《ƘADDARAR RAYUWA》ƘPage 31
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 31
Hajiya suwaiba ce zaune maganganun hajiya babba ne suke dawo mata, me hajiya babba take nufi da cewa tayi gaggawar raba yarima da matar sa, hakan yana nufin matarsa tana d'aya daga cikin waɗanta suke bashi kariya kennan? Har in dai kuwa hakane to tabbas zata samo hanyarda zata rabashi da matarsa, to amma ta yaya kenan? Wannan ne bata saniba domin ko matar tasa bata ta6a sanyawa a ido ba balle wani magana ya shiga tsakaninsu ba, baare har ta samu hanyarda zata isa gareta, koda ta isa gareta batada tabbacin zata amince da zancenta, tunda hhat tashigo cikin gidan sarauta ta tabbata itama da nata shirin ta shigo, toh amma
har in dai raba yarima da matarsa yanada nasaba da cin nasararta to dole kuwa ta nemo hanyarda zata rabashi da ita domin duk wata hanyarda zai kawo mata cikas wajan cika burinta zata tosheta zatasan yanda zatayi tayi maganin wannan hanya,
Bazata lamunci duk wani abunda zai kawo nakasu wa cikar burinta ba,
Wayarta dake gefenta ta jawo tayi dialing number ɗin yaya hadiza, cikin hanzari yaya hadiza taɗaga kiran, hajiya suwaiba bata bari sun gaisa ba tace yaya inason ganinki yanzu, ba'a ɗauko lokaci ba yaya hadiza ta'iso hajiya suwaiba tace" yaya ashe cikin masarautarnan bamu kaɗai muke farautar rayuwar yarima ba, man ta labarta mata yanda sukayi da hajiya babba, yaya hadiza tace ahaf dama ai nagaya miki cikin wannan masarauta kibar kowa da kika ganshi dan babu wanda zai buɗe miki cikinsa ki gani amma da sai kin sha mamaki, duk wanda kikaga yana wani nuƙu-nuƙu to munafunci ne,
Amma zancen hajiya babba nayi mamaki kuma banyi mamaki ba, sai dai fa hajiya kada mu sake da ita domin itama ba abun yarda bane, kada mu sake mu buɗe mata sirrinmu Saboda idan tasan abunda yafaru shekarun baya itace zata fara tona mana asiri sannna ta sanya aci mana zarafi, A wulakantamu a dauki mummunan mataki akanmu,
Advertisement
Dogon numfashi hajiya suwaiba taja tace wannann haka yake bazamu ta6a yin wannan kuskurenba bazamu ta6a barinta tasan wannan sirrin ba,
Yanzu mukoma zancen wannan matar yaronan haliifaa nifa inaga abunda take faɗi gaskiyane yakamata mu rabashi da ita wannan shine cikon burinmu sannan ta hanyarda zamu sameta har mu rabata dashine shine matsalar, murmusawa yaya hadiza tayi tace wannan aiba matsala bace bakuma abun damuwa bane hajiya, ki bani nan da 1week zaki sha mamaki,
Jijjiga kai hajiya sawaiba tayi tace indai 1week ne nabaki yaya hadiza kada ki bani kunya nidai burina yacika ya fiyemin komai gidan duniyar nan, sunkuida murya yaya hadiza tayi sannan tayi da kanta Ƙasa tace aikuwa hajiya har in dai ina rayuwa a doron ƙasa yazama kamar dole burinki sai ya ciki, zan tafi ko bangon duniya ne dan cika miki burinki, cikon burinki ai shine namu, idan burinki ya cika nima nawa yacika, duk wani abunda kikga ina yinsa a gidan duniya danke da ƴaƴanki nake yinsa, haba hajiya ai ki kwantarda hankalinki haba-haba ai indai ina raye burinki zai cika, nan tafara yiwa hajiya suwaiba daɗin baki domin samin shiga wajanta,
Aikuwa hajiya suwaiba taji daɗi tace toh yanzu ki ƙarasa cikin drawer can ki ɗebi abunda yake ciki zuwa gobe zanyi miki aika, ni dai abunda nakeso dake shine kada ki zauna tako'ina shiga zakiyi,
Yaya hadiza tace aikuwa hajiya wannan yazama dole babu zama ahaka sukayi sallama."
—————
Da sauri sadam yawuce palour ɗin Kar mummy ta ganshi yana sanɗa kamar wani ɓarawo kafin ya isa ƙofa ya tsinkayi muryar mummy tana faɗin ina zakaje mummy dake ƙofar ɗaki ta jefo masa tambaya, tsayawa yayi cak sannan ya juyo ya kalli mummy cikin son waskewa yace zanje wajan najeeb ne yanzu zan dawo,
dawo kazauna zamuyi magana mummy tafaɗa haɗeda ƙarasawa kujera ta zauna, ƙarasowa yayi ya zauna sanda mummy taɗan ɗauki lokaci sannan tace sadam menene yake damunka? I smell something fishy, akwai damuwa atattare dakai maza faɗamin damuwarka,
Advertisement
Ɗan murmushin da bai kai zuci ba yayi yace babu komai mummy ni babu abunda yake damuna wani abunne yafaru?
