《ƘADDARAR RAYUWA》K page 94
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 94
Kanta yana kasa tashiga wajan Can gefe tazauna ta gaida mutanen ciki cikin girmamawa mai martaba yace abasu waje dama tun kafin yafada wasu daga ciki sun fara barin falon,
Bayan kowa yabar Falon yadubi Sawwama yace "Hafsa Sawwama ta sake nutsarda kanta a kasa kwarjini da cika idon wannan Dattijon ya hanata dagowa ta kalleshi saida yasake kiran sunanta ta amsa cikin nutsuwa, mai martaba yace "dago ki kalleni magana zamuyi har lokacinma takasa kallon nasa hakan yasa yayi murmushi irinna manya sannan yafara magana,
Nasan ta iya yiwuwa kunyi magana da Yata ta sanar dake batunda nazo matadashi jiya amma inaso na sake jajjada zancena nazo na nemawa jikana aurenki,
Nasan zakiyi mana kallon masu son zuciya mutanennda zakafi son kansu fiyeda kowa abun bahaka yakeba,
Dalilin faruwar wannan lamari bayan zuwanki bayan tafiyarki kuma ciwo yasake dawowa muna saka rai in Allah yayarda za'a samu waraka daga gareki,
Zakiga kamar munason aura miki wani mutum daban, Mai martaba yayi dariya Na manyan mutane sannan yace "Abun bahaka yakeba a zahirin gaskiya bantaba cin karo da wani mutum irin yareema ba A hali da komai ana cewa mutum tara yake bai cika gomaba amma fa inada tabbacin Idan Allah yabawa yareema lafiya kika zauna dashi zakice shi yacika goma,
Idan kika amince da wannan auren Allah yabawa yareema lafiya zaki kasance kullum kina min addu'a saboda hada wannan al'amari danayi,
Yareema mutum ne wanda cikin dubu samunsa ba lallai ba zaki iya tara miliyoyin mutane baki samu daya kamarsa ba, bani kadai na shaida hakanba duniya ya shaida mutanenda suke taredashi sun shaida,
Yareema mutum ne Yareema mutum ne kwarai dagaske Allah ya hadashi da jarabawa daciwo wanda bamusan menene ba,
Amma zuwanki munga canjin Al'amari harmun fara gano bakin zaren Yareema yayi magana radau yanda kowa zai fahimceshi,
Tsawon Awa biyu suka dauka Mai martaba yana bata labarin Yareema da yanda yake tafiyarda rayuwarsa yanda yake mu'amala da mutane tanata mamaki shin dama za'a samu mutum irin haka?
Advertisement
Mai martaba yayi murmushi ganin yanda jikinta yayi sanyi yace "kadan daga cikin halayansa kenan na fada miki saikin zauna dashi zaki tabbatar abunda na fada miki yafi haka, dan inaji ajikina yakusa samun lafiya,
Nisawa kawai tayi batace komaiba amma cikin ranta tana mamaki dama Sarakuna suna sakewa haka suyi magana?
Kodai dan ita yana neman wani abun wajanta ne?
Mai martaba ya daura da fadin ina neman alfarma a wajanki da ki amince da wannan auren in sha Allahu zai zame mana alkahiri gabaki dayanmu, amma yanzu zan baki lokaci kiyi tunani tunda anzo abun a kurarren lokaci kiyi shawara da mahaifanki naso nagansu amma Mahaifin Abubakar (Alhaji) yace "abari sai kin amince tukunna samau mahaifanki nima na yarda da hakan domin abi komai a ka'ida yafi kinada dama da ikon da zakice baki amincewa wannan aurenba amma ina neman alfarmarki akan ki amince in sha Allahu duniya gabaki dayanta sai tayi alfahari da wannan auren,
Sawwama ita dai batace komaiba amma jikinta yayi sanyi,
Bayan yagama ya bukaci Alhaji da Hajiya su shigo ciki suka zauna kasa kamar yanda Sawwama take a kasa, mai martaba yace "mungama magana amma nabata lokaci tayi tunani duk abunda ta yanke saita sameki ya nuna Hajiya ta fada mikk idan yaso maji Allah yasa muji Alkahiri su duka suka amsa da amin banda Sawwama,
Alhaji yace " Mai martaba koni danaji wannan zance nayi farin ciki Allah yasa hakan shine hanyar samun lafiyar Yareema,
Ko Abubakar yana raye Yareema yaga Hafsa yace yanaso Abubakar mai barmasa ne bare yanzu da baya raye da yana raye zaiyi farin ciki da wannan lamari domin yadamu da halinda dan uwansa yake ciki,
Hajiya ita dai batace komaiba har suga gama amasallacin dake cikin gidan sukayi la'asar daga nan Mai martaba kai tsaye aiport kawai yawuce har yaje yadawo basusan abunda yakaishi ba, Hajiya tasake jaddada mata cewa idan bata amince ba tafito kanta tsaye tace bata amince ba dan bataso tayi abunda zuciyarta bata aminta dashiba,
