《ƘADDARAR RAYUWA》K page 65
Advertisement
**
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 65
Dawa kake waya? ta jefo masa tambaya kai tsaye cikin gadara ko juyowa sadam baiyiba yabata amsa da fadin bana tunanin kina bukatar jin wannan amsar, a kufule tabi bayansa tana fadin da wannan mayyar kake waya koh? Bai kulataba yaci gaba da tafiya batareda tabar bin bayansa ba tace "Sadam dakai nake magana fa kana wucewa wannan rashin adalcine kana tare dani kana waya da ita acan gefe wai ance maka zuciyar kashi ne dani? Na tabbata da atare da ita kake bazaka taba yarda ka kirani ba,
Juyowa sadam yayi yace abida muryarki tana cikakin kunne idan kina magana dani ya kamata kina sassauta muryarki danni ba danki bane karki ga mummy tana yimin fada kema kice zakina min duk wani abunda ranki yakeso bazan lamunta ba ya karashe maganar hadeda furzarda huci da alamun ransa ya matukar baci, abida cikin fushi tace menee bazaka lamunta dinba?
Nice dai bazan lamunci rashin adalci ba, wannan wawiyar matar taka akanta kake yimin duk wannan abun, toh sai dai ka zaba koni ko ita,
Haka sadam yaji maganar kamar wacce take zolayarsa ya zaba ko ita ko Sawwama? wata yar dariya sadam yayi cikeda mamaki yace what?
Inzaba koke ko ita? Kinada hankali kuwa?
Itafa ni naganta nace ina sonta amma kefa?
Bance ina sonki ba dole aka sani na aureki dan babu yanda na iya, duk da hakan kina tunanin har matsayinki yakai ki hada kanki da ita? Wacecec ke tukunna ma?
Mtsww yaja tsaki Sadam baida zafin rai amma da gaske Abida takeso ta maidashi mai zafin rai,
juyawa Abida tayi tafice a dakin ya zauna a bakin gado hadeda wullar da wayarsa yaja wani huci hannuwansa buyu yasanya ya rufe fuskarsa, sam bayason raini baya lamuntar raini ko wajan kannensa, Abida tana kona masa rai idan tanayi masa abu cikeda gatsali itafa matarsa ce yakamata tasan irin kalaman da zata dinga fada masa, bai ankareba yaji sallamar mummy da sauri ya dago ya dubeta hijabi a jikinta har kasa ga dukkan alamu tafara bacci amma cikin darennan abida taje ta tasota da wani kallo tabishi kai cikeda ma'anoni da dama sannan tace "Sadam fito falo muyi magana dadynku yana kiranka, miqewa yayi cikeda takaici da baqin ciki yabi bayanta,
A falo ya samesu harda dady sanyeda jallabiya yayinda abida take zaune a daya kujerar dake gefen dady sai wani shesshekar munafurci takeyi,
Ya zauna akasa gefe kusada dady, dady ya dubeshi yace "Sadam me yafaru?" Matarka ta kawo kararka sadam cikin darennan? Koma me tamaka bazaka bari izuwa safiya ku fahimci juna ba? Iyyeh! Meye haka ne wai Sadam shin kai rashin zaman lafiyar dadi yake maka ne? Yakamta ka ringa adalci a tsakaninsu,
Idon sadam ya kada ya ciko da kwalla ya dago ya dubi mahaifinsa yace dady ka yarda da abunda tafad'a maka kenan? Shikenan tana zuwa ta fada saika zauna akai batareda ni an tambayeni ba?
