba menene amfanin zaman taren sadam?
Advertisement
Tabbas sadam yayi gajen hakuri ya dauki dokin zuciya bai bata uzuri alokacinda take buqatar hakanba,
Bai bata uzuri alokacinda yakamataba,
Bai tsaya ya fahimci damuwartaba
Baisan dalilintaba,
Bai karanci zuciyartaba,
Tabbas alokacinda take magana idanuwanta da zuciyarta suna cikeda quna, amma yagaza fahimtar hakan,
Ya rabba yafad'i hed'eda dafa kansa, wani irin zafi yakeyi cikin zuciyarsa,
Yadauki tsawon lokaci baiyi barciba hankalinsa yana can wani wajan,
Shidai bazai iya fadin lokacinda bacci ya daukeshiba."
Da safe bayan yayi breakfast yakoma d'aki bai sake fitowaba sai azahar, dayayi sallan azahar kuwa bai dawo gidaba, gidansu najeeb yawuce,
Acan ya yada zango,
Zamansa wajan najeeb ne yadan ebe masa kewa na wasu lokuta daga nan suka fice zuwa yawansu,
Yamma liqis suka dawo gidansu sadam dayake weekend ne mummy tana gida bataje ko'inaba,
D sallama suka shiga falom suka sameta azaune tana kallo a tv, qarasawa ciki sukayi sadam yasamu kujera yazauna yana maida numfashin yayinda shikuma najeeb ya tsugunna yana gaisheta,
Da fara'a a fuskar mummy take duban najeeb tana lafiya son ya karatu? Kadawo weekend kennan?
Ajere ta aika masa wannan tamabayoyin sosa kansa yayi yana fadin lafiya mummy wallhy kwana biyu ban shigo gidaba shine nace wannan weekend d'in sai nayishi agida saboda muna dosar exam idan mun fara bazan samu damar zuwa gudaba,
Eh hakane kam Ay kuwa dai ka kyauta, ina dai ana karatun?
Eh mummy anayi, da fara'a tace toh Allah ya taimaka kunata dosar exam kaga sadam shima dasai yakoma hostel yazauna yayi karatun exam dinsa dakyau tafad'a tana satar kallon sadam,
Miqewa sadam yayi zumbur yabar wajan yashiga d'aki bai sake jin mai suke fad'iba saiga najeeb ya biyo bayansa yana fad'in sadam yamma tayifa, katashi muje musiyo wannan abun kafin dare yayi,
Wani irin faduwa gaban sadam yayi shiru yayi ya kasa miqewa yanata zullumi cikin ransa,
Saida najeeb yaqara mai-mai tawa kafin sadam yamiqe dakyar yace muje,
Fitowa sukayi najeeb yayiwa mummy sallama sannan suka fita,
Ahankali sadam yake tukin mashin din kamar wanda bayaso dan har saida najeeb yayi masa magana amma bai juya ya kalleshiba ko yatanka masaba, ahaka yaci gabada tukinsa har suka qarasa wajanta,
Tun daga nesa yake zuba mata ido, idanba idanuwansa bane suke nuna masa ba dai-dai ba amma har wata y'ar rama yaga tayi,
Agefe can da nisa yayi parking machine din najeeb ya sauka akai yayi wajanta yana fadin bari yanzu zan dawo, sadam bai kula shiba ya wuce abunsa,
Tsayawa yayi jikin machine din ya harde kafafunsa sannan ya harde hannunsa a qirjinsa ya zuba mata idanuwa,
Sawwama dake zaune wani irin faduwar gaba ta tsinci kanta jikintane yabata cewa yana wajan samun kanta tayi da fara waige-waige caraf idanuwanta suka sauka akansa,
Faduwar gabantane ya tsananta yayinda ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya,
Gabaki daya ta kid'ime ta dibibice tarasa wani yanayi take ciki farin ciki kokuma akasin hakan."
✔️ote plss
Comment
Share
Follo
Advertisement
- In Serial20 Chapters
Stranded In Naruto like world
What do you think will happen if by any chance you are transmigrated into the world, where you know what'll happen in future? moreover, the cast is someone in your family? What were you seek if you have the power and knowledge to change the course of history? What were you seek, if you don't really want anything besides peace? What do you do when the thing you avoid, knock on your door? Let us read the story of him, the trespasser of the world, that should be the world that has a happy ending?... TLN: It's not a naruto world duh, it's naruto like world, it's a revised version of Reincarnated into naruto world?! Meh... not exactly revised but, please enjoy!
8 132 - In Serial29 Chapters
The Failed Assassination of the Thunder God
An immortal assassin who has known nothing but brutality. A God who has walked the path of the divine for all time. On a day like any other, Qian Meng set out to kill a Celestial Being for a sack of gold—something he'd done many times in the past. To him, if the being had committed evil deeds, he deserved an evil end. That was it. And he had truly planned on killing him, that is until the God of Thunder and Justice—Lei Gong—expressed a familiarity to Qian Meng that he did not anticipate. So, for the first time in his long life, he let a man live. Little did Qian Meng know that being benevolent also had its consequences. Someone wished the God of Thunder death and would do anything to make it happen, even drag others through the mud. Pulled together by circumstance, yet accused of heinous deeds, can they uncover the truth surrounding the murderous plot of their brethren? Weekly updates on Friday! This is a glacial-burn BL story without graphic romantic scenes. It focuses on the tragic fantasy plot of our two main male leads.
8 259 - In Serial19 Chapters
Elysium
The first God, Prometheus.A being that transcended simple Godhood. He stood at the apex of power, the pinnacle of creation. But it was his might that became his downfall.His heart corrupted as his lovers and friends withered away with the passing of time. He envied them; their mortality and he thristed for it, more and more with each second.His mind and soul were thrown in an endless maelstrom of envy over his own brethren and raw madness. But before he gave into the pull of insanity he ended his own life.Overloading his own power in an explosion so massive that the fundamentals of space and time were distorted, a lone soul made its way through the cracked dimensions; bypassing nether and purgatory. Astray and confused the small wisp entered its new life.
8 101 - In Serial12 Chapters
Origin of the Best Void Magician
There were five students walking on the way to their own homes. Yet while walking they were flashed with blinding light and a magic cirlces surrounds them, lead them to another world. Is this the what so called Isekai? Being summoned as hero, all five of them first to check their [Skill], ablessing from the goddess. And one of them, Kagerou Ibuki was granted [Void Magic]. But whats this? They gave him a scorned expressions towards him. What? [Void Magic] is useless? Due to that, he was kicked out of the castle. How he will survive with the so called useless [Skill]?
8 176 - In Serial25 Chapters
i knew you - ron weasley
Ron inexplicably broke up with Slytherin prefect Cassiah Black just days before their final year at Hogwarts, leaving them both with broken hearts and no future plans, but too stubborn and too proud to fix things. Will they find their way back together before the year ends, or will the end of their time at Hogwarts be the last time they ever see each other? warnings: slow burn. angst, drug/alcohol use, eventual SMUT (and lots of it) ;) highest rankings (all time)#1 ron x oc #7 ron#7 ron weasley x reader#2 slytherin reader#11 ron x reader#87 ron weasley #400 dracostarted October 21st 2020. updates about once a week. Published on my Wattpad and my Tumblr (theweasleyslytherin). © 2020
8 108 - In Serial16 Chapters
Arranged (Todoroki x Reader x Various)
You and Shouto Todoroki were forced to have an arranged marriage by order of Enji. Although you come to terms with it, Todoroki becomes distant.
8 90

