《ƘADDARAR RAYUWA》K Page 59
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa (z3iiyyb3rw3r)
#Follow me on
"
_Rayuwannan tadawo abun tsoro😢 Allah ya karemu da sharrin mutum da aljan, dole sai mun tashi mun riki addu'a hannu bibbiyu Allah yakawo mana dauki, Allah yashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah muna rokonka ka kare bayinka a duk yanda suke, addu'a tana da kyau sosai kuma makamice_ idan muka riqi addu'a sai Allah ya dubemu yajikanmu samnan kuma ya karemu."
*(Hasbiyallahu la'ilaha illah huwa alaihi tawakkaltu ahuwa rabbil arshir azim)* wannan addu'a tana da kyau yakamata mu riketa mu koyawa kannenmu da yayanmu, safe rana dare duka muringa Karantata kafa bakwai Allah ya karemu."
Page 59
Saida sawwama tayi 2weeks da haihuwa sannan akayi suna, lokacin jikinta ya dad'a warwarewa,
Idan ka ganta ma bazakace CS bane saboda
tana samun kulawa yanda yakamata daga wajan mahaifanta, duk wani abunda zasu bukata daga mai jegom har jariran dady ya tanadar musu dashi, suma mahaifanta suna iya nasu qoqarin dai-dai karfinsu dan ganin sun fidda diyar tasu,
Yara sunci sunan daddy da mummy wanda mummy ce ta bukaci hakan, kokadan ran mahaifan sawwama bai baci ba tunda dama sunsan sukeda iko da yara,
Kuma sunada ikon zabar musu sunanda yadace asaka musu, ko inkiyar da za'a ringa fadawa yaran ma mummy ce ta aiko da wadanda takeso hamdan da hameeda,
Duk wani iko da gadara da mummy ke nunawa babu wanda ya tanka mata mahaifan sawwama sun kauda kansu kawai dan zaman lpy, fun fiso ayi komai arabu lpy cikin mutumci da aminci,
Har akayi suna aka gama yan uwan sawwama ne da tsirarrun wasu daga cikin yan uwansa mummy bata yarda ta sanarwa yan uwa da abokan arziki da yawa ba sai iyakacin wanda tasan idan basu saniba za'a iya samun sabani, cewarta idan abida ta haihu zata sanar musu,
Sadam ma har lokacin bai saniba saboda bata fada masa ba bata kuma bada damar fada masa ba, dukda kullum sukayi waya da mummu yana tambayarta lpyrs sawwaman,
Yakan tambayane kawai amma yasan ba lallai idan tana zuwa dubasu ba, yadai lura kwana biyu akai-akai mummy ke kiransa awaya duk kuwa da yanda samunsa ke wahala,
Mummy koh tana kiransa ne tanaso taji ko sawwama ta bijirewa umarninta ta sanar masa daga nan sai tasan matakin da zata dauka akanta,
Halima da tasan wainar da ake toyawa cewa mummy ce tahana sawwama fadawa sadam zancen haihuwar ranta yabaci sosai, haushin sawwama ma taji na biyewa mummy datayi kuma tanaji kusan kullum sai sadam yakira waya sun gaisa ko wani lokacin yakan tambayi jikinnta dasauki kawai take amsa amsa,
Yakance har yanzu shiru? Kin wuce EDD dinki sawwama takance eh kawai saita canja zancen, dake bawani jimawa sukeyi suna hira ba wani lokacinma ita kece masa tanajin bacci,
Advertisement
Idan suka fara wayar halima ficewa takeyi daga dakin dan acewarta takaicine yake cikata bataga dalilin sawwama nabiye mummy a wannan shirmenba duk kuwa da tasan mummyn ba sonta takeyiba kuma bawai tayi hakanne da wani dalili ba sai dalilin kiyayyar da take mata,
Halima cikin jin haushin sanyin hali irinna sawwama da dubeta tace dan Allah yanzu haka zakuci gaba da zama?
Kinsan ranarda yagane cewa boye masa kikeyi zaku samu matsala?
Ina fata kinsan hakan?
