《ƘADDARAR RAYUWA》K Page 93
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 93
"Kamar yanda kika gani ni yar gidan sarauta ce mahaifina shine Babban sarkin da yafi kowanne sarki matsayi a kasarnan bama kasarnan kadaiba hattada Kasashen waje sunaji dashi saboda kasancewarsa mutum mai ilimi,
Matansa guda hudune wacce muka fara zuwa wajanta bayan saukarmu cikin masarauta itace babba sai mahaifiyarmu nida mahaifin wannan maras lafiya wanda kika ganshi,
wanda kikaji ana kiransa da Yareema,
amma ita mahaifiyarmu ba yar kasarnan bace,
alokacinda akayi gasar karatu acan kasar saudia itace wacce tazo na daya, ba mazauna cikin saudiya bane aslinsu yan kasar ne amma ba mazauna cikinta ba kasar bane suna zaune awani kauye dake yankin kasar,
Alokacin mahaifina yaganta ya nemi auranta toh cikin yardar ubangiji da rabon hauhuwarmu suka bashi auranta dake a wannan lokaci suna masu shirya wannan gasar karatu ta kasa gabaki daya,
Kuma dama shi babban Malami ne wanda yayi suna a duniya baki daya,
Mahaifiyarmu bata kasance yar gidan masu kudi ba amma iyayenta sunada arziki abunda nake nufi da arziki shine sunada Karamci da sanin darajar mutane ba lallai sai kudi bane yake zama arziki akwai abubuwanda Allah yake azurta su dasu, Mahaifiyarmu tanada Hakuri nutsuwa da hankali sannan ga biyayya duk wani abunda mahaifinmu zai sanyata har indai bawai yasabawa addini ba bazata taba bijirewa ba sanin kanki ne ayanda mahaifinmu ya kasance mai cikeda addini bazaima taba kokarin sakata abunda zai sabawa ubangijinta ba tunda shima bazai iya saba masa ba,
Mahaifiyarmu ta fuskanci kalubale dadama a gidan sarauta amma dake ta kasance mace mai hakuri bata taba sanya hakan aranta harya dameta ba halinda na kirki ya sanya tashiga ran mahaifinmu yana matukar kaunarta wanda saida kowa dake cikin wannan masarauta yasanda hakan,
Ana haka mahaifinmu ya karo mata har guda biyu bayan wani lokaci amma dukda haka yacigaba da nuna mata soyayya,
Sauram matan babanmu a yanda suka nuna mana basuda matsala suna nunawa kowa soyayya sai dai bamusan abunda yake a cikiba dan masarauta ba wajene wanda zaka saki jiki da kowa ba dan kawai ya nuna yana sonka a ido,
Yanada yara sai dai dukansu matane sai guda biyu Yareema wanda Hajiya babba ta haifa m sai kanina mahaifin yareema kenan,
Mahaifiyarmu batareda shekarunta sun wani jaa ba Allah ya daura mata ciwo yan kwanaki tarasu munyi kukan rashinta daga baya muka Fawwalawa Allah komai,
Mahaifinmu yacigaba da kewar mahaifiyarmu nan ya dauki son duniya ya daura mana komai mu, komai mu toh anan ne kuma sai Al'amura suka fara cakudewa domin Hajiya babba tafito mana da halinta kiri-kiri ta nunawa duniya ba sonmu takeyi ba,
Bayan wasu shekaru Danta wanda shine magajin mahaifinmu yayi aure matarsa itace Hajiya suwaiba wacce muka gaisa da ita bayan mun gama gaida matan Abbana,
Nima ban dadeba na auri Alhaji nabar kanina a gidan yana ganin kalubalen rayuwa,
Akwana atashi shima ya giram yakai mallakar nasa gidan abbanmu yayi masa aure, a kankanin lokaci Allah yabashi haihuwa shine yareema toh yareema yafara girma baifi shekara goma sha aduniya ba Mahaifinsa kanina kenan da babban yayanmu yareema sukayi hatsari dukansu suka rasu,
Advertisement
