《ƘADDARAR RAYUWA》Ƙ page 77
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 77
Ranar Asabar da safe aka daura auran Sawwama da Abububkar ko walima ba'ayiba zallan daurin aurene,
Sawwama babu abunda takeyi sai kuka Mama na rarrashinta tana fadin in sha Allahu babu abunda zai biyo bayan wannan aure sai alkahiri,
Da dare aka dauki amarya izuwa gidan mahaifansa aka fara kaita daga ita sai can kowa ya watsa cikeda al'ajabin irinna gidanda suka kai Sawwama da yawansu idanba a TV ba basu taba cin karo da irin wannan gida ba, an watse an barta daga ita sai Halima sai wasu biyu yayan yan uwan baba,
Gidan acike yake dam sai da jama'a kai kace taron siyasa akeyi,
kowa yazo taya hajiya murnar Samun karuwa,
Sawwama tayi kuka harta gaji jikinta yayi sanyi har wani zazzabi takeji ita ba aurenne damuwarta ba manufar aurenne ya dameta,
Bacci ne ya dauketa dake dama saida sukayi Sallar isha'i aka daukosu, wata yar yarinyace tashigo bazata wuce shekara ashirin da biyar ba, da fara'arta ta zauna ta gaidasu sannan tace musu an ajiye musu abinci yana falo, da duk wani abun bukata
Duk yanda taso taga fuskar Sawwama abun baiyiwuba haka tafita,
Palour suka nufa komai an ajiye musu abincin sama da mutum ashirin,
Dakyar Halima ta rarrasheta tasamu taci abinci kadan sai dare sosai sannan su Halima ma suka tafi,
Wannan yarinyar datsunne tasake dawowa taganta ita daya,
Zama tayi adakin shiru babu wanda yacewa wani komai, can yarinyar tagaji da zaman shiru tace anty amarya dan Allah kibude fuskarki ni kadaice a dakin,
Sawwama taja gyalenta ta bude fuskar ta murmushi ta sakarwa budurwar itama ta maida mata tace kai ma sha Allah lallai yaa abubakar yayi sa'ar kyakkyawar mata, murmushi kawai Sawwmaa tasake yimata,
Tace ni Sunana Aisha nice autarsu yaa abubakar, hira sosai take tayiwa Sawwama itakuma sa'i-sa'i take amsata, yarinyar tafice tace ina zuwa,
Shashin Hajiya taunufa tashiga tasamu hajiya da yayanta mata da yan uwanta dukda dare yayi amma suna zaune suna hira, aisha ta isa zuwa jikin Hajiya tace Hmm hajiya naga amaryar Ya Abubakar kin ganta? Wallhy kyakkaywa, Hajiya ta fadada fara'arta tace kai ma sha Allah,
Bakiga wani abun mamaki ba hajiya wallhy karamar yarinyace, Hajiya tace eh ance karamar yarinyace ta'iya yiwuwa bazata wuce sa'anninki ba, A'a hajiya batama kaini ba dan wannan bazata wuce shekara sha ba atayi takai ashirin, Hajiya tace ah lallai yarinyace kam toh Allah yabasu zaman lafiya yasa tanada halaye masu kyau, mikewa Aisha tayi tace barina koma dan abunda nazo fada miki kenan,
Hajiya tayi dariya kawai itakuma ta juya yayyunta sai tsiya suke mata wai takawo gulma,
Atare suka kwana da Aisha cikin kankanin lokaci har sun saba, dasafe tayi wanka ta canja kaya,
Da yamma akayi budar kai amma ango bai halarta ba Hajiya ta kirashi tanata fada yace mata bakinda sukazo aurenne basu gama tafiyaba so babu hali yatafi yabarsu,
Kowa sai sanya albarka yake yiwa Sawwama
Advertisement
Da dare Hajiya dakanta tasa yan uwanta suka raka sawwama gidanta,
Gidan ya tsaru sosai wuce tunani, Nasiha da addu'a sukayi mata sannan suka barta,
Wanka tashiga tatsaya kallon tsararren toilet saikace a film, na'urori dayawa bata iya amfani dasuba haka ta taba iya yanda ta iya tayi wanka tafito,
Tana zuwa kwanciya tayi tafara tunane-tunane kawai sai Sadam ke fado mata aranta kuka tayi sosai sannan bacci ya dauketa,
Abubakar yana wajan matarsa ko niyyar fita bayi dashi itakuma kuma bata cemasa yatafi ba dan aganinta tunda ita ta sanyashi yayi aure toh ita zata bashi umarnin yaje ko akasin haka,
Kwanciya bacci sukayi batareda damuwar sunbar amarya ita kadai ba,
Washe gari Hajiya ta aikowa Sawwama abin karyawa hakama da rana harna dare,
Kwananta uku a gidan banda masu kawo abinci da yan aiki bataga idon kowaba,
Bayan tayi sati saiga mama dasu laraba da kannen Baba sunzo dubata bata gwada musu wata matsala ba sunata yaba kyan gidan banda mama wacce tasan zamanta ciki na wani lokaci ne,
Basu dadeba suka tafi sai gabaki daya taji babu dadi, takoma gidan jiya ita daya sai wayarta idan damuwa ta dameta tayi kuka ta gaji sannan ta lallashi kanta."
