《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 42
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on "
Page 42
hijab kawai sawwama taɗauka ta sanya tana jiran isowarsa yana isa ya sanarda ita dan haka tayiwa mama sallama tafita,
A cikin mota yake wannan karon ba kamar yanda yasababa a kullum yazo yakan fito su zauna a yanda suka saba zama ba,
Jira tayi naɗan wani lokaci kozai fito amma taga bai fitoba hakan yasa taƙarasa jikin motan tayi sallama cikin sanyayyar muryarta sai alokacin ya buɗe idanuwansa da suka canja launi maidasu yayi ya lumshe sabida barazanar tarwatsewa da kansa yakeyi ganin halinda yake ciki ya sanya sawwama ranƙwafowa tarage tsayinta cikin kulawa take tambayarsa abunda ya sameshi, kasa magana yayi ya girgiza mata kai alamun babu komai lokaci ɗaya sawwama ta rikice ganinsa cikin wani hali ya sanyata shiga wani halin itama cikin muryarta data fara rawa kamar wacce take shirin sanya kuka tace yaya sadam baka da lafiya ne? Meya sameka? Wani wajenne yakeyi maka ciwo?
Tambayoyin sunyi yawa ya sanya sadam bai iya amsa mata koda ɗaya daga cikinsu ba, hawayene yafara tsiyaya a idon sawwama domin ganin ko magana sadam baya iyawa, shassheƙanta dayajine ya sanyashi buɗe idon akanta, ya rabb yafaɗi murya ƙasa-ƙasa, mai kuma yafaru? Ya tambaya zuciyarshi tana ƙuna da kukan dayaga tanayi,
Gabaki ɗaya jikinsa yayi sanyi saiya nemi ciwon kan dayakeji gabaki ɗaya yarasa kukan sawwama yanzu shine yafi ɗaga masa hankali,
me akayi miki kuma? Yaƙara jefo mata wata tambayar, tura baki tayi cikin yanayin shagwaɓa mai haɗe da yarinta tace bakaine ba, Yanayin yanda tayi maganar cikin wani irin yanayi yasanya ciƙar jikin sadam ta zuba kallo kawai yabita dashi yakasa furta koda kalma ɗaya zuciyarsa tana raya masa inama ace sawwamace yanzu haka matsayin matarsa inama Ƙaddararsa da ita kaɗai zai rayu? Inama ace mummynsa zata barshi yayi rayuwa cikin kwanciyar hankali, akoda yaushe son sawwama yakan ƙaru ya daɗu yafi nada cikin zuciyarsa Akowani yanayi yakan ji soyayyarta akowani lokaci yakan tunata sannan kuma kodawa yake tare, bayajin zuciyarsa zata iya jure rabuwa da sawwama koda na saƙwanni ne bayajin zuciyarsa zata iya hakurin rashinta bayan tsawon lokacin data ɗauka cike da matsananciyar soyayyarta,
tura baki sawwama taƙara yi ganin ya kafeta da idanuwansa bayako ƙiftasu cikin muryarta mai daɗin sauraro tace yayah sadam me nayi kake kallona haka?
