《ƘADDARAR RAYUWA》Q page 10
Advertisement
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Haske writers association💡
Writing by
Zaynab bawa
Follow on
Page 10
Ahankali ta amsa sallamar sannan ta maida kanta qasa,
Ajiyar zuciya yasauqe har saida sautin sauqar numfashinsa yafito,
Wanda hakan yayi sanadiyyar qara d'agowa ta kalleshi idanuwansa yana kanta d'agowar tane ya sanyashi dauke kansa gefe,
Baisan dalilin dayasa yaji wani sanyiba alokacinda ya daura idanuwansa akan fuskarta,
Yarinyar tanada nutsuwa da kamala komai nata kaff-kaff take yinsa,
Itama anata wajan tunani takeyi dama zai dawo?
Itakam tama gama cire rai da dawowarsa, nisawa tayi sannan tace sannu da zuwa,
Muryartace ta katse masa tunaninsa tana fadin sannu da zuwa,
Cikin zuciyarsa ya furta Ya Allah dai daida muryarta sanyi gareta,
Muryarta yana tafiya dai-dai da yanayinta tanada sanyi sosai hakama muryarta,
Ahankali ya amsada yawwa,
Baice komaiba ya miqa mata 200 dari biyu yace tabashi,
Yaso ya bata dari biyar saiya bar mata canjin amma dayayi la'akarida abunda yafaru ranar,
Sam baiso tayi masa gurguwar fahimta,
Kar6a tayi ta zuba ta miqa masa, kanta yana qasa, tarasa dalilin dayasa yakeyi mata kwarjini sam takan rasa duk wata laka na jikinta idanta kalleshi,
Shiyasa take kiyayewa yin hakan,
Sanya hannu yayi ya kar6a yajuya batareda yace komaiba,
Yatafi,
Yana tafiya tasauqe ajiyar zuciya,
Saida har yahau machine sannan tadauke idanta daga kallonsa,
Shikuwa tunda yatafi bai juya ba, har yatada machine dinsa yayi gaba,
Sauqe ajiyar zuciya tayi mai qarfi yau dai
tarabu da kudinsa ta huta tafadi cikin zuciyarta,
Yanzu koda bai qara dawowaba banda wata damuwa,
Shima gida yawuce kai tsaye bai budeba har sanda yayi sallar magrib,
Yana budewa ga mamakinsa yaga abu dayawa,
Mai wannan yarinyar take nufi?
Kyauta ta zuba masa haka kokuma ta maida masa na kudinsa na ranar,
Ko tantama babu wata zuciyar tafad'i,
Lallai kudinsa ta maida masa,
Advertisement
Afili ya furta wannan wace irin yarinyace haka marar yarda,
Yaga alamunta sam batada yarda da mutane,
Saboda ya lurada yanda take wani kaffa-kaffa idan ya'isa wajan,
Iya wanda zai iya yaci yabar sauran da zai fita sallar isha'i ya fitawa qannensa dashi,
Bayan yadawo mummyy tadubeshi tana fad'in wato yauma ka sake siyan abunnan koh?
Kafin yayi magana hassana ta kar6e zancen da fadin mummy Allah da dadi,
Kawai dan bakici bane,
Komai dadinsa bazanci wannna abun kazantarba mummy tafad'i,
Sannan ta kauda zancen tana fadin
Kowa ya isa wajan dinning ta bada umarni sadam yanjin cikinsa ya qoshi dam amma kuma idan yace ya koshi hakan zaiyi sanadinda zaisa mummy tanashi cin awara gabaki d'aya,
Haka yazauna badan yasoba yaci kadan yatashi,
Yayi musu sallama yashiga ya kwanta,
Sawwama anata wajan kuwa, tanajinta sakayau saboda ta sauke nauyin dayake kanta,
Sai kuma wani farin cikinta batasan dalilinsaba,
Toh shima dai wajan sadam hakanne saboda kawai saiya tsinci kansa yana murmushi jifa-jifa,
Wanda idan zaka tambayeshi dalilin yin murmushin bazai iya fad'i ba."
