《ƘADDARAR RAYUWA》K page 95
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 95
A falo ta sameshi yana zaune ta zaune can gefen kujerar akasa itama mama ta zaune gefen kujerarda baba yake
Sawwama tace "sannu da daowa baba
Yawwa sannu mamana nace dai kina lafiya?
Lafiya kalau Baba meka gani?
Shiru baba yayi yana nazarinta sai can kuma "yace yanayinki ya nunamin kamar akwai abunda yake damunki numfashi ta fitar ta dago tadubi mahaifinnata sannan tace "eh Amma bawani abun daga hankali bane,
Baba yadubi mama Yace tashi kibamu waje muyi magana tunda baba yake baitaba yimata hakaba amma wannan karon sai taga bayason yin maganar tana wajan mikewa tayi batareda ta musa ku nuna rashin jin dadinta akan abunda yayi ba,
Bayan tashiga ciki ya dubi Sawwama yace "Mamana inason kisake yimin bayanin abunda yake faruwa inaso naji daga bakinki,
Sawwama ta nisa sannan tayaiwa Baba dalla-dalla sannan tace "Na rigada na yanke shawarar bazan aureshi ba Baba,
Jijjjiga kai yayi na gamsuwa da maganarta sannan yace "ko zaki iya fadamin Dalili?
Shiru tayi takasa kawo masa dalilin,
Baba ya yanke shirin da fadin kon rigada kin yanke hukunci bazan jaa da abunda kika yankeba amma inaso kisani har indai jinyace zata sanya ki ki auransa toh wannan ba dalili bane,
Yanzu arayuwa yakamata ace kingane wani abu guda daya mamana ba komai bane wanda muke iya kallon zahirinsa abubuwa dayawa sukanzo manane oya kallon idanuwanmu bamusan meyeke kunshe aciki ba,
Mamana rayuwarki tazo miki da Kaddara kala-kala amma gabaki dayansu masu kyau ne kowacce kaddara da kika ganta zata iya juyewa tazama mai kyau a rayuwarki,
Inaji ajikina duk wani abubda yake tunkararki Alkahirine make damu gabaki daya,
Ni bance ki amince da wannan aurenba amma sai nakeji kamar akwai wani kulallen abu da Allah kadai yabarwa kansa sani,
Mamana! sawwama tadago ta kalleshi domin yanda yayi maganar yana nuni da yanaso ta kalleshi,
Baba yace "kiduba rayuwarmu abaya kiduba rayuwarmu a yanzu duk ta dalilin kaddarar rayuwarki auren Mahaifin muhammad da kikayi shima haka mukayi masa duba da wata fuskar duba da yanayin da sharrudan da akayi auren amma meh?
Sai Allah ya sanya wannan aure yazame miki alkahiri kukayi zamanku cikin aminci, har Allah yakarbi rayuwarsa,
Amma kiyi addu'a muga yanda Allah zaiyi damu,
Ni kaina bazanso nakai yata cikin wannan rayuwar ba mijinda bayida cikekken hankali toh Amma idan hakan shine Alkahiri a rayuwarta zata zauna cikin kwanciyar hankali tasamu farin ciki fiyeda wanda ni mahaifinta nabata fiyeda wanda mijinki nabaya yabaki wanda har ayanzu kike yabawa zamanku toh ashirue nake dana mika hannun aurenki ma wannan bawan Allah,
Lokacin da m baban muhammad yarasu nayi zataon Allah yasake sanya rabon zama tsakaninki da mahaifin yan biyu toh sainaga abun ba haka bane domin har ila yau bai dawoba baizo neman ki koma ba nasan yanada dalilinsa da yasa yayi hakan domin shidin mutum ne na kwarai amma bullowar wannan lamari sai hankalina ya karkata har indai ta dalilinki wannan bawan Allah zai samu kafiya toh ina fata Allah ya tabbatarda aurenku idan kuma babu Alkahiri Allah ya watsa batun auren,
Sawwama kanta yana kasa amma maganar mahaifinta tashigeta kwarai da gaske,
Baba yace "nagama tashi kije kiji asanyaye ta mike ta yi masa godiya ta nufi hanyar fita daga falon wacce zata sada ta da nata falon tajiyo muryar Baba yana fadin turomin Ummi, Mama kenan dake saudayawa Baba da sunanta yake kiranta,
