《ƘADDARAR RAYUWA》K page 98
Advertisement
*ƘADDARAR RAYUWA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡
Written by
zaynab bawa
#Follow me on
"
Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
* Y'AR FARI*
* YARIMA FAYAD* paid 200
Page 98
Ana shirin kiran magrib taji motsinsa kamar kotsinsa amma kuma data matsa kusa dashi sai taga kamar bashine yayi motsinba,
toilet tanufa danta dauro alwala sai tajira akira Sallah,
ta dauro alwala tafito Ganin mutum a zaune yayi mugun razanarda ita dasuari taja da baya ta dafe kirjinta,
Ajiyar zuciya ta sauke bayan takarewa yareema dake zaune kallo ta isa wajan fuskarta dauke da fara'a ta zauna ta sanya hannu ta tallafi kumatunsa ido ya tsura mata kamar maison gano wani abun takasa gane wane irin kallo yake mata, kamar wanda yakeyi mata kallon rashin sani, kallo mai cikeda tuhuma,
Cire hannunta tayi daga fuskarsa ganin yanda yake dubanta,
Ina Umma? Taji ya tambaya
Ba irin wannan muryar tasanshi dashiba dan haka jikinta har rawa yakeyi tamike tafice bata samesu a palour ba domin dukansu sun shiga sallar magriba sai juyawa tayi tanufi ciki yanda yake mata nune dashin dakin Umma a kofa ta tsaya tayi Sallama Umma wacce fitowarta daga alwala kenan ta amsa jin muyar Sawwama ya sanya tafito dasauri cikin sanyin murya tace Umma yafarka yana nemanki,
Umma tace "yana nemana? Yaya akayi harya nemeni?
Sawwama tace "haka naji yace ina kike, Umma tace "toh muje tashige gaba Sawwama na biyeda ita abaya,
Tana shiga dakin ta ganshi zaune tadan karawa tafiyarya sauri harta isa bakin gadon ta zauna, shi take kallo kamar yanda shima ita yake kallo, murmushi ya samar mata irin murmushin data dade bata ganiba murmushin yake yinsa a duk lokacinda suka zauna tare da ita suna hira kota sanya masa albarka a wannan lokacin sai yayi Irin wannan murmushi dayayi yanzu,
Umma ta shafo fuskarsa da tafin hannunta tace "Yareema? Kana jina? Kana fahimtar me nake cewa?
Ka ganeni kuwa? nice Ummanka,
Murmushin yayi yace "Ummana cikin wadannan tambayoyin wanne daya kikeso na amsa,
Sunkuyarda kai tayi ta sanya hannunta tana buga saitin zuciyarta a hankali a hankali yayiyin shikuma ya rike daya hannun da matse hannun da karfi sannan tadago ta kalleshi tana kokarin danne kukan dayakesp yaci karfinta iska ya furzar sannan ya jata jikinsa yana buga bayanta a hankali a hakandai saida taci karfin kukan dan bata barshi ya fitowa sakeshi tayi sannan ta mamaye fuskarta da murmushi mai kayatarwa wanda ta dauki lokaci batayi irinsa ba,
A fili take furta Alhamdulillhi, Alhamdulillhi Alhamdulillhi, dukkan yabo da godiya ya tabbata agareka y Allah, ya Allah kaine maji rokon bayinsa yau Allah yasa ma dawomin da Yareema, yareeman dana sami Allah na gode maka tafada hawaye na gangarowa akan kumatunta,
Yareema yasa hannu ya share mata hawayenta dake kwaranya akan kumatunta,
Iska ya sake furzarwa kamar wanda bayaso yayi magana sai kuma ya daure yace "Ummana koda bansan abunda yafaru ba kuma banida tabbacin ko wani abun yafaru amma nasan komai ba lafiya ba akwai wani abun daya yafaru dani naji canjawar yanayi sosai ajikina,
jikina yabani hakan, ganin wannan yarinyar adakina dakuma yanayinki ya sake tabbatarmun da abunda nake tunani."