Ahaka dai har bacci ya daukeshi,
Washe gari ma da sassafe yafice zuwa school,
Ya dawo daga school da wuri amma haka baibu wajan sawwmaba,
Shi kadai yasan dalilinsa naqin zuwa wajan, amma bawai dan baison zuwaba,
Can qasan ransa yanason zuwa amma haka ya danne."
Sawwama haka kawai ta tsinci kanta da zuba idon ganinsa duk da cewa jiya tace koda bai zoba batada damuwa amma kuma sai gashita damun."
Saida akayi kusan 2days kafinnan yasake dawowa,
Kamshin turaren da sawwama taji ya sanya gabanta faduwa kamshin kadai ya isa ya sanar matada zuwansa,
Tana juyawa kuwa caraf suka hada ido yana tsaye gefe jikin machine dinsa ya harde qafafunsa yana kallonta,
Gabantane yaqara faduwa tayi saurin juyawa jikinta har yana rawa ta sallami wanda suke gabanta,
Advertisement
Sanda yaga tagama da kowa sannan ya qaraso izuwa gabanta, 6ata rai yayi ya tsugunna gabanta hakan yasata dabur bucewa tarasa mai zatace, a ahankali ta furta sannu, bai amsaba saima jefo mata tambaya
Dayayi,
Menene dalilin dayasa kika zuba abunda yafi qarfin na kudinda nabaki jiya? Ya tambaya yana kallon fuskarta yana mai son gano wani abun,
Shiru tayi hakan yasa ya tsareta da ido yana jiran amsar
Kame-kame tatsayayi tarasa mai zata fada masa,
Uhm— tafara fad'i tarasa mai zata bada amsa,
Zuwan wani yaro siyan awarane ya katseta dasauri ta juya izuwa yaron jikinta yana rawa ta zuba masa,
Binta yayi da kallo yana kallon yanda jikinta yake rawa,
Dariyane taso kamashi ganin yanda duk ta duburbuce amma sai ya matse dariyarsa,
Sanda tagama da yaron sannan ta dubeshi ta kauda ido,
Tasake sunkuida kanta qasa,
Ehem ina sauraronki muryarsa ta katseta,
Huuuuuu ta fidda iska a hankali, sannan ta kauda kanta gefe,
Langa6arda kansa yyi gefen fuskarta yana kallonta,
Murtuqe rai yayi yaqarayi yana fadin in jinki?
Na kudinka na zuba maka tafad'a a tsorace,
Wni kudi? Ya tambaya kamar wanda baisan mai take nufi ba,
Wanda kabari ranar tabashi amsa,
Banace nabaki ba? Ya qara jefo mata tambaya,
Girgizaka kai tayi sannan tace ni bazan kar6i kudinkaba,
Saboda fitowa sana'a nayi ba roqoba,
Aiba ke kika roqeni ba ni nayi niyyar baki,
Maganansa sun fara yawa hakan yasa hawaye yafara zarya akan idanuwanta,
Ganin haka yasanyashi fara girgiza kai yana fadin,
Subhanallahi Please ni kinga bance kiyimun kukaba kiyi shiru na bari bazan qaraba,
Shiru tayi ta share hawayenta, shikuma yamiqe ya danja nunfashi sannan yawwa sai anjima yafad'i,
Harya juya zai tafi tace uhmm juyowa yayi ganin tana neman sunansa yasa yace sadam,
Jijjiga kai tayi sannan ta miqa masa leda,
Bai kar6i ledanba yatsaya kallonta,
Ahankali ya furta keda kika fito sana'a nabaki baki kar6a6a sai nine kike tunanin zan kar6a abunki??
Shiru tayi batace komaiba bai qara tankawa ba yawuce yahau machine yatashi,
Maida numfashi sawwma tayi cikin ranta tana fad'in toshi wannan wani irin mutum ne?