Ajiyar zuciya sadam ya sauƙe haɗeda lumshe idanuwansa a hankali ya buɗesu akan sawwama, sawwamaty tashi kishigo mota shine kawai abunda ya iya furtawa babu musu sawwama tamiƙe tashiga zuciyarta tana ɗar-ɗar bawai dan tana shakku akan halin sadam ba a'a sai dan rashin sabo abunda bata taɓa yiba hirar mota,
Shiga tayi tabar motan a buɗe komawa sadam yayi ya kwantarda kansa akan seat ya lumshe idanuwansa a hankali yace kiyimin karatu da muryarki mai daɗin sauraro kaina ke ciwo stress yayimin yawa,
Advertisement
Cikin tausayawa sawwama tayi narai-narai da idanuwanta nan da nan kwalla yacika idanuwan tace sannu yaya sadam kasha magani? Yanayin yanda yaji muryarta ya sanyashi buɗe idanuwansa dan daff take tasake yin wani kukan kwayar idanuwansa suka sauƙa acikin nata kwallan dake cikin idanuwanta yasakewa idon kamanni yayi wani iri kamae wacce takejin bacci haɗuwar idanuwansu yayi sanadiyyar zubawar tsikar jikin kowanne a cikinsu kauda kansa gefe yayi yace no ban sha ba amma kiyimin karatun inason samun nutsuwa, bbu musu sawwama tafara rera masa karatu cikin zazzaƙar muryarta mai sanyin gaske wacce takeda daɗin sauraro, komawa yayi ya lumshe idanuwansa yanajin sanyi na sauka a cikin zyciyarsa bayan sanyi da nutsuwa na karatun alqur'an gakuma dadi da zaƙin muryarta,
Sun ɗauki tsawon lokaci ahaka har takaiga sadam yanajin zuciyarsa wasar harya manta da halinda yake ciki bashi yabar gidansu sawwama ba har saida dare yafara yi sannan yabar gidan yakoma gidansa yanajin duk wata damuwarsa ta wuce duk wata damuwar dayake tare da ita ta kauce sai wani murmushi yakeyi haka ya isa gida cikin nishaɗi,
Abida tana jiran dawowarsa tayi wanka tayi kwalliya domin duk tunaninta zai dawo cikin wani yanayi saboda mummy ta shaida mata a yanayin da ya fita, dan haka tayi shirinda zai samu tarɓa daga wajanta yanda zata mantar dashi wata can daban zatayi masa abunda bazai sake tunanin wata mace ba balle har yayi tunanin aurota yakawota cikin gidanta matsayin kishiya,
da sallama yashiga tayi saurin tashi ta taryeshi murmushin data gani akan fuskarsa ya sanyata ɗan tsayawa wani murmushin yasake aika mata ya isa zuwa gareta hannunta yakama suka zauna akan kujera cikin nuna kulawa yace nabarki lafiya?
Lafiya ta amsa da mamakinta daya kasa ɓoyuwa shafo fuskarta yayi yace zan shiga wanka ki haɗamin abinci kafin n afito bai jira amsawarta ba ya wuce zuwa ɗakinsa, rage kayan jikinsa yayi gabaki ɗaya yashiga bathroom ya sakarma kansa ruwa sanyin ruwan yana ratsashi yanajin wani sanyin yana ƙara shigarsa, ruwan yana zuba ajikinsa yana tunanin sawwama yanda lokaci guda ta sauƙar masa da nutsuwa a yanayin dayake ciki ya manta da komai, yanzu mumny irin wannan nagartacciyar matar takeso yarabu da ita? Ruwan na zuba a jikinsa saida yaji sanyin yafara yimasa yawa sannan ya murɗa switch ɗin yakoma ruwan zafi nan yagasa jikinsa ya fito ɗaure da towel hannunsa da ƙaramin towel yanaɗe ruwan kansa ya goggoge jikinsa sannan ya shafe duk illahirin jikinsa da lotion mai kamshin gaske sannan yabi saƙo da lungu da turaruka sannan ya sanya singlet da three quater yafito ƙaramin palourn ya nufa kamar yanda yasaba kullum anan suke cin abinci dayake anan dining dinsu yake,
Serving ɗinsu tayi sannan tazauna tadubeshi cikin yanayin dabara tace honey nikam sai naga kamar kana cikin wani farin ciki wani abu ya farune haka?
Advertisement
girgiza kai sadam yayi yana kaiwa spoon bakinsa yace no mai kika gani?
Yanayinka! Bbu komai yafaɗi atakaice yacigaba dacin abincinsa."
Koda dady yaje gida bai nunawa mummy komaiba sam bai gwada mata sunyi magana da sadam ba itama ganin dady baice mata komaiba ya sanya tayi tunanin sadam bai kai ƙararta ba kenan,
Sai lokacin tasamu relief hankalinta ya kwanta sosai."
Washe gari ta safe dady yayi shirin fita aiki itama mummy tafito zata wuce nata wajan aikin dady ya dubeta fuskarsa sake sam bbu wata alamun damuwa yace mummynsu ina akwatin lefennan na sadam na wannan yarinyar da ba'a kaiba? Nan da nan mumy tasha jinin jikinta tace dadynsu mai kuma zakayi da akwaitin lefe, dady yace inaso a maidashi ɗakinane kafinnan ina yarannan kai ya kwalawa su hassana kira yace kushiga ɗakin mummynku ku kwasomin akwatinan lefennan, mumny tana kallo batada nacewa suka kwaso akwatinan suka kawo masa, kallon mummy yayi da mamaki yace yakuma naga akwatinan haka?
