《ƘADDARAR RAYUWA》K page 51
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
"
Page 51
Sadam yadubi mummy fuskarsa bbu alamun bacin rai ko farin ciki sai mamaki dake kwance fall akan fuskarsa yace" mummy me nake gani! Mummy tayi murmushi irin nasu na manya tace mai kuwa sadam banda abunda idanuwanka suka gane maka, karatu zaku tafi kuyi degree dinku na biyu kaida abida a kasar waje, gaban sadam yayi daram yafadi amma sai dake ya kakali murmushi yace ma sha Allah mungode mummy Allah yasaka da alkhairi mummy tayi murmushin farin ciki jin cewa sadam bai yi gardama ba ya amince,
Abida ma cikin murna tafara yiwa mummy godiya ita abunda yafi bata farin cikima kasancewar ita kadai da sadam zasu tafi, zasubar sawwama agida,
Sadam kuwa cikin ransa tunani yake yanda zasu tafi yabar sawwama cikin wannan hali,
Sawwama dake jinsu tasaki murmushi tace Allah ya sanya alkhairi yabaku sa'a baki daya sadam ya amsa da amin yana binta da kallon tausayi dan yasan wannan abun anyishine kawai dan a kuntata mata amma ita bata damuba tayasu farin cikima takeyi,
Mummy tace idan dadynku yadawo zamu shirya yanda tafiyarku zata kasance dan anrigada angama komai next month zaku wuce,
Sadam ya zazro ido yace next month kuma mummy? Abari mu shirya a tsanake mana,
Mummy tace ih next month dai, wani shiri kuma bayan nace maka nagama komai, angama komai kuma mai za'a jira,
Nan danan sadam yaji zuciyarsa ta dagule yanzu zai tafi yabar sawwama kenan gashi bawani cikekken lafiya take dashiba,
Kuma tabbas a dai-dai wannan lokacin tana bukatarsa a kusa da ita tana bukatar kulawarsa,
Sadam yayi shiru sai nazari yakeyi da saka da warwara har dady yadawo daga wajan aiki,
Shima a palourn yazauna yanda ya samesu, ganinsu ahaka yaji dadi yanaso mummy ta kwantar da hankalinta ta rungumi surukanta duka biyu,
Dady fuska cikeda fara'a yace mummy ya yayanta me ake tattaunawane haka?
Mummy tace takardar karatunsu ne na mika musu dady yace ma sha Allah abu yayi kyau sosai, Allah yabasu sa'a, su duka suka amsa da amin, nan suka gaisheshi sawwama ta gaidashi kanta yana kasa dady ya amsa fuskarsa cikeda fara'a,
Sadam yadubi dady yace dady inaso muyi magana! Dady yace maza go ahead inajinka, saddam baiso dady yace yafadi maganar ananba yaso yace suje daki,
Yanzu kuma idan yayi insisting atafi daki toh mummy zata dauki abun da zafi,
Sadam yace uhmm dady dama!
Sawwama ce naga kamar bai kamata mu barta ita dayaba itama ko za'a nema mata acan sai mutafi muduka tare?
Harara mummy ta watsa masa dukda ba ita yake kallo ba amma jikinsa yabashi ta harareshi,
Dady yace eh toh kaima kace wani abu, jarabawarsu tafito ne?
Sadam yayi saurin fadin eh dady tun wancan month din,
Mummy tayi saurin amshe zancen da fadin oh ni sadam kafimu sanin abunda yadace kennan?
Dady yace no bahaka yake nufi ba amna zancen daya fadi yayi dai-dai bai kamata su tafi su barta ba,
Mummy takara watsawa sadam harara, abida kuwa jitayi kamar ta shake sadam tuni tafara aikawa sawwama harara itakuwa sawwama kanta yana kasa tana wasa da yattssun hannunta batamasan tanayiba,
Mummy tace to ai shikenan sai anema mata itama, tafadi zancen bahar rantaba, sannan tadaura da fadin eh zan nema mata itama ai bazai gagaraba, nida farko abunda yasa bannema mataba saboda itadin kasan nata tsawon shekarun yafi nasu tundasu degree na biyu zasuyi ita kuma tafarkoce kaga tsayin shekarun akwai bambamci, kaga bai yiwuwa su dawo su barta acan, amma yanzu ai ko diploma tayi acan din sai shekarar tazo daya da tasu, amma ita nata sai daga baya saisu fara tafiya idan aka sama mata sai tabisu daga baya,
Advertisement
Dady yace to ai hakanma yayi kyau, tabisu daga bayan tunda su nasu anrigada angama komai,
Mummy taji dadin yanda dady yayarda da zancenta yabar mata zabi a hannunta,
Sadam kuwa zuciyarsa tana darr-darr da maganar amma haka ya daure yayiwa mummy godiya,
Mummy tana amsa godiyarsa tana watsa masa harara burinta idanuwansu ya hade waje daya yaga irin kallon datake masa amma sam sadam yaki bari hakan ta yiwu,
Itama sawwama godiya sosai tayiwa mummy, mummy tayi yaken da baikai zuciya ba tace ah ba komai yiwa kaine ai tafadi hakan tana jefenta da kallo ta gefen ido,
Dady yaji dadin yanda mummy ta sauko ta rungumi surukanta hannu bibbiyu,
Mikewa dady yayi yace toh bari na shiga ciki nadan huta, mummy ta mike tabi bayansa, suna shigewa sadam yatashi daga wajan dayake zaune yadawo kusada sawwama cikin kulawa yafara tambayarta bakyajin komai? Babu yanda yake yimiki ciwo?
