《ƘADDARAR RAYUWA》K page 62
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Mahaiafin nabeela ya isa izuwa ga fada bayan sun gama tattaunawa data tarasu mai martaba ya nemi ganinsa a killace,
Mahaifin Nabeelah yanata sake-sake cikin ransa ko meyasa mai martaba keson ganinsa? Ko zancen komawar nabeela zaiyi masa tunda izuwa yanzu ya tabbatarda labarin samun lafiyarta ya iso garesu, amma wannan karon zai roqi alfarma wajan mai martaba kan raba auren yarima da nabeelah kuma cikin ransa yanajin rashin dadin hakan domin shi kansa yasan mai martaba mutum ne, mutum ne gari wanda bbu wanda ba zaiso hada zuri'a dashiba bama ga mulki da Allah yabasu ba, A'a halayensa na gari da tausayin duk wani wanda yake kasansa, Gabaki daya zuri'arsu mai martaba sun kasance mutane nagari masu son takalawansu atarihin kasar kaff sarakunan da sukayi mulki sun kasance masu addini sanin yakamata Allah ya hore musu sani, masana ne na gaskiya gabaki daya illahirin zuri'arsu malamaine, Acikin gabaki daya kaff sarakunan anyi ittifakin bbu wanda yakai mai martaba sarki na yanzu sani da iya gudanar da mulkinsa ta farkin addini,
Cikin y'ay'ansa kaff mahaifin yarima shine yafi kowa wanda ake saka ran zai zama sarki mai adalci kamar mahaifinsa koma fiyeda shi, amma qaddara ta afka masa sai dai yabar baya! Yabar yarima haaliifaa wanda mai martaba ya dauki son duniya ya daura masa sai akaci sa'a yadauko hali irin na mahaifinsa da kakansa,
Yarima ya kasance mutum mai gwarjini fara'a da ilimi da sanin yakamata,
Bayan Abunda yafaru da mahaifinsa sai soyayyar mahaifinsa da mai martaba yake yi masa ya tattaro yadawo dashi akan yariima haliifaa."
Toh in banda lalura a gabaki daya duniya waye bazaizo hada zuri'a da mai martaba ba, waye bazaizo hada tsatso da dasu ba, zuri'a ce wacce ta shahara a gabaki daya duniya, shahara irinta ilimi na addini, mahaifin nabeela yana mai baqin ciki da takaicin wannan al'amari da yazo dashi zuciyarsa tayi nauyi, yanaji kamar bakinsa bazai iya furta neman rabuwa da wannan zuri'a da Allah yabasu daukaka ba, daukaka irin tasu bakowa ke samun irinta ba,
Zaiyi alfahari ace yau jikansa yafito daga wannan tsatso jikansa yazama wanda al'umna zasuyi alfahri dashi, ajiyan zuciya ya sauke yayinda zuciyarsa takeyi masa nauyi."
Gyaran murya mai martaba yayi ya dubi mahaifin nabeelah yace dafarko dai kasance amintacce mutum nagari mai sanin yakamata, a halinda yarima yake ciki ka dauko yarka mai cikeda nagarta da nutsuwa mai ilimi ka aura masa, sannan kuma ka sanyata tayi biyayya ga wannan aure, bazan taba mantawa da wannan halaccin naka gareni ba, kayimin alkahiri kuma shi alkahiri dan aikene in Allah yayarda alkahirinka gareni wata rana zai dawo gareka,
Mahaifiyar yariima ta sameni ta roqi wata alfarma gareni nazauna nayi tunani dakyau, nunfashi mai martaba yaja sannan ya gyara zamansa irinna manyan mutane yace nayi tunani akai sosai al'amarine mai wuyar fassaruwa al'alamarine mai nauyi a fatar baki yayinda zai iya sanyawa zuciya ta kasa samun nutsuwa zai shigarda ruhi damuwa da dimuwa amma duk wannan abune na wani dan lokaci saboda komai mai wucewa ne, shiru mai martaba yayi yayinda ya jefa zuciyar mahaifin nabeela cikin rudani domin yakasa gane yanda ya dosa, mai martaba yaja numfashi yace tasameni da zance akan araba auren yarima da nabeela koda na tambayeta dalili tacemin ita mahaifiya ce akwai lamarin da Uwa kawai zata iya fahimtarsa,
Advertisement
Tabbas zancenta hahkane Uwa itace takeda mahanga dayawa wacce take hango halinda yayanta zasu shiga, tayimin wannan magana ce a matsayinta na mahaifiyar nabeela ba yarima ba,
Na fahimceta kuma nace zan nemeka mu yanke shawara domin mai shawara tasa bata baci, kasa dakai mahaifin nabila yayi duk yaji babu dadi amma tabbas hakan shine abunda yakamata, domin wannan hali data shiga sun razana sosai idan har rabauwarsu shine silar samun lafiyarta, afili kuma yace Allah yasa hakan shine mafi alkahiri ina Adda'u Allah yabata miji nagari shikuma yarima Allah yabashi lafiya, mai martaba ya amsa da amin."
