《ƘADDARAR RAYUWA》K page 86
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 86
Cikin Dr yanzu yashiga watan haihuwa yayinda kulawar datake samu daga Abubakar takara yawa wannan lokacinma Sawwama tayi masa uzuri kodada sau daya bata taba yimasa korafi akai ba hakan kuma yana kara mata kima a idanuwansa sam ita batada hayaniya,
Yayinda zabensu yake kara karatowa har yasiya form na senator ana sanya ran cewa shine za'a tsaida matsayin dan takara,
Yanzu ita kanta Dr dinma kulawarda yake bata tayi karanci, cikin sa'a akayi primary election aka tsaidashi dan takara,
Haihuwar Dr kuwa ana saka rai yau ko gobe,
Ita Sawwama kamma tausayi yake bata dan sam baya samun lokacin kansa,
Yanzu haka ya kirata ya snaarda ita cewa yana zuwa gida a gaggauce tafara shirya masa abinda zaici kafin ya iso tagama,
Ta tura yaran sashin masu aiki da nanny dinsu dan bataso su dameshi tasan dole zai bukaci hutu,
Idan sunanan kuma bazasu taba barinsa shi daya ba saboda sun saba dashi shima kuma bazai iya zama waje daya batareda ya jawosu jikinsa ba,
yana shigowa ta taimaka masa yayi wanka sannan suka wuce dining tayi serving dinsa yafaraci wayarsa tayi kara, hannu yakai zai dauki wayar Sawwama ta canja fuska maida wayar yayi batareda ya amsa kiran ba dan ya fahimci abunda take nufi,
Bayan yagama tace yashiga yayi bacci ko nawani lokacine shima yasamu yahuta,
Yabi yanda takeso din yashiga ya kwanta tabishi tana shafa masa gashinsa har bacci ya daukeshi,
Baccin 3hours yayi sannan ya tashi lokacin harta gama da yaran gabaki daya ta shigardasu dakinsu,
Palour yafito ya sameta ta sanya turaren wuta gidan shiru kamar babu kowa tana jin motsinda takai kallonta kofarda zai fito murmushi ta sakar masa shima yayi mata ya karaso ya zauna,
Sannu da fitowa tace "zaunawa yayi kusada itave yace "yawwa yau nasamu hutu thanks to you, kwanakinnan komai yayi zafi, jikina har ciwo yakeyi zirga-zirga tayi yawa mikewa tayi tadawo bayansa a hankali tafara massaging bayan ya lumshe ido yanajin dadi ta dauki tsawon lokaci tanayi saida ta fahimci yadan samu relief sannan ya barshi a hankali cikin sanyin murya tace "ka rage stressing kanka ba koda yaushe bane yazama dole ace kome za'ayi saika hallara kana samun huta ko yaya, kuma kowani hali kake kaci abinci banaso ka zauna da yunwa,
Zamewa yayi ya kwanta akan cinyarta yace "abinci yanzu idanba naki naci kona hajiya ba sam bayamin dadi, taste din babu armashi aduk yanda nake idanba nadawo naci abincinkiba banajin dadi,
Nagodewa Allah da kika kasance acikin rayuwata, you're very supportive, ina sonki matuka Allah yayi miki albarka ina samun nutsuwa aduk lokacin danake tare dake, murmushi tayi tayi kasa da kanta a hankali tayu masa kiss batareda ta dagoba tace "Amin nagode kaima Allah yasaka maka da gidan aljanna, kai adali ne Allah yabaka shugabanci yabaka ikon yiwa wanda suka zabeka adalci, amin ya amsa yana maijin dadi acikin ransa,
Kokarin mikewa tayi yace "zauna ahaka nawani lokaci inaso na kasance tare dake babu musu ta sake gyara zamamta shikuma ya lumshe idanuwa tana wasada girarsa da hannunta,
Advertisement
Tsawon lokaci suka dauka ahaka sannan ya mike yace "ina yarana?
