《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 24
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
Wannan shafin sadaukarwane gareki JAMILA GUMEL meelarh, Alkhairin Allah yakai miki., nagode kawai da gaske da irin qaunarda kike nunawa rubutuna🥰
Page 24
Yanayin yanda take kai kawo cikin d'akin zai nuna tsanatsar izzarta taku takeyi kamar wanda batason taka qasa dukda kasancewar damuwa tanuna akan fuskarta,
Takai kusan 5minute tana wannan zagayen sallamarda taji alamun shigowane ya sanyata tsayawa wanda take jiran zuwanta kenan sai yanzu ta iso,
Cikin takunta na qasaita ta qarasa gaban gadonta ta zauna ta d'aura daya akan d'aya,
Ta wani jijji da nuna isa da kuma mulki,
Wacce ta shigone itama ta qarasa tazauna a gefen gadon,
Furzarda iska wannan mata tayi tanason yin magana amma nuna isa da izza sun hanata yin hakan,
Wacce ke zaune agefe idanda sabo ta saba da jiji dakai irinna wannan matar,
Daure zuciyarta tayi ta dubi qanwartata tace hajiya suwaiba kin sanya ankirani sannan kuma kinqi cewa komai,
Cikin izza kamar wacce take tsoron magana tace"
Yaya hadiza kiranda nayi miki akan wannan yaro nehaliifa,
Dafa kirji tayi tace shi haliifan menene kuma yafaru?
Kar dai kwabarmu keson yin ruwa,
Girgiza kai tayi hadeda yatsina baki kamar wacce aka takurawa tace"
Kusan hakan domin jakadiya takawomin magana cewa mai martaba dakansa ya dage dayi masa magani yanzu haka zancenda nake miki yafara samun sauqi,
Taqarasa maganar cikin gajarcewa saboda yanayin yanda maganar tayi mata tsayi abaki,
Tagumi Yaya hadiza ta zuba tana fadin ohh ni naga jaraba,
Wannan yaro sai kace d'an gwal mai martaba duk yabi ya tada hankalinsa akansa,
Qara hade rai hajiya suwaiba tayi tace ni duk yanda za'a banso yasamu lafiya,
Yaya hadiza tayi saurin amshe zancen da fadin aikuwa dole musan abunyi zama bai kamaniba hajiya,
Yoh idan yasamu lafiya ai kashinmu ya bushe inada tabbacin da yaronnan lafiyarsa qalau mai martaba daya dade da ajiye mulkinsa yabashi,
Lumshe do hajiya suwaiba tayi ta budesu ahankali sannan tace" yaya hadiza ko nawane zan kashe komai sukeso zan bayar, su dawo da wannan ciwon sabo fill daga nan har zuwa mutuwarsa bana buqatar hankali a gangar jikinsa,
Ko abunda nake dashi zasu qare idan duk wani abunda na mallaka zai tafi saina sanya daya daga cikin yarana sunyi mulki wannan kujera,
Wannan sarauta bazata ta6a kwacewa a hannunsuba,
Haliifa baida damar da zaiyi mulki a qasarnan bazan barshiba, sai dai bayan raina,
Jijjiga kai yaya halima tayi tace hakane yar uwata ina bayanki wannan zalinci da mai yayi kama haka?
Ainaga yayankine manya ai sukeda mulki iyi,
Dan kawai mahaifinsa ya kasance babba sai ace dole dansa zaiyi mulki fisabilillahi ayi mutane babu adalci,
Nisawa hajiya suwaiba tayi tace idanma mahaifinsa shine babba ko qarami wannan bai dameniba yanzu baya raye,
Sannan kuma ni yarana kawai nasani bansan kowaba,
Duk wanda yakeda niyyar shiga tsakanin yarana da mulki zan iyayin komai,
Advertisement
Ban hada mulki da komaiba,
Jijjiga kai yaya hadiza tayi tace wannan haka yake, miqewa tayi tana fadin wanna zancen haka yake yanzu barina tafi can wajansa musan abunyi zama nai ganmuba,
Karkad'a qafa hajiya sabuwa tayi batareda ta furta kalma dayaba tayi mata nuni da drawer,
Tagane mai take mufi hakan yasa cikin sauri ta qarasa gaban drawer tabude kudine aciki ta sanya hannu ta debi iya buqatarta sannan ta maida ta rufe tayi mata sallama."