Sawwama ta sauya akalar tafiya tayi dakin mama ta fada mata kiranna baba sannan tafito tayi dakinta tasamu Hamdan Da muhammad sunyi mata barna Hamdan ya shafe muhammad da man lotion dinta na shafawa tass,
Advertisement
Tsayawa tayi takasa tabuka komai batama santayaya zata faraba tajuya wajan Mama ta fada mata abunda yaran sukayi dan sau dayawa idan sukayi barna mama ke gyara musu jikinsu,
Ta tsinkayo baba yana fadin Ummi banji dadin maganar da kina fada bayan kin sanar dani abunda yake faruwa ba, kisane ko tanada ra'ayin aurensa idan taji abunda kika fada zata iya canja akala bare dama neman hanya takeyi addu'a kawai zmauyita yinata Allah yasa wannna auren yazame mata alkahiri danni dai zuciyata tagama aminta da auren,
Mama tace "kayi hakuri Baban Hafsa kn sha Allahu bazan sakeba Allah yazaba mata abunda yafi alkahiri,
Amin abunda zaki fada kenan matsayinki na mahaifiyarta, da sallama ta karaso ciki daga tsaye tace "mama yarannan sunyi barna banma san tayaya zan fara gyarawa ba,
Mama tajuyo ta dubeta tace Au bakisan yanda zaki fara gyarawa ba? Barsu a wjaan toh,
Yaranki ta'adin tsiya garesu kekuma sanyin rai bazakiyiwa yaro tsawa ko fada ba da zaran sunyi abu saiki wani marairaice haka ake goyin yara,
Baba yayi murmushi yace "kinsan Mamana da sanyin hali kedai kije ki dubasu, mama tatashi tafita tanata mita da taje kuwa saida tayiwa hamdan dindu abaya danshine mao wayo kuma shi yakama kanin ya shafeshi,
Saida tagama gyarasu ta wankesu sannan tafito tasamu baba da Sawwama zaune suna taba hira anan haka yarn suka taso daga islamiyya su duka suka zauna suna hira kiran Sallar magrib ne yatashi baba Yafice dake akwia masallaci kusada gidan,
Su duka sima tashi kowa ya nufi dakinsa domin gabatarda Sallah."
Kusan kwana tayi batayi baccci ba tanata saka da warwara har tasamu ta tsayarwa da kanta mafita kuma zata tunkari abunda ta yankewa kanta suciya daya hadeda karfin guiwa zata cire kowani irin waswasi ya sanarda amincewarta ga auren yareema kuma zatayi tskaaninta da Allah da nufin Allah yabashi lafiya,
Matsayarda data tsayarwa zuciyarta ya sanya tasmau bacci,
———————
Murmushi ya sakar mata mai kayatarwa sannan ya karaso kusada ita ya zauna cikin yanayi mai cikeda zallan kaunarta ya sumbaci goshinta cikin kulawa yake fadin nagode da kika amince zaki zamoni daga cikin kangin danayi shekara da shekaru aciki."
Bata kaiga maganaba kiran Sallat asubahi ya tarkarda ita daga mafarkinda takeyi,
cikin baccin tayi mafarki da Yareema yanayi mata godiya akan shawar auransa data yanke,
ajiyar zuciya ta sauke samnan takara samun kwarin guiwa ta yanke cewa da safennan zagaje tasamu Baba ta fada masa ta canka shawara,
Da safe kafin Baba yafita kasuwa Sawwama ta tardashi yana karyawa bayan ta gaisheshi sai kuma tayi shiru Baba yace "Mamana kaman kinzo da magana koh?
Sawwama tace "zan jiraka Baba ga gama karyawar tukunna toh kawai Baba yace bayan yagama yafito daga dining din ya sameta zaune a falo yace "ina jinki mamana,
Saida tayi shiru tasake nazari akan abunda zata fada sosai sannan tace "Baba na amince da aurennan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi bab ya kalleta "Sosai sannan yace ina bawani bane ya tilastaki canka ra'ayinki ba?