Miqewa sadam yayi yace tunda ba antara mu aji abunda yafaru ta bakin kowa bane babu amfanin zamana anan,
Ganin yanda ran Sadam ya baci ya sanya dady yayi saurin kamo hannunsa yana fadin haba Sadam haba bawai ma goyi bayanta bane kawai ina maka fada ne, shiru sadam yayi baice komai ba ransa yana tafasa mummy tace toh kuma har me akayi na harzuqa haka? naga fada kawai ya maka sadam yace "dady ka sakeni natafi sam mummy bata ganin laifin yarinyar nan komai tayi dai m-dai ne a wajanta, dady yace " yi hakuri naji dawo ka zauna, dawowa sadam yayi ya zauna amma har lokacin ransa yana bace, "inajinka sadam yimin bayani dady yafadi cikin sigar lallashi,
Advertisement
Nisawa yayi kafin yace yau nadawo inaso naje naga matata da yarana tsawon lokaci bana tareda dasu amma haka aka hanani, yanzu meye laifi dannyi waya da ita? Tanada hakki akaina kuma inada damar yin waya da ita naji lafiyarta, dady menene aibu ayim hakan? An hanani ganinta wwayrma baza'a bani wannan damar ba?"
Bayan haka mafa agabanta nayi ba saboda gudun karta ga kaman nayi mata cin fuska yasa nafita wani waje daban, amma wannan yarinyar ta tsaya tana fadamin magana duk yanda taga dama, ni nake aurenta ko ita take aurena?
Wai tana cemin na zaba tsakaninta da sawwama dama ni nace ina sonta? Ko a zatonta auren hadi yafi na soyayya n,,,,,,,, saurin dakatar dashi dady yayi yace "ya'isa haka toh menene kuma na fadin wannan maganganun, kuka abida tasaka tana fadin "kaji koh? Kunji abunda yake fada ba,
Mummy aharzuqe tace "kai sadam menene hakan? Wannan ai wulakanci ne, yanzu wnacan kazar har takai ka wulakanta yar uwarka akanta? Anya kuwa Sadam anya lafiyarka kalau? Kana tunanin bazaji zafin abunda kayi ba shin ita ba mace bace da zakayi waya da wata gabanta,
Sadam yace ba gabanta nayi ba kuma bada budurwa nayi waya ba matata nakira,
Kirji mummy ta dafa tace eh lallai ba lafiya ba sadam mai biyayya amma yanzu muna magana kana maida mana har kana muna maka magana kana tashi zaka tashi zaka bar wajan,
Dady ya daga mata hannu dakata tukunna aiba yayi hakan da wani nufi bane karki juya lamarin, shieu mummy tayi dady yace" sadam waye ya hanaka zuwa ganin matarka? Sadam ya dago idons aya dubi mummy, mummy ya kawarda kansa gefe yace mummy ce tace nagaji basai najeba, da mamaki mummy ta dubeshi dan batayi tunanin zai ambaci sunanta aciki ba, dady yadubi mummy yace "wannan ba dalili bane da zaisa a hanashi zuwa ganin iyalinsa kekuma Abida bakida hujja da zakice bazai kira yaji lafiyar iyalansa ba, bbu wanu dalili da zaisa ki hanashi ganin iyalansa saboda son zuciyarku,
Yadubi mummy yace "bake kike auran masa mata ba kibarshi yayi ikonsa da iyawarsa akansu idan kikaga ya aikata ba dai-dai ba saiki kwabeshi, su dukansu matan yayanki ne, na sha fada miki ki dauke idanuwanki daga gidan yaronnan,
Kai kuma Sadam karka sake nuna wata tafi wata cikin matanka haka babu kyau, ke kuma kiyiwa mijinki biyayya ki dauke kanki daga mu'amalarsa da dayan matarsa tanada hakki akansa kamar yanda kikeda hakki akansa bazan lamunci daya ta cutarda daya a cikinku ba ni wajena bbu wacce tafi daya dukanku matan Sadam ne na daukeki kamar yanda na daukeshi, dady yayita musu fada dukansu babu wanda yabari sannan yadubesy yace "kuje ku kwanta karna sake jin waji abun yataso sannan gobe da sassafe kuwuce gidanki ku tafida masu aiki da hassana da hussaina su gyara muku,
Allah yamuki albarka ya qara muku zaman lafiya da hakuri da juna kutashi kuje, amin sadam ya amsa sannan ya miqe Abida ma ta miqe jiki a sanyaye tabi bayansa,
Suna wucewa yadubi mummy cikin jin haushinta yace "kingani kinga abunda kika jawowa kanki? Kinaso ki zubda kimarki ta uwa a wajan danda kima haifa na fada miki a kullum kifidfa idanuwanki daga raywuar m yarannan amma bakyaji, yanzu in banda abunki menene na hanashi zuwa ganin matarsa? Mummy wacce kr cike damm zuciyarta kamar ta fice ta fado dan bakin ciki ga sadam daya bata mata rai ga kuma dady sai sauke mata masifa yakeyi, afili tace "shin menene aibuna dan naso yarona ya huta naga sun dawo ga gajiya shiyasa na nemi ya huta, dady ya murmusa yace karki fiye son kanki dayawa kefa kinaso kiga danki kusada ke ya kwanta ya huta amma shi bakiso ya kalli jasa yayan da koda sau daya hai taba sanyasu a idanwansa ba, tashi muje mu kwanta dare ya tsalla amma itama yarinyar nan yakamata kija mata kunne ba komai ne ake kaiwa kara ba abubuwa dayawa ma'aurata sukanui a tsakaninsu su shanye batareda wani yaji kansu ba, idan tana irin haka zata fitar masa akai ne ba'aso mace tacika qorafi dayawa. Ita dai mummy batace komai ba tayi shiru kawai abubuwa dayawa take ayyanawa aranta wanda Allah kadai ya sansu."