————-
Umma ce zaune ta kafe yarima haliifa da ido wani irin zafi da tausayinsa takeji cikin ranta,
Rayuwar haliifa na baya take tunawa
Mutum mai cikeda kwajini cikekken mutum mai cika ido, mutum ne wanda kallonsa kawai ya wadatar da zuciya, yana da dabi'u masu matuqar daukan hankali,
Hawayenda ya zubo mata a idonta ta share spoon tadauka ta ebi abinci takai bakinsa kallonta ya tsaya yanayi kamar mai nazarin wani abun,
Haaaa tayi masa alamu ya bude bakinsa bai budeba har sanda takai cokalin tana qoqarin sanya masa abaki ahankali ya bude bakin ta sanya masa abinci sannan taqara share wasu hawayen kawai,
Ummi dake gefe ta kallo umma tana fadin yahya kullum cikin kuka fisabilillahi yanzu yaya kinyiwa kanki adalci kenan? Yakamata ace kin dauki wannan lamari matsayin jarabawa,
Kuma yanzu Alhamdulullahi jikin haliifaa kullun cigaba ake gani, koda yanayinsa ya canja anata kallon cigaba a lamarin uhum kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai shi yasan yanda zaiyi damu kuma shi yasan mai ya tsara gamedamu, tsarin ubangiji shine mai kyau,
Cikin nutsuwa umma ta murmusa tana fadin hakane sadiya Allan yaqara masa lafiya,
Amin ummi ta amsa."
Kwana biyu Al'amuran yarima alhamdulullahi ana ganin sauqi sosai,
Magana ce kawai bayayi amma komai kayi yana binka da idanuwa alamun yana fahimtar duk wani abunda yake faruwa,
Mai martaba ba qaramin dagewa yayiba wajan ganin ya tsaya tsayin daka yana naimawa haliifaa lafiya."
———
Hajiya suwaiba da yaya hadiza wannan karon bada wasa suka shiga lamarinba domin hajiya suwaiba ta shaida cewa ko dukiyarta zata qare aduniya tayi yawo tsirara yariima halifaa bazaiyi mulki ba."
Mai martaba kwana biyu jiki yadan ta6u jiki da jini kasancewar yadan zufa jikin zuba sai ahankali haka kawaima akanyi fama da jiki bare kuma da ciwo,
Awannan lokacin yaya hadiza ta kar6o duk wani qullinda zasuyi amfani dashi,
Ad'aki tasamu hajiya suwaiba ta shaida mata yanda sukayi da mutumin,
Yatsine fuska hajiya suwaiba tayi tace nifa nagaji da wannan zancen wallhy abu yaqici yaqi tura,
Yaya hadiza ta katseta da fadin A'a A'a hajiya aikuwa dai ba'ace yaqici yaqi turaba tunda ko yanzu muna kallon cigaba a lamarin, Yoh dabadan wannan mutumi ba da yanzu aikin gama yagama, na tabbata da yanzu yana kan gadon mulki ba kan gadon haukaba,
Siririn tsaki hajiya suwaiba taja sannan tace ni wannan ba damuwata bace ai kece kika kawo zancen hauka tun farko ban boye mikiba kasheeshi naso ayi,
Advertisement
Uhmm uhmm fa hajiya sawaiba, kinji abunda mutuminnan yafadi da kunneki, kasheshi ba maslaha bane bazai kasu mana yanzuba,
Yatsina fuska tayi tace ni kasheshi bazai zamamin matsalaba aikin sani abayama na aikata bai zama matsalaba sai yanzu akan wannan qaramin yaron,
Kin sani inada hanyoyi da yawa,
Saurin dakatar da ita yaya hadiza tayi tace uhm-uhm idan dai zance yawuce adaina tayar dashi na baya an rigada an aikata,
Yanxu wannan ne agabanmu,
Dan siririn tsaki hajiya suwaiba taja alamun tagaji da duk wad'annan abu buwan burinta yanzu bai wuce ayi abunda za'ayi yawuce ba kawai,
Miqa mata maganin tayi sannan tace ga wannan da man shanu za'a hadashi a tabbatar ya ta6a jikin haliifaa aikuwa komai zai rinca6e yadawo farko, yatsina fuska hajiya suwaiba tayi ta nuna maya gefe tace ta ajiye awajan,
Ajiyewa tayi tana qara nuna mata amfanin maganin,
Da zata fita hajiya suwaiba tace takira mata jakadiya bayan ta fita ta snaarwa jakadiya da kiran uwargijiyartata sannan ta wuce,
Koda jaka diya tazo hajiya suwaiba ta shaida mata cewa takawo mata man shanu cikin qanqanin lokaci tasamo,
Waya hajiya suwaiba tadauka ta tayi kira ta kara akunnenta bayan an dauka tafara fadin salim kazo yanzu ina nemanka amsawa akayi cikin wayar sannan ta katse,
Mintuna qalilan ya iso koda yazo ta shaida masa yanda sukayida yayarta bai amintaba 6atarai yayi yana fadin Ammaah nifa wannan abun duk 6ata lokaci rana daya zanyi aikina nagama da zarar kin bani dama,
Banason ganinsa akwance yana ciwo nafison ganinsa kwance cikin makara,
Dafashi Ammaah tayi tace kada kadamu salim ina gab da baka wannan dama amman yanzu muyi wannan zuwa wani lokaci tukunna,
Miqa masa maganin tayi sannan tace ka shafa a hannunka duk yanda za'ayi kata6a haliifa da hannunka, bude ido yayi yace nikuma,
Amma dai ammah kinsan yanda na tsani ganinsu koh, abawa wata jakadiya mana mai saya saini?