Girgiza kai tayi tace A'a nazauna tsawon daren jiya nayi tunani akan kalamanka amma baba ina neman wata alfarma,
Baba yayi murmushi yace "ina jinki Mamana,
Baba dan Allan kada kafadawa su Baba Zakari irin mijinda zan aura saboda zaki kalli abun da fuska mai kyauba,
Idan mu munsan munyi dan Allah ne su fassararda zasuyiwa abun dabanne,
Baba yayi murmushi sannan ya mike ya dafa kanta yace in sha Allahu bazasuji ba Allah yabashi lafiya Ahankali ta amsa da amin, mama tazo sukayi sallama sannan yafice."
Da fadawa mama ma itama tace Allah yasa hakan shine mafi alkahiri,
Dama sun yanke shawarar cewa idan ta amince zata sanarwa Hajiya,
Advertisement
Da kanta ta shirya ta nufi gifan Hajiya ga mamakinta farin ciki sosai tagani a fuskrta alokacinda tace mata ta amince bayan kuma ta nuna dafarko akan batada damuwa da amince ki akasin haka, sai yanzu ta fahimci cewa Hajiya ta boye soyayyarta ga auranne dan kada Sawwaman taji zata amince kodan ta faranta mata,
Hajiya cikin murna take fadin in sha Allahu Anty Hafsa sai kinyi alfahari da wannan aure Allah ya saka miki da wannan kyakkyawar niyya da kikayi,
Sawwama ta amsa da amin kawai,
Alokacin takira mai maftaba ta shaida masa amincewar Sawwama,
Mai martaba yace zaizo Alhaji yace basaiya zoba ai yareema dansane shida kansa zai nema mas aauren kuma Hafsa ma yarsa ce yanada yagini baza'a samu matsalaba kida baizoba,
Alhaji ya shirya yanufi wajan Baba dama Sawwama ta sanar dashi zuwannasa dan haka baj fita kasuwa ba bayan yaje sun gaisa da kansa ya rakashi har gidan Baba sa'adu,
Baba sa'adu ya dan gyara zmnsa da mamamki su kansu yan uwan mamaki suke al'amarin Sawwama yanzu yawuce yanda suke tunani,
Saida ya nisa sannan yacewa Alhaji kaima yanzu yarkace dan anzama daya kaima mai bada auranta ne idan ka amince kawai saika amshi sadakinta asaka rana adaura aure,
Sai alokacin Baba yayi magana yace "Inaga Baba basai ansaka ranaba kawai yanzu adaura auren ba taro za'ayiba ba komai ba aure bana farko ba kawia daura idan yaso daga baya tatare gidan mjinta,
Alhaji yace "hakanma yayi sosai bari aje anemo goro ko dabino ya tashi ya aiki driver dinsa akan yasoyo goro da minti dakuma Dabino,
Minti talatin drivern yadawo Alhaji yadauko sadaki a cikin mota yabada yayiwa Yareema Wakili yayinda yaya zakari yazama waliyyin amarya aka daura aurensu,
Bayan andaura suka zauna aka tattauna sannan aka watse kowa sai dai kawai yajewa gidansa da goron aure dama kamar wanda aka irga kowannesu huhun goro daya da cotton na minti daya sai dabino,
Baba ma haka ya isa gidansa da dabinon mama ta taryeshi ta amsa ta ajiye tana masa sannu da dawowa baba yace Yawwa sannu,
Yaya kuka tsaida magana ko har an tsayarda rana?
Eh toh magana ta kare dan Anrigada an daura auren zuwa wani satin idan Allah yakaimu saita tare agidanta,
Mama tace dasauri haka? Ih toh me za'a jira?
Aure bana farkoba bana biyu ba, ina fata wannan dai tayishi har abada Allah ya zaunarda ita lafiya yabata ladan wannan niyya na taimako datayi,
Mama tace amin,
Koda aka fadawa Sawwama batayi mamaki ba fan dama tasan abun bazaija ba,
Haka Hajiya ma tasan abun bazaija ba amma batayi tsammani zaizo da sauri hakaba,
Aka sanarda mai martaba yayita sanya musu albarka yayi murna sosai, sannan ya gargadesu da karsu fadawa kowa."
