《ƘADDARAR RAYUWA》K page 29
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 29
Auren nabila da yarima yacika shekara daya yayinda duk wani abunda take yimasa na kyautatawa bata canjaba, duk wani abunda tasaba tanayi bata dainaba har yabi jikinta, amma fa rigar bata sauya zaniba domin kuwa har yanzu yarima baiyi sabo da itaba kuma ko sau d'aya bai ta6a kar6an abincin hannunta ba ko sau d'aya idan kuma tana wajen toshi tashi zaiyi bazai zauna awajan ba saima dai idanda umma ko ruma awajan, amma duk da haka tana qoqari a al'amuransa sosai bata nuna gazawa ko gajiya biyayya sosai take yiwa umma fiyeda tunani,
Hankalin umma yanzu yagama kwanciya da auren yarima duk da wani sa'in ma acan take wuni takan zauna tabashi abinci tazauna dashi na wani lokaci haka,
Ruma kuma gabaki d'aya takoma shashin da zama tana ebewa nabila kewa sosai dake itama ruma tana jin ddin Zama da nabila domin tana da kyawawan halayya,"
Shi kansa mai martaba yana son nabila sosai tashiga ransa saboda yanda take kulawa da al'amuran jikannasa."
———-
Tunda yarima yayi aure hajiya suwaiba tarasa duk wani kwanciyar hankalinta, ko matarsa bata ta6a gani ba,
Shiru labarinsa kamar baya cikin masarautar koda tarinsa baya fitowa,
Wannan lamarin ya sanya tadawo kamar wata ta6abibbiya duk ta yanda zataji labarinsa nema kawai takeyi.
————
Mai martaba zaune a dako da littafi na addini a hannunsa yana dan research dinsa kamar yanda ya saba kullum yana kan bincike akam ilimin addini,
Babban malamine wanda duniya kanta take qaruwa da iliminsa wanda duniya take alfahari da samun malami mai ilimin addini irinsa,
Ya wallafa littafai dayawa na addini islamiyayo a qasashe daban daban nasa wanda ya bude, duk wani burinsa bai wuce akan addini ba, duk wani tunaninsa yana qarewane akan addinin musulunci. Dumbin sanin dayake dashi bai hanashi qara neman ilimin ba komai qanqatarsa tsufansa girmansa da shekarunsa da mulkinsa bai sany ya daina neman ilimi ba, duk wani taronda za'ayi na addini a duniya dole sai ya halasci wajan girmamashi akeyi sosai,
Kaff cikin zuri'arsa yarima haliifa ne ya gajeshi, domin ilmi irinna yarima haaliifaa har ya so tadda na kakansa. Ilimjnsa har yakan bawa mar mataba mamaki wani lokacin, hatta da deegree dinsa akan addini yayita,
Da badan addini irin na mai martaba dakuma yarima ba da andade da kawarda su adoron qasa da yarima haliifa ba baikai iwar haka ba."
Advertisement
Daya daga cikin matan mai martaba itace mahaifiyar mijin hajiya suwaiba tana zaune gefensa tana jiransa ya idda bincikensa,
Sai bayan yagama sannan ya juya yana dubanta yana jiran jin mai yakawota, sannu da gida ranka shi dade kai kawai ya gyada mata,
Nisawa tayi sannan tace yallabai kwana biyu banjin labarin jikin yarima? Allah yasa dai yana kan samun sauqi,
An godewa Allah mai martaba yafada daga ban sai sake cewa komai ba, duk yanda taso jin wani zance gameda yarima haalifa bata samu hakanba."
Bayan ta fita daga sashin mai martaba kai tsaye sashin hajiya suwaiba tawuce, a palour ta sameta tareda mutane dayawa a kofa ta tsaida kuyanginda da take tafe dasu,
Hajiya suwaiba tayi mamakin ganinta dan rabonda ta shiga sashinta zai iya kaiwa 7yrs sai dai ita taje ta gaidata sa'i-sa-i,
Duban mutanen wajan tayi tace ku bamu waje zamuyi magana, cikin girmamawa dukansu suka fice ta dubi daya daga cikin jakadanda suke shirin fita tace ki tabbata babu wanda ya shigo sannan kada kowa yazo kusada qofa maganace mai muhimamnci, cikin girmamawa tace angama ranki shi dade yanda kikace haka za'ayi,
Suna fita hajiya suwaiba ta sauka qasa tana gaida ita gaisuwa irinta saurauta,
Gyada mata kai tayi alamun taji ta amsa, sun dade ahaka sannan ta dubi hajiya suwaiba tace Suwaiba!