Jijijjiga kai ammah tayi tace nasan da hakan salim ba'a ta6a barin wani yashiga wajansa sai yan uwansa baza'a ta6a barin jakadiya tashigaba, kaikuma babu yanda suka iya dakai basu isa hanakaba,
Cikin baqin ciki salim yakar6a ya shafa a hannunsa ya fice."
—————
Umma tana zaune taji sallamarsa yashigo dubansa tayi cikin mamaki daya gaza 6oyuwa domin rabonta da sanyashi a idanuwanta tun kafin su tafi jinyar yarima,
Hasalima dama bawani haduwa sukeba saboda kowa yana harkar gabansa,
Koda yarima yadawo kuwa basu shigo dubashiba,
Gaida umma yayi yana tambayarta jikin yarima ta amsa babu yabo babu fallasa,
Yana tsaye tayi masa umarni da ya zaune kya6e fuska yayi yana fadin no basaina zaunaba nazo duba jikinnasane kawai nawuce dayake lokacin da kuka dawo bana qasar, gyada kai kawai umma tayi batareda tace komaiba,
Mintuna suka dauka ahaka sannan yadubi umma yace yana inane naga jikinsa zan wuce,
Harga Allah gar cikin ran umma bataso suhadu da yarima ba amma babu yanda zatayi saboda yanzu qaramar magana zata dawo babba, yanzu sai maganganu sutashi,
Miqewa tayi batareda tace komaiba tafara tafiya, tsayawa yayi yana kallonta wani baqin ciki yana dukansa cikin zuciyarsa, har cikin ransa yakejin haushin umma itada danta, yanzu hakama da badan yanason ida nufiba babu abunda zai kawoshi wajanta,
Yanda tatafi batareda ta tanka masaba ya 6ata masa rai, ya gane nufinta yabiyota abaya shine bazata iya fada masaba tatashi tawuce abunta,
Tsayawa unma tayi ta juya baya tana dubansa,
Basarwa yayi kamar baisan tajuyoba,
Ka qaraso umma tafada atakaice,
Yaso yayi kamar baijitaba amma kuma saiya daure yafara takawa izuwa wajanta,
D'akin yarima suka nufa kai tsaye, bacci yarima yakeyi hakan yasa taja ta tsaya, shima ganin haka yasa yaja ya tsaya,
Kallonsa yakeyi cikin zuciyarsa yana jin d'aci wani irin tsana yake yiwa yarima, shine kadai abunda ya tsaya masa agaba arayuwa, idanba dalilinsaba da duk wani matsalarsa ta kau,
Kawarda kai gefe yayi yakasa furta kalman sauqi,
Hannunsa yakai ya ta6a qafar yarina yana fadin jikin dasauqi daga haka yafice,
Sauke numfashi umma tayi kwata-kwata batason abunda zai sanya su rabi yarima,
Bawai dan tana zarginsu akan ciwonsaba sai dan yanda tun farko suke nuna tsanar dannata qiri-qiri bbu ko 6oyewa,
Sanda ta nemi abu ta lullu6eshi sannan taja qofa tafice adakin,
Ko kyallinsa bata gani a palour ba,
Zama tayi taci gabada abunda takeyi."
