《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 37
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 37
Sadam yana zaune yana aikin tunani kamar yanda ya saba kwana biyu baida aikinda ya wuce shi, hussaina ta buɗe ƙofa tashiga ɗakin da sallama, juyowa yayi ya kalleta fuskarsa bbu annuri, kafin yayi magana hussaina tayi saurin katseshi da faɗin dady yana kiranka, juyarda kansa gefe yayi yace ina zuwa, dasauri ta juya ta fice saboda yanda taganshi tasan yanzu sai ya hau mata masifa,
Miƙewa yayi ya fita domin amsa kiran dady bai ganshi a palour ba kamar yanda ya barshi hakan yasa ba wuce aɗakin dady kai tsaye yabar mummy a palour tanata waya wucewa sadam yayi zuwa ɗakin mahaifinsa, Mummy kuwa da yayanta commisioner take waya ta tura masa result ɗin sadam shine ya kirata yana tuna mata zancen auren sadam da abida, mummy ta shaida masa kada yaji komai, zasuyi magana soon,
Abida dake zaune kusada mahaifinta bayan yagama waya ta dubeshi tana faɗin abba mai tace maka? shafa fuskar tilom ɗiyarsa abba yayi yace tacemin bbu damuwa zamuyi magana, murmushi abida tayi tace dan Allah abba ka matsa wata Allah bazan iya auren kowaba idam ba shi ba, karkiji komai zaki aureshi abba yabata amsa."
da sallama sadam ya shiga ya zauna dady ya amsa da fara'a kwance akan fuskarsa,
Fursarda iska dady yayi yace sadam ma sha Allah naga result yayi kyau Allah ya sanya alkhairi sannan kuma ya sanya rai aka yiwa, sadam ya amsa da amin dady yaci gabada faɗin toh yau dai sadam ka cikawa mummy burinta kamar yanda ta buƙata saura ita kuma ta cika maka naka burin, da rashin fahimta sadam ya ɗago yana kallon mahafinsa yace kafin na faɗa maka abunda nake nufi inaso zanyi maka wasu yan tambayoyi gameda yarinyarda kake nema?"
Dady yace"
Wacece ita?
Waye mahaifinta?
Yaya tarbiyarta take?
Yaya kuma yanayin tarbiyar gidansu take?
Shin matace ka zaɓawa kanka kai kaɗai kokuma harda ƴaƴanka kayiwa zaɓi? menene dalilinka nason aurenta?
Nisawa sadam yayi yace dady ita ba kowa bace face ƴar masu ƙaramin ƙarfi, ƙaramin ƙarfi ina nufin basuda komai sai godiyar Allah da rufin asiri, basuda dukiya basuda arziki amma zuciyarsu cike take d aabubuwan arziki ina nufin sunada zyciya mai kyau, matsayinda suke dashi na rashi bai sanya sun faɗawa halaka suna rayuwarsu dai-dai su, mahafinta yana fita yayi buga-buga ya samawa iyalinsa abunda zai rufa musu asiri, basuda kwadayi ko kadan yanda Allah yabarsu anan suke barin kansu, mahaifinta ya bawa yarnsa tarbiya rashi bai sanya ya barsu sun sangartaba, yabasu tarbiya kamar yanda nake sanya ran zata bawa yaranda zata haifa tarbiya, sunanta hafsa tanada matuƙar hakuri, halayanta masu kyau suka sanya naji ina son aurenta, dady sam abun duniya bai damesu ba, saboda ko lokacin dana furta mata ina sonta mahaifinta sai ya shiga zancen ya gwadamin muhimmancin ta a wajansa da muhimmanci riƙe amana akan tarbiyar ɗiyarsa, dady in katse maka kawai daga ita har mahaifanta mutanen kirki ne, babanta ma bawani babba bane domin itace babba a wajansa bazai wuce 35-36yrs ba gabaki ɗaya,
Advertisement
Jijjiga kai dady yayi yace status ɗinsu hai dameni ba sadam nidai damuwata ace mutanen kirki sannan kuma sun bawa ɗiyarsu tarbiya duk sanda kake mata har in dai batada tarbiya bazan taɓa bari ka aureta ba, jin daɗi shine ka auri mace tagari wacce zata bawa ƴaƴanka tarbiya, kaga mahaifiyarku kada ka ganta haka tanada tsauri akan yaranta but deep inside mutuniyar kirki ce sosai, saboda har gobe ina alfahari da irin tarbiyarda tabaku,
Jijjiga kai sadam yayi yace hakane dady dan tarbiya kam na shaidi mummy, sannan itama wancan satinda yawuce ta sauke Ƙur'ani, jijji ga kai dady yayi yace ahh toh ma sha Allah kace hafiza ce,
Murmushi sadam yayi dady yace karatun boko fa?