———-
Sawwama gani tayi kamar wadannan kwanaki sunfi kwoane kwanaki sauri acikjn rayuwarta dan batayi auneba taji har sati yazo an sanya ranarda zata tafi Hajiya zata rakata Amma za'a tafi da mama sai Haleema,
Sawwama tarasa abunda yake mata dadi ga rabuwa da iyayenta ga yaranta domin muhammad kam Hajiya tarigada ta karbeshi ko su Hamdan Baba ya shirya cewa bayan tatafi amaidasu wajan mahaifinsu kawai amma ahalin yanzu hardasu za'a raka mahaifiyarsu,
Jirgin yamma sukabi suka isa masarautar washe gari kuma zasu kamo hanyar dawowa.
Ko Umma ba'a sanarda ita aurenba itadai mai martaba yabarta akan cewa yarinyar tace zatayi tunani,
Su Hajiya kuwa dama tunda sukaji mai martaba yace musu kada su fadawa kowa sunaan kowa yake nufi bai ware wani ko wata ba,
Idanma akwai wanda za'a fadawa sunsan da kansa zai fada,
Ba karamin murna su Umma sukayi ba dan gani sukeyi kamarma yareema yasamu Lafiya ,
Suna zazzaune Umma tadubi Sawwama tace "kishiga ki dubashi yana part dinsa amma bacci yakeyi dan kwanansa uku yana bacci sai yau yatashi baifi 1hour ba yasake komawa,
Sawwama ta mike jiki a sanyaye ta fara tafiya tayo hanyar part din nasa daga falon ta fita zuwa wani dan corridor sai wata kofa data sadata da part dinnasa tangamrmem falone komai na wajan a kimshe kamar ba'a taba shigaba dan tsartar wajan komai na falon farine tass ba'a sirkashi da wani colour ba har labulayen sashin yayi matukar kyau,
Tabude da sallama tashiga Dukda tasan bawai zai amsa bane,
A gefen kafarsa ta zauna tana kare masa kallo kamshi mai masifar dadi a dakin tunda take zata iya cewa bata tabajin kamshi mai dadinsa ba,
Zamanta baifi da 2minute taga yana motsi da alamu soyake ya tashi ta tsura masa idanuwa tana kallonsa sai yanzu take kallon kamannin da ake fadi yanayi da Abubakar sai dai kawai abubakar yafishi shekaru naisa ba kusa ba,
Ahaka ya farka ya daura idanuwansa akanta ya sakar mata murmushi itama ta maida masa sai yatashi ya zauna,
Yariko hannunta yace ina kikaje?
Na tashi daga bacci amma banganki ba karki sake tafiya ki barni idan kika barni banajin dadi, tashafo kumatunsa tayi murmushi tace ganinan bazan kara tafiya ba,
Ya kalleta sannan yace "yunwa nakeji ta mike da nufin debo masa abinci yayi saurin rikota yace karki tafi,
Girgiza kai tayi tace ba tafiya zanyiba abinci zan dauko maka ya saketa fuskarsa ta nuna alamun ya gaskata maganarta,
A yanda tabarsu ta samesu tadubi Umma tace "yunwa yakeji yace zaici abinci da mamaki Umma ta kalleta tace yatashi? Dan ita tunaninta tafito ne bayan taganshi,
Eh yatashi yace yanajin yunwa,
Umma ta dubi Hajiya tace "kinga ikon Allah koh?