Anshiga babban tashin hankali a wannan lamari sosai dafarko munyi tunanin Da makarkashiya a hatsarin toh amma wa zamu zarga?(Abunda yafaru shine Hajiya Suwaiba itace wacce ta shirya wannan hatsarin Alhali batasan cewa harda mijinda za'ayi tafiyar ba dan shi bayama kasa, shikuma ya rigada yayiwa kaninsa waya akan yazo ya daukoshi a airport saisu wuce wajan taronda zaije gabaki daya,
Hajiya suwaiba ta aikata hakanne saboda taga yanda Mai martaba yake nuna soyayyarsa ga mahaifin yareema, shine ta shirya kasheshi abun kuma ya auku harda mijinta, dake itada yayarta Hadiza kawai sikasan zancen sai suka boyeshi luff amma tabbas tayi dana sanin faruwar wannan lamarin, taji dama bata kwatanta aikata hakanba domin itama tayi rashin jigo a rayuwarta gabaki daya, bata sakeyin dana saniba sai da taga yareema Haleefa yazoma shinr wanda zai gaji gari da sahalaewar mai martaba instead of yaronta wanda a ganinta shi yakamata abashi kujerar mahaifinsa sai taga ba hakaba
Shikuma mai martaba yayi amfanine da wanda yafi kowanne ilimi hankali nutsuwa uwa uba iya zamada mutane da tausayinsu sannan kuma yabi zuciyarsa na soyayyarda yake yiwa yaron ya nadashi akan wanda zai gajeshi,
Masu karatu yanzu dai ni daku kadai mukasan wannan abun banda sauran mutane)
Hajiya taci gaba da fadin wanda lamari bamusan wanda ya shiryashi ba babu wanda za'ayi zargi fiyeda Hajiya Babba domin itace ta nuna tsanarta a garemu karara,
Amma Idan hajiya Babba ce itama harda nata yaron sonda Mahaifinmu yakeyiwa kanina shiya koma kan dansa yayinda Ya nadashi magajinsa domin shine wanda ya cika zati da sura sannan da kalamar zama sarki shine wanda ya cancanki ya mulki mutanen kasar gabaki daya,
Rashin mahaifin Yareema ya sanya yake kallona kamar mahaifinnasa nima ina sonsa cikin raina ina jinsa wani lokaci har fiyeda yaranda na haifa domin kuwa dan uwana nake kallo a tattare dashi,
Yasaba da yarana sosai barinma Abubakar bazaki taba cewa ba ciki daya suka fito ba bayan kamanni ga shakuwar jini da Allah ya hada musu,
Kullum suna tare zamansa yadawo nan dan shima yafijin dadin nan din domin yana soyuwa agaremu gabaki daya,
Dake mahaifina yana bukatarsa kusa dashi yasa zaman nan yayi masa wahala sai dai duk weekend yana hanya,
Ko ranarda wannan lamari zai auku masa sai da yakirani ya sanardani cewa yana hanya nagama shirin tarbansa najishi shiru naduba lokacin da yakamata ace ya iso bai isoba,
So saina kirashi wayarsa bata shiga hankalina bai kwantaba nayita kiransa nakira yayansa Abubakar naji ko suna tare ya shaidamin sunyi waya yace masa yakusa isowa dan mota yabi ba jirgi ba sai kuma nakira mahaifiyarsa ta shaidamin aiya dawo yashiga daki yana bacci toh kinji daga yanda al'amarin yafara."
Ciwonanm Allah yabarwa kansa sanin abunda yake fili dana badini,
Tunda wannan lalaura tasamu yareema banu taba kallon canji irinna lokacin da kuka haduba bamusan abunda Allah ya kunshe gameda wannan lamari ba,
Amma Hafsatu inaji ajikina wannan lamari alkahirine zai biyo bayansa,
Bazan tilasta kiba bakuma zan rokeki kona nemi alfarma ba dannasan zakiyimin idanna rokeki koda kuwa ace ranki baisoba,
Advertisement
Abunda yake fariwa shine yanzu haka abbana yataso zuwa nan ganin domin nemawa Yareema auranki, dam-dam dam gaban Sawwama yafadi takasa dagowa tadubi Hajiya nan danan idanuwanta suka cike fa hawaye tunani take cikin ranta tana fadin Wannan karon kuma irin Kaddarar da Allah ya jefo mata kenan?
