《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 23
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
Page 23
Sawwama ta maida hankali sosai wajan koyan abunda tajeyi saboda taga sadam nason tayi karatu ita kuma har in dai sadam yana son abu har indai bai sa6awa shari'a ba koda ita bataso zata daure tayi,
Shima sadam nasa hankalin yana wajan exam dinsa haka dai lokaci-lokaci yakan shigo ya dubata."
Sati uku curr su sadam sukayi suna exam sannan suka gama,
Sanda sadam yayi kwana biyu curr agida yana hutu bai zuwa ko ina,
Hayaniya mummy tahana qannensa yi acikin gida saboda karsu takura shi yagama exam yana buqatar hutu,
Mummy lailaya sadam takeyi tanaji dashi sosai,
Bayan sadam yagama hutunsa sai kuma yafara fitan dare zuwa wajan sawwama,
Anan suka fara samun matsala da mummy dan nunawa tayi batasan zancenba bazai ringa fitan dareba
Wai cewarta idan abaya yace karatu yake fit yanzu fa?
Yawan banza ita kuma bazata daukaba,
Sadam yashiga damuwa sosai lokutan dayake exam daurewa yakeyi yake tsallake kwanaki baije wajan sawwama ba gashi yanzu yagama exam lokacinda yake kallon lokacin zuwa wajan sawwama akai-akai yazo amma mummy tana neman hanawa,
Saida dady yashiga wannan lamarin kafin sadam yasamu damar fita tatass yayiwa mummy yace aishi sadam ba yaro bane bakuma mace bace da zata ringa cewa bai isa yafita ba sannan kuma yace mata aiy dade da bawa sadam damar fita zuwa 9:30 yadawo gida dan haka yasoke wannan zance baiso yaqaraji tayi zance akan fita har in dai ba 9:30 yawuce awaje ba,
Mummy dai dady yafi qarfinta kuma tanajin maganarsa sosai haka babu yanda ta iya tana kallo sadam ya shirya yafita abunsa."
Sanda ya biya bookshop ya siyo littafai wanda dama suna rubuce jikin form na islamiya akan zasu siya sannan yakama hanyar gidansu sawwama."
Sadam wajan sawwama yawuce kai tsaye daya isa yadade awaje babu wanda zai aika ya kirawota, sai alokacin yakejin haushin rashin mallaka mata waya da baiyina, yana tsaye saiga baba yazo zai shiga gida yana tura wheelbarrow dinsa,
Saurin durqusawa sadam yayi yana gaidashi baba ya amsa fuska asake yana fadin A'a sadam kaine atsaye nan?
Maman nawa bata fito bane?
Sosa kai sadam yayi yace wallhy baba ban samu wanda zai kirawomun ita bane,
Ashha ashha baba yafadi sannan yace idan irin haka tafaru daga yanzu kashiga da kanka ka kirawota gidan yanzu aiba baqonka bane,
Advertisement
Shiru sadam yyi yana tunanin ta yanda zai fara shiga gidan,
Babane yace to madallah anyi dawainiya da mamana harda qanwarta kuma Allah yayi albarka amma da baka takura kanka bama sadam da zan sanyata,
Kan sadam yana qasa yace babu komai baba,
Gyada kai baba yayi sannan yace" toh shikenan Allah yayi albarka ni barina qarasa ciki sai inyi mata magana,
Godiya sadam yayiwa baba, sai baba yatura barrow dinsa yayi ciki,
Sadam yabishi da kallon tausayawa, ayanda ya fahimta baba baida wasu shekaru matashine sai kuma rashi da wahala da sukayi masa yawa dan a kintacensa baba bazai wuce shekaru talatin da biyarba idan ya daura a da biyar to bada yawaba,
Azamaninnan wasu kamarsa ma samarine basuyi auren fari ba,
Kana kallonsa zakaga cikarsa ta fulani cikakken ba fillatani ne dogo baida qiba,
Matashi amma wahala ya sanya yadawo kamar wani wanda yafi shekarunsa,
Matasa irinsa yanzu sukeji da samar taka da jini ajika,
Gabaki daya tausayin baba ya rufeshi yanaji cikin ransa da yanada hanya daya taimaka masa yafita a halin kunci dayake ciki,
Muryarta mai sanyi da dadin sauroro mai sanya nutsuwace ta katseshi daga tunanin daya fada,
Ajiyar zuciya ya sauke alokacinda ya daura idanuwansa akanta,
Sam baiji takun tafiyartaba bai sanda isowartaba saida yaji sallamarta,
Murmushi ya sakar mata hadeda amsa sallamar,
Zaunawa tayi agefe tana gaidashi ya ama yana tambayarta ya makaranta ta amsa masa da fadin Alhamdulillah sannan ta daura da tata tambayar da fadin ya jarabawa?
