《ƘADDARAR RAYUWA》K page 52
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
"
Page 52
Yarage saura sati biyu tafiyarsu sadam yayinda laulayin sawwama yake kara gaba, kullum cikin wahala take, alokacin hankalin sadam gabaki daya yagama tashi tunaninsa ta yanda zai tafi yabar sawwama cikin wannan halin,
Abida kuwa anata wajan sam yanzu tadaina dagawa sadam hankali domin ita zatonta da gasken yayi mata mata,
Dan haka sadam yanzu yasamu sauki tawajanta, amma halinda sawwama take ciki bakaramin daga masa hankali yakeyi ba,
Sadam yakanson kasancewa tare da ita koda yaushe saboda yaringa bata kulawar data dace kafin su tafi amma yarasa ta yanda zai bullowa lamarin,
Bayan yabari dady yadawo daga aiki yaje har gida ya sameshi,
Dady yana ganin sadam yasan akwai magana domin yanayinsa kadai ya nuna hakan, dady yace sadam maike tafe dakaine? Naga kaman akwai magana a bakinka,
Safam yadan nisa sannan yace uhmm dama dady gameda tafiyarda zamuyine nanda sati biyu, kuma sawwama batada lpy kullum cikin ciwo take!
Dady yace toh! Yanzu me kakeso ayi sadam? Ko kanaso tadawo nan da zamane saboda kula da ita? Kafin itama mummynku da sama mata nata gurbin karatun?
Girgiza kai Sadam yayi yace A'a dady! Nidama yanzunne nakeso na kasance tareda ita sai na ringa kula da ita har zuwa tafiyarmu sai ita abidar tayi hakuri tunda idan muntafi zamu dauki lokaci kafin sawwama tabiyomu,
Nisawa dady yayi yace toh sadam ni yanzu daka sameni da wannan magana banda ikon aikata hakan, dukda zancen daka fada idan anduba hakan yakamata amma ita matarka zakaje kasamu kayi mata bayani idan ta amince toh Alhamdulillah,
Idan bata aminceba kayita lallabinta har kasan yanda kayi ka shawo kanta,
Mummy dake tsaye bakin kofa tana jinsu tun datsu tace dear wannan wane irin danyen hukunci ne? Dakai za'a yanke wannan hukuncin abunda fa yakesonyi rashin adalcine, bai kamata ga bashi goyon bayan rashin adalci tsakanin matansa ba,
Dady yace no ba haka bane wannan bashine ake kira da rashin adalciba kuma koda ita abidarce hakan yafaru da ita hakan zance masa,
Advertisement
Mummy takaraso tazauna tace ni gaskiya ban goyi bayaba dear, dady yayi murmushi yace ke rikici danki rikici da wanne kikeso naji!
Murguda baki mummy tayi kamar wacce kesonyin shagwaba sai kuma tatuna da zaman sadam a wajan saita fuske, dady yace yanzu bamuda huruminda zamu shiga masa zancensa tsakaninsa da matansa wannan ba huruminmu bane shiyasa kikaji dayazo ban yanke masa hukunciba nace masa yake hanemi izininta akwai abubuwa dayawa wanda bazaka shigaba a zamantakewarka da yayanka,
Kai naka nasiha dakuma ido sannan daurashi akan hanyar data dace idan akaga zaiyi kuskure sai a nusar dashi, idan yayi ba dai-dai ba kayi masa gyara. Idan kuma ya karkace a mikar dashi amma kayita shiga shirgin yara sam hakan baida amfani, koda a wajan y'ay'ankane kazamto mai kama girmanka a idonsu yawan kauda ido kayan rayuwar gidan yarka/danka kana kara tausayinka cikin zukatansu,
Dady ya kallo sadam yace kaji maina fada maka koh? Ka nemi yardarta da amincewarta, Allah yayi maka albarka, sadam ya amsa da amin, yayi musu sallama yafice yabar mummy da dady."
Kai tsaye gidan abida yawuce yagama rattabo mata abunda ke tafe dashi, tashi abida tayi ta dire tace wallhy baka isaba ba'a isa yimin wannan abunba eh lallai, kwanana guda daya kadauka kakai mata ban yafe makaba, kuma Allah ya isa idan har kakai mata kwanana, ai wallhy ko mutuwa wannan shadaniyar yarinyar zatayi sai dai tamutu amma minti daya ban iya bata,
Da mamaki Sadam yake kallonta yace nine kike yiwa Allah ya isa? Ni kike jawa Allah ya isa abida?
Abida tatura baki tace aini banja makaba cewa nayi idan kakkwana, aikuma hakkina ne idan kayi inada right din yimaka!
Sadam yace koba right ba! Abida tace shi dai! Girgizaka kai yayi yace toh naji amma kinsan koda kece kike cikin irin wannan hakin haka zannemi izini dan kula dake kuma itafa nan da 2weeks zamuyi tafiya mu barta! Amma ke bazakiji tausayintaba? Wata rana kece zaki kasance cikin wannan halin kuma kema zaki nemi taimako amma inason kisani alokacin da zaki nemi naki taimakon kada kikuskura ki tunkareni dan bazan saurarekiba, kuma a yanzuma haka ganin damane zai saka ban aikata abunda naga damaba, and abu nagana shine koda gigin wasa kada bakinki yakara furta kalmar shedaniya akan matata, bazan daukaba Allah yagani zan dauki mummunan hukunci akai, kiyi duk rashin kirkinki da tijararki amma banda akan matata,
Advertisement
Sadam yana fadin haka yatashi yafice yabar abida tana kunkuni."