Ita mahaifiyarsa ce tanada hanyoyi da zata kare kanta dayawa kuma dole yayi hakuri,
Sanyayyen murmushi sawwama tayi da muryarta mai sanyi tace in sha Allahu zai fahimta kuma
Mummy tayi hakanne dan kada yanar karatunsa dinsa yace zai dawo dan suna gabar fara exam na fahimceta,
Cikin takaici halima ta gyada kanta tace ya kamata daga nan bata sake cewa komai ba,
Dady zaune suke da mmmmy a daki phone dinsa tafara ruri yakai dubansa kan wayar no din sadam yagani, hannu yakai yadauka yana fadin kwana biyu munata dafka sabani a tsakani,
Amsawa yayi yakai wayar kunnensa hade dayin sallama sadam ya amsa hadeda gaisheda dady,
Dady ya amsa gaisuwa yana fadin kwana biyu munata sabani ko shekaran jiya daga kira muna meeting na fito kuma na nemeka ban sameka ba, kasan yanayin samun layinku nacan nada wahala ba kamar yanda ku kuke iya riskomu a saukake ba, shiyasa ma wani lokacin idan na tadda takira bana bi,
Dady yace ko shekaran jiyanma danayi trying akan sunan da kacewa mummynku asakawa yaranne sai naga rashin dacewar hakan amma tunda tace kai kayi insisting kuma nakiraka ban samuba ga lokaci yana kurewa shiyasa, amma alokacin dana sameka dako ni sai ahakura da sunana asaka na mahaifinta hakan shine adalci, tunda dai haihuwa kam in sha Allahu yanzu aka farata idan ba'a saka yanzu ba za'a saka wani lokacin,
Cikin rashin fahimtar zancen da dady yakeyi sadam yace dady yaro! Yaron waye kuma?
Dady yace ungo naka sadam yaronnaka kake tambaya wane yaro?
Mummy dake jiyosu a gefe saita fara share gumi ita batajin na sadam dadynsu batasan yanda zai dauki lamarinba, sake-sake tafarayi a cikin ranta na abunda zata fada masa kafin yagama wayar,
Muryar dady tajiyo yana fadin bani minute saika sake kira zamuyi magana da mummynka, gabantane yayi mugun fadi amma tadake,
Dady yajuya ya kalleta yace nasan baki bukatar karin bayani dan kinji me muka tattauna dashi, yakamata kiyimin karin bayani ina saurarenki? Menene dalilinki nayin haka?
Shiru mummy tayi dady yacigaba da fadin meyasa bakya kama girmanki? Kina shiga hakkin yarinyarnan dayawa, kina tunanin Allah bazai tambayeki bane akanta, kokuwa kawai danta auri danki saita zama abun musgunawa?
Mummy da wtaa idea da fado mata tayi wani narai-narai da fuska tace kayi hakuri da nasan abunnan zai bata maka rai har haka toh daban biyewa yarinyar nan ba,
Advertisement
Daddy yace wace yarinya? Mummy ta kara kasa da muryarta tace ita matar sadam din lokacin tana asibiti ita ta rokeni kan cewa bataso na fadawa sadam saboda yana gab da fara exam kuma ysha fada mata cewa tana haihuwa zai baro can kasar yadawo,
Toh nima dai da ban aminceba sai naduba naga zancenta yana kan manya yanzu idan yataho yabar karatunsa ai kaga ansamu matsala,
Daddy yace subhanallahi kaji wani rashin wayo shidin yana shirun jarabawar zai taho dan akansa aka fara haihuwa?