Alhamdulillah jarabawa angama sai jiran sakamako,
Allah yasa muga alkhairi sawwama tafadi kanta yana qasa,
Samada minti biyar suka dauka babu wanda yace komai sawwama ita kanta yana qasa,
Shikuma sadam ya kafeta da ido yana kallonta tayi masa kyau sosai,
Cikin hijabanda yasiyo mata ta sanya guda daya hijabin ya sutura jikinta gabaki daya ya rufe mata ko'ina,
Fuskarta kawai ta tafin hannuntane awaje,
Sawwama jikinta yabada ita yake kallo hakan yasa takasa daga idonsa saboda tasan tana dagawa idonta sai sauka akan nasa,
Ita kuma nauyinsa takeji sosai.
Tsarguwa tafara yi jikinta yafara rawa ganin haka yasanya ya sake murmushi mai sauti kadan ya kauda kansa gefe yana fadin waini haryanzu tsorona kikeji ne?
Shiru sawwama tayi batace komaiba itadai iya saninta ba tsoronsa takejiba nauyinsa takeji sosai,
Ganin tayi shiru taqi amsawa ya sanyashi kauda zancen da fadin yaya karatun akwai dadi kuwa?
Nodding head dinta tayi tace uhmm akwai dadi,
Advertisement
Dubanta yayi yace lallai toh ina sauraro mai dame kika koya cikin 2weeks?
Shiru tayi kamar mai tunani nan kuma tafara jero masa abubuwanda ta koya,
Mamaki sosai sadam yasha dan baiyi zaton cikin 2weeks zata dauki wad'annan abubuwanba, wajan qur'anine ma yaji tadanyi baya da alamu ba sosai ake koya musu qur'an a ismaliyar ba, sunfi qarfi ta wajan littafai,
Lallai ta maida hankalinta sosai kan karatunta domin ko ayanzu taqaru dayawa,
Jijjiga kai yayi yace ga books dinda ake koya muku saiki qara maida hankaki,
Kar6a sawwama tayi hadeda yimasa godiya,
Sadam bai jima sosai ba yayi mata sallama saboda kada ya wuce lokacinda dady ya sanya masa,
Yayi mata sallama yawuce gida, saida taga tafiyarsa sannan tajuya tashiga gida,
Sanda ta zauna sannan ta miqawa halima littafan tana fadin debi naki ki zubamin nawa adaki,
Murna halima tafara tana fadin kinga dama anata magana akan musaya,
Mama datake zaune tace madallah dama naji kun fadawa babanku bai samu kudi bane daya siya muku gashi sadam ya siyo to Allah yayi albarka,
Amin su duka suka amsa."
————-
Washe gari sadam da zaije wajan sawwama sanda yabiyo ya siyo qur'ani guda biyu masu kyau sosai yakaiwa sawwama,
Qur'an din sunyi mata kyau sosai tayi godiya, aranar yafara daura mata karatu saboda yaga karatun Qur'anainta yaja baya,
Haka tabawa halima daya ta riqe daya,
Haka sadam kullum yazo saiya qarawa sawwama karatu kuma tana daukan sosai,
Tarteel yake qara mata da qur'an idan yayi saita karanta yana koya mata da tajweed,
A kullum yazo saiya sanyata tafara yimasa karatu saboda dadin muryarta kafin daga baya ya daura mata,
Sawwama bata dauki karatunta da wasa ba da qarfinta da dage tanason koyon karatu, Allah saiya dubi zuciyarta yasa take ganewa sosai fiyeda tunanin mutum,
Kuma shima sadam tadage sosai,
Najeeb babu yanda baiyi da sadam ba akan yakaishi yaga sawwama ba amma fir yaqi,
Haka koda sunzo siyan awara ranarda babu makaranta sadam baya karasawa balle har najeeb ya fahimci wani abun."
———
Sadam da sawwama soyayyarda take tsakaninsu tayi qarfi sosai shaquwace mai qarfin gaske atsakaninsu,
Soyayya sukeyi mai cikeda tsafta bbu algus acikinta,
Ana haka result dinsu sadam yafito mummy najin labarin result yafito hankalinta duk yabi yatshi shikanma sadam bai wani damuba amma haka mummy tabi ta daga hankalinta,
Aranar sanda ta sanya yaje yaduba result dinsa,
Sadam yayi mugun qoqari a result dinsa dan bai ta6a irin wannan qoqarin ba kaff department dinsu babu wanda yakaishi cin result,
Sakamkonsa yayi kyau sosai, sadam yasamu kansa cikin farin ciki baiyi qasa a guiwaba ya nufi gida,
Mummy dataga result ina ka saka ina ka aje da sadam yanda kasan zata maidashi ciki albarka kuwa aranar yashata dady yana office amma haka sanda mummy takirashi tadawo gida,
Shima dady nasa wajan ba qaramin murna yayiba,
Sai wannan lokaci hankalin mummy ya kwanta saboda taga sadam dinta yayi qoqari sosai,
Tasan cewa sadam yana karatu sosai,
Abunda mummy bata saniba sadam baya wani karatun daga hankali shidai kawai Allah yasa yanada kwakwalwar fahimtar karatunne,
Mummy har wajan aikj tajeda result din sadam tanunawa frnds dinta,
Adangi kuwa sai kira takeyi tana sanarwa mutane result din yan uwa da abokan arziki,
Babban yayanta takira ta shaida masa result din,
Bayan tagaya masa yayi murna sosai sannan yace tazo gida tanuna masa,
Da yamma mummy ta shirya taje gidansa,
Commisioner ne yayan mummy,
koda mummy ta isa bayan sun gaisa da matansa ta shiga palour wajansa,
Yaga result din sadam yayi murna sosai sannan yace dama inson yin magana dake gameda zancen sadam yanzu saura how many years yagama karatunsa?