Suna dakinsu sun dade dayin bacci,
Zaki rakani na gansu gobe fitar sassafe zanyi bana tunanin zasu tashi kafin lokacin,
Hannunta yana makale acikin nasa ta rakashi dakin daya bayan daya yabisu yayi musu sumabata agoshi kamar yanda yasaba sannan yadawo gareta,
Dakinsu suka nufa,
Ta kwanta shima ya kwanta a gefenta ya jawota tadawo jikinsa gabaki daya cikin rada yace "gobe sassafe zan fita kinsan yanda yanayin tashin safe yake a wajana inaso ki sanyamin karsashi yanda gobe bazanji komaiba koda nafita da wuri inaso nasamu kuzari yanda zanyi komai cikin nutsuwa,
Nutsuwar kuma daga gareki nake fatan samu yanzu,
Batareda tace komaiba ta hade bakinsu waje daya, yau sawwama tabashi mamaki kwarai da gaske baitaba tunanin basirarta hartakai hakaba tunda yake a rayuwarsa baitaba samun kula irin yanda yasamu ayauba, yau yajishi awata duniya yabar wannan duniya gabaki daya yaje yanda baitaba zuwaba, Alabarka kawai yake sanya mata."
Vikeda kaunarta bacci ya daukesu,
Da zaifita sallar asubahi ya tasheta itama tatashi tayi sallah,
Saida gari yafara haske kafinnan ya dawo ga mamakinsa harda shirya masa breakfast maras nauyi da alamu tun da dare ta ajiye duk abunda zatayi amfani dasu intact, tahada da kunun gyada tayi masa, yaji dadin wannan kunnun dan yana daya daga cikin abunda yafiso,
Yaci abinci sosai yayi nak, sannan yashiga wanka a tsinake ya shirya ta fidda masa kayanda zai sanya ta taimaka masa yasaka, har bakin mota ta rakoshi deiver yana jiransa aka har suka tafi tana kallonsu cikeda nishadi tajuya tawuce ciki,
Batayi breakfast dinba takoma bacci sai wajan 10am tatashi,
Ta kintsa yaranta tayi musu breaskfast sukaji,
12am takira wayarsa ya sanar mata sungama meeting yanzu haka wani abun zasuyi yana hanyar fitowa idan yagama zai kirata, bazaifi nanda 1hour ba zai karaso,
cikeda soyayyarsa tace "adawo lafiya Allah ya tsareka yace "Amin Hafsatuna uwar yayana, dariya tayi ta cikin wayar sannan sukayi sallama,
Tana kashewa yakira Dr yaji lafiyarta yabata hakuri akan baisamu damar yazo ya dubata ba fitan asuba tayi, amma yanzu kai tsaye yana gamawa wajanta zai nufo tace shikenan Allah ya kawoka lafiya."
3:45pm aka fara kiraye kirayen sallar la'asar Sawwama tamike ta dauro alwala duk jikinta babu dadi ta gabatarda sallah
Wayarta ta kalla ta sauke wata ajiyar zuciya yace zai kirata amma har yanzu shiru gashi har la'asar tayi bai dawo ba,
Zuciyarta tana bata cewa meeting dinne ya rikeshi amma kuma hankalinta yakasa kwanciya da hakan, batason kiransa ya kasance cewa kuma ta takura masa, tagumi tazuba domin sabonda sukayi yanzu abun har abun mamaki idanta jima bata ganshiba sai tashiga damuwa,
Har yamma tayi bataji duriyarsaba ko awaya,
gabanta sai faduwa yakeyi har lokacin takasa cin abinci,
Can wayarta ta dauki ruri gabanta yayi mummunan faduwa da sauri ta karasa dan ganin wanda yake kirannata, ganin sunan hajiya ya sanyata sauke ajiyar zuciya, ta amshi wyaar bayan sun gaisa taji damuwa sosai a muryar hajiya bazata iya kwatanta yanayin yanda taji muryarba,
Hajiya tace "ki sanya hijab kifito yanzu driver zaizo ya daukeki bata iya tsayawa ya tambayi abunda yake faruwaba dan tasan akwai matsala, hijab tasaka ta goyi muhammad ta kama hannun yaran sukayi waje, tasamu drivern dama kamar wanda yake jiranta tana shiga kai tsaye asibiti yawuce da'ita, asibitin acike yake hankali atashi amma ana ganin motar aka buda suka shige can ciki gabaki daya wajana yana zagaye da jami'an tsaro,
Advertisement
Hajiya, Alhaji da sauran yan uwane a wajan.