Anraba auren nabeela da yarima batareda son ran kowa ba sai dan babu yanda aka iya al'amarinne yayi wani iri."
Umma da ummi sukaje gidansu nabeelah bayan sun gaisa mahaifiyarta na zaune a gefe itama duk yanda taso raba auren bayan an raba saida taji babu dadi,
Kowannensu yayi shiru dakin yayi tsit yayinda nabeela idanuwanta suke zubda kwalla ganin umma yasake tada mata mikin son mijinta,
Ummi tayi gyaran murya tace toh Alhamdulillah mun gode Allah da kika samu lafiya nabeela muna fata nan gaba Allah ya bawa yarima shima lafiya mungode da halin girma da karramawa hadeda zama da kikayi damu tsakani da Allah hakika ke jarumace nabeela dole a jinjina miki Allah ya miki albarka,
Nabila kanta yana kasa bata iya amsawa ba mahaifiyarta ce ta amsa, dakin haka yaqara zama shiru sai can umma taja dogon numfashi tadubi nabeela tayi murmushi tace nabeela ke kin kasance y'a ce gareni ban daukeki wani abun kasada haka ba, kiyi hakuri na yanke shawara batareda neman izininki ba, mu masu laifi ne agareki dafarko munyi miki aure batareda son ranki ba sannan muka raba auren batareda izininki ba, amma dukda hakan kin kasance mai biyayya agaremu, ni uwace zan iya fahimtar irin halinda kike ciki zan iya jurar ganinki kina bautar aure amma bazan iya jurar ganinki kin cutu ba, bana fata nasake ganinki cikin irin wannan hali da kika kasance watannin baya zuciyata bazata iya daukaba, da wanne zanji? Da cwion da yarima yake ciki? Kokuma da ciwon ganin ki cikin wani yanayi?