guda 3 kacal mumy tace eh ai haka suke, dady yace amma naga ita waccar bahaka aka kai musu ba,
Mummy tace to ai dai-dai ruwa dai-dai gari dadynsu ba'ace abunda akaiwa waccar dole itama ayi matab aai karfi ba ɗaya ba,
Yanzu ko kayan ɗakin da aka yiwa waccan ai bazasu iya kwanatata yimata ba,
Jijjiga kai dady yayi yace hakane toh Allah ya kyauta mummy ta amsa da amin amma duk atsorac kijinta e take saboda kar yayi faɗa amma ga mamakinta hakan kawai yafaɗi dai yace su ƙarasa da kayan cikin ɗakinsa suna shigarwa ya kulle dakin sannan yayi musu sallama ya sanya kai yafice zuwa office, mummy ma tafice tanata tararradin abunda dady yake nufi a cikin ransa da karɓe kaya a wajansa,
Sai 3:00pm kafin dady yadawo a office mummy kuwa tun 2:00pm tadawo tazo tasamu kwantar dady wacce take binsa ana kiranta adda saratu tazota, manya da yara haka suke kiranta, itama babbar ma'aikaciyace kuma tanada arzikinta sosai bata ɗaukan rainin mummy ko ƙadan dan masifaffiyar gaske ce shi kanshi dady yana shakkarta da fara'a mummy ta karɓeta suka zaune sukaci gaba da hira har dady yadawo ya samesu, Shima yazauna aka cigaba da taɗin dashi, 30minute after dady yadubi adda saratu yace mushiga daga ciki lokaci yana ƙurewa,
Toh tace sannan ta miƙe suka nufi ɗakin dady,
Mummy tanaso taji mai zasu tattauna amma sam babu halin tabisu,
Dady ya feɗewa adda saratu biri da wutsiya yace wallhy narasa yanda zanyi da ita ta takura yaronnan dayawa saboda taga yanayi mata biyayya bana wasa ba,
Jinjina kai adda saratu tayi tace eh lallai dama haka abun yafaru? Aimu kayi mana gajartaccen bayani ne, baka shaida mana auren dole kukayi masa ba,
Shi namiji har anayi mas aauren dole ne?
Dady yace wai nabata damartane matsayin na mahaifiyarsa amma yanzu tanason wuce gona da ir, har tana ikirarin ɗanta bazai auri ƴar talakawa ba, adda saratu t abuɗe baki tace ai haka! Eh lallai aikuwa yar talakawa kamar ya aura yagama akai mas aauren dolema bare wacce yakeso, ai dole yaro ya auri wacce yakeso, ɗan ƙararramin yaro ficicin yaro an sanyashi a ja'iba sa'anninsa ko shekarun yin aure basu sakaba amma shi an ƙaƙaba masa har mata biyu!
Dady yyace yanzu dai ba wannan ba ga kayancan kamar yanda nafaɗa miki tarage komai komai wai dai-dai ruwa dai-dai gari,
Lallai kuwa zan bata mamaki abunda adda saratu tafaɗi kenan sannan tace akaiminsu mota goben za'akai kamar yanda aka sanar musu ai baza'a maidamu ƙananun mutane ba, bazamuyi magana mu canjataba wallhy ay muba ƙasƙantattu bane kowa ya sanmu da mutumci da darajarmu mu daga babban gida muka tashi ai me magana ya canja shine ƙaramin mutum eheh iyayenmu manyan mutane ne,
Jijjiga kai kawai dady yakeyi mata dan yasan kalar masifarta bata sauki bace, kuɗi yaciro yabata yace gashi aƙara asaya Abubuwanda babu waɗanda sukayi ƙaɗan ma aƙara, amsa adda saratu tayi tace zan duba, sannan tafito,
Mummy nayi mata sai anjima tace majima dakyau, hakan yasa mummy ta fahimci akwai wani abun a ƙasa, bata sareba saida taga ana fita da kaya, aka lodawa adda saratu a mota,
Adda saratu sanda tabiya gida ta bude kayan tagani duk bamasu tsada bane sannan tawuce izuwa kasuwa duk wasu abubuwanda za'a buƙata ta sayosu,
Washe gari ta haɗe mutane aka tafi kai lefen."
