《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 27
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 27
Bayan maganar da mai martaba yayi da amintattunsa washe gari da safe d'aya daga cikinsu yasameshi akan ya amince da a aurawa yarsa ma yarima, tara sauran dukansu mai martaba yayi ya ya tambayesu yaji shawararda suka yanke, babu 6ata lokaci sukayi muhawara atsakaninsu suka shaida masa akan wanda yafara shaidawa mai martaba ya amince yarsa yarima zai aura saboda su dukansu sun amince amma idan akayi la'akari duk cikinsu shine yafara amincewa, cikin fahimtar juna sukayi taro suka watse,
alokacin mai martaba ya shaida mawa mahaifin yarinyar cewa akan za'a kawo komai da akeda buqata cikin qanqanin lokaci yakeson auren nan da sati daya sannan ya shaida masa akan baya buqatar wani shagali duk qanqantarsa a bikin koda su sa lalle da komai bayaso a daura aure mahaifinta ya rako amarya d'akinta,
Bayan sun gama yanke shawara mai martaba ya sanya aka kira umma ya shaida mata mahaifin yarinyar galadiman garin kennan da kuma yanda sukayi dashi ya shaida mata nan da 1week yake buqatar auren umma tayiwa mai martaba godiya sosai saboda yanzu hankanlinta ya kwanta da zancen aurenda mai martaba zaiyiwa yarima saboda yanda taga jikin yarima yana samun sauki sosai,
Bayan umma tafita ta sanarwa ummi yanda sukayi sannan ta ce ahado lefe cikin qanqanin lokaci saboda kudi ta turawa ummi hado lefe kaya ma sha Allah sunyi kyau sosai akwatunane set biyu guda sha hudu masu kyawun gaske da kaya masu tsadar gaske,
Ba'akai lefenba cewar umma idan tazo gidan za'a kai mata kayanta sashinta,
Har daurin aure yarage saura 3days babu wanda yasanda zancen auren acikin masarautar
Duk yanda hajiya suwaiba takaiga son jin wani abun gameda yarima bata samuba saboda ta fannin mai martaba babu wani information dayake fita,
Sai ana gobe daurin auren kafin mai martaba ya sanar,
Wannan zance yazowa mutane ba bazata barinma hajiya suwaiba wacce taji zancen kamar sauqar aradu,
Tashin hankali tashiga sosai irin yanda taji zancen tunaninta daya kodai yarima yasamu lafiyane dahar za'ayi masa aure,
Duk yanda taso samun wasu bayanai abun ya faskara har y'ay'anta ta sanya su naima mata wani bayani ko zasu jiyo daga wata majiya amma babu,
Advertisement
Abunda hajiy suwaiba bata saniba yanzu duk wani abunda ya shafi yarima saninsa yakoma daga mai martaba sai umma atsakaninsu suke duk wani abunda ya shafeshi,
Aranar takira yaya hadiza kafin ta iso ta kirata awaya yafi sau goma dan gani takeyi kamar ba isowa zatayiba,
Tana isowa hajiya suwaiba ta shaida mata halinda ake ciki, cikin tashin hankali tace ni bansan koya samu lafiya bane har zancen takaiga yin aure, bansan wani hali ake cikiba yanzu banda wani bayani akansa,
Shirya yanzu zamu fita tare dake dan yanzu bazan iya zamaba, sam zama bai kamaniba har in dai bansan halinda ake cikiba,
Cikin qanqanin lokaci suka shirya suka tafi tareda salim yaya hadiza takaita wajen wanda tafi yarda da aikinsa, ya shaida musu cewa yarima bai samu lafiya ba kawai dai za'ayi masa aurene saboda su kauda hankalin jama'a kuma yanada tabbacin bawai zama matar zatayiba saboda haukarsa gaba takeyi ya tabbata babu mai iya zama da mahaukaci, haka dai yayita gaya musu magana sannan yabasu wasu abubuwanda zasu qarayi saboda dawwamarda yarima a halinda yake ciki,
Hajiya suwaiba ta karbi iya wanda zasuyi amfani dashi ma karan kansu sannan ta shaida masa yarima basuda wani contact dashi babu mai iya shhiga sashin ya aikata masa wani abun, maida maganinsa yayi yace kubar wannan awajena yanzu dai abada abun yanka tukunna zakuga aiki,
Kudi hajiya suwaiba tabasu wanda ita kanta batasan iya yawansu ba tayi masa sallama suka wuce,
Cikin mota salim sai kwafa yakeyi cikin zafin rai yake fadin ammah tun farko dakin bani dama da yanzu tarihim wannan yaro yaqare amma kullum sai ace ba yanzuba ba yanzuba, yanzu wa gari ya waya? Da yanzu abu bai kaiga 6aci hakaba,
Ammah batace masa komaiba saboda tasan irin zuciyarsa kuma tun a baya itake tausarsa take hanashi aikata nufinsa sai yanzu take dana sanin tsaidashi a wancan lokacin datayi, da yanzu komai yadawo labari da rayuwar haliifa adoron kasa tadawo tarihi,
Bata iya ce masa komaiba har yayi abunda zaiyi ya ja bakinsa yayi shiru,
Ita kuwa yaya hadiza shiru tayi tana jinsu kawai dan bataso hajiya suwaiba ta biyota da kanta ba saboda tana samu sosai aduk lokacinda ta aiketa,
Yanzu kuwa tasan bazata samu komai ba saboda tasan hajiya suwaiba idan bukatarta zata iya kashe ko nawane amma banda haka kawai tadauki kudi tabaka bazata ta6a hakanba,
Advertisement
Tana jinsu har su har yagama bambaminsa sannan yayi shiru ya maida hankalinsa akan tuqin har suka isa kuma babu wanda yaqara tankawa."