Kowannensu hankali atashe da sauri Takarasa wajan dukda cewa batasan abunda yake faruwaba sai kawai ganin hawaye tayi yana kwaranya akan kumatunta,
Hajiya tana kallonta itama sai hawaye agaban Hajiya ta durkusa tace "mai yake faruwa?
Hajiya cikin muryar mai rawa tace "Abubakar hafsatu Abubakar babu lafiya, zama tayi dabass akasa daga ganinsu ya tabbatar mata ba karamin ciwo bane dan asibitin cike yake babu masaka tsinke
Kuka ta sanya marar sauti babu wnada ya iya lallashinta kowannensu da abunda yakeji acikin zuciyarsa,
Sai bayan 30minute da zuwanta Dr yafito Alhaji ya karasa ganin yanayin likitan babu walwala,
Likita yace "Alhaji munyi iya kokarinmu samada 3hours muna aiki akansa amma babu yanda muka iya Allah yayi ikonsa gubar tayi karfi sosai atake ake mutuwa idan aka shaketa shima hikima ta ubangiji dayakau har 3hours araye, ina mai bakin cikin shaida maka cewa Allah yayi masa cikawa,
Daga wajna suna iya jiyo abunda likitan yake fadi, sama-sama Sawwama kejin muryar Hajiya cikin kuka tana fadin Alhamdulillahi, Alhamdulillahi Allah kaine abun godiya kai bamushi alokacin da bamuyi zataba gashi ka kwaceshi alokacin da bamuyi zatazo ba,
Luuuuuu tafadi daganan bata sake fahimtar abunda yake faruwa ba,
Bata farkaba har saida aka yimasa wanka ana shirin kaishi dukda cewa yamma tayi amma dake ba'a kira magribabab sai kawai aka yanke shawarar kaishi,
Mama ce a gefenta ganin ta farfado ya sanya tace Sannu-Sannu Sawwama yaya jikin yanzu me kikeji? Bata kula zancenda mama takeyi mataba ta fara fadin mama baban muhammad yana inane?
Mama tace "Hafsatu sai hakuri shikam Allah yakarbi abunsa,
Kuka sosai takasa wanda ita kanta mama kukan takeyi,
Can aka shigo dakin akace tazo suyi sallama dashi tayi masa addu'a,
Saida aka rirriketa kafin nan ta iya mikewa,
Tana ganinsa kwance gawa saida tasake suma, bata farfado ba har aka kaishi aka dawo,
Iya tashin hankali iyalan wannan gida sun shiga Dr kanma batasan yanda kanta yakeba yanzu haka anshiga da'ita threatre za'a cire babyn da gaggawa,
Abubakar yasamu yabo da halayansa nagari wajan mutane,
Sawwama izuwa yanzu tadaina kuka, kukan zuci kawai takeyi,
Anyiwa Dr CS anciro baby girl kamarta sak da mahaifinta babu wani abunda tabaro nasa,
Har akayi awanni dayin CS din Dr bata farfaodoba saboda yanayin halinda take ciki,
Mama tana wajan Sawwama har akayi kwana uku,
Daya daga cikin kannen Alhaji tasamu hajiya tace "hajiya amaryar marigayi anya kuwa baza'a kaita asibiti ko ayi mata rubutu ba?