Mummy tace wai hakafa inji matarsa haka ya gaya mata, dady yace toh duk dai da hakan da kun fadamin ni kukayimin bayani nasan yanda zanyi dashi bai isa ya taho ba, kiran sadam ne yasake shigowa dan yamatsu dady yadaga yayi masa bayani, yace yo ai kaine ka sanya suka boye maka ai bazakce zakabar karatunka ka taho ba amma dukda hakanma naga rashin wayonsu da sun fadamin ni nasan yanda zanyi dakai,
Sadam shidai baice komai ba Allah-Allah yake suyi sallama da dady yakira sawwama,
Ransa yabaci kam da abunda sukayi masa amma kuma farin cikin dayake ciki dole ya take bacin ransa,
Mummy tacewa daddy idan kun gama banishi nan Zamuyi magana dady yace barshi yanzu yakira matarsa idan yaso idan sunyi waya saiya kiraki, mummy ta hade rai amma batace komai na dady yana nufin waya da matarsa yafi waya da ita muhimmanci kenan, miqewa tayi ta fita a dakin dan sam abunda dady yayi baiyi mata dadi ba,
Sau biyu sadam na kiran wayar sawwama ba'ayi picking ba sawwama kuwa lokacin tana wanka, yaran kuma suna wajan mama,
Ganin batayi picking ba ya sanya yakira mummy,
Mummy da shigarta daki taji wayarta tafara ruri, ganin sadam ya sanya ta saki murmushi saboda tasan wannan tsakanin lokacin bai isa ace har yayi waya da sawwama ba yazo kuma ya kirata,
Mummy tayi picking bayan sun gaisa sannan tace dama hakuri nakeso na baka, sadam yace hakuri kuma mummy? Mummy tace eh mana sadam matarka ta haihu amma munkasa fada maka, sadam yace bbu komai mummy yanzu gashi ai nasani,
Mummy tace toh ai babu dadi ne dan koni da farko data kawo shawarar banyi na'am da itaba amma data cemin zaka taso ka dawo to shine na amince kasanni sam banason wasa da karatu, bana daukan sakaci akan karatu,
Shiyasa kaga kwanakinnan na dage da kiranka wani lokacin haka naketa kira bai shiga ba amma dake abun yana raina inaso na fada maka shiyasa nake nacewa har saina sameka amma kuma saina kasa fadar,
Sadam yace mummy karki damu kanki bbu komai, mummy yaya abidar take?
Lpynya qlau tana dakinta sadam yabata amsa mummy tasake cewa kakira matar taka ne?
Kai tsaye sadam yace mata A'a,
Dadi taji a ranta, tace toh kakirata mana sadam; saida yadanyi jimm sannan ya amsa da toh atakaice dagajin yanda ya amsa maganar kasan ba har cikin ransa ba, ba karamin dady mummy tajiba dan tasan ko babu komai sai sun sami sabani tsakaninsa da sawwama,
Sallama yayi mata ya kashe,
Bayan sadam ya kashe ya ringa tunanin wani lokacine ya fadawa sawwama haka dahar zata sanarwa iyayensa tasan iyeynsa bbu abunda sukeso samada karatu kuma rashin maida hankali da zaiyi akan karatunsa zaisa su iya samun sabani, yadauka koda ya fada mata haka ita mai boye wane karta sanarwa mahaifansa dan kada suga kaman yana musu wasa da hankali kokuma ya fifitata akan muradinsu,
Tunane-tunane kawai sadam yakeyi bai sake daga waya yakira sawwama ba yana cikin tunanin abida wacce mummy tatura text akan taje wajan sadam ta dauke masa hankali ta shigo dakin, tayi nasarar dauke masa hankalin kuwa gabaki daya yanda bai sake bi takan wayarsa bama balle kiran sawwama,
Itako data dawo daga wanka batabi takan wayarta ba dan bakowa ke kiranta ba sai sadam shikuma bai saba kiranta a dai-dai wannan lokacin ba, yawanci lokaci daya tsayayye wanda yake kiranta,
Har dare bai kiraba bata dauki hakan a matsayin wani abunba ta kwanta tayi baccinta kawai,
Washe gari ma harta cire rai da kiransa sai kuma gashi yakira,
Murmushi sawwama tayi alokacinda taga sunan sadam daukan wyaar tayi a hannunta tayi picking ta kara a kunnenta da sanyayyar muryarta tace Amincin Allah ya tabbata agareka."
Kwanaki da yawa babu posting wasunku daga ciki sunsan cewa banda lpy yayinda wasunku basusan hakanba, amma duk da haka ina mai baku hakuri akan rashin samun update, Allah yakara mana lpy Amin."