1month kenan da auransu Abubakar ko matarsa babu wanda yataba lekota aciki,
Suna zaune da Dr, Dr tace Naga baka motsa gameda zancen yarinyar nan ba nayi maka magana kaki cewa komai ko kanaso tayita zama a matsayin matarka na lokaci mai tsayine?
Gara ayi mai yiwuwa ta wuce mana kayi ka tsinke igiyar aurenta akanka,
Kwantarda ita yayi ajikinsa cikin lallashi yace. "Sonda nake mikine banaji zai iya bari na kusanci wata macen bayan ke shiyasa kikaga har yanzu ina wannan abun amma zan san abunyi,
Murmushi tayi tace "ni nasani nasanda irin sonda kake mini amma kuma zamanta a matsayin matarka na tsawon lokaci yafi dagamin hankali fiyeda abunda zaka aikata."
Yau kaje gidanta ka kwana kallonta yayi da mamaki yace kin tabbata? Zuciyarki ta aminta da hakan? Iska ta furzar tace idanma zuciyata bata aminta ba yaya zanyi? Nidai kawai banaso tayita jimawa da auranka nida tana samun ciki kawaima ka saketa ta haihu ka karbi kayanka, murmushi kawai yayi batareda yace komai ba,
Da dare haka ta sashi agaba saida yatafi can, karfe tara na dare yayi parking din motarsa a harabar gidan mai gadi ya rufe gate ya zo yana gaidashi amsawa yayi cikin fara'a cikin takunsa na kasaita yawuce ciki."
Lambobi ya danna kofar shiga palourn ya bude komai na palo farine kujeru set biyu aciki sai can gefe wani palour daban sai dakuna wanda zasu kai 10 haka aciki,
Daya kofara da zata sadashi da palourn ya nufa yashiga dan anan aka shirya masa dakinsa daya dakin kuma yasan natane, kai tsaye dakinsa ya nufa saida yayi wanka yagama duk wani shirin kwanciyarsa sai kuma zuciyarsa take kwadaita masa son ganin matar tasa, wanda shi bada niyyar sanyata a idanuwansa yazo ba,
Wanka tashiga tayi da turaren wanka ta fito daure da towel ajikinta fuskarta sam babu wani walwala,
Advertisement
Bude dakin yayi da sallama ahankali yashiga bata jiyoshi ba saboda yanda yayi maganar baya-baya, idanuwansa ya sauka akanta wacce ta juya baya batamasan da shigowar wani dakinta tun daga kasa yake kare mata kallo gabansa yana faduwa har izuwa gashin daya sauka a bayanta,
Kamshin taji dakin ya dauka gabaki daya ko'ina ya kaure da wani ni'imtaccen kamshi bata kawo komai aranta ba tafara murzawa lallausan fatar jikinta mai kasa tayi da towel na jikinta tana shafawa kawai sai taji kamar ana tsaya ana kallonta a razane ta dago sukayi ido biyu. Gabanta yayi mummunan faduwa dan tadauka aljani tagani. Saurin jan towel din tayi yadawo yarufe kirjinta tayi kasa da kanta, sai yanzu take gane yanda tasan fuskar hoton da Dr tanuna mata cewa mijinta ne, Lallai Allah yayi halitta domin a filima yafi hoton kyau nesa ba kusa ba,
Sake murfin kofar yayi yajuya da baya sai dai ba dakinsa ya nufaba palour ya nufa ya zauna ya kunna kallo amma baya fahintar komai gizo kawai surarta take masa. Anya sajida kanta kalau? Ta kalli wannan yarinya tace zata aurawa mijinta? Bata tsoron abunda zaije yazo? Nisawa yayi ya lumshe idanuwansa bacci yakeso ko zai daukeshi amma yakasa saboda yasan irinsa bazai yiwu ya ganta haka kuma bacci ya daukeshi ba,
Sawwama saurin saka rigar bacci tayi ta kashe wuta ta kwanta,
Bude idanuwansa yayi harsun fara canja kala ya mike ya nufi dakinda take tanajin bude kofarsa tayi saurin runtse idanuwanta, a hankali yake tafiya amma sautin tafiyar yasa za'a gane cewa cikin kasaita yake yinta,
Dake dakin baiyi duhuba yabar kofar palour a bude ya karasa har gaban gadon cikin husky voice yafara magana, tashi kije kiyi alwala kidawo muyi sallah,
A sukwane ta mike bayan yanada alwala amma haka tasake yin wata, sallah yajasu sukayi sannan yayita yimusu addu'oi bayan sun idar ya juyo ya dafa kanta yayi addu'a sai bayan yagama ta iya bude baki cikin sanyayyar murya tace ina wuni?