Tun bayan tafiyarya bai sake yin maganaba koya farka minti talatin zuwa awa daya yayi yawa yakoma baccinsa,
Hajiya tace "Allah kenan
Daya daga cikin ma'aikatan sashinne tazo umma Tabata umarni akan takawo abinci taje takawo umma tamike tayi gaba tace "biyoni dashi sashin yareema,
Itama Sawwama tabi bayansu suna zuwa dai-dai shiga part din sai taga ma'aikaciyar taja ta tsaya, hakan ya nuna mata ma'aikata basa shiga sashin kenan,
Umma ta juyo ta karbi flask din Sawwam ta sanya hannu takarbi plates da cokala suka shiga azaune ta sameshi kamar yanda tabarshi Umma ta karasa da sauri tana kiran sunansa yayi mata murmushi kawai sannan yajuyawa Sawwama,
Sawwama ta zauna gefe ta hude abincin ta zuba kadan a plate ta tsaya yana juyawa tanaso tabawa Umma tabashi sai take ganin kamar hakan baidace ba saboda yanzu nauyin kula dashi yana wuyanta itakuma bazata iya bashi abincin gaban Umma ba fahimtar hakan datayi ya sanya tatashi tafita itakuma tafara bashi a hankali yanaci karyafe ya koshi ya bakinsa,
Bayan yagam yarike hannunta gam kamar wacce zata gudu anan haka su Mama da Haleema suka shigo hardasu Hajiya,
Mama itadai zata iya rantsewa cewa wannan lafiyarsa kalau dan babu abunda yayi kamada rashin lafiya a tattare dashi,
Yanda taga kamanninsa da muhammad ma sai tayi danasanin son hana Sawwama auren datayi abaya,
Yanayin yanda dukaga yana tafiyarda al'amuransa babu wanda zaice yana tattare da wata matsala sai dai kawai hankalinsa gabaki daya yanakan Sawwama ko kallon kowanne daga cikinsa bayayi,
Ko umma ce tayi masa magana sai dai kawai Yayi murmushi,
Fitowa sukayi sukabar Sawwama acan itama saida yayi bacci sannan tasamu tafito,
Ta tardasu Umma natayiwa su Mama godiya Mama tana fadin "Ah haba babu komai anzama daua fatanmu dai Allah yabashi lafiya ya yaye masa sannan ya tsare gaba su duka suka amsa da amin,
Anan suka raba dare sai bayan sun tashi zasu tafi masaukinsu kan Sawwama ya daure tunani takeyi shin tabisune kokuma tatsaya takwana wajan yareema Umma kamar tasan abunda take sakawa a cikin zuciyarta tace kije wajansu Mamanki ki kwana zuwa gobe insun tafi zaiki dawo nan tunda naji sunce gobe zasu koma,
Dama hakan tafiso dan Haka a wajannasu ta kwana da dare Mama tayita yimata nasiha ita kuma Hajiya tana gwada mata yanayin yanda zata tafiyarda rayuwar acikin masarautar,
Da safe bayn sunyi breakfast suka wuce wajan mai martaba yayi musu godiya Sannan yayi mata nasiha sosai yadubi Sawwama yace "in sha Allahu bazakiyi dana sanin wannan zabi da kikayi ba, zamu rikeki tsakani da Allah dan yanzu gabaki daya mun zamo dangi daya, ki zauna kamar yanda zaki zaune a gidanku Allah yayi miki albarka yabaki kadan abunda kikayi su duka suka amsa da amin mai martaba yayi musu kyauta dan nuna godiyarsa da abunda sukayi masa har suga rabu yanayi musu godiya."
Karfe sha daya na safe su Mama suka kama hanyar komawa hardasu hamdan da muhammad sai takeji kamar subar mata yaran,
Lokaci kalilan da tafiyarsu tafara kewarsu tana zaune ita kadai sai hawaye kawai taji yafara zirya akan kumatunta har tayi sallar azahar tanaji babu dadi dan haka kawai saita shiga wajan yareema suna zaune ahaka bawani magana sukeyiba sai dai duk motsinta saiya tambayeta meya sameta har gajiya takeyi da amsa masa,
Har magrib bata fitada tana dakin idan lokacin cin abinci yayi umma tana kawo musu abinci."