Kwana biyu kenan da fa ko magana batayiba ba kuka babu magana waje daya kawai take kallo, shi kansa rashin kukan wani illah ne kada ayi biyu babu ga waccar tana asibiti itama har yanzu bata san a'ina takeba,
Hajiya bata iya cewa komaiba mikewa tayi zuwa dakinda Sawwama take, zama tayi gaban Sawwama cikin lallashi tace hafsatu kina jina?
Kwayar ido kawai sawwama ta juya gareta alamun tanajin abunda take fada,
Hafsat ki saurareni dan Allah ki sawa ranki nutsuwa kar azo ayi biyu babu, Abubakar shikam Allah yarigada ya karbi abunsa addu'a zamuyita binsa dashi kizama mai tawakalli ki dubeni kigani, namikawa Allah komai bawai dan bandamuba saidan nasan damuwtaa babu abunda zai karamin zanyita yimasa addu'a har nima tawa ta riskeni,
Abubakar yasamu shaida kodaga ku matansa irin halinda kuka shiga wannan ma shaidace ta cewa "shidin ya kasance adalin mutum, addu'arku yafi bukata awannan lokaci duk wani mai rai da kika ganshi mamacine ko ba dade ko bajina yanda yatafi muma sai munje, lokacin tafiyarne babu wanda yasani kamar yanda mutuwarsa tazo mana anfita da niyyar dawowa Allah baiyi za'a dawoba,
Sai alokacin Sawwama ta saki kuka tafar yinsa kanar ranta zai fita hajiya nata yimata nasiha,
Cikin kukan take fadin Hajiya mai yayi musu?
Mai yayi musu haka da zafi da zasu kasheshi? Su rabashi da iyalinsa alokacin da rayuwa take ganiyar yin dadi?
Sun tarwatsa mun duk wani farin cikina na rayuwa yabani duk wata kulawa da farin ciki ashe wannan farin cikin bamai nisa bane,
Laifin meneayiwa wannan mutane da zasu rabani da farin cikina?
Hajiya itama kukanne yaci karfina amma tadaure cikin kukan tana fadin "hakuri zamuyi hafsatu Abubakar wa'adinsa ne yazo na tabbata koda su basu kasheshiba Allah ya rubuta abazai wuce wannan lokacinba,
Su kansu da suka aikata tun ba'aje ko'inaba Allah ya nuna musu matsayarsu an kamasu,
Kuma ba farin cikinmu suka tarwatsa ba nasu suka tarwatsa su zasu rayu da wannan bakin fentin amma mu Allah zai dubu lamuranmu yakawo mana wani farin cikin koda ta wata hanya dabanne,
Kuka sosai Sawwama takeyi tanajan Allah ya isa."
Duk wanda yazo ta'aziyya sai yayiwa wadannan mutane Allah ya isa tsinuwa sun shata babu adadi,
Abokin hamayyarsa wanda suka fito siyasa tare Abubakar yayi winning primary election,
shine ya sanya akayi poisoning dinsa ta viron da yayi amfani dashi arubutu wajan wannan meeting din, tun ba'aje ko'inaba aka kamsu da shaidu masu karfi."
Dr saida tayi sati a asibiti kafinnan tadawo hayyacinta kuka kuwa tayishi,
Kullum cewa mahaifiyarta take Mama ki kaini wajan mijina idan akace mata yarasu saita sanya kuka tana fadain dan Allah kuce masa yadawo, yadawo ni nahakura yaso sawwama fiyedani yaso yayanta fiyeda nawa har indai zan ganshi hakan ya wadatar dani, ko yarinyar data haifa bata nemi ganiba kullum ciki. Kuma kiran Abubakar yadawo gareta takeyi abun gwanin tausayi tarame gabaki daya ta fige.