Umma tace "Yareema yanzu ba lokacin wannan zancen bane amma ita wannan yarinyar daka ganta itadin matarka ce,
Sawwama tun datsu ta zuba musu ido kawai tana kallonsu ganin yadago ya dubeta sai tayi kasada kanta,
Yadade yana nazari akanta kafinnan ya juyarda kansa wajan Umma yace "ki sanar dani abunda yafaru wanda har nayi aure banida masaniya akan hakan,
Batareda tabashi amsa ta mike tace "ina zuwa ficewa tayi mintuna kadan suna zaune itadashi sai kallonta yakeyi yanataso tadago su hada idanuwa sanin yana kallonta ya sanya bata dago ta dubeshi ba ahaka Umma tadawo ta samesu ta zauna yanda tatashi tace jira mai martaba yana hanya na tura a isar masada sako zaka ganshi nan bada dadewa ba,
Advertisement
Jijjiga kai kawai yayi yanaso yasan abunda yafaru dashi amma yasan Umma koda zata bashi amsa toh bayanzu ba tunda har ya tanbaya sau biyu bata bayarba sai dai yajira da kanta taji zata bada din saita amsashi,
Lokuta kalilan Su Ummi suka shigo itada Ruma, Ruma tana shigowa yakira sunanta tanajin haka ta daka tsalle ya sake ihu,
Ummi tace "ke shasha meye hakan kuma,
Jijjiga Umma takeyi tana ihu tana fadin Umma yaya yareema yakira sunana, dariya Umma tayi tace Yayanki yasamu lafiya Ruma,
30minute Sawwama tamike ta dauki sallaya tabar wajanda suke taje van gefe tana Sallah sai lokacin Unma ta tuna itama batayi sallar ba fitowarta daga alwala kenan taji sallamar Sawwama,
Mikewa itama tayi tace barinayi Sallah yanzu zan dawo,
Yareema yace "Wace Sallah akayi?
Umma tace har ina kiran isha'i amma ko magrin dinma mu bamuyiba,
Jikinsa yayi sanyi tabbas yasan wani gagarunin al'amarine yafaru dashi, mikewa yayi yace shina zaiyi Sallahn yashiga ya dauro alwala ya fito bashi waje Sawwama tayo yayi magrib ya mike zai fita Ummi tace "Yareema ina zakaje?
Masallaci yabata takaicacciyar amsa,
Ummi ta mike tana fadin kayi hakuri ka rufa mana asiri dawo kayi Sallarka agida idan aka samo bakin zaren ka fita ka jira nasan mai martaba ma yanzu zai karaso,
Zama yayi ransa yana masa daci wai yau shine da Sallah a cikin gida kamar wata mace,
Komawa kan sallayar yayi ya gabatarda sallar isha'i,
Bayan idarda Sallar isha'i mai martaba ya iso su duka suka saika kasa mai martaba yazauna akan kujera idanuwansa yana kan yareema dake zaune akan Sallaya, bai nemi karin bayani ba sukuma babu wacce ta sanar dashi domin sunsan shirunsa akwai abunda yakeso yagano ne,
bayan ya Sallame ya juyo ya dubi mai martaba dake kallonsa ya sakar masa murmushi,
Sawwama dake kallonsa aranta tana tunanin shikuma dabi'arsa kenan?
Kafin yayi magana sai yafara tura aiken murmushi,
Khaalifaah mai martaba yafadi,
Na'am yareema ya amsa,
Alhamdulillhi mai martaba yafadi sannan ya kalleshi yace "sauki yasamu khaliifa toh Allah ya kara maka lafiya ya kareka su duka suka amsa da amin bai dade a wajanba ya mike yana fadin bari naje zuwa gobe saina dawo ka kula sosai da ibada yau da dare kar ayi bacci a zauna ayita fadawa Allah bukatu ayita kiyamul laili ha matarka nan saita taimaka maka nima nawa wajan ba baccin zanyiba mahaifyarka ma nasan haka zuwa Safiyya sai musan abunyi, Yareema ya mike ya rakashi suna zuwa falonsa ya tsaidashi daga nan shikuma yacigaba da tafiya,
Su Umma ma dare suka raba anan sannan suka tafi suka barshi dagashi sai Sawwama,
Daganan aka hau zaman kurame sai da dare yayi nisa sannan ya mike ya shiga ya dauro alwala yafara Sallah kamar yanda mai martaba ya umarceshi ganin haka ya saya itama tatashi ta yi alwala tazo ta jonashi
Akan sallayar bacci ya dauketa saida rana tafara fitowa sannan tafarajin wani sautin kira'an alqur'ani mai dadin gaske a hankali ta bude idanuwanta ta saukesu akanta ganin gari yayi haske ya sanya ta mike dasauri tashige bandakinta dauro alwala yana zaune akan Sallaya yana karatu jin motsinta ya sanya ya sauka gefen carfet itakuma tahau kan Sallayar tayi sallah,
Tana zaune a wajan cikin sanyayyar muryarta tace "ina kwana?