Hajiya tacigaba da fadin alfarmar da zannema wajanki guda dayace itace idan baki aminceba karki zalinci kanki ko kiji nauyina ko kunyata kice kin amince kifito kai tsaye ki nuna abunda yake cikin zuciyarki hakanne zaisa hankalina ya kwanta,
Suna cikin haka Aysha tashigo da Sallama tacewa Hajiya mai martaba ya iso yanzu haka Alhaji sun tafi rakoshi daga Airport,
Hajiya tace "toh Alhamdulillhi tunda ya iso lafiya ke aina kikasan isowar tasa?
Anfara uploading a yanar gitso shiyasa nagani tayi maganar tana juyawa hankalinta nakan wayarta,
Hajiya ta dafa kafadan Sawwama tace anty hafsa bari naje mugama shirya komai, kafin su karaso
Idan kikaji zuwansu zuwa jimawa sai kishigo ku gaisa, dakyar Sawwama ta iya gyada kanta hajiya tafice,
Tsawon 1hour da isowarsa amma bata tashi daga yanda takeba tarasa abunda yake mata dadi a duniya komai yataru ya cunkushewa kwakwalwarta,
Tambayan kanta takeyi
Shin ta amincewa wannan auren? Idanta amince hakan yana nufin zata zauna da wanda baisamma waye kansa ba bare iyayensa itama kawai tasan yanayin rashin lafiyarsa ne yake nuna mata kamar ya santa,
Idan ta aureshi tasan rayuwarta ta dakushe gabaki daya kenan dan babu wani jin dadi ko farin ciki da zata samu a auren wanda baisan menene kansa ba ganaki daya tay-tayi ko hawayene ya digo daga idanuwanta amma yaki zuba,
Gaskiya bazata iya amincewa wannan aurenba ita batama tunanin sake wani auren a rayuwarta tun rasuwar Abubakar takeji bazata sake wani aurenba saboda farin cikin daya bata iya rayuwarta yananan zaune a kwakwalwarta bataso wani yanayi na daban yazo ya dakushe wannan farin cikin da yabarta dashi,
Idan zata sake aure kuwa toh tanaji iya gidan Sadam zata sake iya komawa Masoyin Asali ko wani hali yake? Yana tunaninta koya manta da ita?
Zata koma gidansa su rungumi yaransu Muhammad kam tasam Hajiya zata rikeshi tayi masa tarbiya fiyeda yanda ita zatayi masa amma su hameed da hamdan kam koda idanuwanta ya nuna mata cewa mummy tana kaunarsu bataji zuciyarta zata yarda da wannan kaunar tana zaune ahaka Hajiya ta aiko ayi kiranta jiki a sanyaye tatashi ta fita har falon Alhaji Da sallama tashiga jiki a sanyaye."
—————-
Yau Sadam yafita a dakin Hafsa yakoma dakin Abida har ila yau bai taba yarda wani abun yashiga tskaninsu ba kullum yakance mata bazai iyaba ko yana gajiye ko wani abun kuma tana labe idan suka kebe adaki da hafsa tanajin abubuwanda suke faruwa wani lokacin idan tajiyo ya hanata nutsuwa wani lokacin kuma ya hanata bacci amma kamar aikin Allah sai taje tayi,
Kwanciya yayi abunda yabarta kamr kullum tayi masifa tayi masifa amma yaki kulata daga karshe saita fashe da kuka yana kwance yana jiyo kukanta a hankali zuciyarsa tafara karaya,
Yana daga kwance yafara fadin meye kuma na kukan? Kiyi shiru kibarn nayi bacci,
Kuka ta kara volume hakan yasa ya mirgina barinda take kwance badan ransa yasoba yafara jijjiga bayanta yana lallashinta da wannan damar tayi amfani harta samu abunda take nema a wajansa."