Allah yagani banso rabuwa dakeba amma kuma yazama dole shiru umma tayi ta goge hawayenda yake qoqarin zuba mata tacigaba da fadin kiyita addu'a Allah yabawa yarima lafiya har indai da rabon zamanku agaba sai kiga anzauna idan kuma bbu Allah yabaki miji nagari,
Nisawa umma tayi tace bazan kasance mai son kaina ba nabeelah zanje zanci gabada kulada yarima har izuwa ranarda Allah zai bashi lafiyaa, dukansu wajan jikinsu yayi sanyi bakyajin komai sai shasshekan kukan nabeela da yake fitowa a hankali, ummi ne ta katse shirun da fadin ai ba'a rabuba in sha Allahu za'a cigaba da zumunci ai anyi zaman dadi zama akayi na amana nabeela yarinyar kirki ce kwarai da gaske Allah yayi miki zabin alkahiri cikin rayuwarki,
Jikin mahaifiyar nabila tabbas yayi sanyi da badan ace ciwo ba tabbas nabila tayi sa'ar dangi tashiga ahali wanda suka san me ake nufi da mutuntaka, tabbas sunason nafila so na hakika taga hakan cikin kwayar idanuwansu, tabbas taji babu dadi gameda maganganun da ta fadi a kwanakin baya domin kuwa sai yanzu tasan irin karamcin da suke dashi,
A yanda yarima yake tasan dubannin iyaye zasuso su bashi yayansu ya aura koda kuwa wani abun zai samesu, sanin yakamata irinna mahaifiyar yarima ya ratsa zuciyarta matuka,
Advertisement
Su umma sun dade agidan sannan suka tafi cikeda kewar juna,
Hajiya babba burinta yana kan cika yanzu hankalinta ya kwanta kasancewar tasan yanzu yarima shi kadai yake bbu wata wanda zata taimaka masa sai mahaifiyarsa wannan kuma huruminta daban, ciwon yarima nada wasu sharruda wanda zamansa da mace ya kasance hadarine a tattare dasu,
Hajiya babba tayi zurfin tunani sosai sannan ta sanya aka kira mata waziri, bayan waziri yagama kwasar gaisuwa hajiya babba ta dubeshi tace" Gameda wannan yaro haalifaa shin baka tunanin abarshi haka yafi? Batareda aure ba, sanin kanka ne munji kwakwa kafin musamu abubuwan da mukayi su kama jikinsa, yaran yanzu ba abun yarda bane garin neman gira karmu rasa idanuwa saboda yaran yanzu idanuwansu abude yake ba kowacce bace zata ganshi ta barshi haka nan kamar yanda wannan tayi dan nasha matukar mamaki da wannan yarinya (nabeela) ta kasance babu wayo? Yaran yanzu sunada son duniya ni ban yarda da kowa ba bayan mu kar garin neman duniyarsu su bata mana tamu duniyar kuma kasan abunda hakan zai iya janyowa, shin baza'abar haalifaa haka ba?
Waziri yace tabbas kince wani abun Ranki shi dade kina da zurfin tunani cikin kaskantar dakai dason samun wajan zama yace abunda kika hango mu bazamu iya hangoshi ba, kinyi gaskiya." Hajiya babba ta gyada kai tace Yawwa dama maganar kenan sai asan yanda za'ayi atoshe duk wata gaba da zaisa ayi zancen qara yimasa wani auren, waziri yace ki dauka tamkar angama hajiya."
Hajiya suwaiba itama tayi murna jin rabuwar nabeela da yarima da yawan mutane wanda dama suna da wata manufa cikin zuciyarsu sunyi murna yayinda wasu daga ciki suka tausayawa halinda yarima yake ciki, mutane kowa da abunda yake fadi wani suna kallon laifin nabeela da rashin hakuri na rabuwa da mijinta da tayi dan yanada lalura wasu kuma sunga kokarinta matuka dahar ta iya auren yariima kuma tazauna dashi ahaka mutane kenan, su mutane ahaka suke duk kaiwarki da kyautatawarki sai wasu sunga laifinki yayinda duk yanda kika kai da bakin hali wasu sai sun yabeki."
Wajan su umma rayuwa takoma irin ta baya domin andawo da yarima shashinta yabar sha shin mai martaba ita taci gaba da kula dashi ummi da ruma suna taimaka mata,
Jikin yarima wata aga canji wata rana kuma yayi tsanani umma ta tattara komai ta mikawa ubangiji da zubawa sarautarsa idanuwan, amma cikin zuciyarta bata cire ran cewa wata rana yarima zai samu lafiya ba, tanada yaqini akan hakan in sha Allahu."
Nabeela tashiga wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa hausawa sunce sabo turken wawa, nabeela ba wata shakuwa sukayi da yarima ba ba magana suka taba musaya tsakaninsu ba, bakuma kulawa da soyayya ta samu daga gareshi ba hasalima shi da zamanta da rashinsa duk bai saniba amma ta tsinci kanta cikin kewarsa, kullum cikin tunani wani lokacin har takan koka, ganin hakan yasa mahaifinta ya dagata daga garin gabaki ko zata samu ta manta dashi, tadawo da rayuwarta kamar ta kowa."