Saida yakai karshen ayarda yake karantawa sannan ya rufe kur'anin ya dago ya dubeta."
*Continuation*
Fuskarsa daukeda murmushi cikeda kulawa ya amsa gaisuwarta sai kuma suka zauna shiru babu wnada yasake cewa komai lokaci-lokaci yake dagowa yana kallonta iyakuma tunda tayi kasada kanta bata sake dagowa ba,
Bani ruwa taji yafadi kamar wacce take jira tamike dasauri tafita ta dauko ruwan hadeda cup ta zuba ruwan sannan ta mika masa ya amsa yayi bismillah hadeda kafa kansa saida ya shanye sannan ya sauke yaja nunfashi sannan yace "nagode,
Advertisement
Murmushi kawai tayi sukaci gaba da zaman kurame har Umma tayi sallama tashigo ta samesu a haka,
Fiskarta cikeda walwala rabonta da tayi walwala irin haka tun kafin ya kwanta rashin lafiya,
Murmushi ya sakar mata yana fadin Ummana Barka da safiya ina kwana?
Ta zauna can gefensu sannan ta amsa da fadin lafiya kalau yaya kwanan jikinnaka?
Alhamdulillhi yabata amsa,
Sawwama ma ta gaidata ta amsa cikeda fara'a tana tambayarta mai jiki saida tadan saci kallonsa wanda shidinma ita yake kallo sannan tace "jiki Alhamdulillhi,
Umma tace " toh Ma sha Allahu mungodewa Allah gabaki dayanmu Allah ya biyaki da gidan Aljanna wannan sadaukarwa da kikayi ubangiji kadai zaiyi miki sakayya, mu kam anamau wajan sai dai mu biyaki da kyautatawa amma ba kwatankwacin yanda kikayi mana ba,
Shi bai fahimci zancen ba sai dai ya dauki hint,
Suna zaune ta mike tadubi Umma tace barina hada breakfast,
Umma tace "toh tafice tayi kitchen kamar dai yau haka taga matar jiya ta gaidata itama bata amsaba kuma bata maida mata gaisuwarba kuma koda ta gaisheta ba amsawa zatayi ba,
sawwama zata fara aiki tajiyo muryar matar tana fadin" Rabki shi dade ki fadamin abubda kikeso saina dafa na aiko miki,
Batareda ta kalletaba tacigaba da aikinta sannan kuma tabata takaicecciyar amsa,
"Babu komai
Saida tagama sannan ta kauce daga wajan,
Ta deba kai tsaye tayi shahshinsu,
Ayanda tabarsu haka ta samesu suna taba yar hira sai Ummi da Ruma da suka karu adakin,
A gefensa ta ajiye da plate din sannan ta zuba ta mika masa ya karba hadeda yimata godiya,
Zata sake zubawa Umma tace har indai mune mun rigada munyi karin kumallo ki zauna kawai ku karya,
Plate din ya tura mata gabanta sai takasa gane abunda yake nufi agabansu Umman zasuci abinci tare?