Advertisement
Suna shiga ciki Sadam ya dubi abida yace "rashin kirkin ki har yakai kibi mahaifana ki tashesu cikin darenan koda yake ba rashin kirki bane rashin wayo ne dan a iya tsawon rayuwata banga mace maras wayonki ba, kuma anyi na farko anyi na karshe karki sake hadani da iyayen, narai-narai abida tayi tace kagani koh ina yanzu dady yayi mana fada shine bayan mun shigo zaka sake yabamun baqara magana,
Kwanciya sadam yayi bai ko sake kallonta ba."
Washe gari da safe baba bai fita kasuwa ba bayan sun gama karin kumallo sawama tafito ta samesu zaune kofar daki shida mama da sauran yan kananun yaran wanda ya kasance yau weekend basu kaiga zuwa makaranta ba,
Zaunawa can gefen baba tayi ta gaidasu cikin girmamawa, baba yace mamana jiya ummi ta sanarmin da dawowar mai gidanki tunda yadawo babu amfanin zaman sai kuma ayi maganar komawa ni ayanda naso ki koma dakinki yau toh mamanki tace abarki izuwa ranar litinin ko talata nace mata duk yanda kukayi Allah ya kaimu da yau dakuma litinin ko talata duk dayane a wajan Allah, idan da wasu abubuwan da kike bukata saiki sanar dani idanna shiga kasuwa saina taho miki dashi,
Allah yamiki abarka ko qara hakuri shi zaman aure dan hakuri ne ki zauna da kowa lafiya, kuma zuciya daya, sawwama kanta na kasa tace "in sha Allahu baba, da hantsi baba ya shirya ya tafi kasuwa yayinda mama tacewa sawwama ta shirya izuwa jimawa su tafi lallae washe gari idan Allah ya kaimu sai taje kitso ranar litinin kuma su halima suke su gyara mata gida zuwa talata sai ta koma."