Ina kuke masoyana masoyan rubutuna🥰 hajiyata kin karanta bibiyata akeyi? Nasan bazaki kasa karanta Y'ar fari fa? Dakuma wanda nake rubutawa yanzu Qaddarar rayuwa? To yaya kikaji salon🥰😍 ya qayatar koh? hajiyata wadannan aiba komai bane somon ta6ine cikin shirinda nayi na nishadatar daku hajiyoyina manyan mata Ku biyoni cikin littafina na YARIMA FAYAD🥰 wannan littafin salonsa daban yake akwaia zazza6ar qauna🥰😍 ciki dana tanada muku, 200kacal zaki sameshi, ga dadi ga sauqi🥰 Don neman qarin bayani,
tuntubeni ta wannan no 08161146563,
Kokuma ki biya kudinki ta wannan accnt 0003075326 zainab m bawa JAIZ BANK.
Ku antayo daga ciki😊😌
Hajiyata kada ki bari abaki labari."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial32 Chapters
Null un Voided
Mark Telod hated. This wasn't your normal petty grievance. No this was something no sane person should hold within themselves. Hatred should be released, but Mark? No Mark contains his anger. His hatred can be traced as far back as his own childhood, and oh does he loathe humanity. Now he's given a chance to finally express himself…. So how will humanity deal with the calamities presented before them? Will they overcome them, and rise as one united force? Or will they crumble and fuel Mark’s ever burning hatred…..
8 161 - In Serial32 Chapters
True World
What if you had the ability to learn anything and everything almost instantly? What if you were able to use those knowledge with perfection upon learning them? Hm? You would be able to become a genius? Maybe even become world famous? That's true. But let's broaden your horizon a bit. What if that ability grants you the power to """"conquer"""" a whole world? Nay, worlds, with a plural? A boy who was mysteriously shot and on the brink of death is granted a power far beyond that of a human. As he was about to die, a black box appears in front of him and asks him to choose between Life and Death. As he selects his fate, a piercing light envelops him... *Light gore/death scenes, a few mature languages. Status: Dropped
8 147 - In Serial23 Chapters
Sentinel of the Deep
New chapters Saturday, Monday and Tuesday When Thom's best friend goes missing in the lake in the middle of Juniperville, the townsfolk are out for blood. Thom is the only one who knows about the creature who came out of the lake, who shape-shifted into the young woman who abducted his friend. Seeking answers, he travels to Scotland, where he is invited to join the Modern Folklore Investigation Team (MFIT) as an intern. As he gets closer to an objective truth about the nature and intentions of water beasts, he learns that he has a rare and special power, one with the potential to bring back his friend from the deep. The only one who knows about Thom's power is his MFIT colleague Ondine, who has a secret of her own - one she has repressed for years. Even as Ondine urges Thom back to Juniperville to a reckoning with whatever it was that stole his friend, she realizes that she, too, must face up to the truth of her legacy, and its power.
8 196 - In Serial14 Chapters
The General's Manor Young Concubine Survival Report/將軍府小妾生存報告
Автор - Фэн дэ Линдан/風的鈴鐺Оригинал - http://www.jjwxc.net/onebook.php?novelid=2575677Анлейт (разрешение получено) - https://spicychickentranslations.wordpress.com/novel-translations/tgmycsr/Я думала, что я буду императрицей! Мне оставалось лишь схватить свою удачу за хвост и стать его истинной любовью. После этого мы бы поженились, завели бы детей. Обязательно мальчика! А потом бы мы жили долго и счастливо. Разве не все подобные истории заканчиваются так?!Но вышло так, что я застряла в самом начале, ведь моя удача это...Ах, генерал! _(:з"∠)_ Авторская заметка: Эта работа имеет альтернативное название "Га-га-га" (нет).П/п: авторская заметка отсылает нас к поэме Ло Биньвана "Воспеваю гуся".
8 188 - In Serial20 Chapters
Soulmates who weren't meant to be
I saw the world in your eyesTo know that we could've been so much more Than what we are right nowIf only We could've met each otherAt the right time
8 125 - In Serial71 Chapters
My famous boss (gxg)
In the last 5 years of working behind a desk in the New York Times, Lena Adams sees an opportunity to be an assistant to one of the most paid actresses today.What will come out of it...Highest rankings:#1 lesbian#1 Scarlett Johansson#3 Fanfiction#62 wlw#1 Scarjo#34 Marvel#3 Black widow
8 140