Washe gari da safe mutane suka shaida daurin auren yarima haliifaaa da amaryarsa nabila akan sadaki 500k naira dubu dari biyar,
Duk da bikin ba'ayi wani taro ba amma yadan tar jama'a itama umma nata wajen yan uwanta sunso suzo amma ta hanasu tace daga baya sai suzo suga matar dan bataga amfanin zuwannasu ba,
Da dare kuwa mahaifinta ya sakota a mota driver yana jansu har sashin mai martaba ya kawota,
Bayan isowarsa tun amota yakeyi mata nasiha akan ta zauna lafiya da mijinta sannan ta kula dashi tsakani da Allah tasani cewa shi aure bautane sannan shi yarima mijine a wajanta kada taganshi baida lafiya tace zata rainashi kokuma taqi yimasa biyayya ko ahakan data ganshi yana sama da ita kuma yazama dole tayi masa biyayya,
Nasiha sosai ya ringa yimata ta sunkui da kanta nasiharsa tana shiga kanta,
Yana kaita har palourn mai martaba suka gaisa da mai martaba yayi masa sallama yatafi,
Ba'a dade da kawota sashinba umma ta iso, sosai mai martaba yayi mata nasiha sannan ya umurci umma data kaita wajanda yarima yake,
Riqe hannunta umma tayi ta nufi wata qofa, tana bude qofan tashiga palour ne mai kyawun gaske da kujeru set biyu aciki daya gefe royal chairs ne daya gefen kuma turkish chairs,
Falon yayi kyau sosai sai d'akuna da suke ciki guda uku,
Tsayawa umma tayi a palour d'in ta sanya hannu ta daga gelen nabila hadeda daura mata shi akayi, sanya hannu tayi ta d'ago ha6anta ma sha Allah ta furta a fili nabila kyakkyawace sosai ga kamala da nutsuwa akan fuskarta, cikin jin kunya nabila tayi da kanta qasa,
Kamo hannunta umma tayi tace nabila nabaki amanar yarima dan Allah ki kularmin dashi kamar yanda uwa zata kulada danta, in sha Allah nabila ta furta a hankali, wata qofa ta nufa ta bude tashiga da sallama, yarima haliifaa dake zaune bakin gado ya juyo ya dubesu, ahaka idan ka kalli yarima zakace bbu wani abunda yake damunsa dan komai nashi a kimtse hattada kayanda yake jikinsama sabbi ne, ido ya zuba musu har suka qaraso wajansa zaunarda ita gefensa umma tayi tadubi yarima tace haliifaa na ga nabila nan nakawo maka, matarka ce kaji, ido kawai ya zuba mata harta gama bayaninta tayi musu sallama tafita,
Kallo nabila ta qarewa yarima tsaf mutum har mutum cikakke mai kyawun gaske amma rashin lafiya ta maidashi mutum mutumi, tausayinsa yayi mugun kamata, tadaura aniya aranta zata kula dashi har ranarda zai samu lafiya."
