《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 35
Advertisement
*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 35
Sawwama kwana biyu tana son ganin sadam amma babu yanda ta iya haka ta haƙura batareda ta nuna masa tanason ganinsa ba saboda tasan idan shi yana son ganinta tasan tabbas zaizo,
Haka baba ya lurada yanda sadam ya ɗauke ƙafarsa a gidan amma bai sanya abun a ransa ba balle yadameshi, suna zaune baba ya kira sawwama bayan tazo baba yake tambayarta ko sadam yana zuwa kwana biyu, baya zuwa sawaama tabashi amsa,
Jijjiga kai baba yayi yace toh shikenan bamusan mai yake nufi ba amma Allah ya zaɓarda mafi alkhairi, cikin rashin fahimta sawwama ta kalli baba sai kuma ta sunkuyarda kanta, mama tace badai tunda kukayi maganarba shine bai dawoba, baba yace eh shine amma bamusan mai yake nufiba zai iya kasancewa wani abun ya tsarrmeshi mai muhummanci dan haka zamu jira na wani lokaci mu gani, shiyasa banyi gaggawar bawa yaya zakari amsa ba saboda gudun hakan, gaban sawwama sai faɗuwa yakeyi dan haka tatashi ta wuce ɗaki, tana shiga taji wani gumi yana tsattsafo mata wani zance baba sukayi da sadam kenan har ya sanyashi ya daina zuwa wajanta? gabanta yaci gabada faɗuwa ga zancensa da yayi na cewa shiyasa bai bawa yaya zakari amsaba, mai hakan take nufi kenan? Menene haɗin ya neman auranta da sadam da yaya zakari kuma?
Tambayiyine dayawa fall cikin ranta amma batada wanda zai bata amsa dan haka ta yanke shawarar idan sunyi waya da sadam zata tambayeshi."
cikin sanyin jiki sadam yace dady nagode yana faɗin haka ya tashi ya fita dady ya bishi da kallon tausayi cikin ransa yana kissima abubuwa dayawa,
A ƙofar ɗakin mummy sadam ya tsaya yace mummy dady yana kiranki, da wani kallo ta bishi ganin yanda jikinsa yayi sanyi sai tace me kuma kacewa dadynka nayi?
Baby kawai yana son magana dake ne, miƙewa tayi tana masa kallon tuhuma ta yi ɗakin dady shikuma sadam ya wuce nasa ɗakin yayinda gabansa yake tsananta faɗuwa saboda yana taraddadin yanda zata kaya tsakanin dady da mummy yasan bawani da daɗi zata kaya musu ba,
Advertisement
Mummy zaune gaban dady tayi shiru kawai tana jira taji yafara magana,
Gyaran murya dady yayi sannan yace mummyn sadam dama magana nakeso muyi dake gameda abunda sadam yanzu yazo ya sameni akai,
Kafin na faɗa miki zancen inaso ki yiwa zancen kyakkyawan fahimta ki sanyashi a ma'auni ki auna zancen a matsayinki ke kanki matsayinki ma mahaifiya, inaso idan kika tashi yanke hukunci ki cire son zuciya aciki kiyi masa adalci iya yanda zai iya dauka,
Ni ban tilasta miki ba amma inaso kisani sadam dai ɗanki ne kuma Allah zai tambayeki idan kika musgunawa rayuwarsa duk da kasancewarki matsayin mahaifiyarsa,
Cikin ƙaguwa mummy tace dadyn sadam nikam ka faɗamim mai yake faruwa,
.Dady yace toh shi dai sadam yazo ya sameni da magana man cewa shi aure yakeso,
Zaro ido mummy tayi tace aure? Koba aureba? Shi sadam ɗin yafaɗi haka? nawa yake? Shi yaushe aka haifeshi da har zai fara maganar aure? Yaushema yafara karatu tukunna da zaiyi zancen aure?