Washe gari ta safe duk wata hanya da zatabi dan sanya Hafsa tagane abunda yafaru a tsaknainsu saida tabi Hafsa taji haushi kam sosai aranta amma kuma afili saita nuna ko inkula,
Dan taga abidar ba kaine da itaba idan tabiyeta zasu samu babbar matsala itakuma bata wannan hanyar takeso ta bullo mata ba,
Ta lura ita macecec mai masifar kishi toh da wannan hanyar zatayi amfani wajan cusguna mata,
Zaune suke a falon kowacce danne-danne kawoa takeyi da wayarta babu mai kula wata a cikinsu,
Sadam yashigo daowarsa daga aiki kenan, Hafsa tatashi da sauri tana masa sannu da daowa tana isa wajansa ta rumgumeshi batareda ya lurada Abida dake falonba ashariyarta kawai yaji hakan yasa yasaki Hafsa cikin bacin rai yadubi Abida yace "amma dai kinsan nanba gidan arna bane koh?
Abida cikin takaici tace "au haba? Sadam yaja tsaki kawai yashige ciki zabar bacin raima ya manta dakin abida yake yawuce dakin Hafsa Hafsa kuwa tana kallo bata hanashi ba tabi bayansa, suna shiga takarbi jakar hannunsa ta taimaka masa yafara rage kayan jikinsa,
Tana kokarin zugr zip na wandonsa dan tayashi cirowa Abida tashigo domin tana gama zagin datsu ta juyarda kanta gefe batada yanda yashiga ba saida tabishi daki ta kare masa bala'i bata ganshi ba shine ya biyoshi nan,
Tana kallonsu haka tayi kan Hafsa tana zaginta Sadam yayi saurin shiga tsakani domin kokarin kai mata duka take, rai bace yace "wannan wani irin haukane Abida? Zaki shigo mana daki kai tsaye haka harma kina neman kaiwa matata duka ,
Abida cikin bacin rai tace Au ni bakuga abunda kukamin ba dake nice uwar bakin jini laifina kawai kake kallo?
Sadam yace "dakata me akayi miki? Yanzu bazan taba daukan wannan haukar ba kisani idanma rabuwa dakene kikeso nayi zan rabuda ke kije dannagaji da wannan haukar yakamata ace yanzu nima nawa hankalin ya kwanta,
Jin zancen rabuwa ya sanya jkkin Abida yayi sanyi tasaka kuka tace "kai baka kallon laifinta yanzu fa kwananne kazo dakinta tana cire maka kaya kuma kunsanda hakan sai acuceni nayi shiru,
Dafe goshi yayi dominshi ya manta ma da hakan, da sigar lallashi yace "kiyi hakuri na shafa'a bata kulashiba taifice yabi bayanta Hafsa tatabe baki."
Ayita Hakuri dani har Allab yakawo na kammala gabaki daya school ne sai daukan zafi take nagode sosai da muna kaunarku da wannan littafi, in sha Allahu komai yazo karshe saura kiris."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial41 Chapters
Freelance Saga
What would you do if you were given the chance to do something extraordinary? What if a world existed where life was a game? You could gain levels, fight monsters, and get into sexy situations. You could become a truly powerful person.Would you take up the call to explore this brave new frontier, or give up on the adventure of a lifetime?Scott Hunter made his choice, and life is about to get sexy.Freelance Saga: Learning Curves is the first episode in a series about a man who enters into a real-life fantasy world designed like a game. While it seemed perfectly normal, if highly advanced, at first, he soon learns that the world is a place filled with opportunities for developing both his strength and his perversity.Scott Hunter, freelance monster trainer, is a new beta-tester for Alterra International. The relatively unknown corporation shares their secret, the ability to travel to a world where life is literally a game! Treating that reality like a virtual existence, Scott enters but soon discovers that things are far more real than he expected.