Sadam yace she's 16 dady sai wannan year ɗin zata gama secoundry, dady yace amma sadam kana gani iyayenta zasu yarda suyi mata aure a 16yrs?
Eh kawai sadam yace dady yace toh shikenan tun farko abunda yasa ban amsa makaba ina bari naga yanda mahaifiyarka zata ɗauki zancen, nabata damarta a matsayinta na mahaifiyarka amma tana neman wuce gona da iri shiyasa na yanke shawarar cewa d aamincewarta da babu zanyi maka aure, tunda har kunyi yar jejeniya akan zaka cika mata burinta kayi karatu ka fito da result mai kyau sai ita kuma ta cika maka naka burin, toh a yau kacika mata nata, inaso ka dauki wannan abunda zanyi kamar shine nata alƙawarin da zata cika maka,
abu na biyu kuma danakeso ka sani shine zan sanya amin bincikr akan yarinyar da mahaifinta har in dai naji wani mummunan abu to bazaka aureta ba, dammm gaban sadam ya faɗi dady yace iya adalcin da zan iya maka shine zance ka nemi wata ka aura, sannan zan nema maka aiki kafin lokacim bikin yanzu zan kira abokina ayau ko zuwa gobe zai baka aiki a ministry ɗinsu, saboda ministry ɗinsu tafi tamu kyau shiyasa zan nemi a wajansa aamma da a tamu ministry ɗin zan baka,
amma kuma banso ace ni kai da mummynka duka muna aiki ministry ɗaya,
Zaka iya tafiya Zuwa gobe zan saka ayimun bincike idan anyi zan kiraka, kafin katafi ka sanar dani sunan gidansu da anguwarsu,
Advertisement
Godiya sadam yayiwa dady sosai sannan yayi masa saida safe ya fita,
Yana jin abu biyu a ransa ga fargaba ga daɗi, amma daya tuna baba ya taɓa faɗa masa bbu wanda yasan da faruwar hakan zai yaji daɗi,
Washe gari dady ya aiko akazo akayi masa bincike akan ita yarinyar da mahaifinta duk wani abunda aka samo akansu akazo aka faɗawa dady,
Dady ya kira sadam domin faɗa masa abund aya jiyo,
Sadam yana zaune gaban dady duk idanuwansa yayi zuru-zuru, dady yayi gyaran murya yace sadam! Da faɗuwar gaba sadam ya ɗago ya dubeshi yace na'am dady, dady yace nasa anyimin bincike toh ma sha Allah sadam kayi zaɓen mace ta gari da gida na gari, domin an shaidamim cewa mahaifinta shekararsa sha bakwai anguwarsu amma har rana mai kamar tayau ba'a ta6a jinsa da wani ba, sa'insa bata taɓa shiga tsakaninsa da wani ba, sannan kuma maganar tarbiyar yaransa an shaidesu nan ma,
Yanzu abunda zance Allah ya sanya mana alkhairi akan abunda muke shirin yi, gobe in sha Allah zamuje dan nema maka auranta,
Washe baki sadam yayi yafara jerowa mahaifinsa addu'a dady yana amsawa da amin."
Suna zazzaune a palour mummy itama tana zaune ranta fari ƙal yanzu hakama result ɗin sadam ne a hannunta, dady ma yana zaune a gefe,
Mummy ta dubi sadam tace sadam na yarda zan barka kayi aure, da mamaki sadam ya dubeta ganin yanda tayi magana bbu ko alamun ɓacin rai a tattare da ita, mummy taci gabada faɗin idan kayi aure sai kaci gaba da karatunka, dama burina ba anan zakaci gabada karatun ba, waje zan fiddaka idan zaku tafi da matar can sai ku tafi saboda itama matarda zaka aura ɗin acan zataci gaba da karatunta, amma da sharaɗi,
Kallonta dady yayi yana jira yaji sharaɗinda zata faɗa."