D'agowa hajiya suwaiba tayi ta dubeta har cikin ranta batajin dadin yanda uwar mijin nata ke kiran sunanta babu ko wani sakayawa aciki ga yanda take gwada mata mulki da iko duk ranarda danta yahau mulki ita kana kakartasu ba barinta zatayiba,
Magana nakeso muyi suwaiba hajiya suwaiba dataji zafin zancenta tadaure tace hajiya aida kin aiko sai nazo basai kinzo da kanki saboda lafiyar qafarki,
Murmusawa hajiya babba tayi sannan tace babu damuwa dama yakamata ina dan taka qafar tawa,
Suwaiba duk abunda kike aikatawa a masarautar nan nasani nasan cewa ciwon yarima da hannunki aciki,
Da sauri hajiya suwaiba ta d'ago tana dubanta da mamaki tsoro duk ya kamata kasa magana tayi ta yida kanta qasa gabanta yana dukan uku-uku tana tunanin wannan magana taje gaban mai martaba aita kade ba itaba har y'ay'anta abun zai shafa gashi burinta bai kaiga cikiba,
Muryar hajiya babbace ta katse mata tunaninta da fad'in kada ki zurfafa tunani duk wani abunda kikeyi nasani suwaiba babu abund bn saniba komai kike aikatawa akan idonane,
Advertisement
Cikin tashin hankali wanda tunda hajiya suwaiba take bata ta6a shiga irinsaba sai yau ta dago tana duban hajiya babba tasan hajiya babba sarai bata lamunta a cutarda wani ko yaya kuwa, balle ma idan tasan abunda ta aikata shekarun baya hukuncin mai tsanani ne,
Ga mamakinta sai taji hajiya babba tana fadin da nadauka zakiyi abun arzikine ya sanya ban saka hannun ba nazauna na zuba miki ido jna jira naga abunda zaki iya ashe ba komai zaki iyaba, tunda yanzu labarin yarima ma baya isoki bakisan wani hali yake cikiba,
Da mamaki hajiya suwaiba ke kallon hajiya babba saboda zancenta ya daure mata kai sosai, kiyi azamar rabashi da matarda yake tare da ita idan kinason ganin yayanki kan kujerar sarautar nan, kiyi gaggawar nemo hanyar datse wannan auren banaso lamarin yakaiga saina saka hannuna ne aciki kisamu mafita tunda wuri, dasaur hajiya suwaiba ta amsa cikin jin dadin hajiya babba na gefenta, tashi hajiya babba tayi takoma shashinta tabar hajiya suwaiba da dumbin mamaki, cikin ranta tana fadin masarautarnan sai dai kaga kowa kabarshi kawai saboda hajiya babba babu wanda yakaita kiran Allah da nuna son jama'a da nuna babu ruwanta abaki,
Tunani kawai hajiya suwaiba keyi dama ba ita kadaice keson kallon bayan yarima b dama sunada yawa haka? To ko su nawane haka wannan tambayar ne batada amsarta domin batasan cikin kowaba."
Kuma ta tabbata ba duk wani abunda takeyi hajiya babba tasaniba ta tabbata da tasan wasu abubuwan abun bazai kai iwar haka hajiya babba bata dauki mataki da kantaba."
———————-
Alhamduillah Allahummar rahamni bil Qur'an waj'alhuli imaman wa nuran wa hudan wa rahma, Allahumma zakkirni minhu ma nasitu wa allimni minh na jahiltu aruzuqna tilawatahu ana al laili wa adrafan nahar waj al huli hujjatan ya rabbal alamin sanda yakai qarshen addu'an sannan itama sawwama ta karanta rufe qur'annin tayi shima ya rufe tanajin wani sanyi cikin ranta wani farin ciki takeji wanda tunda take bata ta6a tsintar kanta acikinsa ba,
Miqa mata qur'anin hannunsa yayi yana fadin alhamdulillah komai yayi farko zaiyi qarshe yau sawwamaty ta had'a qur'ani, qur'anan tarteela,
Da fara'a a yalwace akan fuskarta tace nagode, nagode yaya sadam Allah ya biyaka da mafificin alkhairinsa kasamu rayuwata acikin duhu ka maidata cikin haske ka haskakamin rayuwa ka gyaramin addinina ban ta6a tsintar kaina acikin farin cikina irin nayau,
Murmushi sadam yayi sannan yace amin kema harda ke ai saboda kinada dagewa wajjan karatu wasu koyaya za'aso suyi karatun bazasuyiba amma kiduba cikin shekara daya kika hada tarteel na qur'ani Allah yasa mai amfamine,
Amin yaya sadam nagode kaima harda jajircewarka akai Allah yabiyaka, ahankali ya amsa da amin,
Sai abani tukuici,
Tukuicin me kakeso yaya sadam ka cancanci komai, mutuminda yabaka kyautar ilimi ya cancanci duk wani tukuici da za'a bashi,
Kice kina sona shine tukuicina, danna lura dake idanba roqa nayiba baki ta6a fad'amin, rufe fuskarta tayi tace ina sonka yaya sadam matukar so,
Huuuuuuuuuuuuu ya furzarda iska yar dariya yayi sannan yace sawwamaty ansan matuqar so,
Turo bakinta tayi tana fadin da idan ban san matuqar soba waye zai sani, bayan kaima matuqar so din kake nunamin,
Aduk lokacinda taturo bakinta wani kyau takeyi masa yakan samu kansa da kasa daina kallon ta,
Nisawa yayi yace na yadda toh ina nuna miki matuqar so ni yaushe za'a fara nunamin nawa matuqar so d'in?