Sawwama ta girgiza kai tace babu komai banajin komai,
Sadam yace idan kinji dai ki fadamin bari mummy tazo muyi mata sallama sai muwuce, sawwama ta gyada kanta, wani dogon tsaki abida taja mtswwww wanda dukansu suka kai kallonsu gareta,
Sadam baibi takanta ba yamike yace ina zuwa yayi cikin gidan,
Yana fita abida ta dubi sawwama cikin rashin mutumci tace toh yar matsiyata yar talakawa anzo ansamu gida an ishisshire an barbaje, dama ance yayan matsiyata basu iya samun wajeba,
Matsiyaciya gara tun wuri kinemi wajan zuwa dam sadam yana gabb da rabuwa dake, shegiya mai fiki-fiki idanuwan, sawwama tayi kasa da kanta hawaye yacika mata idanuwa tam, taki runtse idanuwantane saboda bataso su zubo, abida ta sanya hannu ta zumguro kan sawwama tace shegiya munafuka kawai, tsoro yayi bala'in kama sawwama saboda ita iya tsawon rayuwarta bata tabayin fada da wani ba, ba kawaye take dashiba balle ace koda sau daya cacan baki yahadasu,
Takure jikinta tayi a waje daya tayi kifi-kifi da ido kamar wacce za'a cewa fattt ta ruga da gudu,
Abida ta matsa daga kusa da ita saboda tasan halin sadam idan yazo yaganta ahaka koda bata yiwa sawwama komaiba tsaff zai zabga mata rashin mutumci akan wannan kazar mayun,
Jakarta tadauko ta dauki chewing gum ta sanya a bakinta tafar taunawa tana kass-kass sannan tadauko powder tafara shafawa tanayi tana yar wakanta, maida powdern cikin jaka tayi taciro turare mai kamshin gaske tafara fesawa, taciro body spray tayi fuuuuu shuuuuuu fuuuuu ta feshe jikinta gabaki daya,
Nan da nan cikin sawwama yafara hargitsewa yana haustinewa jitakeyi kamar wacce ake jujjuya mata komai ana kada mata komai a cikinta amaine ya tunkarota tayi saurin sanya hannu ta rufe bakinta, hakan yayi dai-dai da shigowar sadam,
Karasawa yayi kusada ita ya zauna, ganin yanayinta ya canja ya sanyata fara tambayar abunda ya sameta bata iya amsa masaba saboda tana bude bakinta amaine zai fito, dagowa yayi yana yiwa abida kallon tuhuma,
Abida ta tabe baki ta nuna kanta da hannu sannan ta girgiza kai hadeda karkada hannunta alamun nii a'a, sawwama tana nunawa sadam bakinta da hannunta, amai? Ya furta dasauri, saurin daga masa kai tayi,
Mikarda ita yayi yanufi toilet din dake cikin palourn da ita,
Nan tafara kwarara amai fitowar mummy kenan taji kakarim aman sawwama ta iso palourn tana tambayar wayake amai? Abida da jikinta yagama yin sanyi ta mutu mudus tace sawwama, zaro ido mummy tayi tace badai cikiba? Abida da hawaye harya cika mata idanu tace nima haka nake tunani,
Advertisement
Mummy takasa zama tsabar tashin hankali bata kawo samun ciki dawuri wajan sawwama ba tunda taga abidama ta aka riga aurota bata samuba,
Tunaninta daya yanda zata fara hada jini da matsiyata jinin talauchi, wani kolulun bakin ciki takeji sadam ya cuceta daya auro mata yar matsiyata, dama mastiyata bbu abunda sukafi iyawa kamar tara ya'ya,
Sawwama tagama aman sadam ya wanke mata jiki hadeda baki yagyara wajan sannan ya rikota suka futo, ganin mummy ya sanya sawwma tafara kokarin kwacewa amma sam sadam yaki sakinta, saina kara rukota dayayi dan yasan idan tayi amai jikinta duk yakan zama babu wani karfi,