Dakyar aka rarrasheta tafara kulada yarinyar data haifa,
Gabaki dayansu itada Sawwaman sun dawo abun tausayi sun rame sun fige,
Babu wani kwanciyar hankali, Dr batasan tayi mummunan rashin mutum mai kyakkyawan haliba sai yanzu datake zaune da yan uwanta komai arayuwa idan bai saba sharia ba tace tanaso abubakar zaiyi danya faranta mata sam bayason bacin ranta, hausawa dama sunce baka sanin amfanin abunda kake dashi sai lokacin daka rasashi."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial29 Chapters
Seeker
The Gods are dead As they bled dry, so did the magic which gave them birth. In the new era of technology, its pathetic remnants must hide in the shadows or be locked away. In the ancient era of magic two beings often stood out: Galileo, an immortal scholar obsessed with knowledge and Angelica, the most loyal servant of the greatest among the now dead Gods. But why are they worthy of mention? Because after millennia of isolation, the two emerge in the new world beyond their reckoning. The entire story is told from the third person, however, each chapter will be told from the perspective of only one of the characters. This will be signified by the first letter of their names after the chapter number to avoid confusion. I submitted this fiction as a [participant in the Royal Road Writathon challenge] as well as a participant in National Novel Writing Month. The original challenge had been to finish this entire faction within the month of November reaching the 55.5k word minimum. This goal had been achieved. I do not own the cover picture
8 230 - In Serial7 Chapters
Let's Shine
So, first things first, this here is a magical girl thing. There are girls in it, they have magical abilities, fight supervillains (who have magical abilities, too, but in a more menacing way, like superpowers), and also do girly stuff. But it's not for children. Or at least not entirely. The idea is, it should be cute, but at the same time serious. Cute-serious, yeah… So, this is experimental for me. I'm planning to make short updates for as long as I can keep it up or until the plot resolves itself, whichever comes first. Most of all, I'm planning to not overthink or overedit things as much as I usually do, so there are bound to be mistakes and inconsistencies. I'll try my best to keep them to a minimum, though. But if you notice something, please feel free to tell me!
8 179 - In Serial32 Chapters
Louisiana Nights
lavishworld | 01______________________________________- How will the Wests' second chapter go?Previously known as "Undercover Wests".
8 196 - In Serial32 Chapters
Sakura TimeTravel
Madara/kaguya's won the 4th ninja war. Naruto sacrifices himself and sends sakura back to past.----------------------------------------------------------#1 in inosai (3rd July 2020)#1 in bijuu (2nd Feb 2020)#2 in teamseven (11th July 2020)#1 in madara (21st September 2020)#2 in sasusaku (22nd Dec 2020)#2 in sakura (9th Jan 2021)#4 in strong-female-character (9/1/21)#3 in kurama (1st April 2022)
8 164 - In Serial28 Chapters
Supergirl
Crystal Kent, daughter of Clark Kent (A.K.A. Superman), never knew moving would be this hard. She is forced to go to a new, prestigious high school called Gotham Academy where she is now considered the "new kid." Having trouble finding a good aspect of moving, Richard Grayson enters the picture. Handsome, confident, and mysterious, he intrigues her and she can't help but fall for him. Her father notices her problem with the move and tries to cheer her up by offering to let her become Gotham's Supergirl. Accepting the offer excitedly, Crystal then learns that becoming a superhero is more than just wearing a tight suit. She has to face new enemies and overcome many problems, Crystal is wondering if she can get through this. But Nightwing is there to help her and show her how to be Gotham's hero. Crystal starts to have her own wars within herself, but when her childhood crush shows up she doesn't know what to do. And when the Joker takes an interest in her, Crystal really believes the move was the worst thing that could ever happen to her."Your Joker impression is impeccable." -Keatingeb"This book is REALLY good! I COULD NOT put it down." -olaola9"I love this book so much nobody will even understand!" -pandapoxx
8 60 - In Serial45 Chapters
Pipe Dream || Timothée Chalamet
in which a lost Columbia student spills coffee on the sweater of an esteemed actor --real life x social media
8 171