Kauda maganar sawwama tayi tace yaya sadam yaushe result dinku zai fito?
Murmushi yayi aduk lokacinda zance yafara nauyi ya lurada sawwama kawarda zancen takeyi, bazata yarda aci gababa,
Ummmmm ban saniba ba amma soon in sha Allahu. Allah yayarda yasa muga alkahiri cewar sawwama,
Amin dai ya amsa, yadan dade awajanta kafin yatafi,
Bayan takoma gida baba yace mamana yakamata yanzu sadam yaturo manya su shiga zancen tunda yanzu ai yarigada ya gama karatun idan yazo gobe ki sanar dashi,
Toh sawwama ta amsa a kunyace."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Toh Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial31 Chapters
Rise of the Empress of Stars
After sacrificing herself for the Stellar Dimension, Empress Aeon was reborn in a Highlevel Primordial World as Zera Lynx.This is the beginning of the rise of Zera Lynx and her friends from an orphanage in Tibet to .....From convincing her parents to let her establishing her own mercenary team consisting of little guys around three years old to the journey of establishing her own Empire and war of dimensions is a road full of challenges.________________________________________________________________English is not my first language, so please tell me if you found any grammatical errors or incorrect words. Very much appreciated!The picture is taken from Google and not mine.
8 113 - In Serial153 Chapters
Theory of Rifts (LitRPG)
You can join my Discord here. Keynes Kid is gifted with a photographic memory and being several months away from receiving Level 1, and a Talent, he finds himself in the center of attention of people who want to shape his Talent. If they can get him an intelligence related Talent, they will hit a jackpot. The Talent Unlocking ceremony finally comes and Keynes Kid receives… Error… Anomaly (What?) His new talent is… useless. Why then does the World Government want Keynes so badly they will silence anyone who knows about his Talent? At the same time... Somewhere in the Universe, ancient beings stir from their slumber, awoken by the system alert and the wall of glaring red warnings. Their greatest fear just manifested and they are hell-bent on erasing it from existence. -------- It is a slow-development story, so you won't find the MC with super powers at the beginning. -------- It is a coming of age story and focuses on a Talent system (in the beginning) with several additions that bring to the table upgrading of a planet’s tier and such (a bit later). There will be quite an amount of rebuilding society as new, unknown resources enter the economy, and a lot of travelling, delving and naturally, unlocking the secrets of the Universe. As for the setting, the story starts in XXI century, which technology-wise isn't much different from what we have now, but it is enhanced by magic associated with Talents. This allowed the humankind to colonize the solar system, but the technology that allows for interstellar travel doesn't exist (yet). Because it’s my first attempt at LitRPG, please be forgiving but constructive. I hope you will enjoy the story! --- Cover by Daniel Gembus https://www.artstation.com/daniel_gembus instagram.com/danielgembus
8 156 - In Serial229 Chapters
A Hero Among Us
Adam Hayze, an orphan whose parents were famously known for their incredible prowess as healing Super Heroes. Hayze dreamed of following in their footsteps, but his superpower paled in comparison to theirs, and he had to face the reality that he could never become a hero. Hayze didn’t give up, though, and he trained his mind and body day in and day out to triumph over his shortcomings. However, his efforts weren’t enough to get into the school he always dreamed of attending, U.A., the best hero education institute in the country. After failing the preliminary entrance exam for the 9th time, a board member arrives at his home one day to inform him he only has one more chance to pass. The news forces Hayze to face his greatest fear: losing his dream. All hope seems lost when a doctor makes him a unique offer.
8 242 - In Serial55 Chapters
I Hate You Master
A man, relentlessly pressed into training since a young age to be an elite mage, is forced to face the cruel reality that he just does not have what it takes to achieve that goal. After being thrown out by his father, the arch mage, he turns to the one option left. He becomes a demi-human tamer and sets out to gather resources to continue his studies.Also, he's a cold and calculating jerk who sees those Demi-Humans as simple trained animals, as is the custom in that part of the world. Enjoy!Mature Content Warning: This story features the purchase and sale of cute girls, and the use of said girls as gladiators for spectators. Concepts such as sexual enslavement and general disinterest in civil rights abound.
8 376 - In Serial48 Chapters
Harvest Factory ~ a Farmer Life
A story about a boy with talents in both farming and cooking. Follow him in his journey of cultivating rare and legendary fauna and flora while cultivating his strength in the side. " little brother, what's that thing you're eating? "" Jade Crocodile sausage. "" isn't that a rare beast only found in Azure Swamp?! how did you get it?! "" I raised it. "" what's that you're drinking? "" Golden Snow Pear juice. "" ..... did you raise it too? "" un. "
8 178 - In Serial13 Chapters
The Will Of The Cat
A young boy must work through the hardships of training and being an average kid whilst trying to learn about a raging war with spirits. One problem: his teacher's a talking cat that is near omniscient and wants nothing to do with him. The young boy has to prevent the war, but how will he do it without any knowledge of what to do?
8 179