Hajiya tafita a dakin dake dama sun koma dakinta Aysha tashigo ta zauna kan sopa dake cikin dakin jikinta duk yayi sanyi itama Sawwama anata wajan hakanne jikinta yayi sanyi duk tarasa abunyi, ta dubi Sawwama tace "Anty Hafsa kekam yar Sa'a ce dafarko Yaya Abubakar gashi yanzu Ya Yareema,
Advertisement
Gabaki daya salihan mazan kike kwashewa, iska ta furzar tace bazan boye mikiba Anty Hafsa naso Yaya yareema kamar hauka, tun bansan sonsa nakeyiba har nadawo nasan sonsa nakeyi soma mahaukaci wanda hana iya controlling dinsa idan akace zaizo gidannan kamar anyi mini gagarunar kyauta nakeji koda yake zan iya cewa garama ace anyimun kyauta wannan mai saukice ko muryarsa naji zan iya wuni cikin farin ciki,
Na dade inata kissima yanda zan fada masa ina sonsa inataso na tsara yanda zai amince dani domin naga shi nasa wajan bai daukeni da komaiba,
Alokacinda wannna abun yafaru dashi hauka naso nayi,
Har nadebi shekaru bankuala wani saurayiba smamma yanzu gashi nan kamar ba'ayiba sai dai har yanzu ina sonsa,
Sawwama tasamu kanta da tambayar ko meyasa kike sonsa?
Aysha tayi wani murmushi wanda Sawwama bata gane ma'anarsa ba tace kinga halin Yaya Abubakar?
Toh wallhy Yaya Yareema harya fishi kirki dole mace idanta zauna dashi taji sonsa aranta, kamar kwai haka yake treating na mata shi yanayjn hakan domin kyautatawa amma keda yakeyi miki hakan dole zuciyarki ta tsinke har indai bata kashi bace,
Sawwama tace "kina masa irin wannan son meya hanaki auransa?
Aysha tayi murmushi tace Allah baiyiba amma kam naso Ya Yareema,
Kekam yanzu Allah yabaki, sai nakeji damana nine ke,
Sawwama taso tace kizama ni din mana ki aureshi sai dai kawai taki fadi dan kawai tana ganin suna zuga halinsa ne danta aureshi,
Koma ta aureshi yanzu ina halinma yake idanma da akwaishin kenan dan samun mutum mai irin halinda suke zayyano mata da kamar wuya,
Mikewa tayi tace "Anty Hafsa kiyi tunani mai kayu kiyiwa kanki zabinda gaba bazkaizo kina dana saniba,
Tana gama fadin haka tayi waje,
Sawwama bata bar gidanba sai magrib Hajiya ya sanya aka kaita,
Aranar ta yi bacci cikeda damuwa cikin dare tafarka saka makon wani mummunan mafarki
Sak shigen mafarkin datayi alokacinda akayi maganar aurenta da Sadam wannan mutumin nan dai wanda yake neman taimako wajanta cikin mafarkinya yau fuskarsa tafito mata tass ba kowa bane sai yareema tarasa abunda wannan mafarki nufi,
Washe gari haka tatashi mama saida yakasa hakuri ta tambayeta abunda yake damunta,
Ta shaidawa mama Abunda yake faruwa sannan tace "ni ban dauka dawani abuba shiyasa ban fada mukuba koda muka dawo ma ni namanta da yafaru sai gashi naj yazo kamar yanda nafada miki wai ciwo yasake tashi Mama kasa cewa komai tayi dan dai ita ranta bai amince da wannan aurenba tayyaa za'ace yarta taje ta auri wanda baimasan kansa ba gabaki daya, sai dai har cikin zuciyarta takejin tausayinsa amma tausayinsa bazaisa tayi tsautsayin barin yarta ta aureshi ba,
Bayan Baba yadawo a kasuwa dayake yanzu karfe hudu ya dawo yabar yaron shago Mama ta jere masa abinci akan dining ya zauna yaci bayan yagama tashiga masa bayanin abunda yake faruwa, sannan ta daura da fadin amma ni ban amincewa wannan aure ba tayaya za'ace ta auri wanda shima baisan kansa ba sucire son zuciya a wannan lamarin,
Amma Baba baice komaiba har washe gari Baba baice komai gameda lamarinba,
Bayan ancika kwana biyu Baba yana zaune ya kishingida jikin kujera Mama tace "Baban Hafsa nayi maka bayanin abunda yake faruwa amma bakace komai ba,
Nanma dai kamar bazaiyi maganaba sai kuma can yace "kiramin Mamana,