Sawwama ta kira Sadam bugu biyu ya dauka da sallama ta amsa hadeda fadin "ina kwana yaya sadam? Lafiya qalau Sawwamaty kun tashi lafiya? Ya yarana? Lafiyarsu qalau ina ina lafiya tabashi amsa atakaice sannan ta daura da fad'in 'yaya Sadam inaso zanje lalle, lalle! Sadam ya maimaita Eh sawwama tace sannan ta daura da fadin naso alokacinda zaka dawo zanyi maka ado na lalle da kitso yanzu zan cika alqawarina dan nasan kitso da lalle suna daya daga cikin abunda kafiso. Murmushi sadam yayi sannan yace tabbas barinma idan ya kasance lallen a fatarkine kitson kuma a kanki suna matukar yimiki kyau, yar dariya tayi najin dadi sannan tace "aikuwa zanyi maka kwalliyar na lalle da kitso domin nishadantar dakai kuma duk wani abunda kakeso nima shi nakeso tayi maganar cikin sauti madaidaiciya, lallai Sadam dan gata ne wajan Sawwmarsa dariya tayi tace "dole sadam yazama dan gata a wajan sawwama kamar yanda itama sawwama tadawo take yar gata wajan yaya Sadam, dariyar jin dadi sadam yayi sannan yace toh shikenan jirani ganinan zuwa na kaiki, Sawwama tace "ina jiranka yaya Sadam sai kazo, sallama sukayi sannan ta shirya tana zaman jiransa,
Awah daya ya dauka kafin ya iso yakira wayarta ya sanarda ita yana qofar gida cikin kankanin lokaci suka gama shiryawa suka fito itada halima,
Jingine yake jikin motarsa ya harde hannuwansa da kafafunsa yana jiran idowarta yayinda yake sanye da light blue din shadda sai sheqi takeyi kansa sanye da hula sai bakin takalmi budadde daya kawata kafafunsa hannunsa daure da agogo na fata shina baki Sadam yayi matukar kyau sosai yayinda ya dauke hankalin Sawwama ta shagala da kallonsa shima kallon nata yakeyi har suka qaraso yanda yake sallama sukayi masa sannan suka sake gaisawa basu dauki lokaci ba suka wuce izuwa wajan lallen shago yakaisu dake da layi ya sanya yabasu kudin kawai yace idan sun gama ta kirashi ya juya."
Kai tsaye wajan najeeb ya nufa dake sunyi waya kafin ya fito ya sanar masa wajanda yake,
Najeeb yayi murna sosai ganin sadam, shima sadam haka ne anasa wajan, najeeb yadubi sadam yace "tunda yanzu kadawo zan bar komai a hannunka kaci gaba da shirye-shiryen biki, Sadam ya dan dara sannan yace "najeeb ango, najeeba ma dariyar yayi yace saura kiris ayi babu kai, haba-haba ai hakan bazai yiwuba dole nasan zan dawo kafin zuwa lokacin tayaya za'ayi bikinka bana nan Najeeb? Aiko da ace bangama abunda yakaini ba zan dawo ayi bikinka sai na koma,
Najeeb yace kai ina karka manta baka dawo saboda an haifa maka babys ba tayaya zaka dawo saboda aure na?
Sadam yace "wannan daban kowanne da muhallinsa kuma nafada maka cewa ni banma san anyi haihuwar ba sai daga baya dan qin fadamun sukayi daga mummy har Sawwama kuma dalilin dayasa basu fada ba kenan suna tunanin zan iya dawowa, nisawa Najeeb yayi yace "koni daka sanar dani nasha mamaki duk da tawata gabar basuda laifi konine idan naga zaka ajiye abu mai muhimmanci ka taho dan bikina toh bazan fada maka ba, cigabanka shine namu idan zakama wani abu nan gaba nima bansan me zan zama ba, ta dalilinka gashi yanzu na samu aiki mai kyau na gina gidana har ina shirin ajiye iyali Sadam kai aboki ne na kwarai ba Mummy da Sawwama ba kadai ko nine bazan fada maka abunda nasan zaisa kayi sakaci da cigabanka da ban gaba zai amfanemu gabaki daya ba,
Uhmm kawai Sadam yace ya canja wani zancen, lokaci-lokaci yake duban wayarsa ko sawwama zata kira amma shiru, lokaci ya duba kusan 3hours kenan yanzu da kaita wajan yaci ace sun gama, Najeeba daya fuskanci cewa hankalinsa yana wani waje daban ya taboshi juyawa gareshi Sadam yayi Najeeb ya yayi kasa waving hannu alamun yana tambayarsa mai yafaru, Dan siririn tsaki sadam yaja sannan yace "3hours fa kenan dana kai Sawwama wajan lalle amma har yanzu shiru, Najeeb yayi murmushi yace "Sadam na Sawwama idan aka zauna dakai kana iya kiran Sawwama sau ba adadi, wanda yake tare dakai har kosawa yakeyi da zancenta sannan ya daura da fadin "kwanatr da hankalinka har indai lalle ne irinna mata dana sani to tabbas yanzu basu saka shekarar gamawa ba sukan dauki wuni guda wajan lalle,
Nisawa sadam yace Najeeb mutum yana gajiya da fadin abunda yake sone? Ni inason Sawwama yanzu ankai matakin da banajin zan iya boye sonta gaban ko waye, yanzu bazaka fahimta ba amma kabari kayi auren tukunna na tabbata zaka fahimta, Najeeb ya murmusa yace nasan soyayya sadam tunda ina yinta amma abunda nakeso ka gane matanka biyu ne ba daya ba, ko sau daya kana zancen abida haka koda kwatankwacin yanda kake na sawwma idanba haka ba zataji babu dadi, harara sadam ya watsa masa yace "kasan soyayya? Aina kasan soyayayr? Malam dakata kana shirin saninta ta dai, soyayyar baki kadai ce maka akayi ta isa akirata soyayya? Kana nan wani katon tuzuru dakai ana magana kan soyayya kana saka baki A fusace Najeeb yace "kaga dakata malam dama kazo nanne dan ka gayamin magana?" Sadam ya miqe kafarsa a doguwar kujerar falon hadeda lumshe idonsa a fili a furta "kanka akeji, za'aji kanmu ma Najeeb yafadi'i a kufule."