______________________________
Wajansu sawwama kuwa hamdan da hameeda sai girma sukeyi sun kara wayo sosai sunyi bul-bul abunsu gwanin sha'awa akai-akai dady yake musu aike sammam yana sanya mummy taje dubasu koda ranta bayaso tana zuwa tunda dai tasan koda taqi sawwama bazataqi jinin sadam ba, harda madara sawwama take hadawa yarn domin suna samun karancin nono, mahaifinsu kuwa koda yaushe da zarar yasamu hutu to yana kan wayarsa video call yana kallon matarsa da yaransa a kullum ji yakeyi kamar yayi tsuntsu ya taho ya qosa yaga yaransa yana matukar kewar matarsa, duk da kasancewa anan wajan itama abida tana bashi kulawar daya dace da taimakon mummy da take koya mata abubuwa kala-kala wanda zatayi danta kula dashi kafin su dawo ya kasance ta sace zuciyarsa, ita abida ji takeyi kamar su zauna acan domin zamansu haka su kadai yafi komai yimata dadi bataso sawwama ta qara shigowa rayuwarsu, tafiso tayi nesa dasu dan yanzu tana samun kulawar data dace wajan mijinta, tanada tabbacin idan sawwama tana nan bazata samu kwatankwacin wannan ba,
Abida ta matsawa mahaifinta akan ya sama musu aiki acan ita acan takeson ta zauna,
Ya shawarci mummy, mummy tayi murna sosai dan ita duk wani cigaba tanaso taga yasamu yayanta, kuma gara yatafi yayi nesa da sawwama ko hankalinta zai kwanta, batareda bata lokaci mahaifin abida yafara nema musu aiki acan."
Lokacin da aka deba na karatun su sadam har wuce kullum suna waya kuma bataji yana mata zancen dawowa ba, sawwama tayi kewar mijinta amma haka ta daure ta zubawa sarautar Allah idanuwa mahaifanta dake basusan dama aihini lokacin da aka deba na dawowar sadam ba yasa basu damu ba,
Har yaran sawwama suka fara zama sadam bai taba yimata maganar dawowa ba amma suna waya kuma bbu wani canji data gani agareshi, soyayyar dayake nuna mata bata raguba saima qaruwa da takeyi kullum,
Kwana daya harda wuni sawwama bata samu kira daga sadam ba kuma dama yawanci shi yake nemanta sau dayawa idan ta nemeshi ba samunsa takeba amma hakan cikin damuwa tayita nemansa wayar bata shiga, aranar har mama saida tagane sawwama na cikin damuwa amma tunda bata nemi tasani ba sai ta kyaleta itama bata nemi ta fada mata ba, saboda tasan da tanaso ta sani toh da ta sanar da ita,
Bata sani ba ko sun samu matsala da mijinta ne idan hakane kuma bata bukatar sani domin wani lokacin bai kyautuba a saka iyaye cikin yar qaramar matsalar gidan aure wanda kedashi kun isa ku magange kayanku, dan haka mama taja tayi taja shiru tana addu'a Allah yasa ba wani abun da zai cutar mata da ya bace, har izuwa magrib haka sawwama take sumu-sumu dama gata da sanyin rai sai abun ya hadu tadawo kamar wata marainiya, bayan an idda sallar magrib mama ta sameta a dakinta tazauna bakin gado tadauki hamdan tana fadin dan lukuti kenan wannan yaro yafi karfin goyonki hafsatu, murmushi sawwama tayi tace saina barmiki shi ai mama, itama mama murmushin tayi tace nagode kurike kayanku, a wajan mama ta zauna har bayan isha'i saida taga sawwama tasake kamar bbu wani abunda yake damunta kafin tatafi dakinta lokacin baba yadawo."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial167 Chapters
Chronicles of Sora: Ruler of Rules
Some find him an idiot, some find him a genius, some find him weak and others strong. He has been close friends with Tori (the vampire), fallen for (and been beaten up by) Seoyoon, and has even been trained by the Geomchis - yet none of them will remember him. This is the story of Sora and his adventurers in the game that no one knows about Ruler of Rules. Author's note:1. Don't kill me for the typos etc - I know there are mistakes just comment and let me make the corrections.2. Don't kill me for other reasons - Comment and explain to me where I go wrong. I too want this to be an awesome story.3. Chances are either you will dislike this FF or love it. Very few will find the middle ground. Either ways, do read till chapter 17 and let me know if you are enjoying the journey!4. I hope you laugh lots and enjoy the story!