Mama tatashi tayi wajan Sawwama tashiga falon da Sallama sannan ta karasa ciki ta sameta kwance su muhammad kuma na wasa tsakar dakin Hameeda na gefenta tana bacci, itama idanuwanta a lumshe amma ba bacci takeyiba tsabar tunanine kawai mama tadan dade akanta amma bata saniba saida tayi mata magana sannan tace" Hafsa Babanki yana nemanki Ahankali ta bude idanuwanta ta mike dan amsa kiran mahaifinnata."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial97 Chapters
Spell Analyst
Synopsys: Jude a Systems Analyst and Murl a Physicist find a new universe created through absorbing information from our own. This universe is quite different as it was overly influenced by computers. During one experiment to create avatars to explore said universe the two get sucked in themselves. Somehow Jude gets sent thousands of years later than Murl and he finds himself in a world of magic and swords. However, there is a game like system that seems to control everything. Jude decided to gain levels and power so that he can find out what happened to his friend Murl. Along the way, he stumbles across a quest that will lead him to the truth of the Universe. WARNING: MAY CONTAIN GOD AND SATAN Authors Goals: 3 Chapters a week M-W-F One chapter a week on Mondays 2k-3k words per chapter Over 3k per chapter A solid ending Improve writing This fiction is part of the Pledge. This story will be finished no matter what!
8 229 - In Serial107 Chapters
In Range
A young, talented, and aspiring archer makes his way to the Olympic Archery Qualifiers; however an accident prevents him from ever making it. An accident which took the final years of his adolescence, his dream of ever becoming an Olympic Gold Archer, and most importantly someone who meant the world to him. Rehabilitating for a year in a hospital, the despair and dread of being alone and having nothing left worth living for finally got to him. Finding his way to the rooftop, he decided fall, but where he expected death, something else appeared; a blue message. A chill and simple LitRPG story that I just wanted to write. Note: I write with the Dark Theme setting, so if I make a colour mistake it’s probably why. I also strangely prefer using the Imperial System to measure Height, while I use the Metric System for almost everything else (Canadian by the way).
8 343 - In Serial76 Chapters
Anuseena - Anubhav & Haseena
This story revolves around DSP Anubhav Singh and Haseena Malik #pure fanfiction#rulki#maddamsirwatch maddam sir at 10.00 pm on sony sab..
8 175 - In Serial45 Chapters
Idol By Laulau20
Lily is a shy and lonely girl. but when she overheard about Eiden Online from her classmates. she quickly asked her father for a capsule and the games thinking that maybe she could change.take a look as she made new friend in alternate reality of Eiden. and how will the experience she found in EO affect her personality in real life? can she change from the way she used to be?....A/N:.the game name was Royalroad but i decided to change it into Eiden so i can easily made new places and systems. most of the chapter still contain RR names and others. sorry for the inconvenience but i will not fix them. too lazy to do it. ..Status:This fiction is already completed
8 213 - In Serial8 Chapters
Eternal Love
Finney escapes and the 5 are given a second chance. . . But under one condition. Read to find out. I'm new to this shit and unsure what to do.100+ views reached Tue Oct 18200+ views reached Wed Oct 19300+ views reached Fri Oct 21400+ views reached Sat Oct 22500+ views reached Tue Oct 25700+ views reached Wed Oct 26 900+ views reached Wed Nov 09 1000+ views reached N/A1500+ views reached N/A
8 130 - In Serial31 Chapters
airplane. •SOPE•
hoseok has been in love with the idol min yoongi from bts since he can remember, what happens when he meets him on an airplane? -sope/yoonseok.-explicit language.-it's my first story don't be ROOD🗿-short story- is thirty chapters short?? KSJDJS idkstarted June 19th 2019.ended july 3rd 2019.lowercase intended.©️diorapline
8 248