Har ya'iso da ita ya zaunar da ita babu wanda ya iya cewa komai, akan babban kujera ya zaunar da ita ya juyo ya mikar mata da kafafunta ya kwantar matada kayi, ta kwanta flat, mummy dan bakin ciki kawarda kanta gefe tayi,
Dawowa yayi dai-dai kanta ya daga kan yazauna sannan ya kwantarda canka akan cinyarsa, hujab dinta taja tarufe har kanta dan har lokacin akwai kamshin turaren a dakin,
Mummy kuwa tazama mutum mutumi dady yafito daga dakinsa zai fita zuwa masallaci ya dubesu ganinsu ahaka ya sanya yace subhanallahi mai yafaru? Mai yasameta? Sadam yace batajin dadine, amai takeyi, dady subhanallahi to awuce asibiti mana kazauna anan! Sadam yace munje dady,
Dady yace toh takwaana biyu batada lafiya kenan? Aida baka daukota ka fitoda itaba sadam sai abarta ta huta, Allah yaraba lpy dady yace sannan yafita,
Mamaki yakama sadam har dady ya fahinci juna biyu take dauke dashi kenan, kasa-kasa ya amsa da amin,
Jin kalaman dady ya sanya zarginsu mummy yazama gaskiya,
Kuka sosai abida tasaka tana fadin mummy kin ganshi koh kinga irin rashin adalcinsa koh?
Mummy kiganifa ni yafara aura amma tsabar rashin aldalci ni baiyimin cikiba ita yayiwa ciki,
Wallhy bazan yardaba mummy Allah bazan yardaba sai daia azubar da cikin aini yafara aura saina fara haihuwa kafin ta haihu, wani kukan tasake sawa tana fadin wallhy mummy bazan yardaba sai dai azubda cikin tajira idan yafara yimin sai itama yayi mata, kawai dan yafison sonta shine zaiyi mata ciki yafison ya haihu da ita baniba,
Mamakine yakama sadama domin maganganun abida bbu wanda zaiyi irinsu sai wanda addini bai isheshiba,
Karasawa mummy tayi wajan abida tana bubbuga mata baya batareda ta iya cewa komaiba,
A kufule sadam yace sai kizo ki zubar idan ke kikayi cikin ko idan ajikinki yake kizo ki zubar banza kawai kina magana cike da rashin sanin addini, ita haihuwa ba Allah yake bayarwa ba, sai kizo kisaka nayi miki cikin ai, abida kara wani kukan tayi da karfi tace mummy kinjishi koh? Kinji abunda yake fada koh? Wallhy ko kaso ko kaki nima saika yimin ciki, tsaki sadam yaja ya mike yakama hannun sawwama yadubi mummy a kufule yace saida safe kai kawai mummy ta iya daga masa yaja hannun sawwama suka fice,
Saurin mikewa abida tayi tana kuka zata bishi mummy takamota, kokarin kwacewa takeyi tana fadin mummy kingani koh? Kingani mummy tafiya fa zaiyi,
Mummy tajawo hannunta ta zaunar da ita itama ta zauna tace nutsu-nutsu ki saurareni kiji dakyau, mekikeci nabaka na zuba?
Tafiyafa zakuyi ku barta anan keda shi, idan cikin kikeso zaiyi miki acan, abida tasake saka kukan tabara tace amma mummy cikin jikintafa nifa banaso tarigani haihuwa, mummy tace share hawayenki share hawayenki badai zaku tafi ku barni da itaba? Ai nasan yanda zanyi da ita kuma shirunku, abida tace amma mummy aikince zaki aiko mana ita daga baya, mummy tace zancene kawai bazan turata ba, tana nan harku dawo, abida ta share hawayenta tace dan Allah mummy karki turota, mummy tace bazan turataba abida nafiki tsanar yarinyar nan sam bana kaunarta banason ganinta kusa dake da mijinki,
Ki kwantar da hankalinki a zaman da zakuyi acan ki jashi jikinki, ki nemi soyayayrsa,
Abida ta jijjiga kai mummy tace toh maza tashi ki tafi gida nasan zuwa jimawq zai koma, alokacin abida tatashi tawuce gida."