8 161 - In Serial12 Chapters
Soul of the Academy.exe
Adam Geoffrey is a programmer for a minor software company by day, and an avid Time Management Strategy gamer by evening. His life is tolerable, but he wishes he could find a way to make a living with his true talent in management, rather than coding.Then, he gets an offer from an unlikely and suspicious source...
8 183 - In Serial11 Chapters
Clashing Worlds (Hiatus)
Zetsu Nozomu is a 13 years old middle school student, Lives in Tokyo Shibuya district, Japan together with his dad. One day he was walking home from school, when he was about to cross the street. A truck came at him, but just before he was hit, he teleported to weird place, what seemed to be a destroyed city. As Zetsu was looking around confused, a man wearing a cloak suddenly jumped from a destroyed building and appeared right before him, starting an adventure that might put an end to his unsuccessful daily life as a self proclaimed failure. Follow Zetsu Nozomu as he discovers his ability to travel between his world and other dimension as he trying to find answers while exploring the new alternate version of Japan.
8 459 - In Serial6 Chapters
Infested
One billion people from one hundred thousand universes have been dropped onto a singular planet five times larger than Earth. In the corner of their eye were three numbers: 1,000,000,000. 15. 10. Nobody could figure out what it meant until fifteen years after the initial transportation, as out of the blue, a message repeated itself in their minds for twenty-four hours. “Only ten can return. The rest will die. There is no time limit,” Following the global message, genocides ran rampant, with established friendships broken, families ripped apart, blood alliances betrayed, and leaders felled in seconds. How? [The Evgnomon] The Beholden; hidden throughout the realm were artefacts: weapons, information, tools from beings and societies of a higher plane. It was up to the humans to scour the land and take them by hook or by crook if they ever wished to go back. Whisked into this world as a mere babe, I suppose it was lucky I didn’t die in the chaos. But as I stare into the rotten, tattered pages of the accursed book laid upon the pedestal in front of me; and the unnerving gaze of our professor trained onto the back of my head silently pressuring me to become the avatar of grotesques unspeakable and undecipherable to the human mind. O, how I wish I did...
8 87 - In Serial16 Chapters
Red and White's little conversation corner (Side-story)
''Hi! I'm Red :D'' [And I'm White...] ''It's nice to have you all read our conversations :)'' [It's not.] ''It is.'' [IT'S NOT!!] ''YES IT IS!'' [NO IT'S!!....oh we're still typing...] ''So......this goes into the description or not'' [Your choice] ''Fuck it...it's going in'' [Welcome......to a shit show] ''Imagine the jurassic park music with that :D'' [Oh my god that'd be awesome] ''...we're still on the description...'' [Oh...to the story now] ''Oh right....I...we can't update this as regularly as the other story so....just read the other one while you wait it's RE: Books.''
8 81 - In Serial7 Chapters
Jump-Verse: Prelude
After the events of Prometheus' takeover of the Jump Worlds and Earth, All Jump worlds went back to normal, or as normal as they could get, anyways. But one day, A teenage boy who longs to once more see his favorite heroes uses the power of an umbras cube to make his dream come true. Not realizing the full extent of its power, he's able to fulfill his wish, but accidentally brings back some of the most feared and deadly enemies back, with some new ones too. Will he be able to help Jump's greatest heroes save the world once more, or has he just doomed the planet?
8 118