Cikin fara'a mummy tace' yanzu kennan zasu shiga final year masha Allah yafadi sannna yace naga cewa shine danki babba shiyasa nayanke shawarar hadashi da abida diyata saboda qarin zumunci,
Dariyarda take fuskar mummy cakk ta dauke, wani iri taji harga Allah bazata iya barin sadam yayi aure kwana kusa ba,
Dan har frnds dinta sunayi mata magana akan ko zai nemi ya'yansu amma ta qirmishe idonta tace batasan zanceba,
Ina sauraronki me kikace akan hakan?
Yaqenda bai kai zuciba mummy tayi sannan tace yayaa kasan sadam qaramin yarone kuma karatun yanzu yafarshi waida inaso yadanyi nisa akaratune,
Dududi yanzu baifi 24yrs ba da dai za'a bari yadan qara karatu da shekaru ai abun zaifi,
Tunda naga abidanma yanzu itama karatu takeyi,
Dududu itama nawa take bazata wuce 22yrs ba, ai duk abun na gidane abida ai 'ya tace amma sudai yi karatun tukunna su mallaki hankakin kansu,
Jijjiga kai yayanta yayi sannan yace to shikenan zadai muga yanda za'ayi,
Toh kawai mummy tace jiki asanyaye tayi masa sallama tatafi ita dai komai zai faru bazata yarda tabar sadam yayi aure yanzuba."
———-
✔️ote
Share
Comment
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial10 Chapters
dreams
alberu has dreams where he's in a relationship with a trashy bastard who he's never even met beforeso it's a bit awkward to have to meet himshipalberu crossman x original cale henituse
8 69 - In Serial35 Chapters
Ascension VR
2021, Apex Corporation is about to release the first Virtual Reality game - Ascension. The whole world is anticipating the release. The objective of the game: rise to the top, no matter what path you chose and break through mortal limits to... Ascend. Surpassing limits has always been humanity's strength, but are there lines we should not cross? In a game which blurs the lines between virtual and reality, find out what lies beyond...
8 586 - In Serial9 Chapters
2nd Floor
Matthias is a struggling writer finally able to move into his first solo apartment. He's thrilled to have a place free of roommates and siblings, even though the building is decrepit and is inhabited by an odd assortment of people including an intrusive neighbor, a little girl who wanders freely, and an overweight orange cat named Cheese. As Matthias settles in things begin getting stranger. Something vile is growing in the dark and it's coming from somewhere on the second floor... where Matthias happens to live.Author's note: this is me trying to get back to my roots: a character driven novella with horror elements. The story of people struggling against an inscrutable enemy, as well as the day to day trials of being poor in America. I have no idea how often I'll update or even exactly how this will all go down because y'girl is a panster. So strap in because this is the first draft and you all get to see it being born!Feel free to comment whatever comes to mind, and helpful critiques are always welcome.
8 208 - In Serial29 Chapters
I Cant Help Falling In Love With You {L.S}
A series of short stories about two boys falling in loveLarry StylinsonFluff and smut (⚠️) one shots•Highest rankings 🏅#20 in work#71 in niall #44 in novel#84 in liam#21 in fangirl#72 in zayn#174 in louis#436 in harrystyles#179 in larry#269 in larrystylinson#32 in larryisreal#1 in louisandharry#9 in larryfluff#41 in fluffandsmut#19 in fanfictiononedirection#313 in onedirection
8 190 - In Serial23 Chapters
PERYL EDIT - cheryl blossom & peter parker
This book will be about Cheryl Blossom (Riverdale) and Billy Hargrove (Stranger Things s2). (chilly)HATE WILL BE BLOCKEDi will give credits to the people, don't worry © Par propriété exclusive de l'auteur, la copie et les utilisations partielles ou totales de son travail sont interdites; conformément aux articles L.111-1 et L.123-1 du code de la propriété intellectuelle. Tous droits réservés.
8 111 - In Serial43 Chapters
The Throne
Anna has had a very hard upbringing, but she's defeated every hurdle thrown her way. But what will happen when her biggest secret comes to light and how will her life change?
8 139