Dake da layin amare a shagon ya sanya su sawwama basu sami lallen dawuri ba hakanma masu lallen ba sunada yawa, ganin bata lokacin da suke a zaune ya sanya kawai tashiga shahin da ake gyaran kai aka gyara mata kafin agama lallen yazo kanta ma halima aka fara yiwa sannan bayan an gama gyara mata kai itama akazo kanta, Sadam yakirata hakai sau uku duka tana ce masa basu gama ba, tun lokacin sai qunquni kawai yakeyi yana fadin wannan ko wani irin lalle ne haka? Shi yaranma yafiji akan manyan yasan dole zasu galabaita."
Lallen Sawwama yayi matukar kyau sosai kamar na amare haka mai lallen ta zauna da zane mata shi yanda kasan inji ne yayi, ita kanta sawwaman ganin lallen takeyi cikeda sha'awa, duk mutanen da suke wajan saita suka tofa albarkacin bakinsu gameda lallen Sawwama wata ciki har tana fadin itama irinsa za'ayi mata, abunda duka kasa gamewa shine Sawwama ita tayiwa lallen kyau ba shi ya mata kyau ba."
Sun gama ana daff da za'ayi magrib hakan yasa Sawwama tacewa halima su wuce kawai basai sun kirashi suna tafiya izuwa bakin titi sukaji halima na goye da hameeda yayinda ita Sawwama ta goyi Hamdan horn din mota akeyi a bayansu alamun anaso su tsaya, Sawwama ta juya a zatonta Sadam ne sai taga bashiba hadeda rai tayi ta juya taci gaba da tafiya adai dai lokacin mai adaidaita yazo wucewa suka tsara suka tafi, tana lurada wannan motar har lokacin bata bar binsu a baya ba da sauri suka sallami mai adaidaita suka shige gida."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial228 Chapters
Lament of the Slave
The world is not always as beautiful and forgiving as one would imagine, and Korra Grey, a young florist, who is abducted by a creature of the children's books, finds herself in another world quickly learning that life can be even crueler than she thought.After more than a year of pain and suffering in the madman's cellar, she gets what she sought the most, freedom. Though changed by cruelty she suffered. Either she learns to live with the mutations or finds a way to reverse them while she struggles to find her own place in a world utterly unknown to her, hunted not only by the nightmares of her past.
8 1046 - In Serial6 Chapters
Rivers of Rogue
In the span of only a heartbeat, River is transported from the comfort and security of her room to a world of monsters, magic and violence. River finds herself suddenly at the bottom of a dark chasm with sheer walls of unscalable stone all around. The blue skies and clouds of the outside world stare down at her from far above, unreachable from these depths. The only path left open leads into the Hollow Delve, a gluttonous dungeon of stone and magic teeming with slavering monsters and enchanted treasures alike. Giant featherweight swords, explosive hammers, magic cloaks and aberrant, monstrous bodily transformations make up the treasures and boons of this twisted labyrinth. Faced with brutal combat for the first time in her life, a war of despair, pain, hope and ambition rage inside River as she struggles to improve her abilities and fight to survive. Because in this hollow chasm, death is only a reprieve. (Updates Tuesdays)
8 54 - In Serial14 Chapters
When God Is Bored He Builds New Worlds… Mine Was Next, Unfortunately...