———
Sadam sunata shirin tafiya bai fadawa sawwma har sanda komai ya kammala ranarda kuwa daya fada mata tayi murna sosai amma sai dai taji batajin dadin rabuwarda zasuyi nadan wani lokaci batajin zata iya jure rashin ganinsa na wannan lokacin shima kansa sadam nasa wurin hakene yana daurewane kawai amma yana tunanin halinda zai shiga a dan wannan lokacin."
Ranar litinin jirginsu yatashi zuwa saudia,
Kwanansu uku acan sadam yadamu sosai sai yanzu yaga rashin azancinsa narashin saya mata waya dabaiyiba yasanda cewa idan yaji muryarta koda wani abunne zai rage masa,
Haka dai duk babu dadi yawan ibada da sukeyine ma ya sanya wasu lokutan baya samun lokacin tunanin
Sau dayawa addu'oinsa bai wuce akanshi da sawwma ba, har mummy sanda yaringa sanyawa cikin addu'arsa saboda itace yake kallon zata bashi matsala a aurensa da sawwama,
Itama sawwama awajanta tanajin jiki sosai na rashin sadam a d'an wad'annan kwanakin, kullum cikin irgen kwanakin dawowaraa takeyi kamar yanda ya shaida mata cewa 2weeks kawai zasuyi yanzu a lissafinta 9days kenan da tafiyarsu."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Toh Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial61 Chapters
Lost In Translation
If you're one to travel the roads, you may have heard of me. You may have heard my Names in the stories, the songs, and the whispers of the road. Perhaps you've even seen me during my travels, speaking to a bird of blue light, or on a city street, performing small acts for coin and repute. Or perhaps you may know me as the Skystrider, who walked with the wind. Or the Voiceless, a man of song without speech. You may know me as the Tutor, who taught the Lion of Summer how to fight, or the Traveler, who has walked all the roads of the earth. I am all of these things. And people have branded me a myth. But people don't understand what a myth is. They haven't heard the songs lost to our tongues, nor have they seen the things I've seen. They haven't gone to the places I've gone. My feet have walked the plains, the seas, and the clouds. I have spoken languages unspoken; tongues lost to time. I have sung to the earth, held the moon in my arms, and walked the roads that your heroes hesitate to even mention. I have outwitted Demons. I have danced with the Fae. My songs have been heard by lords of wind and ash, and my steps have echoed in the bellies of gargantuan beasts the likes of which you have never seen. These are what real myths are. And me? I'm no legend. I'm just the bard stupid enough to poke the real ones with a stick. Discord link here. [Disclaimer: Book 1 of this story will likely be published in KU by around the start of 2022, so please keep that in mind. Book 2 and onwards will continue here until they are published as well.]
8 310 - In Serial15 Chapters
I. Galactic War
Follow General Rostov as he fights for the Galactic Federation against the Galactic Empire while carving a place out in this vast galaxy for him and continuously expands his power base to become a force to be reckoned with. Inspired by Star Wars.
8 199 - In Serial16 Chapters
Guardians by Design - Land
When the land and Designer alike choose Dahj to be the first recipient of groundbreaking physical augmentations, the fallen leader reluctantly learns that they have been granted to him under life-threatening stipulations. Accompanied by two other ‘Guardians’ and a banded assassin, Dahj must defy the monotonous cycle of his templated life to travel to the land of grandeur now known as Yellowstone National Park. Here, he will ‘visit unique geographical features throughout the land that strongly represent the corresponding element’ to re-empower the depleted appendage of a unique deity, and bring an end to the pressing threat of adapting predators. Join the Guardians on their elemental path as they face powerful adversaries including jets of boiling water, deceit, vicious carnivores, and most importantly – doubt.
8 207 - In Serial11 Chapters
len's first weird love (lenxmiku)
this story is a lenxmiku fanfiction .... so i don't own VOCALOID i'm just a fan Of lenxmiku hope u like it ^•^/ Love chu ♥♥♥
8 165 - In Serial100 Chapters
Riddles WITH ANSWERS ❣️
Over 98K views and 1K votes, y'all! TYSM!! >;3*DISCLAIMER*These aren't mine. I found most of them online. :)The pic belongs to yandere-woman on DeviantArt.Enjoy, peeps!!'Shortie :P'
8 168 - In Serial33 Chapters
The Gotham Ghost King
Then, the Fates flash in. Go become superheros, they say. Go to Gotham City, they say. Go to the city with the worst crime rate in the county and cozy up with the local superheroes they say. Oh yeah, if it makes you happier, you can take your boyfriend. Like that's going to make this trip better.
8 83