* FITATTU BIYAR NA KUD'INE.*
*FEEDOHM - SILAR WAYE?*
*ZAINAB BAWA- YARIMA FAYAD.*
*ZEE YABOUR - DR MUHRIX.*
*HAJJA CE - ANNURIN ZUCIYA.*
*NANA DISO - GIMBIYA SUHAYMA.*
LITTAFI BIYAR AKAN___500,
IDAN HUDU KIKE SO___450,
IDAN KUMA UKU NE___400,
IDAN BIYU KIKE SO___350,
IDAN KUMA D'AYA KIKE SO 200.!
TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT D'IN.
3126584401 FIDDAUSI MUSA FIRST BANK TARE DA SHAIDAR BIYA A 08036953516
KO KUMA.
ACCOUNT NUMBER:- 0003075326 ZAINAB M BAWA
Jaiz bank SHAIDAR BIYA TA 08161146563.
*KO KATIN MTN TA WANNAN LAMBAR 07065283730 TARE DA SHAIDAR BIYA.*
*SANNAN MUYI ADDING D'INKI A FITATTU GROUP🌹...*
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
- In Serial10 Chapters
The Artificer: A Viridian Gate Online Novel DLC 1
October, 2042In two weeks, the world will die, murdered by a nine-mile-wide, extinction-level asteroid.And Robert Osmark—billionaire and savvy tech-genius—couldn’t be readier for the fiery apocalypse.Unlike the shortsighted masses, he’s been diligently preparing for this day from the moment the asteroid first appeared. Through his relentless efforts, digital salvation now awaits anyone bold enough to take the leap and permanently transition into the brand-new, ultra-immersive, fantasy-based VRMMORPG, Viridian Gate Online. And Robert Osmark will lead this new world he has created.But even with every advantage skewed in his favor, Osmark faces powerful opposition. A rogue faction of global elites led by US Senator Sizemore isn’t content to merely survive the apocalypse. They have their sights set much higher, and are recruiting dangerous allies, undercutting Robert’s efforts at every turn, and hiring VGO’s most deadly assassins to get what they want. To win, Osmark will need to viciously crush all opposition before his plans turn to ash. ?
8 110 - In Serial421 Chapters
The Thousand Kingdoms - Vol 01: Interregnum
A rational, progression fantasy with modern tactical military combat and magic. Long ago, magic began to weaken. In an act of desperation, the Emperor of the known world sealed it away. But now those seals are failing and magic returns to the world. Ella, a physics grad student, becomes a pivotal figure in the return of magic. Chapters are published at least three times per week - Tuesday, Thursday, and Sunday - on RoyalRoad first and then my website at thethousandkingdoms.com. My website has character guiides among other things but can have spoilers as well. So tread carefully.
8 70 - In Serial44 Chapters
Crystal Blue Disguise (Avenged Sevenfold)
Becca starts her new job and meets the love of her life. Problem is, he's already with someone. Will things work out for Becca or will her entire love life crumble right before her eyes?
8 139 - In Serial11 Chapters
The Little Mermaid (MirAndy Style)
You guessed it! Andrea is the mermaid, and Miranda is the Queen...Follows the plot of the original Disney movie pretty well, but I also added some things. I just really love the idea of Mirandy as the starring roles in the Little Mermaid!(fanfiction.net)
8 195 - In Serial43 Chapters
when the night comes | poems
Self-written poems about sleep paralysis, nightmares and all the things I experience when the night comes.
8 158 - In Serial24 Chapters
Whodunnit? Murder On Mystery Mountain
"Blood dripped down from the wall. Giles watched the dark liquid cover the wood of the cabin like a blanket. Stunned into silence, Giles could only stare at the horror before him. He knew one thing for certain. Death had found him, once again."Believing he has finally escaped the evil that has plagued his life, Giles accepts a job at a sleep away camp in America. This time, he is prepared for anything, bringing protective weapons with him. He even reconnects with Lana - his previous maid- who brings her own ghosts with her. Everything seems to be fine, that is until Giles discovers a message written in blood. The evil has once again followed him, but Giles is determined to change the rules. However, the killer has a few tricks up their sleeve. With every day, another man is murdered, and the stakes increase drastically, until the most gruesome finish yet.
8 165