Kallonta ya tsaya yanayi bai amsaba amma kamar yanda tayi masa kyau haka muryarta tayi masa dadi, jin shiru ya sanya ta dago tana dubansa, idonsu ya hade waje daya tayi saurin sauko nata kasa shikuam yazuba mata kyawawan idanuwansa yana kallonta, kara nanatawa tayi ina wuni? Sai a sannan ya amsa sannan yace jeki kwana babu musu ta hau gado taja bargo ta kwanta, yayi tsawon minti araba'in yana zaune yana addu'oi sannan shima yahau gadon ya kwanta,
A hankali yafara tabata ta runtse idanuwanta zuciyarta tanayi mata zafi na sanin cewa zai kwanta da itane kawai dan yana neman haihuwa amma badon wani shauki ba,
Mirginota yayi zuwa jikinsa kamshin turarensa ya sanyata lumshe idanuwa sai takeji gabaki daya kamshin yafi dadi datazo kusadashi,
Wata duniya daban ta fada zuciyarta tayi saurin dawowada ita duniyar asali,
Abubuwan da yake mata sun fara wuce tunaninta hawaye yafara gangarowa a fuskarta toh indai haihuwa kawai yake nema menene duk na wannan abubuwan? take tambayar kanta,
Wahala sosai Sawwama tasha hannun wannan bawan Allah, ta yabawa aya zakinta. Kuka sosai tayitayi dukda gakan bai rabuda itaba har saida ya cimma gaci, rumguneta yayi ajikinsa Kamar wanda yake bacci, yayinda ita kuma kuka takeyi maras sheshsheka Allah sarki Sadam ashe yana sonta sosai shiyasa yake tausaya mata amma yanzu data shiga hannun wanda baya kaunarta yanemi kasheta,
Ahankali ta zare jikinta ta shiga toilet ta yi wanka tadawo ta kwanta duk abunda takeyi yana jinta harta da kukan da tayi maganganun ne kawai baijiba dake azuciya tayisu, saida bacci ya dauketa kafin yatashi yakoma dakinsa acan yayi wanka, amma hankalinsa yana wajanta."
Bayan tatashi tayi Sallar asubahi tana gamawa ta kwanta wani baccin ya dauketa har 10am sannan tatashi tasamu masu aiki sun gama shirya mata komai, bata nemi ganinsa dan bata bukatar hakan shima kuma tasan yagama aikin daya kawoshi bazai sake nemanta ba sai wani,
taci abincinta ta koma daki."
Da asuba kafin yayi sallah dakin Sawwama yafara wucewa yadade akanta yana kallon wanda shi kansa baisan dalilin kallon ba,
Jin motsin rufo kofarsa bayan yafita ya tadata a bacci amma dake a baccine batayi tunanin wanine yashigo dakinba, ganin babu kowa a gefenta yasa ta kyabe baki wato dama zuwa yayi kawai ya kusanceta koh? Shikenan yagam bazaima iya kwana da ita daki dayaba, dama ko ba'a fada ba tasan ita ba sa'ar auransa bane ganinsa na yau datayi da raina kanta domun Allah ya hada masa kyau kudi ga aji da nutsuwa,
Sallan tayi sannan tadawo da kwanta da safema kafin ya fita dakinta yasake komawa nanma tana bacci yafice yakoma gidan Dr,
Sassafe Dr taganshi ya shigo da kallon tuhuna tabshi cikin kishi tace kaje ka kwana da ita shine sassafe zata taso ka dawomin nan?
Zama yayi gefenta hadeda rumgunota yace "nayi missing dinki ne shiyasa na taho sassafe, batareda ta sake fuskaba tace "kun kwana tare kenan?
A'a ni kadai na kwana aina fada miki bazan iya kwana da wata bayan keba yasamy kansa dayi mata karya, ajiyar zuciya mai karfi ta sauke da saida yabashi mamaki, toh dayace mata yakwana da ita baisan yaya zata dauki abunba."
Mikewa tayi tace ni zan wuce Asibiti saina dawo peck tayi masa a kumatu sannan ta kama hanyar tafice, bayan fitarta shima ajiyar zuciyar ya sauke."