Mummy ta tsaya tana ƙare masa kallo daga yanda yake magana zaka gane cewa baida gaskiya, mummy tace sadam kada ka maidami ƙaramar yarinya nifa mahaifiyarka ce kada kace zakayimin wayo, wayo kuma mummy? to akanme zanyi miki wayo? Nifa ɗankine, ki yarda dani da gaske nakeyi babu komai idanda wani abun ke zan fara zuwa ina faɗawa kinsan banda wanda yawuceki kinsani mummy dafa shoulders ɗinta yayi yace to mai yasa can ɓoye miiki damuwata ma? Kefa mahaifiya tace ki kwantar da hankalinki, miƙewa yayi yace mummy dare zaiyi bari naje yanzu can dawo bazan daɗeba yana gama faɗin haka yayi wane da sauri, da kallo mummy tabishi amma sam bata yarda da abunda yake fad'aba saboda jikinta yana bata cewa yana tareda damuwa dan gabaki ɗaya kwanakinnan ya canja,
Miƙewa tayi tana faɗin koma dai menene idan yayi tsami zanji,
Wajan sawwama sadam yaje bai daɗeba yadawo saboda yaga idon mummy yana kansa zata sanya ido taga lokacin dawowarsa,
Bayan yadawo ya kirata a waya anan suka qarasa hirar tasu."
Baba yana zaune bayan isha'i yadawo suna d'an tattaunawa da mama, sallama sukaji daga zauren gidan baba yace muryar wa nakeji kamar ta yaya zakari? mama tace anya kuwa baban hafsa yaya zakari awannan lokacin? Kodai muryarce tayi kama,
Sake yin sallamar da aakayine mama tace toh nima dai yanzu kamar hakan naji ka duba mana,
miƙewa baba yayi yana amsa sallamar da wa'alaikasslam ya fita waje domin ganin mai sallamar."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial19 Chapters
RENAISSANCE. A Constantine Palaiologos Self insert story
RENAISSANCE is an alternate history science fiction novel/Wikipedia.55-year-old American book sales executive and ex silkscreen craftsman Michael Jameston wakes up in the body of Constantine Palaiologos, Despot of Morea, and soon to be the last Byzantine emperor.James initially wonders whether he is dreaming or delusional, but he quickly accepts his fate and sets out to survive. As a silkscreen printmaker, antique weapons collector, and alternate history geek, he has enough understanding of various devices used before his time but after the fifteenth century to be able to reproduce them by the means available.Let's explore together the new world that our protagonist will create!
8 73 - In Serial24 Chapters
Bloodsong
Lara's days have been filled with emptiness since she woke from a past she can't remember, five decades into the devastating aftermath of a nuclear 20th century. Lost in the desolate remnants of the world, she is plagued by shadows, nightmares, and whispers in her mind. But one day she’s taken from the small abandoned home she's known since her awakening, to one of the last remaining hearts of the country: the mountainous city-state, Circa. Along the way, she is exposed to the drastic differences in humanity's survival, and upon stumbling into mortal danger, becomes entangled in the world's last struggle for power, only to discover the crucial key to her memories. As secrets unravel, Lara struggles to find balance between her humanity and the inexplicable power growing within her - calling to the shadows. And in a world-shattering discovery, unearths her role in history's tragic turn, and her unending bond with Death as an instrument of fate.
8 187 - In Serial28 Chapters
Solace Curse: Part I
I promise you, there is light in this dark world, if only you know where to look.My tale is one of magic and wonder, of evil and justice-of power and servitude. But it is also a story of sacrifice and suffering. There are great feats of courage and and malicious acts of deception. But there is also the quiet heroism of one good deed and the unpraised comfort of one loving heart.#1 in Adventure 04/09/2019#3 in Adventure 04/12/2020#1 in Adventure 01/29/2021#2 in Fantasy 03/30/2021#2 in Action 05/15/2022
8 116 - In Serial60 Chapters
The Power of the Moon
What happens when Uchiha Madara finds out the true purpose of the Infinite Tsukuyomi? Uchiha Madara bumps into an interesting girl along the way and they may even end up sealing their fate.A Madara x Hyuga OC reading.#1 on clans, Nov 2020.
8 116 - In Serial19 Chapters
UQUBAR UWAR MIJINA
Based on true life storylabarine akan wata baiwar Allah wanda uwar miji tajefata cikin matsanancin baƙin ciki ɗa gararin rayuwa,sanadin hakan ta..just read and find out
8 104 - In Serial200 Chapters
FEMALE FACECLAIMS √√
For those of you in search of the perfect female faceclaims for your characters, this is the book for you.
8 207