Wallhy ban yardaba ban amince sadam yayi auren ba bada yawuna ba kwata-kwata nawa sadam ɗinyake? har yaushe aka haifeshi da zaiyi magaanr aure? wani mataki yakai a karatu? Yaushe ma yafara karatun da zai bijiromin da maganar aure? Idan wannan maganar nema gaskiya ni kada ka matsani saina amince dan banjin zan iya amincewa,
Jijjiga kai dady yayi yace ni ni bance can takuraki dole sai kin amince ba ai ɗanki nefa kinada hakki akansa, nidai abunda nakeso kisani har in dai yaro zai fito ya dubi iyayensa yace ayi masa aure to zancen abun dubawa ne lallai idan anason a zauna lafiya, saboda yafaɗi hakanne dan gudun faɗawa halaka, idan kuma anƙi to yaro zai iya faɗawa wani hali alokacin ɓarna zata yaɗu, sannan kuma kafin asamu hanyarda zata ɗinke wannan ɓaraka sai anyi da gaske, kuma har in dai ya faɗa halaka bashi kaɗai keda laifi ba mu kansa mahaifansa akwai namu gudumawar, sannan Allah zai tambayemu, wallhy ko sau ɗaya banason Allah ya tambayeni akan nakasa bawa yarana tarbiyarda tadace kokuma wani gazawa akan yarana, to ke idan kika hanashi aure meye ribarki?
Advertisement
Mu ba abun muyi murna Allah yabamu yaro mai sanin ciwon kansa ba, maimakon yafaɗa halaka sai yazo yafaɗa mana gaskiya, wallhy ban taɓa sanin hankalin sadam yakai haka ba sai yanzu, yarone mai tsoron Allah da hankalin gaske, sai yanzu nagane zan iya barinsa yaje bangon duniya banda damuwa,
Sannan karatu ai koda aure ana karatu, ni ina age ɗin sadam na aureki ban riƙeki ba? ban kula dake ba? Alokacinda naci gabada karatu mun haifi sadam, haihuwarsa ta hanani karatu bare aurenki?"
Dadyn sadam bazafa ka haɗa yanzu ta da ba shekaru nawa baya, yanzu lokaci ya canja, jijjiga kai dady yayi yace hakane lokaci ya canja babu komai taji kije,
Miƙewa tayi ta fice tabar dady da ɗumbin mamaki baiyi zaton cewa abun mummy har yakai hakaba, amma wannan abun mumny akan karatu kaɗai take yinsa? Kokuma tana ɗaya daga cikin mata masu kishin araɓi ƴaƴansu saboda kar yayi aure kulawarda yake basu ta koma man matarsa ne oho?
Kai tsaye ɗakin sadam mummy tawuce atsaye ta tsaya ta bishi da wani irin kallo sannan tace ka kyauta kaji daɗi ka ɓatamin rai tana faɗin haka ta juya tayi waje sadam ya bita da kallo kawai iska ya furzar ya kwanta bai daɗe da kwantawa ba wayarshi tafara ruri, yana dubawa yaga sawwama wani irin daɗi yaji a cikin ransa, sawwama kuwa anata wajan tarasa sukuni hakan yasa akaro na farko ta ɗaga waya ta kirashi,
Picking yayi ya kara a kunnensa, cikin nutsuwa sawwama tayi sallama lumshe ido yayi ya buɗe saannan yaji wani sanyi cikin ransa,
.Bayan sun gaisa sawwama ta tambayeshi mai suka tattauna da baba bai ɓoye mata ba ya shaida mata har yanda sukayi da dadynsa ya shaida mata sai dai yaɗan ɓoye wasu abun saboda baison tashin hankalinta, baiyi mata bayani yanda hankalinta zai tashi ba,
Wayarda sukayi da sawwama ita ta kwantar masa da hankali yaji kamar bai cikin wata damuwa ma gabaki ɗaya."
Mummy ta ɗauki abun da zafi sosai dan 2days sadam yana gaidata ko amsawa batayi hakan yasa ya shiga damuwa sosai,
Ranar ya yanke shawarar ya sameta a ɗaki ya bata hakuri sannan yaji opinion ɗinta tunda shi daga dady har mummy bbu wanda yace masa ga abunda suka tattauna akai,
Da sallama ya shiga ɗakinta, a ciki-ciki mummy ta amsa sallamr ta kauda kanta gefe, ƙarasawa yayi ya zauna agabanta ya tankwashe kafafu, yace mummy ina wuni?."
* FITATTU BIYAR NA KUD'INE.*
*FEEDOHM - SILAR WAYE?*
*ZAINAB BAWA- YARIMA FAYAD.*
*ZEE YABOUR - DR MUHRIX.*
*HAJJA CE - ANNURIN ZUCIYA.*
*NANA DISO - GIMBIYA SUHAYMA.*
LITTAFI BIYAR AKAN___500,
IDAN HUDU KIKE SO___450,
IDAN KUMA UKU NE___400,
IDAN BIYU KIKE SO___350,
IDAN KUMA D'AYA KIKE SO 200.!
TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT D'IN.
3126584401 FIDDAUSI MUSA FIRST BANK TARE DA SHAIDAR BIYA A 08036953516
KO KUMA.
ACCOUNT NUMBER:- 0003075326 ZAINAB M BAWA
Jaiz bank SHAIDAR BIYA TA 08161146563.
*KO KATIN MTN TA WANNAN LAMBAR 07065283730 TARE DA SHAIDAR BIYA.*
*SANNAN MUYI ADDING D'INKI A FITATTU GROUP🌹...*
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial15 Chapters
Live Life Homunclus
The end is not always the end. Nothing is permanent, and even death itself is merely a transition. This fact holds true for a certain young man who died quite tragically on Earth. Lucky for him, a new life was just around the corner. A world filled with magic, adventure, and oh so many dangers awaited. Everything would be perfect, if it wasn't for the fact that he reincarnated into a homunclus. An artificial life-form said to possess almost zero combat capabilities. An exemplary example of pure breed cannon fodder. Surviving in a world where dragons roam the skies and monsters stalk the lands, wasn't this a bit too unreasonable?
8 195 - In Serial6 Chapters
To Snag A Vampire
Where you would expect a brother-knight to be a paragon of virtue, discipline, and modesty — Oliver Arborough is a little off the mark, what with his frivolous, flippant nature and the tendency to give in to worldly desires. Teetering on the line between the finer things in life and the order’s tolerance, he faces a challenge that might just send him over the edge; On a routine assignment to kill some local legend terrorizing a rural countryside, our strapping young knight encounters an unparalleled beauty in the form of a young woman called Lenora — who happens to be said local legend terrorizing said rural countryside. And so begins the tale of a young knight and his reluctant companion, in a journey that the order most definitely would not approve of and could very well spell a life of hardship and strife for him in the future — but hey, doesn’t that just add to the thrill of it?
8 131 - In Serial16 Chapters
Somatic Horizon - A LitRPG Odyssey
The World of Zones. An untamable realm of XP and Levels where almost anything can happen and yet amongst that chaos one group stands at the top: Outlanders. A class of immensely powerful humans who appear only a handful of times in a millennium, claiming to be from a place called "Earth". Their arrivals—for better or worse—often mark the beginning of a new era. Huay Celashen is one such Outlander except, unlike her predecessors, she has no dreams of venturing through unknown lands or conquering the world's nations. All she wants is a peaceful life but, despite her unparalleled talents, that goal seems further out of her reach with each passing day! Chapters will probably be weekly for now.
8 133 - In Serial15 Chapters
Lyrica of a Hundred Tails
Voyaging in the middle of the sea with her family, Lyrica finds herself in the middle of a thunderstorm! Fortunately for her she managed to overcome the storm unscathed. Unfortunately for her she's stranded alone in the middle of the sea! Enjoy the show as our heroine travels from city to city around the world to reunite with her family, learning economic lessons and the various cultures as she sings her way into becoming the "Best Pop Idol"!
8 161 - In Serial7 Chapters
Ehwa - Gathering Storm
Ehwa is a very large, old, and mysterious world. It is a world where danger that could end your life creeps at you at every corner outside the known borders. But it is also a world where those who are brave and lucky enough to seek fortune or rise in power can do so. Where feats of supernatural powers are normal to some and mistrusted by others. A cruel yet beautiful and mysterious world that is full of wonders and dangers. Not many know how humanity ended upon it and the truth is even more diluted by the many legends and myths of the past. Delve into the world that is Ehwa and read the many stories and legends that have happened here.
8 181 - In Serial85 Chapters
The Best Kept Secret
Can you keep a secret?Dong Hua Dijun the former ruler of the universe still adheres with his firm beliefs that his life is destined to be without love. Bai Feng Jiu will go on living her life destined without being with her beloved. Not giving up on her love for Dong Hua Dijun she embarks a journey full of discoveries that will lead up to uncover the best kept secret of all times. What will it be? Who will uncover it and what will the outcome be? The answers are waiting for you to read...
8 115