Tun wannan lokacin da sadam yafita abida bata sake sanyashi a idontaba har washe gari, washe garinma karfe sha biyun dare yashigo gida yawuce zuwa dakinsa, yasaka key koda tazo tana knocking bai budeba sanda tayi yin kanta tabari takoma dakinta, sadam daga sallar asubahi bai sake komawa gidan abida ba har wani washe gari nanma bacci kawai ya maidashi daga sallar asubahi kuwa bai komaba,
Haka sadam yakeyi yanzu idan yafita daga gidan abida bazai sake komawaba sai ranar kwananta hakanma bacci kawai ke mayar dashi da asubahi yafice,
Halinda sadam yake nunawa abida ya isheta ranar daya kasance a gidanta zai kwana tahana idonta bacci ta zauna a palour tana zaman jiransa dan tun safe take kiran wayarsa baya picking, har bacci yafara ebenta sai bude kofar sace tatasheta zuruf tatashi kamar wacce aka zabura tasha gaban sadam da sauri, sadam yaja yatsaya yace tofa! Menene haka kuma?
Takai dubanta jikin agogo karfe dayan dare, sannan tadawo da dubanta kan sadam tace tsabar dumbin tashin mutumci sai yanzu karfe daya zaka dawomin gida?
Sadam ya jijjiga kai yace nine mai dumbin rashin mutumci? Kuma tuhumata aka saka kiyi? Gadina aka baki? Hade rai yayi yace matsamin a hanya bacci nakeji, kare tare hanyar tayi tace ai kasan kanajin baccin kaje ka raba dare wajan wancan banza jahilar, bata rufe bakiba sadam y sauke mata mari ya hankadata tafada kan kujera ya nunata da yatsa yace nfada miki koda da gigin wasa kika kara zagarmin mata saina dauki mataki, stupid yafadi hadeda shigewa dakinsa,
Abida rikeda kumatunta tasake kuka tatashi tashiga daki tana jan Allah ya isa kuma tana fadin saitabar gidan, sadam ko juyowa baiyiba saida yakaiga dakinsa ya ja yarufe da key daga dakinsa baya jiyi kukanta,
Key din motanta tadauko hadeda gyalenta tafita zuwa harabar gidan, key tasaka ta bude jikin gate din tacire lock 🔒 tsorone yakamata ganin yanda wajan yake shiru ko motsi babu sai haushin karmuka, dasauri taja tarufe takoma palour gabanta yana faduwa kwanciya tayi akan kujera da nufin sassafe zata fice,
Shikuwa sadam yana shiga daki bayan ya kwanta sai danasanin marinda yayiwa abida yakeyi sam hankalinsa yakasa kwanciya saboda yasan bai kyautaba bai kamata ya maretaba, amma zafinta dayakeji ya hanashi tashi yaje ya rarrasheta,
Da asubahi zai fita sallah yaganta kwance baje-baje a kasa dankwali yayi can gashinta duk ya barbaje murmushi yayi kawai yafice yatafi,
8:00am sadam yaji kira yana dubawa yafa lambar dady gabansanr yafadi yadauka da sanyin jiki,
Dady ko amsa gaisuwar sadam baiyiba yace ashe dama bakada hankali sadam? Ina tunaninka yatafi? Sadam dahar zaka sanya hannu da duki macen auranka, sadam yace nikuma dady? Dady yace A'a kaniyarkace bakaiba koma menene kazo ina nemanka yanzu, kafin sadam yace wani abu yakashe wayarsa dill,
Sadam yafi wayar da kallo gabansa yana tsananta faduwa tabbas yasan abida yakai kararsa gara ya nemi mafita kafin ya karasa wajan dady da mummy idanba hakaba yasan al'amarin bazaiyi masa dadiba."
Ku saurareni zuwa jimawa idan Allah yyarda🥰
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial33 Chapters
RE:VIVAL
A world where everyone dies at the age of 25...A world where Gods exist among humans....A world where Magic is habitual.....Mortis, a common Adventurer is found to be guilty of belonging to an evil race named-- Darkel. He is led to believe that running is his only way to save his skin, but on that path lies a dreadful truth.A world where everyone dies at the age of 25 should or shouldn't exist?
8 185 - In Serial39 Chapters
The Bird and the Fool
Kesil is stranded very far indeed from his home. Despite a gift from the fair folk that allows him to understand and speak any language, he has very little idea of what’s going on around him (though he likes to pretend he does). But this doesn’t stop him from getting into trouble in the port city of Edazzo, in the ancient empire of Duri, and elsewhere, doing his best to find love, escape snares of ancient magic, and hopefully return home in the end.
8 71 - In Serial18 Chapters
The Last Boss
First, English isn't my first language Second, this story isn't edited or passed by a proofreader, yet. Third, Don't worry that I will finish the story arc, even if there is 1 person reading. Furthermore, I plan the Average Release of each chapter taking from 1 to 2 days. Finally, if you are kind you can comment on the mistake and as soon as I can I will correct. ------ https://imgur.com/a/F4mSA (for whom it may have trouble with the shadows) ----
8 71 - In Serial30 Chapters
Mystic Messenger AU [FF//ONESHOTS]
Mystic Messenger OneShots and Fanfictions :))[ D O N E ] 10/17/16
8 139 - In Serial11 Chapters
The Creature from the Dark (HIATUS)
What happens when the protagonist of a story isn't even remotely human? This story is about a fairly intelligent but ignorant creature and the chaos brought into its simple life by the first encounter with humans it has ever had. I intend to take it fairly slow. I hope you enjoy it. :)
8 79 - In Serial30 Chapters
writer in the dark - neil perry
bet you rue the dayyou kissed a writer in the dark.in which the dead poets have an alluring, quiet girl from their sister school join their club and neil perry takes an interest in her and her writing.-dead poets societyneil perry x fem!oc@lovrsrck 2022
8 530