Daukan wani spoon din yayi ya sanya a cikin abincin ta zaune ta dauki spoon din jujjuyawa takeyi kawai amma takasa kaiwa bakinta shikam ko ajikinsa cin abincinsa kawai yakeyi, ganin abunda takeyi yasanya ya tsaida nasa cin abincin cikeda kulawa yace "meyafru? Naga bakyacin abincin, sai lokacin hankalin Umma yakai kansu murmushi kawai tayi danta gane Sawwama nauyi takeji,
Umma tace "nauyi takeji shiyasa bataci kizuba naki daban karki zauna da yunwa,
Hannunsa ya daga cikin abincin yace "no taci wannan zan zuba wani,
Dasauri ta girgiza kanta tace "No zanci basaika zuba wani ba,
A hankali tafara tsakuran abincin takai bakinta kadan taci sannan tace "ta koshi,
Shikam dai bai koshi ba dan zama yayi yaci abincin sosai kuma yayi masa dadi,
Dama ta lura tun bayida lafiya baya wasada cikinsa yana farkawa abunda yake fara tambaya shine abinci,
Sai wajan Sha daya kafin mai martaba yashigo bayan sun gaidashi duka yadubi Yareema yace Khaliifa yaya karfin jikinnaka?
Murmushi yayi saannan yace "Alhamdulillhi,
Toh ma sha Allah haka akeso Allah yasake warware mana al'amura, su duka suka amsa da Amin,
Saida yayi gyaran murya gabaki dayansu suka dawoda hankalinsu gareshi sannan yace "Nasan bakada masaniya akan abunda ya sameka da halinda ka kasance aciki,
Wata jarabawace ta sauka maka tsawon lokaci wanda muka kasa gane kan lamarin domin lamarine mai wuyar sha'ani, tsawon lokaci ana abu daya bazamuce dai babu cigaba ba angodewa Allah domin wani lokaci al'amuran saimu gansu da sauki wani lokacin kuma abubuwa sukici suki cinyewa,
Kwanakin baya Allah yakawo mana Wannan baiwar Allah matarka Hafsatu ya nuna Sawwama tundaga zuwanta sai Allah yafara buda mana al'amura muka fara ganin canji sai sauki yazo,
Mungodewa Allah daya kawo mana ita cikin rayuwarka, bansaniba amma dole akwai wata alaka mai karfi a tsakaninku ko ince tsakanin abunda ya sameka dakuma ita domin itace makarin Al'amarin,
Mai martaba dalla-dalla yafi abubuwanda sukayita faruwa ya sanarwa Yareema, har zuwan Sawwama,
Yareema saida yayi kwallah jin tsawon shekaru yana wannan, jikinsa yabashi kam yana cijin bacewar hankali na wani lokavi amma hai dauka abun yayi misa hakaba,
Kuma gashi wai matar dan uwansa itace tadawo matarsa ta dalilinta Allah yakawo masa saukin jinyarda yayi shekara da shekaru yana fama da ita,
Muryar mai martaba ta katseshi da fadin ko akwai wani abunda kasani gameda wannan lamari?
Nisawa yayi sannan yace "Abba haka yareema yake cewa mai martaba Abba kamar yanda yayansa suke fada masa,
Munyi waya da Hajiya na shaida mata zanje can dama kamar lokacin danake zuwa ne,
Nadauki hanyar garin kafinna isa nafara rasa hankalina zuwa isana garin narasa hankalina gabaki daya amma zan iya fadan abunda na aikata tabbas a wannan lokacin bana cikin hayyacina amma nasan abubuwanda yafaru,
Bansaniba nasamu kaina cikin matsananciyar sha'awa dana kasa iya controlling kaina kamar mahaukaci haka na kasance yayibda tukinma ya gagareni, tsayawa yayi kamar wanda bayason cigaba da magana har saida mai martaba ya tanka yace "akwai wani abunda yafaru bayan haka kokuma ka mance bazaka iya tunawa ba?