8 190 - In Serial18 Chapters
The Entropic Knight - a litRPG Story
[Participant in the Royal Road Writathon challenge] Jarrod is a young, quiet unassuming man from a dead-end village with nothing much going on. He loves his family but wants to see more. Wants to experience more. Wants to find where he really fits in. At the age of 18 he is due to gain access to the Great System, the plaything of the Gods - and from there is able to go off on adventures as he see's fit. Read on if you want to see a young-man try and find his own way in the world, where he doesn't quite fit. This will be a voyage of discovery / adventure / slice of life story whilst primarily focusing on Jarrod. He has been born into a world with the system already in place, not dropped in, and intrinsically understands the rules.
8 225 - In Serial30 Chapters
Snowstorm
Told that his life was a lie and whisked away to a strange new world with unfamiliar magic, Snowflake struggles to find where he belongs. Join him as he meets vibrant people from different worlds, explores the complex ways of Skills and Classes, and does his best to fulfill his benefactor's last wish. With a bit of luck and more than a little Skill, he may just have what it takes to reclaim his world from the System. If he can survive that long. Author's Note: This is the Adventures of a Unique Snowflake rewrite. I plan to release a chapter (roughly 3k words) per week. Shout out to the Facebook group LitRPG Books! https://www.facebook.com/groups/LitRPG.books/
8 183 - In Serial13 Chapters
Stained Warriors
Tattoos can be found in different cultures all over the world. It is an ancient art form that holds deep meanings and beliefs. Some cultures believe that tattoos are given to a man or a woman who undergoes the rite of passage of adulthood. Tattoos are perceived as a symbol of a warrior or badge of honor and richness. Tattoos have different meanings yet different people and different cultures practice such art form. We now accompany the warriors in an epic journey in a world where tattoos come to life and provide powers you can only imagine. We shall uncover the mysteries of the world of PenTerra.
8 129 - In Serial18 Chapters
Scarlet Fate
Peacefully living in isolation away from society, Akane and her family lived peaceful lives. Until she met a badly wounded girl on the field near her home, despite knowing the dangers she may bring to her family Akane helps the girl nonetheless. This fateful encounter marks the end of her peaceful days.
8 202 - In Serial64 Chapters
Gone
Virgil Anxiety Black was in his room recovering from a panic attack when the castle is stormed. His best friend, Remus Lucious, has just enough time to help him escape before throwing himself back into the battle in an effort to save his boyfriend and Virgil's brother, Crown Prince Janus. Virgil finds himself running through the woods and unknowingly crosses the border between his kingdom and the kingdom next door. There Virgil is found by Crown Prince Roman, Remus's semi-long not exactly lost twin. Not recognizing Virgil as royalty and only seeing the garbs that show him as a citizen of another kingdom Roman does what he thinks is best.He gives the poor boy a panic attack while simultaneously arresting him and throwing him in the dungeons.While Roman recruits the help of his two best friends to help him figure out who Virgil is and why he's in their territory Virgil is rightfully panicking over the recent events. After a few hurt feelings and a couple death stares the Light Realm learns what transpired next door. In an effort to help both kingdoms Roman's and Virgil (now acting King Virgil) make a truce and put aside their differences. Roman and his two friends, Marquess Patton and Lord Logan, join Virgil in this epic quest to save their brothers, and the Dark Realm kingdom.Like any great tale this book is filled with Fear! Love! Betrayal! Heartbreak and Despair! And let's not forgot proper non homophobic LGBTQ representation!Extra stuff:-Virgil is a seer -Virgil, Logan, and Janus have magic-Virgil is selectively mute but does speak a few times (rarely. Like only three times in the whole book)-Aro Patton. No he's not gonna date anybody please stop asking.-Ace Remus-Remus and Janus are madly in love and no one can stop me!#2 in Creativetwins 9/14/20#3 in platonicmoxiety 9/14/20Cover by Winstermagic on Wattpad
8 217