Kuyi haƙuri da wannan na gobe in sha Allah zaifi haka yawa."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial36 Chapters
Only Me wasn't brought to another world, at least for now....
Left in this world alone as an abandoned, live alone in a world full of animals which hate humans to the cores... I am Alone... feeling saddened, I thought of... why can't I just create my own person to talk to myself? Thus, My life on the world which being left behind by the humanity, which being abducted by aliens comes to open its curtain, and... by the time humanity come back on earth... the curtain of the show, which being played by the earthlings' blood and tears starts while Me? I am Alone... [Father! the show gonna start soon!] well, not anymore... *the story has some resemblant with EER(everyone else is a returnee) but not all...
8 242 - In Serial7 Chapters
Project Daily Grind (Mirror World Book #1) by Alexey Osadchuk
Opening chapters were published at the request of the author Alexey Osadchuk.This is a new book in the LitRPG genre.The ads enthused, ""The virtual lands of Mirror World await you! Live out your most secret dreams in our world of Sword and Sorcery! Become a Great Wizard or a Famous Warrior! Build your own castle, tame a dragon, conquer a kingdom! All those desperate, lonely and insecure - Mirror World offers you a chance!"But Oleg isn't meant to become a great wizard or a famous warrior. He'll never have a castle of his own. Neither will he ever tame a dragon. And he's definitely not the type to conquer a kingdom, however virtual it may be.Oleg is doomed to toil away in the recesses of Mirror World's mines. His goal is to raise enough money for a heart transplant for his dying six-year-old daughter. The clock is ticking. Will he make it?
8 146 - In Serial11 Chapters
Mecha Stalin Massacre (An alternate-universe steampunk LitRPG)
A nerdy underdog, an ex-KGB* operative, and an unorthodox bard must work fight murder their way out of a 1937 Soviet Gulag. What would it look like if you combined a LitRPG with a gritty historical thriller and a big dumb action flick? It would look awesome, that’s what. Expect narrow escapes, intimate murders, harsh status ailments, tactical gunplay, philosophical musings, and an overpowered Mecha Stalin. * Back then it was called the NKVD
8 64 - In Serial30 Chapters
His Adventure In The Soul World
In this world of the Mok Soul, every creatures have distinct features. People who travels to this world from Earth are called travelers. They have the ability to snatch the distinct features of the local creature. Our MC is one such traveler._-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_-_ Along the journey, -------- he found friendship and treason. He encountered eternal love and deep hatred. He experienced happy endings and tragedies. - All that make him a mature young man. -------- He found strange creatures. He encountered strange materials. He experienced strange events. He has some abilities the others lack. He lacks some abilities the others have. But he can't stop his adventure no matter what. - All that make him question what existence is?-------- Oh, he is our MC, Cank.
8 141 - In Serial8 Chapters
Restless Night, Pleasant Dreams
I lived my life as a dream. Waking up to attend parties with those of my elk, sleeping with the bright and pretty, leaving behind many promises and lies. I woke up from all of that nonsense. No... it is better to say that I was— shock awake.. I watched my father die like a dog trying to protect my mother. I watch my mother take her own life after my father died. I clearly remember sitting in the steam carriage, nursing a hangover. Praying for this trip to be over. I clearly remember the amber eyes and twelve foot wing span. I clearly remember the sound of iron doors being ripped open as if it was paper wall. I clearly remember other drivers screaming and the sound of collisions and explosions as people rekt in panic of escaping. I remember the death around me and the fear that gripped me. The soul stirring feeling that sent me fleeing while my parents were suck clean of blood. I remember thinking, berating myself hours later. Gripping my hair, slapping my palms into my forehead, questioning why I didn't carry my tools. Weeks pass since that time.. My guilt is gnawing at me and this pain isn't something I like. I almost feel like the man in the mirror isn't me. The me I used to be. Maybe, if I take revenge. I can put these demons to rest? Maybe, if I put these bastard in a grave. I can be someone new? Maybe, after they all die. This mirror won't haunt me with their faces?
8 175 - In Serial178 Chapters
The Fragile Monster Lord
A Story About a guy who choose to leave his world by accident and gained the ability to control monster will he survive with his fragile body ?!(I am no good with descriptions comment down bellow and tell me good description please)I edited the previous chapters on this site ! https://kakemonoko.wordpress.com/
8 678