Girgiza kai yayi yace "koda nace bana cikin hankalina amma zan iya tuna abunda na aikata,
Na fito daga mota domin nakasa tukun narasa abunda yake damuna wani irin nunfashi kawai nakeyi, yayinda hadari ya hado sosai a lokacin walkiya da tsawa kawai akeyi,
Gabban jikina gabaki daya sun mutu, jinakeyi idan ban sauke sha'awata ba alokacin mutuwa zanyi amma dukda hakan na gwammaci na mutu,
Ana haka saiga wata yarinya kamar wacce aka jefota,
Izuwa yanzu Sawwama gabanta faduwa kawai yakeyi domin tafara fahimtar yanda zancenaa ya dosa,
Abba nayiwa wannan yarinya fyade ya karashe maganar murya na rawa, sannan yacigaba da fadin koda bana hayyacina amma bazan iya mantawa da mummunan aikin danayi ba,
Yakasa karasa maganar yayinda zuciyarsa take zafi nunfashi kawai yake fitarwa,
Dakin ya dauki shiru na wani lokaci sautin numfashinsa kawai ake iya jiyowa,
Ya dauki mintuna kafin yace "a wajan nabarta nakamo hanyar gida domin bazan iya zuwa wajan Hajiyaba, naji kawai nadawo gida bayan nadawo kuma daga nan bazan iya sake tuna abunda yafaru ba,
Mai martaba jiki a sanyaye yace "kafin kafita kaci wani abunne?
Batareda bata lokaci ba yace naci abinci, agida ko awaje? Ya gida yabada amsa, jijjiga kai yayi yace aje ajira masa matarda take daga abinci a shashin Umma,
Rumace tafita domin kirannata,
Umma hawaye kawai takeyi idanuwanta har kala suka canja, tarasa me yareema yake fada, tarasa me zuciyarta takejina gabaki daya har wani daci takeyi mata,
Yareema yacigaba da fadin,
Abba na aikata laifi domin banida dalili ko uzurinda zai wanke abunda na aikata bansan wani hali nabar yarinyar ba tamutu tana raye, Abba zanje na nemeta duk yanda take kuma zan karbi kowanne irin hukunci ne,
Sawwama takasa rike kukanta domin yaci karfinta kuka kawai tasake mai karfi su duka suka juya suna kallonta babu wanda ya iya rarrashinta amma mai martaba ya zuba mata idanuwa yanaso ya karanci wani abu,
Umma tayi karfin hali ta dafata tace "kiyi hakuri da abunda mijinki ya aikata nasan zakiji zafi amma inada yakinin bahaka Yareema yakeba dole akwai wani abun akasa,
Mai martaba ya fitarda numfashi mai nauyi ya gyra zama sannan yace idanna kintata dai-dai ba abunda ya sakata kuka ba kenan tana kukane saboda itace yarinyar da yareema yayiwa fyade sai yanzu nagano alakarta dashi wanda su kansu basusanda hakanba,
Saurin daga hannuwa daga cikinta Umma tayi danta razana sosai,
Itakuma Sawwama kukannata ya karu su dukansu kallonta sukeyi ko zata musanta abunda mai martaba yafada amma a'a kukanne kawai takeyinsa,
Mai martaba yace "ki tabbatarmun Hafsatu kece wannan yarinya ko bake bace?
Har yanzu bata bada amsaba kuka kawai takeyi wanda hakan ya tabbatar musuda zarginsu,
Tsugunnawa Yareema yayi akan kafafunsa ya riko hannunta yakasa furta komai yayinda itakuma kukan kawai takeyi ko kokarin kwace hannun batayiba,
Ana haka ruma tashigo tace mai abincin tazo mai martaba yabada Umarni ashigo da ita sanna yace Ruma tafita,
ganinsu ahaka yayi matukar tsoratata dama ita tunda taga wata tafara shugowa tana dafa abinci jikinta yabata akwai matsala,
Da zube guiwowinta akasa tana kwasar gaisuwa babu wanda ya iya amsa mata,
Mai martaba kai tsaye yace "Abincinda Yareema yaci ranarda ya kwanta rashin lafiya me kika zuba aciki?