Project is not DROPPED. Status is incorrect!! Have you ever been pulled into a conversation that you didn't want to be a part of? I have. Recently. With a beautiful Angel in her underwear. She thinks I'm some sort of mastermind. Well, I'm not. I'm just a lazy NEET. She must be an idiot! NEW CHAPTERS EVERY WEEK! Fatal:Extra Check out the NEW* Official Fatal Chapters Art on the Patreon and get access to Fatal:Extra! Fatal:Extra is a side series of Fatal Chapters that focuses on the backstories of some of the characters. This features over 90 pages of content including new detailed fantasy worlds and a dive into the fictional mythology of the Asla'ati. ????? ????? ????? ????? ????? ????? An Introduction to Fatal Chapters Each chapter is in a different style! So continue on, noble knight! Pass each level and earn yourself a new reward! From comedic isekai, to dark fantasy, to game world adventure! We've got it all in gacha form! Which one's your favourite? Well, you better vote before a FATAL CHAPTER occurs. Because after that, your favourite may be NO MORE! Are you Team Raito, or Team Kirev? Or Maybe Team Ledger? Team Amelie? On our Discord you can join your team of choice and battle to win in the finale! ????? ????? ????? ????? ????? ????? How do I play a part? Shape the story by voting on the polls for your favourite chapters and characters. It's almost like a Reader Interactive, but much more passive in nature. I'm just writing for fun and love to write what you like to read! The least popular characters may even suffer fatal consequences as the story progresses so tread carefully and vote with your heart! Lives are at stake when we take part in these FATAL CHAPTERS. ????? ????? ????? ????? ????? ????? What is at stake? A grim demise may very well be the consequence for characters of chapters that constantly place last on the board. Characters with the highest votes and best results from the polls will receive more chapters as their reward! Don't let your favourite character down or something we call the Fatal Chapter will be released for them. It's not a pretty sight! ????? ????? ????? ????? ????? ????? ...Who will be the last one standing...
8 410 - In Serial7 Chapters
Bloodmancer System
Henry died from bone cancer at the age of twenty only to awaken in an eighteen-year-old necromancer. Barely surviving an attack from a vampire. He finds himself awakening in a magically technological world that is at war with the magical beasts that invade from another world. Fighting his family, rivals, and other species while trying to go to the Academy to learn to use his powers. Shame on those that try to take Henry's new lease on life. He is not going to lay back and life takes away his second chance at power, money, and love.
8 181 - In Serial10 Chapters
The Girl Lost in the World of War
A battle slave named Halberd release herself from the arena. She started her new life as an adventurer. After a series of events, she found herself again in the arena. Then, she was found in the middle of war, dancing with her weapon, creating countless corpse in her path. A story about a beastgirl trap in the middle of war trying to free herself from the world of battle.
8 85 - In Serial21 Chapters
The Street Festival: How A Wallflower Became The Hero (updated)
Marty, is a quiet, shy kid, a loner with no close friends. He's always felt like an odd, uncomfortable, awkward person with zero social skills. With no positive male role model in his life, he hasn't gained much insight into what it means to be a man. He doesn't know how to act manly and doesn't show interest in traditionally manly pursuits. As a result, he's picked on and made fun of at school, called a wimp, a weakling and worse. When you add to that his straight "A" status in all his classes and his reputation for preferring the company of sci-fi stories & movies and comics over other humans, you start to understand the other name they call him, "nerd." He doesn't see the perks of being a wallflower and doesn't want to continue going through life as one. When his mom lands a job in another city, he sees an opportunity to reinvent himself, become the cool jock, or someone else the people at his new school will respect, and want to get to know.But will it be easy to do and will it work out like he plans?*This story was written by Sabrynabrooklynne on Wattpad. If you aren't reading it there, it's been stolen. Please report the website. It's probably not the final version either.*
8 121