————-
Cikin 6acin rai salim yashiga dakin mahaifiyarsa wacce ke jiran dawowarasa, yana shiga ta dubeshi dason jin qarin bayani,
Zama yayi gefe sai wani huci yakeyi, hajiya suwaiba tayi saurin qarasawa sukadashi tana fadin ka aikata kasamu ka ta6ashi?
Tsaki yaja sannan yadubi mahaifiyarsa yace"
Ammah natsani wannan mata da danta aduk lokacin da nahau mulki zasubar cikin masarautarnan bazan ta6a juran ganinta tana nunamin isaba,
Dafashi Ammah tayi tana fadin kwantarda hankalinka wannan shine zahiri barin cikin masarautannan yazama kamar dole,
Yanzu fadamin yaya ka saka?
Jijjiga kai yayi alamun eh" murmushi tayi tace Ina alfahari dakai nasan bazaka ta6a bani kunyaba,
Yanzu zuwa gobe zamu jira muji sakamakon aikin,
Zuwa gobe idan banji komaiba nasan abunyi yafada sannan yamiqe yafice."
——————————————————————————-
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Toh Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial7 Chapters
The Tests in Life
Degen Vasir is being tested. He just doesn't know it. After death, he was given another chance at life. In his new life, he has the power to make a difference. The problem is living long enough to change the world. In a world with gods and monsters, death is always a looming threat. Can Degen survive without losing sight of who he is, or will he be forced to cover his hands in blood? Will he stand out or become like all the others who were given the same chance? Disclaimer: This is mainly just a test of commitment, to see how long I can keep this going. I'm not a particularly good writer and I'd appreciate criticism. This is set in the DC Universe
8 122 - In Serial7 Chapters
The Crippled Seed
Even a small child in Adrias knows that everyone is born with some magic. It is common knowledge that magic blooms at around the age of 13, and even though the gift of magic varies from person to person, everyone possesses it. When Nina is 14 years old, her magic tests report that she has no magic inside her. To hide that fact, she has to quit school against her wishes and live a sheltered life. That lifestyle, however, lasts for a mere two years as bandits strike her village and she has to move out, forced to survive and be something—anything—in this world full of magic...without possessing a single speck of it.
8 165 - In Serial8 Chapters
I Became The Dungeon Master
Eve was just an average salary woman. But one day as she was going home from her trash job. She was hit by a truck.Waking up confused she found herself in a cave. A dungeon. Walking she felt as if she was getting pulled toward something being led there. When she found were she was being pulled to. It was the core of the dungeon placing her hand on it a voice spoke. [System Installing, Registering New Dungeon Master] This was the start of her new life as the owner of a great dungeon. But will it be an amazing new beginning, or the start of a horrible end.
8 238 - In Serial108 Chapters
Legend of the Sword Immortal
Some cultivators use swords, but they are not swordsmen. Some mortals are swordsmen, but they are not cultivators. Mu Chen would have also been the same as every other cultivator, if not for an unfortunate incident that changed the course of his life-he was crippled and left incapable of cultivating. Fortunately, the event also led Mu Chen to rediscover his passion for the sword. And in doing so, he stepped onto a completely different path of cultivation. A hitherto unknown path. But with no one to guide him on his journey, how far will Mu Chen walk the path? And where will it lead him to? DISCLAIMER: I do not own the cover pic. If you enjoy reading what I write, consider supporting me on Patreon: https://www.patreon.com/IDreamNovelsor you can buy me a coffee:https://ko-fi.com/idreamnovels Copyright © 2020 by IDreamNovels
8 403 - In Serial27 Chapters
Black Butler/Kuroshitsuji 7 Minutes in Heaven
Another set for the 7 Minutes In Heaven game! A simple meeting in the closet in seven minutes can change everything! Even the unlikeliest of friends may change into the unexpected. Of course, who wouldn't turn down the offer of playing a game when there are pleasant-looking, marriageable bachelors surrounding you?
8 166 - In Serial12 Chapters
(Very slow updates) A.I. LIe. ance. (Book 2) DRV3 & Ibuki x reader
Note If you haven't read A.I.liance I HIGHLY recommend you do so trust me it will be worth your timehttps://www.wattpad.com/story/226268110-a-i-liance-danganronpa-2-au-chiaki-nanami-andYour name is Aizakku Adoman you are the ultimate entertainer/friend it's been 6 months since you've helped Class 77-B graduate from the killing school trip and you Ibuki and chiaki have been living together but you've been getting mail nonstop about joining the gofer project to help stop another killing game hopefully it will be the last
8 185