Jikinta yadauki rawa alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita tafara kame-kame,
Amma gwarjinin mai martaba ya sanya takasa canko karyarda zatayi ma,
Shekara nawa kikayi kina zuba abu a abincinsa? Amsa daya kuma gaskiya nakeso idan baki bani yanda ya kamata ba hukuncinki zaiyi tsanani domin babu azzalumi kamar mutumin daka yarda daci ya zalinceka,
Shekara tara tafada sannan ta saka kuka tana fadin ayi mata rai, bazata sakeba,
Murmushi kawai mai martaba yayi sannan yayi umarni atafi da ita,
Bayan sun fice yace "ayanda na fahimci lamarin asirine abune mai yiwuwa sunyi tsawon shekaru sunayi bai kamashi ba shine suka yanke shawarar farawa da abincinsa, ta iya yiwuwa abun sha'awa suka bata dafarko tazuba masa hadeda asirinsu domin sai alokacin bayida tsarki zasu samu cin gabaka akansa, saboda sunga baida mata bare su kintaci lokacin zai tara da ita kuma yareema kamilalle ne bare asamu hanyarda zata sanya yasamu najasa ajikinsa,
Dole wannan hanyar zasubi kafin su samu su aikata abunda sukeso shine sukabi hanyarda zasu sanyashi yayi mummunan aiki,
Ina kintatar abunda yafarune bance lallai hakan bane yafaru amma babu yanda za'ayi wannan lamari ya kaucewa haka, kuma koda bamu saniba alamu ya nuna mana ita yarinyar daya tarada ita itace suka hada makarin ciwon da ita, atunaninsu baza'a taba samunta ba,
Wani abunda basu saniba shine da Allah yaga dama toh da zai bashi lafiya koda bada makarin ciwonba,
Amma sai Allah yagwada musu iyakarsu ya gwada cewa duk nisan wannan makari zaizo ya sameshi har yanda yake, yabarsune sunyi ikonsu an wani lokaci Ahalin yanzu kuma zai gwada musu nasa ikon wanda ya zarce duk wani ikon mai iko,
Babu wani mai iko sai wanda Allah yabashi damar yayi hakan."
Yadubi Sawwama yace "Hafsatu ba ina fadin wannan abun bane dan yazama dalilin da zaisa na wanke yareema a wajanki kona kareshi ba,
Tabbas Yayi miki laifi mummuna ya aikata miki ba dai-dai ba ya kuntatawa rayuwarki,
Amma a matsayina na mahaifi gareshi domin ayanzu nine mahaifisna ina baki hakuri kiyi hakuri bawai ina baki hakuri bane dan ki yafe masa ba A'a wannan shi zai nema, ina baki hakurine saboda abunda aka miki mu dukanmu mun cancanci mubaki muneni gafararki, nasan a wannan lokaci rayuwarki ta kasance cikin kunci ta dalilin abunda ya aikata miki amma shi bawa ako'ina yake baya wuce kaddararsa ke dashi haka KADDARAR RAYUWAR ku tazo."
Ba editing fa dan ina school ma na karasa wannan shafin dan na jiya baiyi yawa ba kuma banaso pages din su haura yanda nake tunani."
✔️ote
Comment
Follow
Share plss
To be continued
Zaynab Alabura
💞
Advertisement
- In Serial18 Chapters
The Axe Falls
-This story does -not- have a Harem.- -This is not a finished product and will contain spelling/grammar/editing errors-Dominic has lived his life in a backwater village without any hope of attaining a strong Class. His life was destined to be lived as a Villager at worst, or a Farmer at best. A young man lacking in prospects, wealth, or a future. Destined to live and die without much to show for it. Except over the next day, he's going to get everything he hoped for, while also losing anything he depended on. He'll go from being a nobody to a Prince-In-Hiding, becoming the last of a long thought extinct Royal line. To wield the family's weapon and take back the throne that was stolen from his ancestors. It's time for the axe to fall, and heads to roll.