Nisawa tayi ta maida ledan,
Amma duk sai taji wani iri dabai kar6a6a,
Washe gari sadam yadawo koda yazo bai siyaba kuma data bashi bai kar6aba kawai ya kada kan machine dinsa yayi gaba,
Wasa gaske kullum sadam sai yabi wajan watarana yasiya wata rana kuma kawai saiya tsaya ya kalleta batareda sunyi maganaba ya kada kan machine dinsa ya wuce,
Wannan abunda yakeyi ya zama masa jiki wanda shi kansa idan zaka tambayeshi dalilin dayasa yakeyin hakan bai saniba,
Akwai wata rana daya tsallake baijeba saboda sun fara test amakaranta aranar bacci 6arawone kawai ya saceshi,
Sai yake ganin daren yayi masa nisa,
Sawwma kuwa ta rigada tasaba ganinsa ko basuyi maganaba zata hangeshi a can nesa hakan yasa itama ranar da bata ganshiba tadamu sosai,
Haka tayita juyi akan yar yololuwar katifarta,
Kafinnan daga bisani bacci yadauketa,
Wasa gaske sabo mai karfi yashiga tsakaninsu duk da kasancewar ba wani magana ke shiga tsakaninsu ba."
✔️ote
Comment
Share
Follow
To be continued
Zaynab Alabura
Advertisement
-
In Serial10 Chapters
Local Minima
[Entry for the June Royal Road Community Magazine Contest] A prisoner named Gemmei is gifted a chance to put her life on a better track after being transferred to the Hibiya Correctional Complex, a lower security prison allegedly intended for less violent offenders. However even though the walls keeping her in are no longer visible, plenty of barriers are in the way that prevent Gemmei from returning to the world she once took for granted. Chief among them is the Houzou Hakkyou, a special tattoo every prisoner in the system receives that alters how they can think and feel through forced sedation. The curse the Hakkyou enforces ensures compliance and docility among the inmates, but as Gemmei finds out, cruelty is born from more than emotion alone.
8 82 -
In Serial46 Chapters
Smoke and Murders
Ilden grows colder with each passing year, as smoke and smog cool the city, but no one cares about that, it is just the way things are.Three people, a teacher, a company's heir and a low life, who should have never met become entangled in each other's lives, have no choice but to work together, for change various “way things are”.Alhough, it may not even matter, at this point.__________________This work may feature very strong language and potentially triggering content as mild as it may start. A simmering slow burn is my intentions with this so be forwarned. I would provide a warning in advance in the chapters themselves. Contains art work every chapter all done by me which includes the cover amoung other art pieces
8 132 -
In Serial8 Chapters
Revenge By Name
Humans share spirits with Deity's of the world, your spirit pre-destined by your ancestry, your surname represents your spirit. Your place in the world determined by your spirit. Everyone fights to claim the world throne. The position only available to the strongest of Humans. Redo believes to be an unlucky case, as his surname is only "Name". Abused and neglected he is told his surname is a placeholder for having no spirit. His abusers, his classmates and family. He believes the world has it out for him, his school won't support him. he's considering ending it all, he stands atop a bridge. When a little voice whispers in his ear he'll get his revenge. Until one fateful day, they push Redo a little too far, making a break for it his bullies landing what they believe to be the fatal blow, he accepts his fate. But instead of death he meets a familiar face.
8 125 -
In Serial17 Chapters
That is true? Sorry, now it's false.
Prologue in the chapter Reincarnation Op System
8 114 -
In Serial20 Chapters
r a i n y d a y s >>> greys anatomy
"you don't hate me?" "no, i don't."•nobody knows where they might end up, not even madelyn grey. • started 04/30/18status: discontinued. <>@mschubert 2018
8 178 -
In Serial13 Chapters
Girls Like Me (BENNY RODRIGUEZ)
Eliza has been living in the Valley for two years now. She has two best friends . Eliza has always been like the duff of her two friends. Lola and Sabrina. She has always had a crush on Benny Rodriguez.what happens Lola befriend the sandlot boys .What happens when girls like her don't get the guy.
8 153