Yareema ya rigata kwanciya, tun datsu yayi bacci dan haka itama saida tagama addu'ointa sannan ta kwanta can nesa dashi bacci yafara daukarta taji ya matso kusada ita a hankali taji ya sanya hannuwansa ya rungumota ta ciki."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial7 Chapters
Calamity of Hope - A Divine Apocalypse LitRPG
Hope is a dangerous thing. Yet for Mark, it's the only thing still keeping him alive. Thrust onto a dying world by the Crazed Titan, and forced to suffer through the whims of ancient deities, he must first fight against the titan's maddening power coursing through his very veins. And from the relentless waves of monsters, to the poison that is the aether-saturated atmosphere, the residents of Mark's new world have all but resigned themselves to their inevitable fate. Will Mark's efforts manage to restore the people's hope? Or will the titan's gamble plunge the world into a new age of calamities? Author's Note: Contestant in the [Royal Road Community Magazine]. This is supposed to be a somewhat darker power fantasy, were the MC struggles to overcome and come to grips with the obstacles that lay before him. What to expect: - A simple LitRPG system - Challenges & loss, not just wins - Few, hard won but versatile abilities - Desperate people in an unfair world What NOT to expect: - real world takes on religion - harem/romance etc. Feedback is both welcomed and encouraged!
8 59 - In Serial9 Chapters
Seeking the Lost Relic: An Interactive Litrpg
Join Theric the ice wielding Guardian of the Frost, Aeslin the blade channeling Silver Mage, and Xaveon the mysterious vampiric Spell Shroud, as they embark on an epic quest to retrieve an ancient lance of mystery and great power. Each chapter you, the readers, will be able to choose the next part of their quest. Will you the seek the dungeon or head to the tower? How will they take down the epic boss battle? Do they raise the army to strike at the heart of the vampire city? Who knows? Only the readers will decide!!! Will our intrepid young adventurers complete their quest? It is up to you!
8 171 - In Serial6 Chapters
Dungeon in a xianxia
Where am I? hey why the hell are those people wearing robes and swords?! whats a dragon doing there?!! what the hell is a dao!?!? why does this look like a xianxia?! note-this is just for fun, I'm an amateur writer who's just trying this out. I accept criticism, and this novel might not be that good enjoy. P.s-may or not be gore added the tag just in case pp.s-if some thing sounds like something from another novel please tell me and I'll change it it's probably an accident ppps-I will not update regularly sorry but I'll try at least once a week pppps I'm bipolar and so is my writing and my characters Ppppps point out any gramer problems
8 140 - In Serial40 Chapters
The Lonely Girl
When Cami moves in with the 2 most popular guys in school in a new foster home placement, she realizes that her tragic past just might make it so that she will stay lonely forever. ***Cami has been lonely since her life was destroyed five years ago and she ended up in foster care, bouncing around from house to house with no set direction--until she ends up at Hartingrove Academy, where she meets the enigmatic player Colton, and his best friend, golden boy football star Parker. The boy's feud threatens to make Cami collateral damage as she finds an unlikely ally in the outcast brother of her crush--Grey Hartingrove--who just might have even more demons than her. But when her home placement is changed and she finds herself living in Grey and Parker's house, the lines of romance become even more blurred.Faced with insurmountable obstacles in her home and social life, Cami realizes that, in the end, she might just be truly alone after all.
8 201 - In Serial6 Chapters
Rise Of The Black Dragon The Rising Of The Shield Hero X Male Reader
Y/n L/n a boy who watches The Rising Of The Shield Hero he wants to go into that world to teach Motoyasu and the bitch Myne a lesson thankfully his wish has come true he suddenly gets transported to the world of Melremarc and he gets to follow out his dream but he gets to have any power he wants so let this adventure begin
8 127 - In Serial13 Chapters
Sherlock Holmes: A Study In Scarlet by Sir Arthur Conan Doyle (On-Going)
(Not mine.)Book 1 of Sherlock HolmesA Study in ScarletWritten by Sir Arthur Conan DoyleSynopsisDr John H. Watson meets the great detective Sherlock Holmes and together they solve a case of murder, in which Watson is amazed at Holmes' "science of deduction".The novel is split into two quite separate halves. The first is titled "Being a Reprint from the Reminiscences of John Watson, M.D., Late of the Army Medical Department". This part is told in first person by Sherlock Holmes' friend Dr Watson, and describes his introduction in 1881 to Holmes through a mutual friend and the first mystery in which he followed Holmes' investigations. The mystery revolves around a corpse found at a derelict house in Brixton, London with the word "RACHE" scrawled in blood on the wall beside the body.
8 116