8 382 - In Serial13 Chapters
Monster Buffet
Earth was changed forever when the first gate opened. Damon's parents were among those who survived the event.Most of the people born to the survivors of the first gate had inordinate powers compared to the other avatars. Incredible systems, skills, and stats. Damon only gained incredible struggles. He fought tooth and nail just to provide for his parents, spending years raiding, but was never able to level up. Trapped inside of a gate and abandoned by his party, he finally learns what it takes to level up- and it's all you can eat. Inspired by stories like Solo Leveling and Dungeon Mage
8 190 - In Serial18 Chapters
The Paradigm - LitRPG Apocalypse
Blair Corbin finds herself whisked away from her first-ever job interview and to say she’s confused is an understatement. However, she’s a realist. If something has happened, it has happened. She has to live with its repercussions, and Blair now finds herself in a concrete jungle where people are more than willing to throw each other under the bus and beasts roam the streets. In a world where electricity has disappeared and everything has collapsed, she struggles to find her place among the survivors. She has no skills that are of use to this new community. After all, what use is a programmer when there aren’t any devices to run her code? That's when she realizes that she's good at killing things. Tread carefully. Despite what the Cover may say, the Protagonist will not get a hold of a trident for a good while. Those things are like mid-game weapons, you know? Average Chapter Length: 2k - 5k Schedule: 1 Chapter on Fridays
8 121 - In Serial130 Chapters
Incursions
This blurb concerns Incursions book 1: Incarceration. If you could buy superhuman abilities, but they might kill you—or worse—would you do it? Ten years ago, in a world not so different from our own, people with powerful abilities appeared. The new powers were dangerous, dangerous to acquire—dangerous to have—dangerous to wield. World governments raced to find and eradicate the abilities and those who possess them while using the media to rule by fear. Whereas corporations sought to exploit the abilities for profit. Raz Owens was living the dream - a rising star at a job he enjoys, a girlfriend he loves, but it all comes crashing down when Raz disregards his late father's advice. He is pulled into a chaotic underworld of clandestine labs, shadow organizations, and super-powered criminals. Used as a human test subject in a place where few survive the day, he must last long enough to escape. His only advantage? A power that seems nearly useless—a heads-up display. Contains: monsters, violence, death, dismemberment, gamelit, superpowers, superpower consequences, good guys, bad guys, good guys who might be bad guys, bad guys who think they are good guys, good guys that might go bad, bad guys that might turn good, guns for hire, competence, incompetence, continence, incontinence, conspiracies, and some of what I just said wasn't true. This story is written in third person limited POV. That means you can expect to know many of the thoughts and inner dialog of one character, and only see the actions of other characters. This POV does include scenes without the main character, and thus the reader can and will know things the main character does not. Further, this means characters act on what they know, which is almost always less than the reader knows. Something else to know. These books do not hold your hand. If you're reading it and thinking "Gosh, why aren't 'they' doing some 'obvious' thing." Bad news. You probably missed something that explains exactly that. If you're seeking a light read that doesn't ask much of you as the reader, you're invited and very welcome to come on in, but this might not be the story for you.
8 167 - In Serial73 Chapters
Trial of Monsters and Summons
Humanity faces complete annihilation after nukes are launched all over the world at the end of WW3. A deity intervenes moments before the bombs explode, preventing the destruction of all life remaining on Earth. This action isn't without a price though, as the deity gives humanity a chance to survive by placing them in a trial of its' own making to prove their worthiness. Thus beginning the Era of Summoning, and everything humanity knew is turned on its' head. Suddenly the world revolves around summons being used to fight monsters hellbent on wiping out humanity. "Will humanity band together to become stronger and fight off the monster hordes, or will they remain as they were and continue on the path they were previously set on and bring about the complete annihilation of their race?" Link to my Patreon if anyone wants to support me- https://www.patreon.com/Porkiepie PayPal- PayPal.Me/lucasbaird99 I've also created a Discord for the novel with the title as the server name, I'm still pretty new to it though. Link- https://discord.gg/Y8X2ZCA
8 125 - In Serial44 Chapters
Resurrect Nobody
Dreams are concepts that should guide you through life on a path towards a better future. For Colt West, his dream brought his life to a complete standstill. One day, as he is making his way through the halls of his university, he crosses paths with the one thing he wants to destroy: Death. This incident ends his life as he knows it, leading him down a spiral of madness and insanity. Having been given a second chance at life, will he be able to capitalize on it to seize his dream of resurrecting the dead?
8 86