Karfe uku na yamma Hajiya takirashi bayan sun gaisa take cemasa yakawo mata Sawwama, yace bayan la'asar zai kawota sukayi sallama,
Wanka ya sakeyi ya sanya farin shadda ya saka hula sannan yawuce gidanda Sawwama take,
Sawwama na zaune a palour na biyu tana kallo kamshin turarensa ya sanarda ita zuwansa dukda cewar tun jiya kamshin turarensa baibar gidanba, sallama yayi a hankali ya shigo ciki ta amsa ta dago kai ta saci kallonsa aranta tana fadin ikon Allah shi komai ya sanya kenan sai yayi masa kyau?
Karasawa yayi ya zauna a kujerarda take kallon nata a kunyace ta gidashi ya amsa yana mai kare mata kallo so kawai yakeyi ta dago idonta amma taƙi dagowa."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial36 Chapters
Path of the Berserker (A Daopocalypse Progression Fantasy)
A world destroyed. An axe to grind. And a path to infinite power. Welcome to my reality. When the cultivators came to Earth, they destroyed our entire civilization in a matter of hours. Armies fell, cities burned and that was before the moon turned red and filled our world with monsters. Now, over a decade later, what’s left of humanity slave under the heels of our Qi infused masters. The luckiest of us might even become one of them, they say—if we serve the Dynasty well enough and harness the power of Qi. But I want none of that. I’m sick of serving and I want nothing to do with their world. Instead, I want them to pay for what they did to mine. Maybe that’s why she found me. The dark, angry goddess who showed me a different path. Apparently, Qi is not the only route to power. I may be too late to save my family, but it’s never too late for revenge. Now, I’ll fight to take back my planet, to grow strong enough to beat the cultivators at their own game. I will free humanity or die trying. For that’s the Path of a Berserker. Path of the Berserker is progression fantasy novel for fans of western style cultivation fantasy, post apocalypse and xianxia. Click to enjoy now!
8 220 - In Serial7 Chapters
Legends of Bitworld: A Misnomer's Tale
“Hello, and welcome to Bitworld. Our names are One and Zero. People refer to us as Gods. This world is inhabited by adventurers of all different classes, each with their own path. Your path…wait, what was your name again?” […GREY…] “Grey. That’s a fine name! You are entering our world in a time of peril. We are no longer in possession of the Nine; the Wizard Al’eron Con and his legion of glitches have captured them. Soon, we too, will be corrupted. Bitworld is in danger, it is up to you.” Discworld meets a roguelike dungeon crawling LitRPG, and shakes the hand of the classic Hero’s Journey in this nostalgic coming-of-age story. Follow Grey, Damsel, and Crow into the illustriously pixelated gamescape of Bitworld. Traverse the misty mountains, hacking and slashing through laggy levels of familiar monsters, and grind your way to destiny…but first, please wait while we load the next screen.
8 130 - In Serial62 Chapters
Reincarnated Nobility
There is a kingdom in a world of magic where children with the best scores in subjects from agriculture, to politics, to magic are selected to join the prestigious school, Nobility, to be trained as the country’s next generation of leaders. I am one of those children, and I have my eyes set on the position of Queen… but people keep misunderstanding everything! The Queen and the King are never married, by law. They are just coworkers who happen to live in a giant castle. Why do I want to be Queen? Well, I used to be a person from some lame place called Earth, and here the Queen governs magic! This was an otome game? So? (Warning, this story is a definite first draft and my current focus right now is finishing it. Editing will come later) This story can also be found at https://jlynnbattleworthystories.wordpress.com
8 378 - In Serial195 Chapters
A dream come true
Edward never appreciated his boring repetitive life on Earth. One night he has a strange dream and suddenly wakes up in another world. Will he thrive in it or will he feel stranded in an alien and dangerous environment? Follow his journey in this novel. The release schedule is two chapters per week.
8 144 - In Serial11 Chapters
Mystic Reality
SynopsisLong ago, there were 15 Gods that bicker and babbled on their own prowess. The Supreme God, the one who rules the 15 Gods, thought of a competition to determine their prowess by themselves. But the game had a twist, because the Gods are immortal, the competition would be done by a mortal representative that would be called champions. The game was a competition of strength and wit with limitless champions that would represent each God. The arena would be a world that is created by the Supreme God. The prize of the representative will be to rule the whole world as an Emperor. While to his God, they will become the fated successor of the Supreme One.And so, the competition begins.
8 129 - In Serial27 Chapters
The Facebook Stalker
Kate Anderson, a girl from a small farming community in Glendale, Wisconsin just got the break of her life -- she was accepted to Chicago's University of Illinois College of Medicine. Ready to take on the Windy City, nothing can stand in her way. Except for one thing -- the night she accepts a 'friend request' on Facebook from a Pete Peterson.***Updated Regularly***
8 116