Sadam aranar kamar bazai komaba dake a gidan abida yake dakyar sawwama ta tilas tashi yatashi yatafi,
Adakile yashiga gidan dan ransa yayi matukar baci da abunda abida tayi yanda yake son cikin dake jikin sawwama bayaji akwai abunda zai iya bari ya taba cikin bare har ayi zancen zubdawa,
Kai tsaye dakinsa yawuce ya kwanta yana kwance saiga abida tashigo dakin ko kulata baiyiba ta tsaya agabansa tacire kayan jikinta kaff-kaff ko arzikin pant da brazier bata samuba ta tsaya tace gani nima kaimin ciki, wallhy yau idan kwana zakai kana abu daya bazan hakuraba saika yimin ciki, duk bacin ran da sadam yakeji sanda dariya taso kamashi,
Sadam yace zonan ki zauna bbu musu tayi saurin zama a yanda ya nuna mata, yace ciki kikeso koh? Tayi saurin gyada kai yace toh zanyi miki yanzu kuwa amma da sharadin duk abunda nayi miki bazaki hananiba kuma yau bazaki gajiba, tayi saurin gyada kai tace na yarda,
Sadam da gayya yake yiwa abida komai zafi-zafi da mugunta-mugunta gashi yadauki tsawon lokaci yana abu daya yaki ya bari, abida ta galabaita ta fitaa a hayycinta amma dayake ciki takeso bata nuna gajiyarta ba,
Har saida sadam ya tabbatar ta nuku sannan yabarta, amma abida da abunda tafara magana shine kayimin cikin? Eh sadam ya amsa mata, tace toh ai banji komai acikinaba, yace ai yanzu bazakiji komaiba har sai nanda 3month, abida da farin ciki da murna ta kwanta tayi bacci, shiko sadam yadade baiga mutum mai yawan shekaru amma shashashaba irin abida, baisanma ita doluwa bace sai yau, idan dagewa kesakawa ayi ciki da babu wanda zai zauna bai haihuba batasan haihuwa da rashinta lamarine na ubangiji ba,
Gashi dai shi kansa da kadan ya girmi abida dan bai kai shekaraba amma rashin hankalinta da rashin tunaninta karamar yarinya bazata yiba,
Girgiza kai yayi kawai ya mike yashiga toilet dan yin wanka."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial15 Chapters
HIVE - LOCKED UP IN SPACE
Somewhere in the vast universe, an alternate reality to what we know.. which occurs in the year 3016 where Earth has already made contact with other sentient beings of space and has become much more technologically advanced. Meet the good-for-nothing anti-social NEET Jasper. Let's just say that he was born under an unlucky star, being wrongfully incarcerated in the galaxy's most infamous private maximum security prison, home to serial killers and many cut-throat criminals. Will Casper be able to prove his innocence and adapt to the cruel and oppressive prison system and rise up the food chain? --------- Alright. Before I start off, this is going to be my first fiction. It could be dropped anytime and there might be random hiatus inbound. This fiction is basically a first draft~ish.(?) So please pardon my two-dimensional characters or my shitty grammar or poor use of descriptive words in this fiction. Doing this purely for fun and it's going to stay that way. Let's take this step by step alright? [There isn't really a set in stone plot drafted so it might flop after a bunch of chapters lmao] Reviews with constructive criticism are appreciated, I will try my best to improve as we go along.
8 196 - In Serial18 Chapters
Class Systems
A random young man wakes up in a random new world rife with violence, magic, and power. Finding himself in a body that already has abilities, he has to learn to manage his rage if he wants to survive.
8 102 - In Serial27 Chapters
Of Misclicks and Magic
What happens when those given power of unimaginable proportions fulfill their objective and become without aim? Some may continue to use it wisely, but, more often than not, it is abused. In so many isekais (or fantasy stories in general), the protagonist remains a beacon of morality with the temptations of power seemingly non-existent.In the world of Luvitov, however, upon the demon king's demise, the heroes splintered and their intentions became warped with their new immortal lives. They engage in an endless power struggle for the only ones that can oppose them is each other.Here in this world of might and magic, a reincarnated man makes a small mistake, he accidentally skipped the skill and stats screen in the process of reincarnating. His stats are nothing but ones and has no innate skills or talents. He sits yearning for a life undetermined by others.If you have reached this point and are willing to put up with my garbage along with my inconstant uploading, then welcome and I hope that you find some enjoyment out of this, even if aimed at myself.
8 130 - In Serial7 Chapters
In the Name of the Unholy Spirit
On his dying breath, the five year old Silas is saved by the angel Arkun. To save the boy, the angel shares a part of his broken halo, and in doing so, he ends up making the boy the first human with angelic powers in the world. Follow the adventures of Silas and Arkun as they build an Empire and shape the world according to their desires. "Participant in the Royal Road Writathon challenge."
8 185 - In Serial25 Chapters
R U L E S
"Jesus Christ." I called out, this was the first time I was finding out my body could be so sensitive, I was so used to the five pumps and done but James was showing me something different, he was showing me to myself. "He can't help you now." His husky voice had whispered.
8 208 - In Serial11 Chapters
Ignore this
Just ignore it
8 192

